Showing 66001 words to 69000 words out of 191031 words

Chapter 23 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67969

matan ne ke zuwa maka da wani abu da bai maka na? Ko kuma kai ne kake jin wani abu a game dasu?"

A hankali ya 茩ara girgiza mata kai, burinshi a yanzun bai wuce kawai ya ga ya bar 茩asar nan ba da yake jin ta masa 茩unci, shafa bayanshi ta fara yi ta sake cewa" *Auren ne ba ka so*?"

A hankali ya 蓷aga kanshi ya kalleta, hannaye biyu yasa ya cire rawanin da gaba蓷aya hular da ke kanshi, cike da tausayin kanshi yace" Ummi ina so, ina so na yi aure nima, na samu wacce zan kira da *iyalina*, idan ina cikin damuwa na fa蓷a mata ta rarrasheni, idan ina farin ciki na sanar mata muyi tare, Ummi ina so na haifi 拼a拼an da zasu kirani da Abi, su kira *matata* da Ummi, sannan su kiraki Maami, amma..."

Sai kuma ya 茩ara wara idanunshi a kan fuskarta ya ri茩o hannayenta yace" Ummi ki ce na tafi, Ummi ba zan iya awa 蓷aya a garin nan ba, na ro茩eki Ummi ki ceci rayuwata."

Jin kamar zai fashe mata da kuka yasa ta lumshe idanu a sanyaye ta furta" Ka sha furar sannan."

Marairaicewa yayi kamar zai yi kuka ya girgiza mata kai, tsurawa juna idanu sukayi tana kallonshi da tausayi tace" Babana, kai a ranka me kake ji game da mace? Ranka yana 蓳acewa ne idan ka ga mata?"

A firgice ya kalleta da tsoro da kuma mamakin furucinta, da sauri ya girgiza mata kai yace" A'a Ummi, Ummi ba wai ina 茩in mata bane, hasalima dan kare kaina daga fa蓷awa halaka na za蓳i yin azumi duk kwana 蓷aya, Ummi ni ka蓷ai na san me nake ji, dan Allah ki barni na tafi."

Kukan da take ri茩ewa ne ya taho mata, hakan yasa ta fa蓷a jikinshi tana kuka, bayanta ya shiga shafawa shi ma kamar zai yi kukan sai dai dakakkiyar zuciya ta hana, jin ana 茩ara ingizashi ya bar 茩asar yasa shi saurin jayeta daga jikinshi ya mi茩e, kallonta kawai yayi yace "Ummi na tafi, ki min addu'a a duk inda na ke."

Juyawa yayi a sukwane zai bar falon, da 蓷an 茩arfi tace "Babana..." Sai dai bai tsaya ba dan ba yin kanshi bane, barin masarautar nan ne ka蓷ai mudi'inshi a lokacin, dan haka kai tsaye 蓷akinshi ya koma ya ha蓷a abinda zai ha蓷a kawai ya fito dreba ya jashi zuwa filin jirgi.


*Yana* fita 茩anenshi da shi ma na蓷in ne ya dawo dashi daga makarantar Say dake babban birni Niamey yana karatu kan shari'ar addini ya shigo, ganin mahaifiyarsu na kuka ya dinga rarrashinta, cikin kuka tace "Akwai abinda ke faruwa sa shi, tabbas akwai abinda Babana yake 蓳oye min."

Ajiyar zuciya yarima *Abdul Karim* ya sauke yana ci gaba da shafa bayanta yace "Hakane Ummi, nima na fahimci haka, mu masa addu'a kawai."

Shigowar sarauniyoyi biyu yasa suka kimtsa kansu dan kar a fahimci damuwarsu, musamman da sarauniya Ramlat ta fahimci kamar shiga gaban 蓷anta aka yi, zazzaune sukayi kowace da hadimarta kafin su basu wuri, cike da jimami uwar gidan tsaka da amarya suka jajanta mata kan abinda ya faru, amma sam ta 茩i fa蓷a musu ai ya ma bar garin yanzu haka, kawai tana so ta san me ke faruwa da 蓷anta kafin kowa ya farga.




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:49 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_25_




Har 11:00 na dare Ardiya na tare da Gaishata suna tattauna batu akan auren nan, daga 茩arshe ne dai Gaishata tayi 茩o茩arin fito ma Ardiya a mutum ta hanyar fa蓷in "Kinga 茩awata, ni fa sai dai kiyi ha茩uri, amma gaskiya 拼ar nan taki sai na koya mata hankali, wallahi na tsani yarinyar nan har zuciyata."

Da ma蓷aukakin mamaki Ardiya tace "瞥ata kuma? Wace 拼ar ta wa? Me ta miki?"

Dan fahimtar da ita tace "Ba fa cikin 拼a拼anki ba, Saleema nake nufi."

Wata ajiyar zuciya Ardiya ta sauke tace "Ohhh! Wannan? Hmmmm! Me ta miki ita kuma?"

Cike da balbalin bala'i tace "Alhaji ne fa ya ce ita ta bashi shawarar ya aura wa Mu'awwaz 茩azamar yarinyar can, ita ta zugashi har ya ha蓷a 蓷ana da kucakar can, wallahi ba zai yiwu ba, sai ta gane kurenta."

Da wani sabon mamakin ta sake kallonta tace "Ita ce? Ta ya ya? Shi ma dai Alhajin kamar wani..."

Sai kuma tayi shiru tuna maganar ba lallai ta ma Gaishata da蓷i ba, Gaishata data fahimta jinjina kai tayi tace "Ai ni da fari zarginshi ma nake cewa yana son yarinyar, maganar aurenta da aka fara da Mu'az ne yasa na janye zargina."

Zaro idanu Ardiya tayi dan bata san da maganar ba sam, duk da ta ga 拼an kwanakin nan yana yawan zuwa gidan, amma bata kawo komai ba saboda Hadeeya ta fa蓷a mata yace yana sonta, ba tare da mamaki ya bar fuskarta ba tace" Mu'az kuma? Yaushe suka fara soyayya da Saleema? Ta ya duk ban san haka ba?"

Cike da tabbaci Gaishata tace" 茦warai, ta ha蓷a 蓷ana da 拼ar aiki 茩azama, ita kuma za ta shigo gidan nan a matsayin suruka, ta fito daga daula ta shigo wata daular, ba zai yiwu ba, in dai ina raye wallahi ko zanyi yawo tsirara sai yarinyar nan ta 蓷an蓷ana ku蓷arta, Mu'awwaz tanadi na masa da shi kanshi bai san burina a kan shi ba, kawai rana 蓷aya ta wargaza min komai, gashi Alhaji ya gindaya sharu蓷a masu tsauri, wanda idan na ce na dage to tass zai sakeni sannan ya tsinewa Mu'awwaz, duk a kanta ita 蓷aya? Ba zai yiwu ba."

Ardiya sa ta ji zuciyarta na tafasa na wai Saleema za ta auri Mu'az, to yaushe ma aka tsara haka ba tare da ta sani ba, 拼arta kuma da ta ce ya ce yana sonta? Ta san dai Hadeeya ba za ta mata 茩arya akan wannan maganar ba, kenn yanzu rashin matsayin na ta har ta kai a fara tattauna lamari irin wannan Alhaji Yusuf ya kasa sanar mata? Lallai da ita suke magana.

A sanyaye ta kalli Gaishata dake ta cika tana batsewa tace "To yanzu ke me zaki mata? An riga da an 蓷aura fa, ki barshi ya wuce kawai."

Girgiza kai tayi a hassale tace "Na fa蓷a miki ba zai yiwu ba, ita ba nan za ta shigo cikin farin ciki, tana murnar ta samu ha蓷a蓷蓷e kamar Mu'az, to dole ita ma ta tasashi ko tana so ko bata so."

Da mamaki tace "Ban gane ba?"

Rai 蓳ace tace "Wai ke ba kya ganewa ne? Ba zan bari auren ya faru ba bare har ta shigo gidan, kuma wacce ta yi sanadiyar shigowar ta ta gidan nan sai na fitar da ita."

Wani shu'umin murmushi Ardiya tayi daya fito da ha茩oran makkarta guda biyu cike da siga ta makirci tace" Ke yanzu kika fara da ita, ni kuma da uwarta nake kishi, abu ne da ba zan yarda ya ta蓳a faruwa, 拼a拼ana mata uku ban aurar da ko 蓷aya ba, a ce Saleema ta fara aure kuma da namiji kamar Mu'az, tana da茩i茩iya wawuya a ce ta samu namijin da ya kereta a komai."

Sassauta 蓳acin ranta ta fara yi ta kalleta sosai tace" Hakan na nufin za ki taimaka min kenan?"


Jinjina mata kai tayi sosai tace" *茦warai kuwa, ke burinki dakatar da aurenta da Mu'az, ni kuma burina akan Saleema, hanata auren duk wani wanda zai iya zama gata a gareta.*"

Yanzu kam mamaki ne ya bayyana a fuskar Gaishata tace" Ban gane ba? Gata kamar ya?"

Ba tare data ha蓷iyi murmushin muguntarta ba tace" Nufina shine, duk wani namiji da zai iya zama wayayye, mai zurfin ilimi na boko, sannan 蓷an manyan gida, bugu da 茩ari wanda yana ri茩e da babban aiki na gwamnati ko kuma 拼a拼an banki."

Jinjina kai Gaishata tayi tana murmushi tace" Amma ta ya zakiyi haka bayan ba ke ce ubanta ba?"

Murmushi tayi tace" Ki zuba idanu ki gani, ba mahaifiyarta na tun茩aho tana rayuwa a gidan mijinmu ba duk da bata da ilimi kamar ni? Ba boka ba malam zan ruguza rayuwarsu ba tare da sun ankara ba, ilimina ne zai anfaneni a karo na ba adadi."

Ha蓷e fuska tayi sosai ta kalli 茩asa cikin jin haushi tace" Har ni zai fara wula茩antawa saboda wata banzar nasara da Saleema ta yi, har yake fa蓷a min ka蓷an ya rage ya fara ciyar damu da arzi茩nta, hmmmm! Zan gani."

Kiran da ya shigo wayar Ardiya ne yasa ta kallon wayar dake kan gado, saida ta ta蓳e baki tace" Ka tuna bana gidan kenan?"

茦wafa tayi sannan ta 蓷auka, a ta茩aice daga 蓳angarenshi yace" Kina ina?"

A yatsine tace" Ina inda ka kawoni mana."

A dake yace" Ki fito gani 茩ofar gidan." 茦it! Ya kashe kiran ita kuma ta aje wayar ta mi茩e tana fa蓷in" Kinga wani sabon rashin mutumci kuma, sai da ya zo sannan ya kirani."

Da haka sukayi sallama ta fita da ba wa juna tabbacin zasuyi waya da safe. Haka suka rabu kowace zuciyarta fes na samun matallafi akan burinshi, wani 蓳angare kuma 茩una ce ta 蓷aukar fansa akan bayin Allahn da ko tunaninsu ba sa yi bare su cutar da su.


_Zan iya cewa yanzu ne za mu fara wasar, *BAIWATA* ba wai iya baiwar Saleema ta 蓷inki bane kawai yake magana a kai, akwai wasu 蓳oyayyin baiwar ma da sai kun bini a sannu za ku fahimci haka, maudi'unmu ba wai wa zai koya mata 蓷inki bane, *wanda zai tallafa mata* wajen tsaya mata akan cikar burin na ta shine maudi'unmu, da ba dan haka ba ai za mu iya saka mahaifinta a matsayin tela wanda zai koya mata, amma anan burinmu shine fito da baiwar yaran da ake tauyewa ta hanyar hanasu nisawa wajen cimma burikan rayuwarsu, baiwar Saleema za ta fito ko babu *Huzeifa*, kamar yanda wanda suke ganin sai ta auri Mu'az ne burinta zai cika, ba haka abun yake ba a tunani, 茩iyayyar wasu ga Saleema ba za ta barta zaman lafiya da farin ciki a gidan dayawa daga cikin mazajen da suke sonta ba, ni kuma littafina ban tsarashi da tunanin rubuta gwagwarmayar rayuwar aurenta ba, zan iya saka. Hakan dan nisha蓷i amma ba gundarin labarin ba, maudi'ina shine ta ya Saleema za ta cika burinta? Sannan yaushe burin zai cika? Kuma waye zai taimaka mata wajen cikar burin? Sannan *me ce ce ha茩i茩anin BAIWAR SALEEMA*? Wannan shi ne._



*Da* mugun sauri ta juyo tana kallon 茩ofar, har ga Allah ta 蓷auka surukarta ce dan ita har yanzu a tsorace take da matar, ajiyar zuciya ta sauke ganin Mu'awwaz ne ya shigo, kakkare jikinta ta fara yi dan ta gaji da zaman, yanzu ma tashi ne tayi har ta cire zip 蓷in rigar da niyyar yin wanka. Tafiyarshi da yanayinshi take suka nuna mata ba lafiya yake ba, saidai ta fi ta'alla茩a hakan da maye, tsaye take bata gusa ba kuma bata daina kallonshi ba har ya zo daf da ita yana layi sai dai ba irin cancan ba, yadda yake matsota sosai yasa ta fara ja baya tana yatsina baki saboda warin sigarin daya daki hancinta.

Gaff! Ta dangane da jikin bango, amma sai ya sake matsawa yana 茩are mata kallo da jajayen idanunshi yana fa蓷in "Wato amaryata, hahahahaha! Wai ke ce Abbana ya aura min ko? Kuma na san farin ciki kike, to ni bana yi saboda bana sonki, kawai dai..."

Sai kuma ya ha蓷ata da bangon tare da 蓷ora hannunshi na hagu kan cikinta, sannu sannu ya 蓷aga rigar ya 蓷ora hannun kan fatar jikinta ya matsa cikinta, rufe idanu tayi tasa hannaye ta turashi tace" Mu'awwaz ka dawo hankalinka fa,."

Kallon fuskarta ya yi duk da ba wani bu蓷a idanun yake ba yace" Keee! Ni ne ma ban da hankalin? A gidan ubana fa kike, sai in miki rashin mutumci."

Sake turashi tayi dan ita warin nan neman sakata amai yake tana sake fa蓷in" Ka matsa daga gareni."

Har yayi baya sai kuma ya sake saurin matse mata wuri sosai har numfashinsu na gauraya, hannu ya sake kaiwa jikinta da yanayi na zafi-zafi yana son since zanen dake jikinta yana fa蓷in" Ke kin isa ki dinga tureni haka? Dama ba abinda kike so ba kenan har kika yarda kika aureni, to zan miki shi yanzun nan ki ji da蓷inkiiiii."

Bakinta da yake laluba yasa kaucewa a rikice tace" Mu'awwaz karka wula茩antani haka mana, dan Allah ka da ka keta min haddi alhalin kana cikin maye."

Wawan mari ya kashe fuskarta da shi tare da cewa" Zan kasheki kika sake min magana a nan, ke za ki fa蓷a min me zan yi ne? Rayuwata ce fa, ina ruwanki?"

Fashewa tayi da kuka saidai ba ta sake 茩o茩arin hanashi abinda yayi nufi ba, tana ji tana gani ya mata kaca-kaca a darensu na farko ba tare da bin ko wace irin 茩a'ida da ya kamata abi ba, daga gurin bai sake motsawa ba baccin masifa ya 蓷aukeshi, sai ita ce ta yi jinyar kanta dan lokacin da aka 蓷an samu rabon da wani abu ya shiga tsakaninsu da taimakon wata 茩awarta ta 蓷an kimtsa kanta, duk da ba wani gagarumin gyara bane, amma dai ta san jikinta ya kar蓳eshi daga abinda ya faru yanzun, dan ma birkitaccen ba a hankalce ya shigo mata ba.



_______________



Yau fa ko da suka tashi gidan da shirye shiryen shagalin murnar da Hadeeya ta shirya suka tashi, daga yadda suka fara kai da kawowa da kuma irin matan da suke taruwa a gidan da yadda ake iface-iface da shewa ya tabbatarwa Safiya kawai shiri ne na hassalata ko a 蓳ata mata rai tare da cin mutumcinta, dan kiyaye haka tunda ta shiga 蓷akinta yin sallah la'asar ba ta sake fitowa ba duba da a lokacin ne ma za'a fara taron. Kuma gaskiyarta ne dan kuwa da gayya Ardiya ta dinga gayyatar 茩awayenta da 拼an uwa wai dan Safiya ta gani ba irin taron da ita tayi ba sa'ilin saukar Saleema, ku蓷in da ya bata kuma a 茩alla saida ta zuba ninkinsu sau biyu wajen shagalin nan, dan kayan da take so Hadeeya ta saka kawai sai da ta bayar da 蓷inkinsu ga ma蓷inkiyar da ko baka kai mata 蓷inki aka ambaci sunanta za ka santa, musamman saboda shagalin nan saida ta 蓷an ci bashin bankin da take a aiki, a ganinga za ta biya nan kusa kuma a aljihun Abbansu Hadeeya ku蓷in za su fito.

Saleema ma dai duk da ba ta yi wani tunani game da taron ba, amma dai ta san 拼ar uwarta ce ke shagali, tunda ta fito da niyyar kama musu aiki suka canza harshe daha hausa zuwa french da buzanci, sai kawai ta ji ta tsargu ta komawarta 蓷akin Mamanta ta yi zamanta. Saida ta yi sallah la'asar ta sake 蓷aukar wayarta dan yanzu ne take 茩ara fahimtar wayar sai kuma Mamanta tace "Ki shirya ki fita kema, kar a ce ha蓷in bakine daga ni har ke babu wanda ya fita, yanzu za'a ce ba茩in ciki muke."

Ba ta musa mata ba illa "To Mama." Da ta fa蓷a ta aje wayar ta shiga ban蓷aki, shirin na ta ba wani dogon lokaci ya 蓷auka ba, dan kuwa bayan mai da ta shafa sai turare, ko hoda ba ta shafa a fuskarta ba sai kwalli da ya zama sabo a gareta tun tana 茩arama, doguwar rigar shadda ce ta saka kalar ruwan zuma mai 茩yalli, 蓷aurin zara buhari ta yi sai takalminta masu tudu da ta saka, sar茩ar da Gwamna Naseer ya sako mata a cikin kyautar nan ta ma茩ala mai shegen tsada duk da ba wani 蓷aukan hankali gareta ba, ba ta 蓷auki hijabi ba duba da a cikin gidansu take, kuma ko addini bai tilasta saka hijabi a cikin gida ba, hasalima wata mazhabar na gani indai a cikin gidane ko babu 蓷an kwali ba laifi bane indai ba waje ta fita ba, a nan ne mala'iku za su tsinewa kan da yake bu蓷e.

Tana fita jikinta yayi sanyi ta tsaya daga nesa tana hangen mutanen dake zaune can kusa da 茩ofar shiga 蓳angaren mahaifinsu, wurin ya 茩ayatu sosai da kujeru da hotunan Hadeeya kala kala wanda bbabu 蓷aya inda kanta ke rufe, ga flawowi da suma suka 茩ara fito da kyawun wurin. Kujerar da ta gani ta musamman wacce ta saka wani teburin glas tsakiya da aka sha茩eshi da tsadaddin lemuka da ruwan gora ha蓷e da chacolate da su alawa da biscuit, abun ya yi kyau sosai.

Ba komai ya kayar mata da gaba ba sai yadda 茩awayen na Hadeeya da suka fara halarta ta ga kowace ta 茩ure kwalliyarta yadda ka san gasar za蓳en sarauniyar kyau za su je, 蓷inki iya 蓷inki, kwalliya iya kwalliya, shiri na musamman da ya fito da surar kowace, ajiyar zuciya kawai ta sauke ta 蓷ora hannayenta kan gajeruwar kagantar da ta mata shamaki da su ta tallabe ha蓳arta kawai tana ci gaba da kallon 蓷inkin jikin kowace, ba wai dan sun birgeta ba, a'a sai dan ji ina ma a ce dayawa daga cikin 蓷inkunan ita tayi su?


*茦ara* kallon fuskar Hadeeya ta yi ganin yanda 拼arta ta fito ka rantse balarabiya ce ko ba'india, a gaskiya dole ma 拼arta ta auri babban 茩waro, irin wannan kyau haka da tsaruwa? Murmushi ta saki tare da mi茩awa mai kwalliyar da ta gama ha蓷a kayanta za ta tafi wacce suka yi babbar sa'a ta biyo gidansu ta mata kwalliya saboda ta riga ta fito yin kwalliyar kenan, ba dan haka ba sai dai su sameta har in da take, kar蓳ar ku蓷in tayi ta musu godiya su ma suka mata godiya ta fita.

Hadeeya dake tsaye gaban madubi wayar da a yanzun take tutiya da ita ke ri茩e da ita ta kara a kunnenta fuskarta 蓷auke da damuwa, duk da idanunta suna hango mata tsantsar kyawun da ta yi, irin 蓷aurin kallabin da aka kashe mata abun ya matu茩ar birgeta, ga doguwar rigar dake jikinta ta wani tsadadden cotton boil, irin 蓷inkin da aka mishi ya bi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login