Showing 51001 words to 54000 words out of 191031 words
son karantawa ne, haka ita ma ta za蓳i in bayani akan girma da darajar iyaye, gaba蓷aya a harshen larabci ne rubutun, tunda ta fara da mu茩addima malaminsu ya yi sa茩e yana fatan kar a samu matsala, dan a ganinshi yadda aka bata takardar a 茩urarren lokaci ba lallai ta haddace inda yake da bu茩ata ba. Amma abun mamaki, sai ga Saleema na karanta takardar nan tamkar balarabiyar da ta sauko daga jirgi kai tsaye ta zarto wurin taron, irin yadda muryarta ke fita da 茩arfi, ga wani sanyi da nutsuwa a cikin muryar ha蓷e da rawar da muryar ke yi na kukan da take na rashin sabo sai ya hakan ya 茩ara ma muryar armashi.
Tsaye malamin ya mi茩e daga kujerarshi jin tana ci gaba da karanta har wajen da ba ya tsammanin ta kai can wajen da ya rubuta.
兀毓馗賲 賳噩丕丨 賱賱兀賳爻丕賳 賮賷 賴匕賴 丕賱丨賷丕丞 賴賵 兀賳 賷毓賷卮 賲毓 賵丕賱丿 賷賴 賵 兀賳 賷賰賵賳 賱胤賷賮丕 賲毓賴賲. 兀丿乇賰 丨噩賲 賴匕賴 丕賱禺爻丕乇丞 賲丕 毓丿 丕賱兀孬乇賷丕亍 賵丕賱兀氐賵賱 賰亘賷乇丞 噩賳亘丕 廿賱賶 噩賳亘 賲毓 丕賱孬賵乇丞 丕賱賴丕 毓賱丞.
_(Babbar nasarar 蓷an adam a rayuwar nan ita ce ya rayu da iyayenshi da kyautatawa, idan har suka shu蓷e ba sa farin ciki da kai, ha茩i茩a ka yi asarar da kwatankwacinta tamkar rasa iyalinka da duk abin da ka mallaka ne lokaci 蓷aya, babu wanda zai gane girman asarar sai mai kyakyawan ahali da manyan kadarori.)_
Ci gaba take yi ba alamar dakatawa, a hankali ya kai hannunshi saman goshinshi har yayi nasarar tunku蓷e hularshi ya mayar da ita baya, bai san sanda sakakken bakinshi ba ya furta masa "Tabarakallahu ahsanul khali茩in, masha Allah, lahauka wala-茩uwwata illa billah!"
Duk hayaniyar da ta kara蓷e wurin ta dandazon mutane, a hankali ta fara ragewa har aka yi shiru baki蓷aya sai 茩us-茩us kawai kake ji yana tashi daga 茩asa, malaman da aka 蓷orawa alhakin kiran sunayen 蓷alibai da kuma dakatar dasu, tsagwaron larabcin da take yi yasa su mantawa da aikinsu, ba wai yadda take futar da harufan bane abun mamaki, a'a yanda take karantawa babu takarda a hannunta alamar haddaceshi tayi, da kuma sauri-saurin da take yi da ya nuna ya zauna mata a kaine sosai, hakan shi ya fi basu mamaki, a ganinsu ko wata 蓷aya daya wuce take haddar nan, iya abin da za ta iya yi kenan. Duk sanda ta ambaci "Ya ku mutane ku ji tsoron Allah, sannan ka da ku ha蓷ashi da kowa, sannan ku kyautatawa iyayenku..." Jinin kowa sai ya sake hauhawa ya tsuma, mafi aksarin mutanen wurin ba sa jin me ake fa蓷a a harshen na larabci, amma daga yadda take yawan anbaton sunan Allah ya tabbatar musu abu mai matu茩ar mahimmanci ne, a hankali sai 蓷ai蓷aikun mutane suka fara 蓷aukar karatunta a wayoyinsu wanda abu ya shiga ransu matu茩a, duk da akwai masu 蓷auka na musamman da makarantar ta tanada har ma da 蓷aukar hoto mai motsi, amma hakan bai wadatar ba.
Sai da ta kai shafi na biyu sannan aka dakatar da ita tare da mata godiya kamar yanda aka ma sauran, daga ita 蓷alibai biyu ne sukayi karatu aka tashi bayan an kira kowane 蓷alibi an bashi kyauta, babban abun da ya birge Saleema shine yadda babban limami kuma malamin da yana 蓷aya daga cikin malaman da take matu茩ar 茩auna da aiki da fatawar da suka bayar ta manyan malamai gabata shine ya bata kyauta. Daga nan suka rabu da Aunty Lubna dan basu son su tafi gidan tare mahaifinta ya yi tunanin wani abun, da sauri ta 蓷auki hanyar komawa gida dan magriba ta gabato sosai.
A lokacin da kowa ke ta hada-hadar gabatar da sallah, lokacin Saleema ta shigo gidan bayan ta 蓳oye duka hannayenta cikin hijabinta sakamakon kyautar littatafai da littafi mai tsarki da take 蓷auke da su da kuma envelope 蓷in da babban malamin nan ya 蓷ora mata a kai da ba ta san me ye ko nawa ne a ciki ba? Tan shigowa farfajiyar ta sake rage saurin tafiyarta sakamakon ganin mahaifinta tsaye a daidai 茩ofar shiga falonsu, ha蓷a蓷蓷iyar fuskarshi da kuma hannunshi mai ri茩e da labceciyar wayar lantarki suka nusar da ita lallai akwai matsala babba.
Cak! Ta tsaya tana kallonshi daga nan da idanunta da ke cikin ni茩ab har sun tara ruwa, da hannu ya mata alama tare da fa蓷in "Zo, zo nan."
A hankali ta laluba hannunta ta cire ni茩ab 蓷in da tunanin ko idan ya ga fuskarta zai ji tausayinta, kamar wacce 茩wai ya fashe a a ciki ta fara takawa zuwa gareshi tana ci gaba da takwaf takwaf da fuskarta. Ikon Allah kafin ta isa gareshi wayarshi tayi ruri, rai 蓳ace ya jawo wayar daga aljihunshi yana ayyana "Wai waye wannan kuma yanzzzzz..."
Bai 茩arasa fa蓷a ba saboda ganin wannan kira, babban kira ne a wajenshi dan kuwa duk siyasarshi bai ta蓳a samun darajar kira daga gwamnan garin nan ba, sakin bulalar hannunshi yayi yasa hannu biyu ya ri茩e wayar sannan ya 蓷auki kiran jikinshi har rawa yake.
Daga 蓳angaren gwamna ne aka fara amsa sallamar da Alhaji Yusuf 蓷in ya yi kafin a 蓷ora "Ya baka sanar da mu har da 拼arka ake ma sauka ba? Dai da na je a matsayin babban ba茩o na ji an ambaci sunanta da na ka, daga jin haka na tabbatar 拼arka."
Tar! Tar! Ya zubawa Saleema idanu da tunda ta ga ya 蓷auki waya ta dakata tana kallonshi, kallonta yake kamar wanda ya ga aljana a gabanshi, shi mamakinshi bai wuce yadda a tunaninshi saukar 茩aramin lamari ne ta je ta zubar masa da mutumci, amma kuma gashi gwamna na cewa ya je. Baki na masa rawa-rawa ya 蓷an sosa 茩eyarshi yace "E..to...yalla蓳ai, da yake ai abun..."
Gwamnan ne ya katseshi da cewa "Zan shiga masallaci yanzu, amma lamari irin wannan a dinga sanarwa, idan ka samu lokaci zan so ganinki a gidana...tare da 拼armu, ta yi fa蓷akarwa mai kyau, ina son ganinta a zahiri."
Sake zaro idanu yayi yana rarrabasu tamkar mayen da ya ha蓷u da aljani ya fara in'ina yana fa蓷in" Ya.. Yyya..yalla蓳ai, to yalla蓳ai."
茦it! Ya kashe wayar wanda hakan yasa shi kallon wayar sai kuma ya juya zuwa falon da sauri dan har ga Allah ya ma manta da Saleema dake tsaye, ganin haka ya sa Saleema biyo bayanshi da sauri, saidai ganin ya nufi 蓷akinshi sai tayi saurin kama hanyar 蓷akin mahaifiyarta.
Wani 茩aramin littafin da yake rubuta lambobi saboda gudun matsala ya 蓷auko ya 茩ara duba lambar gwamna da ya rubuta wanda shi ma bai ta蓳a kiranshi, idan yana da bu茩atar magana da shi sai ya nemi hakan daga mataimakinshi an bashi lokaci sannan, tabbas dai lambar ce kuma gwamna ne, aje littafin ya yi ya shiga ban 蓷aki ya 蓷auro alwala, yana fitowa kira na yankewa a wayarshi, dubawa ya yi sai ga kira ne na wasu manyan mutane da yake mutumtawa saboda shekarunsu da kuma matsayinsu a cikin al'umma, sam zaune yayi bakin gadon ya kasa gabatar da sallah ya maida musu kira 蓷aya bayan 蓷aya, abun al'ajabi shine duka magana 蓷aya suke fa蓷a masa, wai an ga 拼arsa a wurin sauka kuma ana masa murna sannan Allah ya mata albarka. Shi fa dama wani abokinshi ne ya kirashi yake fa蓷a masa wai gashi nan a wajen sauka, kuma dama har da 拼arsa shine bai fa蓷a musu ba? Shine ya fantsamo ya zo gidan, tsaron kar ya titsiye Safiya a samu matsala akan cikin nan yasa ya tsare 茩ofar 蓷akin ya na jiran dawowar Saleema ya ji daga bakinta.
A 茩alla ya samu kira goma sha uku daga zaunen nan ne daga na abokan arzi茩i har zuwa na 拼an uwa da su ma mamakin yanda basu sani ba yasa suke kiranshi, dan labari har ya fantsama inda status 蓷in Saleema ke ta yawo a wayoyin wanda suka santa da wanda kawai suna 蓷orawa ne dan ta birgesu ko dan san a sansu kamar dai halayyar wasu daga cikin mutanenmu na yanzu.
Hamdeeya ce ta fa蓷o masa 蓷akin tana fa蓷in "Abba wai ka zo ga Tonton nan ya zo."
Kallonta ya yi yace "Wane tonton kuma yanzu ko magriba ba'ayi ba?"
Duk da yarinta amma dai ta ji babu masallacin da ake sallah a yanzu, hakan yasa tace "Abba an gama sallah fa, kuma tonton 蓷in da muka je gidanshi ne ya zo."
Zunbur ya mi茩e ya aje wayar tare da duba agogon dake bangon 蓷akin, gaskiya ne an gama sallah, aamma ya ya manta haka? Da haka ya fito da tunanin me ya kawo Alhaji Auwal yanzu? Kuma bai kirashi a waya ba?
Yana zuwa falon ya ja ya tsaya, ganin Alhaji Auwal da duka matan na shi da sauran yara yana magana da Safiya akan saukar nan, fushinsa kawai yake nunawa wai ya za'a yi haka bai sani ba? Ita dai ha茩uri take bashi saida ta ga mijin na su ya fito ta nunashi tace "Yawwa gashi nan."
Juyawa yayi ya kalleshi ranshi 蓳ace yace "Ya haka Yusuf? Me na maka da zafi hka?"
A hankali ya 茩araso yana ma matan da yaran kallon kowace ta kama kanta, ai kam sannu sannu suka sulale suka barsu su ka蓷ai, nan yake shaida masa shi ma abun ne ya zo mishi bazata, kawai dai ya manta ne saboda kwana nawa ba sa gidan, suna dawowa kuma lokaci ya gabato, shiyasa bai fa蓷a ma kowa ba dan kar ya 蓷orawa kowa nauyi.
Abunda ya sake hassalashi kenan yace "Au! Shiyasa ka 茩i fa蓷a mana? To wallahi kar ka sake min irin haka, kuma sai mun yi walimarmu dan godiya ga Allah, ka jima ba ka mutu ba dan ba茩in ciki."
Ficewa ya yi daga gidan gaba蓷aya Alhaju Yusuf ya bishi da kallo, yau kam ikon Allah ikon da ya fi 茩arfinshi yake gani, abun bai 茩ara bashi mamaki ba har da Ardiya kanta sai zuwa bayan sallah isha'i da dangi da ma茩ota aka dinga tururuwar zuwa taya su murna, ta wani 蓳angaren Alhaji Yusuf gani yake ai duk kuyi ku 茩ananen 茩wari, tunda har ya samu kira daga gwamna, ai a dalilin haka ma yana hangowa ya zama magajin garin wannan gari.
*Cike* da kunya take zaune kan kujerar inda kanta ke sadde sakamakon 茩ura mata idanu da yayi ya tallabe ha蓳a, tsarguwa ya sakata fito da hannayenta daga cikin hijabi tana wasa da wayar hannunta, ganin wayar yasa shi kallonta ya 蓷auke hannunshi da ha蓳arshi yace "Babyna, wannan wayar fa? Ya kamata ki ajewa Mama wayarta tunda dai kin samu taki."
Gam-gam ta li茩e idanunta sakamakon mararta da ta fara juya mata wanda tun sallah magriba take jin haka ka蓷an ka蓷an, saida ta huro iska kafin ta kalleshi cike da kunya tace" Wannan ai tawa ce."
Da mamaki yace" Ta ki kuma? Matata saurayi ya siya miki waya?"
Yatsina fuska tayi ta girgiza kai a hankali, cike da tuhuma yace" To ina waccen 蓷in?"
Ciwon da je neman rikitata ne yasa ta cewa" Waccen Hadeeya ce ta nuna tana so, kuma shine na farko a rayuwa da ta fara neman abu a wurina, saboda wayar nan har aunty ta kirani, shiyasa na bar mata waccen ta bani wannan."
Da ma蓷aukakin mamaki ya gyara zamanshi yana kallonta yace" Kika bar mata waccen? Saleema kin san tsadar wayar nan kuwa?"
Turo baki tayi tace" To miye waya kuma dan Allah, 茩anwata ce fa, kuma idan ban musu ba wa zai musu?" Ta fa蓷a tana kai hannunta 茩asan mararta ta dafe sosai.
Ajiyar zuciya ya sauke yace" Saleema, wayar nan na so ri茩e irin ta hannuna, amma Abba ya ce sam ban isa ba, idan aka ganni da ita za'a ce da ku蓷in al'umma na siya, duk da a lokacin da ku蓷ina zan siya, amma cikin sau茩i ranar da za ku taho ya bani ku蓷i na siyo miki ita a cewarshi kin fi 茩arfin wannan wayar, da akwai wacce ta fi ta ma zai siya miki, shi ne kika 蓷auketa a sau茩a茩e haka kika bayar? Kin kyauta kuwa baby?"
Da 蓳acin ran da sam ba 蓷abi'arta bane idan ba watanta bane ya yi ta kalleshi tace" To wai me kake nufi? Wayar da na ba 茩anwata shine kake min wannan fa蓷an? In dai Abba ne matsalar zan kirashi na masa bayani, ni na 蓷auka ma kai ka siya min wallahi."
Da irin 拼ar hararar nan ya kalleta yace" Oho! Kenan ni ne ban da daraja?"
Tsamukawar da mararta ta mata ua sa ta mi茩e tsaye da sauri tace" E 蓷in, ka ga ni ka daina min fa蓷a, idan so kake na biyaka ka fa蓷a m..." Da gudu ta juya ta yi hanyar shiga falonsu tana ri茩e matarta tana fa蓷in" Mama, Mama..."
Da kallo ya bita bayan ya mi茩e tsaye, dafe 茩ugu yayi da hannu 蓷aya yana kallon hanyar da ta bi, sakin murmushi ya yi ya girgiza kai yace" Shikenan dan watan zuwan ba茩onki ya yi sai ki yi ta min masifa, tsakani da Allah yaushe na miki fa蓷a?"
Sai kuma ya 蓷ora hannunshi shatin zuciyarshi yace" Laifinki ne, dole ki tayani yin ha茩uri da ita."
A nutse ya shiga takawa yana nufar motarshi, shi dai koma menene har yanzu bai ji haushi ba, ta ya zai fara hushi da yarinyar da girmanta ya fito a yau 蓷in nan, yarinyar da yammacin yau ta nunawa kowa kalar ta ta *BAIWAR*, shi kanshi dalilin haka ya 茩ara samun wata daraja, haka kawai abokananshi ake ta tayashi murnar samun ustaziya, duk da wasu da izgilanci ne ake masa maganar, wasu suna ganin ta ya zai la茩ewa 拼ar yarinyar islamiyya bayan ya gama jin da蓷insa a rayuwa? Amma dai hakan bai dameshi ba, ko ba komai wasu daga zuciyarsu sukayi maganar, har suna ganin suma idan na su auren ya tashi kamar shi za su yi, a islamiyya za su samu yarinya dan samun zuri'a mai kyau.
*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:48 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_21_
Tana shiga 蓷akin ta cire hijabi ta jefar ta kwanta kan gado tace "Mama bani maganina na sha."
Cike da kulawa Safiya dake 蓷aura 蓷an kwali tace "Marar ce?"
A wahalce ta furta "E mama." 茒auko maganin tayi da ruwa ta kawo mata, saida ta tashi zaune ta kar蓳a ta sha, tana komawa ta kwanta tace mata "Mu'az 蓷in har ya tafi ne?"
Saida ta tusa kanta a tsakiyar filo tace "Ban sani ba Mama, ni marata ce ta sha min kai shi ma kuma ya tsarenk da masifa dan na ba Hadeeya wayata, shi ne na taho na baro masa wurin."
Dariya kawai Safiya tayi dan ita kam ta san ba fa蓷an ya mata ba, kawai idan tana wannan yanayin ne ha茩urinta kan zama ragagge sai saurin hushi. Fita tayi a 蓷akin ta rufo mata 茩ofar dan zuwa wajen mahaifinta ta ji ya zasu 茩are kan lamarin da ya jijjigasu yau, dan ita kanta bata 蓷auka a haka abun zai zo ba.
Da sallama ta shigo 蓷akin na shi, amma ganin yanda gaba蓷aya ya tattara hankalinshi kan waya ya sakata ha蓷e murmushin dake kan fuskarta ta shiga takowa har ta zo kusa da shi ta zauna kan hannun kujerar da yake, a tsanake take ci gaba da kallon fuskarshi mai 蓷auke da yanayi na mamaki da al'ajabin wani abu, matse 蓷an 茩aramin bakinta tayi tace "Abban Hajia."
Zabura yayi ya kalli inda ya ji maganar, dan sam bai ji shigowarta ba bare zamanta, ganin haka ya sakata mamaki sosai har tace "Yalla蓳ai, me kake tunani haka?"
Zuba mata idanu yayi yana tunane tunane, to shi bai san ya zai mata ba, shin ya ri茩e wuyanta ya jijjiga ne saboda 蓳oye masa lamarin nan? Ko kuma dai ya rumgumeta har sai tayi 茩arar wahala sannan ya mata godiya kan haifa masa *darajar gidansa*? Sai ya ke ganin duk wanda ya yi a yanzu za ta cutu, kuma cutuwar ta ta ce ba ya so duba da abinda ke cikinta.
Sai kawai ya girgiza kai ya kalli wayar dake hannunshi yace "Mutanen nan ne ke bani mamaki, duba fa duk status 蓷insu yarinyar nan ne."
Murmushi ta saki a nutse tare da 蓷an sunkuyar da kanta a ladabce tace "Lamarin Allah kenan?"
"Hmmmm!" Ya fa蓷a yana jinjina kai alamar hakane, a hankali ta 蓷ora hannunta na dama akan hannunshi dake kan cinyarshi ya na ci gaba da kallon wayar tace "Ka yi ha茩uri dan Allah, ba mu da wani za蓳i ne da ya wuce mu aikata hakan ba tare da saninka ba, ka yi ha茩uri ka yafe mana."
Wani murmushi yayi mai kama da ciwo kawai ya girgiza kai yace "Ba komai, ya wuce."
茒ora ha蓳arta tayi a kafa蓷arshi tana fara'a tace "Nagode sosai mijina, Allah ya saka da alkairi."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fa蓷in "Gobe ki ce ta shirya da wuri, zamu je ganin gwamna tare da ita."
Da sauri ta 蓷ago tace "Gwamna kuma? Wane gwamnan?"
Kallon fuskarta yayi kamar wacce aka ba tsoro yace "Gwamnan garinmu mana, yana son ganinta ne, har 茩orafi ya yi wai ban fa蓷a mishi ba."
Jiki a sanyaye ta sake maida kafa蓷arta tace "Allah ya nuna mana goben, Allah ya sa mu ji alkairi."
"Ameen." Ya fa蓷a, dan fa shi tunaninshi bai wuce dalilin haka zai sa gwamana ya 茩ara jawoshi a jiki har yayi nasarar cimma burinshi akan siyasa ba.
*Washe Gari*
Doguwar rigar shadda ta saka wacce ke da 蓳oyayyar tsaga daga baya, ma'ana tsagar da ka shatinta amma ba ta fito ba, shaddar kalar kore ce sosai da ta 茩ona, hakan yasa ta saka takalmi kalar yelow mai duhu da hijabi kalar takalmin wanda aka mishi hula a kai da kuma ha蓳a, sannan ga hannayenshi na roba sannan har 茩asa, ita kanta duk da ta san ba kyawun fuska gareta kamar na 拼an uwanta ba, amma dai ta san ta fito tsaf da ita sannan kamalarta na 拼a mace da darajarta sun fito ras, dan kuwa saida Mamanta ta sakata saka kwalli a idanunta, hakan yasa fuskarta fitowa tass!
A nutse ta fito falon ta samu Abbanta