Showing 27001 words to 30000 words out of 191031 words

Chapter 10 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67966

ma ta gyara fuskarta tace" Muje na rakaki."

Jinjina kai tayi ta bu蓷a wata drower ta 蓷auki magunan sannan suka fita a madafar tare. Yanda su ka barsu nan suka same su, sai dai su Hadeeya sun fito daga 蓷akin suna zaune kan kujera, ganin Hameeda da Hamdeeya sun sa Mu'awwaz tsakiya duk sun shige jikinshi suna kallo abu a waya, kuma kowa na kallonsu ba mai tunanin komai, ga amarya da hakan ma ya mata da蓷i a ganinta suna fahimtar junansu kenan.

A sukwane Saleema ta yi kansu, ta na zuwa duka hannayensu ta kamo ta jawosu da 茩arfi ta watsar a gefe, hakan ya sa Hamdeeya fashewa da kuka ta tashi da gudu ta nufi Hajia Rabi, rai 蓳ace Saleema ta nunawa Hameeda yatsa tace "Ki yi nesa da shi, idan ba haka ba ranki zai 蓳ace."

Mi茩ewa Hameeda ta yi za ta yi magana sai kuma cikin hargagi Saleema tace "Wannan zaman 蓷a'a ne da kunya? Ki na mace kadarar da ta fi kowace kadara daraja ne za ki wani shige jikin wanda ba ki san halinsa ba, to ki kiyaye."

Wani dogon tsaki ta ja tare da wurgawa Mu'awwaz da ke kallonta baki sake harara sannan ta fice ko ta kan iyayen ba ta bi ba, wani salihin murmushi Mu'az ya saki tare da 蓷an girgiza kan shi ya mi茩e ya koma 蓷akinshi dan 茩arasa shiryawa ya fuce aikin shi.

Amarya kuma da abun ya 茩ona mata rai fiye da kima mi茩ewa ta yi ita ma ta kalli Mu'awwaz tace "Biyoni 蓷akina."

Jiki a mace ya mi茩e ya bi bayanta inda sauran suka bisu da kallo, ajiyar zuciya Alhaji Auwal ya sauke yana tunanin lamarin yarinyar nan da zuciyarshi ke neman raya mi shi ko dai *waliyiya* ce.

Suna shiga 蓷akin cikin 蓳acin rai ta kalleshi tace "Kai, kana son Hameeda ne?".

Mamaki tambayarta ta bashi sosai, sai ya 蓷auke kai cike da rashin ba wa abun mahimmanci ya zauna bakin gadonta yace "Wane irin so kuma?"

A hargitse tace "So dai so, so wanda ka sani."

Ta蓳e baki yayi yace "Ban ta蓳a jin haka ba, wata茩ila ko nan gaba."

Mi茩ewa ya yi zai bar 蓷akin tace "Dan ubanka magana na ke magana."

Tsayawa ya yi ya kalleta yace "Ina jinki."

Kallonshi tayi sosai ba tarz da damuwa da yanda ya ce kna jinki ba 蓷in kamar wata 茩awarshi tace "Idan na sama maka aurenta za ka amince?"

Tsura mata ido ya yi yana mata kallon nan na nesa yace "Wai me ye matsalar? Auren me kuma ina zamana a haka? Shekarata nawa ne duka da za ki wani ce ki min aure?"

Da sauri ta matso ganin kamar ta na hassalashi ta dafa kafa蓷arshi cikin rarrashi tace "Haba yarona, kai ba ka ga Hameeda kyakyawa da ita ba, ga ta da wayewa da ilimi, ga sura mai kyau da iya kwalliya ga hasken fata kamar dai kai 蓷in."

Kashe masa ido 蓷aya tayi tace "Haba dai na wa, ka duba da kyau ka gani mana."

Shiru ya mata ya na sauke numfashi tare da tunanin abin da ta fa蓷a, samun kansa ya yi da murmushi sanda she蓷an ya raya masa "Hameeda ai kamar tuffa ce, ka yarda ka aureta ko dan ka yi ta gatsar abar ka duk sanda ka so."

Wata sahihiyar dariya ya saki ya kalli amarya yace "Shikenan to na amince."

Ya fa蓷i hakane dan auren Hameeda ba shi zai hanashi gudanar da rayuwarshi yanda ya so ba, wani irin da蓷i ne ya kasheta da fara'a tace "Yawwa 蓷an mamanshi, je ka yanzu bari na kira mahaifiyarta na fa蓷a mata."

Juyawa ya yi ya fice ta bishi da kallo musamman ma 茩ugunshi dake 蓷auke da sa蓳ulallen wando irin na gayu. 茒aukar wayar tayi ta dannawa Ardiya kira dan ta ji yanda za su 茩arke.

*Wajen* Saleema kuma ganin sun zagaya ta inda jiya ta kama Nafissa da Mu'awwaz yasa ta fa蓷in "Wai a cikin gidan yake dama?"

"E, nan baya 蓷akinsu ya ke." Da mamaki ta sake kallonta sai kuma ta maida hankalinta kan 茩ofar da Nafissa ta tura suka shiga ciki, mangaza (store) ne na ajiyar kayan abinci da sauran abun bu茩ata, kallo ta dinga yi har suka ratsa kayan Nafissa ta bubbuga wata 茩ofa, daga ciki ta ji muryar dattijo da za ta iya kira da tsoho aka ce "Shigo."

Tura 茩ofar Nafissa ta yi ta shiga da sallama, Saleema da al'ajabi da kuma tunani suka mamayeta a lokacin a 茩asan ma茩oshi ta furta "Assalama alaikum."

Tun daga bakin 茩ofa ta ke kallon 蓷akin, ba wani datti a 蓷akin dan aikin Nafissa ne kula da 蓷aki, sai dai yanayin da ta ga tsohon, bayan ga manyanci ga rashin isassar lafiya, sai ya ba ta tausayi lokaci 蓷aya. 茦arasawa su ka yi Saleema ta tsuguna ta na kallon tsohon da ya rame sosai, maganin Nafissa ta bashi kamar yanda take bashi kullum, saida suka gama har za su fita Saleema ta kalli tsohon ta 蓷an ri茩e hannunshi tace "Baba, kana jin da蓷in zama a nan kai ka蓷ai kuwa? Sai na ga shiru ya yi yawa wurin."

Murmushi ya mata irin murmushin nan da ake ce ma na babba da yaro, girgiza kai ya yi alamar sam baya ji, amma kuma a bakinshi sai yace "Ina ji 拼ata."

Ita ma murmushin ta mishi, dan ko ya fita shekaru zai iya ninketa ta bai-bai, ta 蓷an karance-karance wanda ta hakan za ta iya fahimtar sigar kowane kallo indai ta lura da kyau, jinjina kai ita ma tayi alamar shikenan kawai sannan ta saki hannunshi suka fita a 蓷akin. Suna hanyarsu ta shiga ta kalli Nafissa tace "Ta ya za su bar tsohon nan a bayan gida? Bayan gidan ma a 蓷akin ajiye kayan abinci? Haba dan Allah."

Cike da jimami ta girgiza kai tace "Ko da na zo gidan nan a nan na same shi, kuma ni na ke bashi magani kullum."

Daf da 茩ofar shiga falon suka ha蓷e da shi, fa蓷uwar gabanta da kauce masa dan wuce a tare suka gudana, amma sai ya tsaya a hanyar bai da niyyar wucewa ko kauce musu, harara ta dalla masa ta juya da niyyar barin wurin gaba-蓷aya har ya tafi ta dawo, amma ta na juyawa ruff! Ya dam茩o hijabinta wanda hakan ya tilasta mata tsayawa ta juyo, takowa yayi ita ma ta shiga ja baya tana jan hijabinta da fa蓷in "Ka ga malam sake min hijabi."

Nafissa na ganin ya gusa a hanyar ta yi saurin shigewa ciki, ganin ya na biyota kuma ya 茩i sakin hijabin yasa ta nuna 蓳acin ranta sosai a fuska tace "Sake min hijabi na ce." Ta fa蓷a tana fizge hijabin, 茩wayar idonshi ta kalla ta nunashi da yatsarta manuniya da sigar garga蓷i da fushi tace "A rayuwata ban ta蓳a tsintar kaina a yanayi na fushi ba sai da na zo gidan nan, idan ka na son na ci gaba da girmamaka matsayinka na wanda ya fi ni shekaru, to ka kiyaye yi min watan-gaririya da mutumcina, dan kimata ba abar wasarka ba ce, idan kuma ka ci gaba to zan nuna mata abin da mahaifiyata ta ce na yi wa duk wanda ya kawo min wargi game da mutumcina... Ka fahimta?"

Kashedi ta ke masa! Garga蓷i mai lasisi ta ke buga masa! Amma wani farin ciki da da蓷i irin na bugawa a mujalla ya ke ziyartarshi a tsayen nan, tabbas ba kyakyawa ba ce kamar 拼an uwanta, amma rufaffen jikin nan da kamalar fuskarta, sun fi mi shi *lu'u lu'u* haske da she茩i. Tsintar kansa ya yi da sakin murmushi ya zuba hannayenshi a aljihun 蓷amammen wandonshi da ya dace da shi ya na ci gaba da kallonta, cikin sanyayyar muryar da bai san ya yi magana da ita ba yace "Na fa蓷a miki ina son ki, me ki ka ce?"

Wata harara ta wanka masa tace "Ni? Allah ya tsareni, me zan yi da kai?"

Murmushi ne ya su蓳uce masa tare da 蓷an sunkuyar da kan shi, yo in ba haukan yarinyar nan ba, shi ne za ta ce me za ta yi da shi? Ta dubeshi da kyau mana, ko 拼ar uwarta Hadeeya ba ta fishi jar fata ba duk da ta na mace, a haka ma dawowarsa 茩asar nan ne rana ta fara lalata masa fata, sannan ya na da ilimi da ku蓷i, to me take nema a jikin namiji? Da ba za ta samu a wurinsa ba.

Hijabin da ke jikinta ya nuna da yatsa yace "Me ya sa ba kya cire wannan abun ko dan ki huta?"

Murgu蓷a masa baki tayi tace "Saboda shi ne mutumcina."

Kallon tuhuma ya mata yace "Me ye mutumcin gaba-蓷aya?"

Cikin ido ta kalleshi tace "Shi ne kimata."

Ta蓳e baki yayi yace "Me ye ita kimar ke nufi?"

Numfashi ta feso ta 茩an茩ance ido tace "A wajena kimata ita ce madogarata."

Da mamaki na fasahar harshen yarinyar yace "Madogara? Me ye ita kuma?"

Ba tare da shayin komai ba tace "A茩idata."

Tsareta ya yi da ido kamar ba zai yi magana, dan abun da ya fahimta ba za ta rasa abun fa蓷a ba, sai kuma ya numfasa yace "Me a茩idarki ke nufi?"

"Addinina." Ta fa蓷a kamar dama jira take ya sauke maganar ita ta 蓷auka, da mamakin amsarta ta 茩arshe ya nunata daga sama har 茩asa yace "Idan na fahimce ki dai-dai kina so ki ce ke karan-kan ki ke ce addinin?"

Da sauri ta girgiza kai tace "A'a, ba ni ba ce, nufina a nan shi ne, duk wani da yake amsa sunan musulmi, to ya kamata q na ganinshi gaba-蓷ayansa a ga musulunci, a tattare da musulunci kuma akwai, imani da tauhidi."

Girgiza kai yayi yana murmushi yace "Maganarki nan fasa min kai take, na fahimci wasu kalaman na ki amma ban gane wasu ba."

Rumgume hannayenta tayi a 茩irji tace "Ka yi imani da Allah?"

Cike da tabbaci yace "Sosai ma, ko shirka ban ta蓳a kwatanta yi ba."

Kallon fuskarshi tayi da 蓷an jin ya birgeta ta wannan fannin sannan tace "Ka yi 茩o茩arin tsayawa a kan wannan sai蓷arar, dan laifin shirka shi ne laifin da Ubangiji ba ya gafartawa mai yi idan har ya mutu bai daina ba, sannan ranar 茩iyama idan har ba'a samu da-idai da 茩wayar zarra na shirka a aikin bawa ba, sannan aka samu sallarsa cikakkiya, to akwai yiwuwar ya zama 蓷aya daga cikin wa蓷anda Allah zai saka aljanna da rahamarsa ba tare da hisabi ba."

Wani kallo ya aikawa fuskarta mai cike da birgewa yace" Sallah..." Sai kuma ya sauke numfashi ya 蓷an sosa 茩eya yace" Zan yi 茩o茩arin tsayar da ita a kan lokacinta, babu sallan da ke kubce min, matsalata 蓷aya wasu lokuta sai lokacinta ya kusa fita ko ma ya fita na ke gabatar da ita."

Waro ido tayi tace" Subhanallah! Kasan kuwa illar da ke cikin yin hakan?"

Cike da rashin sanin babban abu ya ke aikatawa yace " Ai ina yi ba wai ba na yi bane, kawai dai..."

Dakatar da shi tayi da cewa"...




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:40 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_13_




Dakatar da shi ta yi da cewa "Hakan ai babbar matsala ce, in har da gangan ka ke bari sallar sai lokacinta ya wuce, to ya za ka ji idan aka ba ka tabbaci wannan sallar da ka yi ba a kan lokacinta ba Allah ba ya kar蓳a?"

茒an bu蓷a baki ya yi da yanayin mamakin nan sai kuma ya yi murmushi yace" Dan茩ari, da an samu matsala babba ai."

"Dan haka sai ka kiyaye." Jinjina mata kai yayi da fara'a yace "Zan kiyaye."

茒an murmushin ya茩e ta mishi ta ra蓳a za ta wuce, da kallo ya bita yace "Nagode."

Juyowa ta yi tace "Akan me fa?"

Da murmushi a fuskarshi yace "A kan komai ma."

茒aga girarenta tayi sama sannan ta yi shigewarta, sai da ya ga shigarta ka蓷ai ya kama gabanshi shi ma ya na jin yarinyar na 茩ara shiga gaba-蓷aya zuciyarsa, ruhinsa da ma gangar jikinsa.


______________



Bayan sun gaisa sosai a tsanake ta fara da "茦awata, dama wata shawara na ke so mu yi da ke, ban sani ba ko za ki yi amanna da abin da na zo miki da shi."

Duk da ba gabanta take ba amma fuskarta a sake tace "Haba 茩awata, ai tsakaninmu babu haka, ki fa蓷a ko ma menene ni na san zan amince, saboda ra'ayinmu na zuwa 蓷aya a mafi yawancin lokuta."

Numfasawa amarya tayi tace "Hakane, dama Mu'awwaz ne ya nuna sha'awarsa ta son auren Hameeda, shine na ce ya bari na fara tuntu蓳arki da maganar, dan na san burinki a kan yaran nan, ba yanzu ki ke so suyi aure ba har sai sun cimma wani matsayi na rayuwa, amma na ce ya bari yanda mukayi sai ya ji."

Wani da蓷i ne ya ziyarci Ardiya har saida ta dafe 茩irjinta ta waina ido tamkar ta na gaban mijinta cike da farin ciki tace" Haba 茩awata, wannan abun arziki har sai kin nemi shawarata? Kai tsaye fa kina iya turowa a nema masa aurenta, ai Mu'awwaz 蓷ana ne kamar yanda Hameeda ta ke 拼arki, duk so na burina kuma in dai a kan ki ne ai zan iya ruguje shi, sannan fa karki manta Mu'awwaz yana da ilimi sannan ya san mahimmancin boko da ribar da ke cikinta, ina da tabbacin ba zai hana Hameeda ci gaba da karatunta ba."

Da farin ciki amarya tace"Tabbas haka ya ke 茩awata, ai ko bai tsaya mata ba ni mai taimaka ma ta ce a kan karatunta har mu ga ta tsaya da 茩afafunta, kuma na ji da蓷i sosai, hakan na nufin zumuncinmu zai 蓷ore ta hanyar sake zama surukan juna."

Da haka sukayi al茩awarin sanar da mazajen na su idan suka dawo sukayi sallama kowace ranta fess tamkar an mata bushara da aljanna, domin kuwa burikansu ne za su cika ta hanyar ha蓷a auren nan na *茩warya* ta bi *茩warya*. Ardiya a ganinta nasararta ce kuma sa'ar 拼arta ce samun namiji kamar Mu'awwaz, matashi mai matasan shekaru, ga kazar-kazar da birgewa, ga shi kuma 蓷an babban gida, a ko ina Hameeda ba za ta ji kunyar nuna mijinta ba musamman a cikin 茩awaye.

Tana kwance kan doguwar kujera ta gama waya da Mamanta tana 蓷an wasa da wayar Nafissa ta fito daga madafa ta tsuguna gaban Hajia Rabi tace "Hajia na idar, ki kawo sa茩on."

Fuskarta ba yabo ba fallasa ta jawo 茩aramar jakarta a gefenta tace "Yawwa, har kin gama duka?"

"E." Ta fa蓷a a ladabce, ku蓷i Hajia ta fito da su ta bata tana fa蓷in "Yawwa gashi, kuma dan Allah ki yi sauri ki dawo, sannan ki shiga 蓷akina akwai rigata wacce aka kawo ranar da ta yi yawa a wuya, ki kai masa sai ya rage min ita."

"To Hajia." Ta fa蓷a tana mi茩ewa ta yi hanyar 蓷akin, jim ka蓷an ta fito hannunta ri茩e da leda, Saleema na ganin haka ta aje wayar ta tashi zaune tace "Mama zan iya zuwa tare da ita?"

Kallonta tayi ta kalli Saleema tace "Me ya sa za ki tafi tare da ita? Wajen mai 蓷inki ne za ta je."

Amariraice tace "Mama na gaji da zaman ne ni ka蓷ai, kuma ai na ga ba 茩asa za ta tafi ba."

Ba wai dan ranta ya so ba tace "Shikenan, tashi ku tafi, amma kar ku jima." Dan ita a ganinta 拼ar aiki ba tsararta ba ce da za su fita har su jera tare a gansu. Cike da zumu蓷i Saleema ta shiga 蓷akinsu ta 蓷an fesa turare sannan ta 蓷auki hijabinta kalar ruwan 茩asa mai hannayen roba da hula mai kallabi, tsaf ta 蓷aure abunta a baya inda a baya kuma har 茩asa ya ke ja idan ta na tafiya saboda tsayi, fitowa tayi ba tare da 蓳ata lokaci ba suka kama hanya dreba ya ja su zuwa shagon.


Ganin irin tafiyar da aka yi yasa Saleema kallon Nafissa tace "Wai yanzu tun daga can su Hajia ke kawo 蓷inki har nan?"

"E, ya yi nisa ne?" Nafissa ta fa蓷a tana kallonta, girgiza kai tayi tace "Gaskiya akwai nisa, wannan ya za su yi idan mai 蓷inkin ya sa蓳a musu al茩awari? Sai a yi ta kai da kawowa kenan?"

Dariya Nafissa ta yi tace "E to gaskiya sai na ce mi ki ba'a sa蓳a musu al茩awari, bai ta蓳a min 蓷inki ba bare na bayar da shaida, amma dai daga yanda Hajia babba da Hajia 茩arama suke sa ni zuwa kar蓳o musu 蓷inkinsu, ya tabbatar min da shi 蓷in mai al茩awari ne, dan ban ta蓳a zuwa ya ce bai ida ba, shiyasa ba na zuwa da fargabar abin da zan tarar."

Jinjina kai Saleema tayi ta 蓷an maida dubanta ga titi. Dammmm! Ta ji gabanta ya yanke ya fa蓷i, da sauri ta wara idonta a 茩ofar da tunanin ko wani abu ne ke faruwa a wajen, sai dai ba abin da ta gani kuma ba ta ga fuskar da ta sani ba, a hankali ta sulale ta jingina kanta a madubin 茩ofar ta na ci gaba da kallon hanya, a can 茩asan zuciyarta kuma a nutse ta ke jin gabanta na ci gaba da bugawa zuciyarta kuma na harbawa a tsanake. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe ido tare da furta "Hasbunallahu wani'imal wakil, La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntum mina zalumin!

Daga cikin kwana dreban ya faka motar suka fito saboda rashin sarari a inda shagon yake, hakan yasa suka 蓷an tako a 茩afa suka tsallako titi, daf da titi shagon yake ga kuma samari da ke zaune 茩ofar shagon da alama ma har da ma蓷inka, amma a haka kuma gida na kallon shago sai 茩aramin masallaci a gefen gidan, Nafissa ce ta kalli samarin da ke zaune tace "Sannunku."

"Yawwa Sannu." Suka amsa mata, 茩arasawa sukayi da sallama a bakunansu suka shiga ana amsa musu. 茒an tsayawa ta yi tana sake bu蓷a idonta dan tabbatarwa kanta abin da take gani, tabbas dai shine tunda gashi shima ya mata kallon sani duk da ya 蓷auke kanshi kamar wanda aka tsorata, dogon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login