Showing 147001 words to 150000 words out of 191031 words
goya marayu sarkin sarakuna sarki mai adalci, na san za'a 蓷auki mataki ko dan gaba."
Wanda ke kusa da sarki Abdus-samad a tsaye ne yace" Sarki ya ji kokenka Baba, ka share hawayenka ka samu adalcin mai adalci."
Bu蓷a idanunshi yayi da suka 蓷an canza launi, da yanayin 蓳acin rai sai dai a sanyaye sosai ya bu蓷a muryarshi yace" A garin nan? A gari mai cike da dattawa? Shine za'a samu wannan fitsarar?... "
Dakatawa yayi na sakwanni kafin ya ci gaba da cewa" Ba zamu lamunci wannan ba, ba za mu yarda 茩alilan su ja mana hushin ubangijinmu ba, dan haka saga yau sai yau, ba maganar ana biki a ko ina ne a garin nan da kewaye a aza mana ki蓷a..."
Numfashi ya sauke kafin ya kalli wazirinsa dake zaune da 蓷an-galadima yace" Na 蓷oara alhakin hakan akan wuyanku, yau ba sai gobe ba a sanar a gidajen redio cewa wannan 蓷in umarnina, idan har muka kama wani ya taka mana doka, to ya kuka da kanshi."
Liman dake zaune gefen damanshi ne yace" Allah ya taimakeka, Allah kara lafiya da nisan kwana, wannan shine daidai, dan lamarin nan yayi 茩azantar da ba za ka so ganinta da idanuna ba, wasu shekaru da suka wuce fa wata wa茩a aka zo da ita, haka za ka ga idan ana bugata mata na cire zanin jikinsu suna musaya a tsakaninsu, wasu fa har wuntsilawa suke tamkar suna kan katifar iyayensu."
Kallon liman 蓷in yayi a kausashe yace" A garin nan?" Sai kuma ya kalli 蓷an-galadima yace" Kana ina ake irin haka? Na 蓷auka kai ka dinga kula da harkokin da suka shafi masarauta tun bayan rasuwar mai martaba."
Sunkuyar da kanshi yayi yana hararen liman ta 茩asan idanu yace" Allah ya huci zuciyar sarkin sarakuna, Allah ja zamaninka lamarin..."
茒aga masa hannu yayi yace" Dakata, a 蓷auki mataki akan lamarin, kuma kar ku 蓷auka ya wuce daga yanzu..."
茦ara sautin muryarshi yayi yace" Zan bibiyi komai da kaina a lokacin da babu wanda yayi tsammani."
Dogarin dake tsaye bayanshi ya ma alama ya matso kusanshi sosai ya rusuna, a tausashe yace" Duk wanda aka kama a gabatar min da shi, ni zan masa hukunci da kaina."
Kirari aka shiga masa tamkar ba wani sai shi tare da ci wa tsohon nan albassa ana masa godiya aka masa izinin fita, a daddafe ya fita daga fadar yana mai godiyarsa a ransa da ka 蓷auki matakin da ya dace.
*Cikin* gida kuma Saleema na gama aikin da ta saka kanta ta tattare kayan ta aje sannan ta kwashe 茩yallayen ta zubar, ta juya za ta shiga ban蓷akin kenan wayarta ta shiga ruri, dawowa tayi ta 蓷auka fuskarta 蓷auke da murmushi, a hankali ta zauna bakin gado kafin ta 蓷aga tayi shiru, gaba蓷aya shiru ya ratsa wurin har saida ya cira la蓳蓳ansa yace mata "Barka."
A nutse ta amsa da "Barka ranka shi da蓷e."
茒an gajeran tsaki yayi yace "Haba, a nan fa abinda ake ta kirana da shi kenan, a gidana ma sai a kirani haka?"
Da fara'a a fuskarta tace "To me zan ce? Kana so a ce na kiraka da wani sunan da ba wannan ba?"
A 茩asan ma茩oshi yace "Um, ina jira."
Sanyayyen numfashi ta sauke kafin tace "Zan fa蓷a a inda ya dace."
Ajiyar zuciya yayi har saida ta ji sautinta kafin yace "Ya jikinki?"
Saida ta sinne kanta 茩asa tace "Ba komai."
A nutse yace "Kin warke kenan?"
Da gatse tace "Kana tambayata ne dan ka sake famani anjima?"
Murmushi yayi mai sautin da yasa ta murmusawa ita ma yace "Kinga laifina ne? Sabon shiga ne ni, lamarin ne ke zautar dani."
Kya蓳e baki tayi tace "Nima haka, amma ni mutuwa nake akan wannan lamari naka."
瞥ar dariya yayi yace "Na fi kowa sanin haka, dan kuwa ni na fara bi ta hanyar, kuma har abada ni zan ci gaba da wucewa."
Da mamaki tace "Uhummm?" Cike da tabbaci yace "Um! Ko kina shakka?"
Girgiza kai tayi kamar tana gabanshi tace "Ba wannan ba, yanzu fa蓷amin me zaka ci anjima da rana?"
A sanyaye yace "Me yasa kike tambaya? Akwai mai dafawa ai."
A tsanake tace "Hakane, amma daga yanzu ni ce zan dinga dafa abinda za ka ci."
"Me yasa? Baki san duk wanda kika sa aiki a gidan nan ba zai yi?" Ya fa蓷a a tausashe, cike da tabbaci tace "Na sani, haka kawai nake sha'awa, bansan zan auri sarki ba, shiyasa nake da burin hidimtawa mijin da na aura, da ya zama kai kuma me zai sa na yi 茩asa a gwiwa saboda akwai hadimai? Kenan su zasu kwashe ladar?"
Girgiza kai tayi kamar tana gabanshi tace "Ban yarda ba gaskiya."
Murmushi yayi kamar tana gabanshi yace "Shikenan, na baki za蓳i yau, idan na ji kin iya girki sai na fara za蓳a da kaina."
Waro idanu tayi tace "Kai, na iya fa, a gida ma ni nake wa Abba."
Jinjina kai yayi yana lumshe idanu yace "Shikenan, zan tabbatar."
Numfasawa yayi yace "Zan iya sake kiranki anjima?"
Sadda kanta tayi tace "Yadda mai mara蓷awa ya so."
A yangance yace "Ki kula da kanki."
Asnyaye ita ma tace "Kai ma haka."
Da haka sukayi sallama ta aje wayar ta shiga ban蓷aki, tana fitowa hijabinta ta saka ta fito, tare da jakadiyarta suka shiga madafar inda ta samu Mariya har sun kama aikinsu, a nutse ta shiga gabatar da komai, su kansu saida suka dinga kallonta lokaci lokaci saboda aiki ne take mai wahala, amma a nutse take kai da kawonta cikin kwanciyar hankali tamkar bata son motsawa, duk da jakadiyarta na taimaka mata saida akayi sallah azahar suka kammala, tare da jakadiyar suka 蓷auki kwanukan suka nufi 蓳angarenshi, akan teburin dake falonshi na biyu suka jere kwanukan tare da jug 蓷in kwalba mai 蓷auke da sanyayan lemu, suna fita ta rufe 蓷akin ta shiga nata dan yin wanka.
*Alhamdulillah.*
26/06/2022 脿 22:53 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_48_
Sosai ya zuba mata idanu yana kallon takonta, yadda take karya 茩ugunta da Allah ya hore mata, da yadda 蓷inkin nan ya kam jikinta ya fito mata da komai, sai yanzu ne ma yake gama sanin da wa yake zaune, a kwana biyun nan ya dai shafa jikinta ne kawai a cikin siririn hasken da zai iya sa su gane junansu, amma bai ga ainihin zahirinta yadda take ba.
Shi fa yadda 茩ugunta ke ka蓷awa ne ya fi bashi sha'awa, dan haka ma da ya ga za ta tsaya kusanshi za ta zuba masa abincin yace "Mi茩o min remonte?"
Rufe kwanon tayi ta nufi inda remonte 蓷in suke ajiye, juyowa tayi tace "Wace a ciki?"
Lumshe idanu yayi yace "Kowace ma."
Da mamakin amsar da ya bata ta sake kallonshi, sai kuma ta 蓷auko gaba蓷aya har da ta ac ta kawo ta zube gabanshi, 蓷aga idanunshi yayi ya kalleta, kallon remonte 蓷in yayi ya 蓷auki ta tv yace "Mayar da sauran."
茒auka tayi ta mayar tana juyowa ta ga idanunshi akan kumkuminta, ba ta damu ba ta 茩araso ta shiga zuba masa abincin, dake flate 蓷in mai 蓷an fa蓷i ne, hakan yasa ta zuba gasassar kazar da ta ma jan gashi gefe 蓷aya sannan ta zuba dafadikar da tayi kalar yelow shar gwanin kyau tare da cabage 蓷in da ta dafashi a manyan yankanshi da karas, daga sama ka蓷an ta saka mishi ha蓷in mayonnaise da dankalin turawa da aka saka comcombre a ciki, sai 蓷an jus 蓷in moutarde da tarugu da kuma koren tatttasai duk da bata sakasu dayawa ba saboda bata sna shi 蓷in mai son yaji bane ko akasin haka.
Kallon abincin yayi yana murmushi yace "Ke kika dafa?"
Lemun comcombre da ya sha citta 蓷anya ta zuba masa tana fa蓷in "Na fa蓷a maka ai na iya girki."
Tura mishi tayi gabanshi sannan ta zauna tana jawo kujerarta ka蓷an ta yi tagumi tana kallonshi yana shirin fara cin abinci, lomar farko da bismillah ya kai bakinshi, irin shirun nan yayi yana so ya tantance me yake ji, jinjina kai yayi ya sake 蓷ebo loma ta biyu ya kai bakinshi, sannan ne ya kalleta ya kasheta mata ido 蓷aya yace "Zan baki kyautarki anjima."
Zaro idanu tayi tace "Ina fata dai ba sai mun shiga can 蓷akin ba?" Ta nuna 蓷akin baccinshi, tsura mata idanu yayi yace "Yanzu kuma *turakar tawa ce abar tsoro wajenki*?"
_馃槍Malam turakar nan muna dai shiga ne dan sauke ha茩茩i.馃槀_
Girgiza kai tayi tace "A'a ba haka nake nufi ba."
Ta蓳e baki yayi ya kalli gabanta da ba abinci yace "Ke fa?"
Girgiza kai tayi tace "Ka fara ci, nauyin mutane dayawa ne a kanka, ba ka rintsawa sai ka tabbatar da ka sauke, ba zai gagareni sauke ha茩茩in 茩osar da kai ba."
Ta 茩arashe tana sunkuyar da kanta, kamar darensu na farko hannu 蓷aya yasa ya jawo kujerar da take zaune a kai ta zo daf da shi, 蓷ebo abincin yayi a cokali ya nufi bakinta yana fa蓷in" Uhum! Nima kuma ba zan gagara sauke nawa ha茩茩in ba, ba zan yarda ki kwashe duka ladar ba."
A hankali ta bu蓷a bakinta cike da kunya ta kar蓳a, 茩ura mata idanu yayi tana cin abinci haka ya dinga bata tana kar蓳a har suka gama yasha lemon nan sosai, tashi yayi tsaye yana kallonta a sanyaye yace "Zan shiga ciki, za ki zo ne muyi bacci?"
Da sauri ta girgiza kai tace "A'a bana ji."
Langa蓳e kai yayi yace "To muje ki tayani."
Shiru tayi tana kallon 茩irjinshi dake daf da ita, jinjina kai tayi ta mi茩e tace "Tom." Kama hannunta yayi suka shiga 蓷akin, kan lafiyayyar sofar ya kwanta sannan ya jawota ta hau kanshi, kallonshi tayi tana kawar da kanta tace "Ba bacci za ka yi ba?"
Idonshi a rufe yace "Um." Kya蓳e baki tayi tace "To amma wannan ta mana ka蓷an."
Ba tare daya bu蓷a idanunshi ba yace "Um um!" 茒an muskutawa tayi saboda ita dai kwanciyar bai mata ba, a kanshi fa take 蓷aro-蓷aro kuma ya yi ram da kunkuminta, sake ri茩eta yayi gam a sanyaye yace "A haka nake son yin baccina."
Marairaicewa tayi tace "To amma za ka iya yin amai."
Bu蓷a idanu yayi ya kalleta da mamaki yace "Me yasa?"
Cikin jin kunya tace "To ai yanzu ka ci abinci, kuma na tausheka sosai."
Murmusawa yayi yace "Kenan nauyi gareki?"
Turo baki tayi irin ba ta ji da蓷i ba tace "Ai ka ji."
Girgiza kai yayi yace "Um um, ban ji komai ba."
A hankali ta karkata ta fa蓷a daga 茩uryar kujerar hakan yasa ya zama shine a baki-baki, saidai matsatsin wurin yasa dole 茩afafunta a nashi 茩afafun suke haka kuma kanta a 茩irjinshi, tsam ya ri茩eta ya sake rufe idanunshi yana son bacci ko na awa 蓷aya ne ya 蓷aukeshi.
*03:54 na yamma*
Murmushi ta sakar masa ta sunkuyar da kanta tace "Ka yi kyau, Allah ya bada sa'a."
A nutse ya jawo 茩ugunta ya ha蓷a da na shi yana kallon fuskarta, yatsarshi ya 蓷ora a la蓳蓳anta yana zagayawa, a tausashe ya shiga fa蓷in "Idan na fita ki rufe min kayan nan dan Allah...ko kuma na..."
茒an satar kallonshi tayi tace "Wane kaya?"
A nutse ya ma mazaunanta wata sassau茩ar cakuma sannan ya mata alama da idanu cewa "Wa蓷annan."
瞥ar dariya ta saki tare da kwantawa kan 茩irjinshi tace "Ashe baka da kunya *Abdul*?"
Kya蓳e baki yayi yana tuna wa茩okin da maza ke yi dan ko蓷a mata, wato abinda suka sani kenan game dasu, lallai duk mulkinka da ikonka a waje ne, a gida kuma tamkar magen da bata da ha茩ora ne, cikin kunne ya ra蓷a mata "Daga ranar dana sanki ne na koma haka."
茒an dukanshi tayi a 茩irji tace "Ba wani nan, nima da ma ko gaisawa ba mu yi ba a ranar da muka fara ha蓷uwa."
La茩ace mata hanci yayi yace "Wawiya, ba waccen ranar ba, daren da ya gabata."
Shagwa蓳e fuska tayi kamar za ta yi kuka tace "Kaiiii Abduuuuul."
茒an ja baya tayi ka蓷an tana 茩ara gyara mishi rawaninshi tana fa蓷in "Abdul, ka ga dai kai sarki ne ko, kuma mulkin nan da Allah ya baka ba wai dan dubararka ko kuma ya fi 茩aunarka bane akan sauran bayinsa, jarabawa ce gareka, dan ya jaraba imaninka ne ya baka, Allah kuma ya na jaraba wanda ya so ne, inma dan 茩arfin imaninshi ana so a sake tantanceshi, ka kula ranka shi da蓷e wajen tafiyar da al'ummarka, kada kirarin da suke maka da kurantaka da suke na nuna maka ba wani sai kai, kada hakan yasa ka shagala ka tauye wani a kan ha茩茩insa, duk sanda za'a zo maka da wata shari'a, ka kasance mai taka tsantsan kafin yanke hukunci sannan daga 茩arshe ka fa蓷a musu yadda Annabi Muhammad (S. A. W) ya ke fa蓷awa wa蓷anda zai ma hukunci cewa _"Idan har na kasance na ba wani ha茩茩in wani saboda iya tsara zancenshi, to ya sani ba komai na bashi ba face wuta, ni kuma ban san gaibu ba ina yanke hukunci ne da abin daya bayyana gareni."_, ka sani ranka shi da蓷e akwai ranar tsayuwa, ranar da zamuyi shekara dubu hamsin a tsaye ba tare da Ubangijinmu ya ce mana uffan ba, ranar da za'a kusanto da rana izuwa 茩o茩unan kawunanmu tana tafasa mana 茩wa茩walwa tamkar talgen tuwo, ranar da za'a taramu daga 蓷an adam na farko har zuwa na 茩arshe, ranar da za'a tara annabawa na farkonsu da na 茩arshensu, ranar da mala'iku zasu zagaye aljanu, aljanu kuma su zagayemu, a wannan ranar adalci ne ziryan, ranar da hatta dabbar da ta soki 拼ar uwarta da 茩aho sai an tsayar da su an musu hisabi, ranar da nauyin aikinmu ne yake yin sama, sharrinmu kuma ke yin 茩asa sa蓳anin sikelin duniya da nauyin ke yin 茩asa, yalla蓳ai..."
Numfasawa tayi tace" Ka sani a wannan ranar babu wani sarki, babu hadimai, babu bayi bare dogarai, babu wa蓷annan masu maka kirarin da kurentaka, a wannan lokacin da kowa ke ta kanshi, 蓷a ba zai taimaki ubanshi da komai ba, duk soyayya dake tsakanin uwa da 拼a拼anta ba zata anfanesu da komai ba, ranar da aka fa蓷a mana tsabar masifar dake cikinta uwa za ta saka hannu ta jawo 蓷an dake cikinta ta fito da shi sannan ta jefar da shi shima yayi ta kansa, a wannan ranar ne ubangijin duka talikai, mamallakin ranar sakamako zai ce da kowa *yau mulki na waye*?... "
Murmushi ta saki ta tsurawa fuskarsa idanu wanda suka riki蓷a sukayi ja tace" Babu wani mahalukin da zai iya amsa wannan tambayar, Allah da kanshi zai ce *mulki nawa ne ni ka蓷ai*..."
Hawayen da suka 蓷an gangaro mata a kumatu ne yasa yatsarshi ya share mata, shi kanshi tsoratarwar da ta mishi ta sakashi kukan zuci, idanunshi sun ka蓷a ya 茩ara jin tsoron ubangijinshi, ha茩i茩a wannan ita ce matar da ta dace dashi, wacce za ta dinga tunasar da shi waye shi ma karan kanshi.
A jikinshi ya rumgumeta sosai yana fitar da numfashi, ita kuma shashe茩ar kuka take yi har ya 蓷an dinga bubbuga bayanta yace "Nagode zam-zam."
茒agowa tayi ta kalleshi tace "Ka tafi, an kusa tayar da sallah."
Babbar rigarshi ya gyara yana kallonta yace "Zam-zam, wa ya kamata na yi abota da shi a fada? Kowa sadda kanshi yayi idan ina wurin."
Ri茩o hannunshi tayi tace "Wanda zai fa蓷a maka gaskiya komai 蓷acinta, wanda zai fa蓷a maka halin da al'ummarka take ciki, to shi ne ya dace ya zama abokinka."
A sanyaye yace "Gaskiya ne, nagode zam-zam."
Murmushi ta masa shi kuma ya fita zuwa masallaci, ita ma nata 蓳angaren ta nufa dan gabatar da sallah, tana idawa kuma ta 蓷auki makullin madafa ta shiga dan 蓷ora girkin dare.
*Tana* cikin aikin gimbiya Kubra ta shigo madafar, da ladabi Saleema dake yanka albasa a saman katako ta juyo tace "Barka da shigowa ranki shi da蓷e."
茦arewa madafar kallo tayi kafin ta kalli Saleema tana yatsina fuska tace "Uhum! Me kike ne?"
Da fara'a tace "Girki." Matsawa gimbiya Kubra tayi kusanta tana kallon aikin da take tace "Me yasa za ki za蓳i raba kawunanmu?"
茒an kallonta Saleema tayi sai kuma maida dubanta kan aikin da take tace "Ba raba kawunanku zan yi ba."
"To me kike yi yanzu haka da kika raba abincinmu da mai martaba?" Ta fa蓷a tana tsareta da idanu, sai kuma ta kauda kanta tace "Ko kuma dai dan yana sarki ne sh..."
Da sauri Saleema tace "A'a ranki shi da蓷e, ni na yi hakane saboda aure nake a gidan nan, a ganina kamar bai kyautu a ce ba wani abun da zai ha蓷ani da shi na daga hidima ba."
Da wani kallo ta bita tace "Ba kina zuwa turakarsa ba?"
Ita ma wani kallo ta jefeta da shi da yasa ta ji kamar matar bata da kunya, hakan yasa ta 蓷auke kanta tana murmushin mugunta tace "Ni me nake yi a turakar? Ai yalla蓳ai ne ke 茩o茩arin, shiyasa na fi so na ciyar da shi daga ingantattun kayan masarufin da yake da bu茩ata a jikinshi dan 茩arin lafiya."
Wata muguwar harara ta watsa mata gyara tsayuwa cike da takaici tace "Kinga yarinya, mu nan ba ma haka, ki dakatar da wannan munafurcin na ki, daga gobe za'a ci gaba da girki tamkar yadda kika samu ana yi, sannan ki maida makulli a hannun Shamsu, shi zai ci gaba da sa kula da komai."
Tana gama fa蓷a ta juya ta fita a madafar, da kallo ta bita kafin ta ta蓳e baki ta ci gaba da aikinta ba tare da jin wai za ta aikata abinda gimbiya Kubra ta fa蓷a ba.
*Washe gari* da safe a madarar dake 蓳angarenshi ta girka masa abun kari har ya fita, na rana kuma a madafar waje tayi, lokacin gimbiya Kubra ta sakankance cewa ta ji abinda ta fa蓷a ne da ta ga da safe bata shiga ba, amma yanzu da aka kai mata labarin tana madafar tana aiki sai ta garzayo ta zo gurin gimbiya Ramlat ta kawo mata 茩orafin.
Ajiyar zuciya gimbiya Ramlat ta sauke ta kalleta da kyau a tsanake tace "Ina ga da mun ba wa lamarin nan baya, gidan mijinta ne tana da damar da za ta yi duk abinda ta ga dama, yi masa girkin da kanta ba laifi bane, sai dai..."
Numfasawa tayi