Showing 114001 words to 117000 words out of 191031 words
cikin muryar jimami da alhini tace "Yaya ka kirashi ya dawo, wata茩ila kai ya ji maganarka, har an fara jin 茩amshin shekara amma har yau ce min yake zai dawo, na gaji da wannan halin na shi, ga fargaban rashin sanin me yake damunshi da kuma tunanin me yake aikatawa a can."
A nutse dattijon da ba laifi an girma sosai saidai ilimin addini da kuma bin dokikin Islama yasa jikinshi tamkar na wani ingarman doki ga fuskarshi da ke cike da haiba, hannu yasa ya 蓷an ja jelar farin rawanin dake kanshi ya mayar baya sannan ya sake zuba mata fararen idanunshi da suka fito tass a cikin babban farin gilashin na 茩ara gani, cike da dattako yace "Ramlat, a kullum ina fa蓷a miki ki kwantar da hankalinki, sannan ki daina zubar da hawaye a kanshi, ranar da kika kirani a waya munyi magana dashi sosai kuma ta fahimta."
Gyaran murya yayi wanda manyanci ya kawo hakan sannan yace "Abinda ke damun mai sunan Baba ba 茩aramar matsala bace da zamu fa蓷a mata kai tsaye ba, na nazarci lamarin sannan na yi duba da zahirin daya bayyana a gareni."
Shiru ya sake yi na wasu da茩i茩u kafin ya 蓷ora da "Ramlat, Babanmu ya kusa aure da izinin Allah, duk wani sihiri da sammu dake kanshi ya kusa rugujewa, sai dai wani akwai abu..."
Da sauri ta kalleshi tana 茩ara gyara zamanta tace "Me ye Yaya? Yaushe? Da gaske ya kusa aure shima?"
Jinjina mata kai yayi yana lumshe idanu kafin ya kalleta yace "Ban san yaushe ne ba, saidai Allah ya nuna min shima zai yi aure kafin ya bar duniya, kinsan wani mafarkin ilhama ce ta faruwar wani abun, dayawa daga abubuwan dake faruwa damu ana nuna mana su a mafarki, saidai rashin sanin fassararsa yasa muke kasa sanin me ke shirin faruwa da mu?"
Da sigar 茩aguwa da damuwa tace" Amma Yaya baka ka ce baka san ranar ba? Kenan har yanzu ba lokaci?"
A tausashe yayi murmushi ya gyara zaman babbar rigarsa yace" To me yasa zamuyi hanzari? Kin san me na gani kuwa Ramlat?"
Hannu ya mi茩a mata yace" Matso nan 茩anwata, zo ki ji." Mi茩o masa hannunta tayi ta matsa kusa da shi tana kallonshi tare da ci gaba da share hawayenta, cike da son kwantar mata da hankali yace" A mafarkina na ga Abdus-samad hannayensa biyu ri茩e da wata farar kwalba, bayan 蓷an lokaci sai wannan kwalbar ta bu蓷e da kanta kawai ruwa suka dinga fitowa, ruwan na gama zubewa sai fuskarshi ta fa蓷a蓷a saboda murmushi, yayin da tsabar hasken annurin fuskarshi ya isa ya haska gidan nan da kewayenshi... Shin kin san me hakan yake nufi?"
A hankali ta girgiza masa kai tace" Ban sani ba Yaya."
Cike da sanin ilimin abun yace" Kwalbar na nufin matar da zai aura, ri茩on da ya ma kwalbar kuma alamu dake nuni yadda zai ri茩e matar da zai aura da kyautatawa kuma hannu bibbiyu, ruwan cikinta na nufin za ta haihu da shi, sai dai haihuwa nawa? Allahu a'alam, fitowar ruwan alamu na zata haife duk abinda zata 蓷auka a cikinta, farin cikin daya mamayeshi kuma bayan haka, alamu ne na girman soyayyar matar gareshi. Wannan ka蓷ai ya isa ya sakamu farin ciki, sannan muyi masa fatan alkairi, kar mu ce zamu gaggauto da lamarin, garin haka kwa蓳armu zata iya yin ruwa, amma mu barwa Allah komai, shi yasan me yake nufi da jinkirin na shi."
Sadda kai tayi tana share hawayen farin ciki, dan ita yana fa蓷in maganar nan hango komai take a idonta har ma ya faru, murmushin daya bayyana a fuskarta ne yasa shi fa蓷in" Ko ke fa, yanzu ki koma gida, ki ci gaba da masa addu'a, sannan kiyi ta addu'o'in dana baki, sannan ku yawaita sada茩a dan na fa蓷amiki ita mabu蓷in alkairi ce sannan mai cinye zunubai, sannan kamar yadda na fa蓷amiki sirrinki na ki ne, koda kishiyoyinki ba komai ne zaki zanta dasu ba a kai, haka ma *galadima* da su shamaki, idan akwai wanda zan ce miki zaki iya neman shawararsa a fadar nan, bai wuce liman da kuma 茩anin margayi mai martaba ba, kin fahimta."
Kallonshi tayi da yanayi na tsoro tace" Yaya, sai kasa na ji ina tsoron kowa dake gidan nan, Yaya a ce rayuwa ba amana, ba wanda za ka iya tattauna matsalarka da shi, yanzu ya zanyi kenan? Idan fa mutanen dake kewaye dani sune musababbin shiga Abbana wannan halin fa?"
Murmushi ya mata irin na babba da yaro kanshi sadde 茩asa, kamar ba zai ce mata komai ba sai kuma ya kalleta yace" Rayuwar kenan, kawai kiyi abinda na ce, sannan kada kiyi komai sai da shawarata."
Jinjina kai tayi tace" In sha Allah Yaya, nagode sosai, Allah 茩ara girma da lafiya."
A tausashe yace" Ameen, ki kula da kanki." Jinjina kai ta sake yi ta mi茩e tana sake masa sallama, tana fita jakadiyarta da ta yarda da ita na zaune a 蓷aya falon, tasowa tayi da sauri ta rusuna tana mata barka da fitowa, gaba tayi ba tare da ta ce komai ba ita kuma ta rufa mata baya.
Saida suka koma gida ta zauna a 蓷akinta ita ka蓷ai ta sake 蓷aukar 茩aramar wayarta ta kira lambar Saleema. Lokacin Saleema sun sauka a Jiddah ta gama waya da Mamanta kenan kiran ya shigo, cike da tunanin irin ku蓷in da za'a ja Saleema ta 蓷aga suka gaisa, ga mamakinta sarauniyar cewa tayi "Saleema, dama alfarma nake nema a wajenki, ko zan samu?"
Sosai ta ji mamakin sarauniya guda na neman alfarmarta, amsa mata tayi da ko me ye za ta yi, saida ta sauke numfashi tace "Dama ina so ne ki sakamu a addu'o'inki, sannan a islamiyarku ma ki ro茩a mana barar addu'a gurin sauran 蓷alibai da malamenku."
Da girmamawa tace "In sha Allah Ranki shi da蓷e addu'ata tana tare da ku, sannan zan isar da sa茩on ga malaminmu, sannan na yi al茩awarin ro茩a muku Allah a wajen da ya fi tsarki, in sha Allah komai zai daidaita."
Sai lokacin ne ta san a inda take, bata sake janta da wata hira ba sukayi sallama, hakan yasa Saleema mamakin wai me ke damun matar nan jama'a da kullum take cewa a sakata a addu'a? Ita ba alamar rashin lafiya, kuma dai ba matsala ce ta talauci ba, to kenan me ke damunta?
Cikin amincin Allah haka suka 蓷aura niyyar yin abinda ya kawosu sannan suka fara gabatar da 蓷aya daga cikin farillan da suka hau kawunansu sai dai banda Hamdeeya da ko balaga ba ta yi ba, wannan kwanakin sun kasance mafi daraja ga Saleema, baya ga kasanxewarsu ranakun da ta gabatar da aikinta, haka ma ranaku ne da suka kawo sha茩uwa tsakaninta da 拼an uwanta, dan kullum suna tare kuma komai tare suke yi, hatta waya da iyayensu mata da suka baro a waya 蓷aya suke yi, mahaifinsu dama tare suke haka ma wajen kwanansu 蓷aya sai dai shi yana 蓳angaren maza ne. Kwana tashi a wurin Allah ba wuya sai gashi sun kammala tsaf sun dawo 茩asarsu ta haihuwa, duk wanda ya ji zuwansu bai yi 茩asa a gwiwa ba wajen zuwa yi musu barka da zuwa da kuma brka da sauke farali.
*Sati 蓷aya* suka kwashe kafin yau dai Saleela ta shirya fita hannayenta 蓷auke da tsarabar da ta tanadarwa Fareeda da Mama da Mubarak da kula chief telor馃榿, drebansu ne ya kaita saidai a nan ya barta da cewa zai dawo ya 蓷auketa, haka ta shiga ciki ta zube musu kayan arzi茩in da ta kawo musu, ba ta jima a gidan ba ta fito tare da Fareeda suka shigo shagon, sai dai sun samu wata matashiyar budurwa zaune.
Da murmushi a fuska Saleema ta kalleshi tana 茩arasawa kusa da shi tace "Yalla蓳ai barka."
Da mamakin ganinta dan bai san ta zo gidan ba ya kalleta da fara'a da tsantsar farin cikin daya kasa 蓳oyuwa yace "Haleema, ke ce? Yaushe kika zo gidan?"
Hararar wasa ta masa tace "Ba wani nan mana alhudahuda, kai dai kawai hankalinka na kan 蓷inki."
Dariya yayi ya nunota da yatsa yace "Zamu fara ko? Daga zuwanki?"
Dariya tayi ita ma wacce ta bayyanar da ha茩oran makkarta guda biyu tace "E mana, na yi kewarka *komai daga gareka ne*, shiyasa na kasa ha茩ura ma har na zo yau duk da ina son yin bacci."
Dariya yayi yana jin kanshi a sama, dan fa shi gani yake yarinyar na matu茩ar sonshi kamar yadda yake ji a zuciyarshi game da ita, sai dai kafin yayi wata magana matashiyar nan ta mi茩e fuuuu! Ta fice a shagon, da harara Fareeda da ta bita dan yadda ba ta 茩aunar Sharhasila haka bata son yan gidansu, Huzeifa kam ko kula da tsiyar yarinyar bai yi ba duk da kuwa Sharhasila ce ta turota kar蓳an makulli saboda ta jefar da nata wajen yawo, shine ta dawo gidan take neman makulli ta turo a kar蓳a kuma ya aiki Mubarak da motonshi kuma makullayen suna ha蓷e dana shago da gida da duka wani abu mai mahimmanci, zaman da take ma ya ce ta jira ka蓷an ne yanzu zai dawo.
Rashin zuwa dreban 蓷aukarta yasa ta zauna suka shiga ta蓳a hira sama sama. 茦anwar Sharhasila kuma tana zuwa ta sameta 茩ofar gida a mota tana jiran dawowarta, cike da son kunna wutar husuma tsakanin ma'aurata ta shiga labarta mata duk abinda ya faru a shagon, mamakinta bai wuce kalmar da Saleema ta fa蓷a cewa ta yi kewar komai nashi ba, sai kuma yadda ta san Huzeifa ko ita dake 茩anwar matarshi ba ya mata fara'a, amma yau wata take ma dariya ha茩ora waje.
A haukace, a gigice, a kausashe, a matu茩ar hargitse Sharhasila ta fito a motarta, gyalenta ne ya fa蓷i 茩asa amma ba ta bi ta kanshi ba, boot 蓷in mota ta bu蓷e sai huci take tana fa蓷in "Ni zai wula茩anta? Kenan mahaukaciya ya 蓷auke da bai yarda dana fa蓷a masa zan babbaka duk wacce na gani tare da shi ba? Yau zai gani, yau zai san 拼ar tasha ce ni kamar yadda yake fa蓷a, wallahi ku蓷inmu da gatan da na samu bai sa na zama sakarya ba."
Babbar ma蓷aura (ban san me zan kirata da hausa ba, abar da ake 蓷aure ko kunce 茩usa) ta 蓷auka ta nufi hanyar shagon, da gudu yarinyar ta biyota tana fa蓷in" Shar, Shar ki tsaya dan Allah, ki saka gyalenki mana."
Ko kulata ba ta yi ba haka ta tunkari shagon ba kunya ba tsoron Allah, ga cikin dake jikinta fiye da wata shida, amma haka ta biyo titin tamkar mahaukaciya sai sambatu take tana jinjina ma蓷aurar nan a hannunta.
Kwatsam fa蓷owarta shagon suka gani, kallo 蓷aya Saleema ta lata ta 蓷auke kai dan abu na farko da ya zo mata shine mahaukaciya ce, ita kuma mahaukaci indai ba mai bugu ba bata tsoronshi, Fareeda da ta san sai mummunan abu ya faru a take ta mi茩e tana zare idanu, Huzeifa ma da yana ganinta tsakaninshi da Allah saida gabanshi ya fa蓷i ganin yanayin da ta shigo da shi shagon, tabbas yasan ba lafiya ba! Da idanunshi ya ga ta jefi Saleema da mummunan kallo sannan ta nufo kanta gadan gadan, ganin abinda ke hannunta da mugun sauri ya mi茩e har yana neman yin gaba da telar dan gani yayi ta tsayar dashi sosai, kafin ya fito ya iso inda suke tuni Sharhasila ta shammaci Saleema da ba ta zaton wani abu kwatankwacin haka ya faru ta soka mata wannan zundumemen 茩arfe a ciki, dan dama zama ne tayi duka hannayenta na bayan telar dake bayanta ta jingina, hakan yasa 茩arfen nan ya shiga jikinta sosai.
茦arar da tayi ya sake tsumar da shi da gudu ya 茩araso, Fareeda dake tsaye ihu ta buga ita ma ta juya da gudu ta nufi gidansu dan sanar da Mamansu. Huzeifa kuma na ganin abinda ta aikata ya 蓷ora hannaye biyu a kai ya 茩walalo idanu yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna..."
Juyawa yayi kan Sharhasila dake ysaye tana huci tana fa蓷in "Gobe kya sake kula mijin wata, banza 拼ar iska kar..."
Marin da ya sauke mata yasa ta 蓷auke wuta duf! Daidai da shigowar 茩anwarta ya sha茩i wuyanta da duka hannayenshi da iya 茩arfinta yana fa蓷in "Kin kasheta fa, kin kashe 拼ar mutane Sharha, me ta mikiiiiii?"
Duk da wuyar da take ji na sha茩ar da ya mata dan idanunta a waje suke, amma haka ta saki murmushi tace "Ka kasheni nima, ko ba komai na kashe 蓷aya daga cikin masu bibiyarka, ban da asara dan na mutu yanzu."
Sakinta yayi a haukace ya sake juyawa kan Saleema da tuni jini ya wanke mata doguwar farar rigar da ta sako da hijabi tana kwance a kan teburin da take zaune tamkar gawa. Kafa蓷unta ya kama yana jijjigta tare da kiran sunanta a haukace, a lokacin su Mama suka shigo a rikice ita da Fareeda.
Tashin hankali bayin Allahn nan sun ganshi tsagwaronshi, yarinyar da mahaifinta bai ko san tana zuwa wajen nan da sunan 蓷inki ba, a ce ita ce haka ya sameta? To yanzu me zasu fa蓷a musu? 瞥arku ta rasu? Rashin sanin abun yi yasa Huzeifa sake juyowa inda Sharhasila take lokacin da Mama da Fareeda suka tallabi Saleema aka saka a adaidaita sahu, kifeta ya sake yi da mari ya nuna mata hanyar fita daga shagon a 茩ufule sosai yace "Fita daga nan Sharhasila, karki bari na sake ganinki, ke mai kama dake ma bana son sake gani a rayuwata, na tsaneki na tsaneki Sharhasila, sannan na sakeki saki 蓷aya."
A sukwane ya nufi hanyar fita sanda Sharhasila ta 蓷ora hannuwa a kai ta fashe da kuka, tsayawa yayi tare da kamo hannunta ya wurgo bayan 茩anwarta da tsoro yasa ta fit a shqgon, da hannu ya shiga nuna mata yace" Ni kika kashe Sharha, saboda kin *kashe yarinyar da nake so*, ba zan yafe miki ba wallahi, na tsaneki, kin ci albarkacin 蓷ana da yake cikinki, wallahi da kema na kasheki in ya so a kasheni."
A hanzarce ya shiga adaidaitar suka 蓷aga zuwa asibiti, suna tafiya kuma dreban na dawowa, 茩anwar Sharhasila ce ta fa蓷a mishi an tafi kai ta asibiti, dan daga kwatancen daya mata ta gane ita yake nema, bayansu ya bi cike da zulumin me ke faruwa.
Da fari kamar gaske haka ake kar蓳esu, amma da aka ga raunin sai likitocin suka ce dole a zo da wani jami'in tsaro saboda tayiwu fa蓷a ne aka yi, lokacin da aka tabbatar musu tana raye hankali tashe Huzeifa da ba mai son hayaniya ba yace "Duk da tana da rai har yanzu ba zaku dubata ba, wannan ai dokar banza ce da wofi, kenan sai abar rayuka su salwata saboda doka?"
Malamar asibitin cike da tausayawa tace "Ka yi ha茩uri, ni ba abinda zan iya yi muku, yalla蓳ai ne bai bada damar ba, kula yana ganawa da abokinshi ne ya ce kar a takura masa."
A gigice Huzeifa ya fita daga asibitin dan yin abinda ya dace, a shirye yake da ya mi茩a kanshi a matsayin mai laifin indai za'a duba Saleema ta farfa蓷o. Fareeda na kai kawo daga wannan bango zuwa wannan, Mama tana zauna kan benci ta kifa kanta sai gunjin kuka take tana ta maimaita "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Ita bala'in nan ta na dubanshi ne ta wata fuska daban, shiyasa take fatan Allah ya zame musu gata kawai, suna haka *Mu'az* daya fito daga ofishin babban likitan ya gansu, tausayin halin da ya gansu ne yasa shi tsayawa yana tambayar Fareeda lafiya Mama ke ta kuka? Da sauri Mama ta taso a rikice ta kalleshi tana fa蓷in "Yalla蓳ai dan Allah ka taimaka mana, yarinya ce muka kawo amma sun 茩i dubata wai sai jami'in tsaro ya zo, dan Allah ka taimakemu ka mana rai."
Da yanayin tausayi yace "Tana ina yarinyar? Me ya sameta?"
A tare suka nuna mishi 蓷akin da aka kwantar da ita, da sauri ya shiga takawa ya nufi 蓷akin, yana bu蓷ewa idanunshi suka sauka kan Saleema daya kwashe watanni rabon da ya sakata a idanunshi idan ba hotonta 茩waya 蓷aya tak da yake da a waya kuma yake kallo ba kullum.
A rikice ya isa gareta tare da kai hannayenshi yana neman rumgumota yana fa蓷in "Saleema, Saleema, ke, ke! Dan Allah ki bu蓷a idanunki, likita!!!! Likitaaaa."
Juyowa yayi da gudu zai fito sai ga Fareeda da Mama sun taho a sukwane jin 茩arajin balagaggen matashin nan, a hukace y nuna Fareeda da hannu yace "Saleema ce wannan, me kuka mata? Me ya sameta? Jini fa take zubarwa, kira min likita..."
A duburburce ta juya ba tare da sanin ina zatayi dan kiran likitan ba, saidai tana fitowa ita ma suka ha蓷e da likitan wanda wannan 茩araji da yayi na 茩arshe ya fargar da duk wanda ke kusa a lokacin. Mu'az da wata malamar asibitin ne suka tsaya a kan Saleema dan ceto rayuwarta, wacce kafin komai saida aka fara 茩ara mata jini, sun dai yi mata aiki da ya茩inin jijiyar wuyan hannunta dake harbawa a matu茩ar sai蓳ance, wanda hakan shi ya fi 蓷agawa Mu'az hankali har yake tunani zuwa yamma idan bata farfa蓷owa zai sa Abbanshi a maganar ne a 蓷auketa a jirgi marasa lafiya a fita da ita ko ina ne ma dan ta samu lafiya.
Huzeifa ya dawo tare da wani jami'in, saidai sun samu har an mata aiki, jin ba'asi da neman fitina yasa jami'in har ya 茩uresu saida suka fa蓷a masa yadda komai ya faru, adireshinsu ya tambaya tare da ba da tabbacin dole Sharhasila ta fuskanci hukunci ko 拼ar wacece, Alhamdulillah dake jami'anmu da zafin nama da kuma ba wa kowa ha茩茩inshi, sai ga Sharhasila a hannunsu a karo na ba adadi wanda ita hakan ba ba茩on abu bane a wurin, dan indai rikici zai ha蓷ata da kai to ta yankeka ko ta sokeka 茩aramin aiki, hakan kuma ya samo asali ne daga ahalinsu. (bana so na fa蓷i sunan halin馃ゴ)
*Mu je da sauri*
_(Rikicin na gaba)_
Babu hankalin wanda bai tashi ba da jin wannan lamari musamman Safiya da tsabar rikicewa sai Alhaji Yusuf ne ya biyota da yaron a baya, ta yi kuka kamar ranta zai fita, Alhaji Yusuf da Alhaji Auwal da shima ya zo suka shiga kai da kawowa daga yadda za'a nema mata lafiya zuwa maganar Sharha dake ri茩e, a lokacin ita ma Babanta ya san maganar ya fara nuna na shi