Showing 144001 words to 147000 words out of 191031 words
tamkar *tsokar naman da aka jefata a tsakiyar kuraye ne*, a lissafinki ya zasu farauci wannan tsokar?"
苼oyayyen numfashi Saleema ta sauke kafin tace" Wawaf da zasu daka a kanta abun 茩ayatarwa ne wajen kallo, sai dai abun tausayi ne ga su kurayen, dan kuwa duk kurar da ta samu ba zata anfaneta da maganin yunwa ba, bayan cutar da kawunansu da zasuyi, dan akwai yiwuwar su kashe kawunansu wajen 蓷aukar wannan tsokar."
Murmushi tayi tace" Da kyau Saleema, to wannan kujerar da mijinki ke zaune a kai ita ce tsokar naman, kinga kuwa ba za'a sameta ba sai babu kowa a kai, idan kuma ya zama akwai wani mahaluki a kant? Hakan yasa suke kawar da duk wanda ya nemi shan gabansu."
Ajiyar zuciya ta sauke kamar za ta yi kuka ta sassauta murya sosai tace" Saleema, abu biyu zan fa蓷a miki da zai taimaka miki wajen zamanki lafiya a gidan nan, na farko ri茩e sirrinki, duk tsanani duk wuya kada ki ta蓳a fa蓷awa wani abinda ya shafeki ko ya shafi ke da mijinki, komai girman mutum ko matsayinsa a gun mijinki, dan wasu zasu iya anfanin da matsayinsu a gareshi su shiga jikinki, idan bakiyi sannu ba za'a dinga tuntu蓳arki rayuwarki ko zamanki da mai gidanki, ta haka kuma za'a samu 茩ofar da za'a shiga a cutar daku."
Numfasawa tayi tace" Na biyu kuma shine, ba kowa ne dake miki dariya ba kema zaki yage masa baki, wani dariyarsa iya la蓳蓳ansa ne kawai, Saleema a cikin mutane sama da 蓷ari da zaki zauna da su, bai fi kaso talatin ba da zaki iya samun dariyar gaskiya daga garesu ba, sauran duk za'a miki ne dan kawai ba yadda zasuyi, idan kika zama mai lura da saka idanu zaki fahimci haka, amma sai kin zama mai takatsantsan da lamarin kowa a gidan nan, abu na 茩arshe da zan fa蓷amiki shine..."
Numfashi ta ja ta sauke sannan tace" Kada ki zama mai bawa hadiman gidan nan yarda akan abinda ya shafeki da kula wanda ya shafi sarkinki, bakinki da su ya zama abinda kawai su ne zasu iya yi miki, amma in dai zaki iya da kanki to kiyi, Saleema... *kada ki yarda hadimai ne zasu gyara miki makwancinki*, bawai zan hanaki hutawa ba ko hanaki kiyi ikonki yadda ya dace a matsayinki na *matar sarki*, amma dai a nan kusa ya kamata ki zama mai kula sosai, domin kuwa nima na yi irin wannan sakacin, wanda shi ya kaini ga halin da muka samu kanmu a ciki har ya zama silar shigowarki rayuwarmu..."
茒an tsagaitawa tayi kafin tace" Ruwan wankansa, takalmin 茩afarsa, da ku蓷in da suka fito daga gareshi, da su aka ha蓷a aka masa sihirin da ya fi shekara takwas dashi a jiki..."
Hawaye ne suka wanke mata fuska tasa hannu tana sharewa tana ci gaba da fa蓷in" Ba dan iyayena masu hali bane, da mun yi bara saboda larurar *Abdus-samad* sai da na dinga siyan da kadarori dan na sama mishi lafiya, ba dan Allah ya azurtamu da ka蓷autashi shi ka蓷ai ba, da mun yi shirka kamar yadda wasu malaman ke nuna mana sai ta hakane zai samu lafiya, shiyasa na 蓷auki lamarinki da mahimmanci Saleema, shekarun da aka 蓷auka da ku蓷a蓷en da aka kashe, ashe maganin na nan kusa da mu ga wata yarinyar da ba wanda ya santa...abun al'ajabi."
Sake ri茩e hannayenta tayi sosai tace" Ki zama mai kula akan komai Saleema, dan wannan mulkin da kika gani wasu a shirye suke da su *raba mijinki da rayuwarsa* ma."
A tsorace Saleema ta kalleta, ha茩i茩a maganganunta sun shigeta sosai kuma ta 蓷auki aniyar kiyayewa, sai dai maganar rasa rayuwar nan yasa ta jin fa蓷uwar gaba har ta fara hasasho idan fa hakan ta faru da gaske? Idan fa aka yi nasara a kansu kenan? Za ta zama mai *takabarsa* kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ta ambata a ranta, wane wace irin rayuwa ce? Me ye a mulkin da za'a so raba wani da ransa saboda shi? Sosai ta shiga ru蓷ani da kuma tsoron zaman gidan, dan gaba蓷aya ji take tamkar ko numfashinta da zai fito daga ruhinta akan idanun wasu zia sauka tsabar saka ido, tsoro matu茩a ta ji ya kamata har ta gagara tashi ta koma inda take, ji take ma kamar ba lallai ta kai 蓳angaren na ta ba.
A 蓷an rikice Saleema ta kalleta tace " *Umma*, to a ina suke cin abinci?"
Da rashin fahimtar kalamanta tace "Su wai? Kowa a 蓳angarensa, sai dai wasu lokuta mu kan ha蓷u gaba蓷aya a ci abinci, kuma haka tun mai martaba yana raye ne, har yanzu bamu daina ba, sai dai ba wani shau茩i a wajen cin abincin."
Saida ta ji ta dasa aya sannan tace "Su nake nufi, yalla蓳ai mai martaba."
Kallon tsanake ta mata cike da jin ta birgeta, ashe fa Abdus-samad take nufi da su, hakan ya birgeta sosai, kuma duk da ba amsar tambayarta ta bata ba, bata katse mata numfashinta ba saida ta dire maganar sannan, hakan girmamawa ne daya samo asali daga lafiyayyar tarbiya, murmushi ta mata tace "Daga 茩aramar madafa ake fidda mana abincinmu tare da na shi."
Jinjina kai Saleema tayi tace "Nagode Umma, kuma in sha Allah zan kiyaye duk abinda kika fa蓷amin."
Sakin hannayenta tayi tana fara'a tace "Nagode *sarauniyata*, za ki iya tafiya 蓳angarenki."
Jinjina kai tayi ta mi茩e a hankali, da sauri ta mi茩e tsaye ita ma tana sake ri茩e hannayenta tace "Uhyemmm! Kuma kina ji, Saleema 蓷ana ba waliyi bane bare na ce ba zai miki ba daidai ba, saidai duk yadda ranki zai 蓳ace game da shi idan ya miki ba daidai ba, dan na ro茩eki kada ki bari wasu su fahimci sa蓳aninku, zaki iya hushinki a 蓷aki dan kema 拼ar adam ce, amma da kin fito waje ki nunawa kowa lafiya lau kuke zaune ta hanyar sakin walwalar fuskarki, dan kuwa sanin sa蓳anin naku shi zai bada damar da wasu zasu shiga tsakani dan a farra茩u."
Murmushi Saleema tayi tace" In sha Allah Umma, zan kiyaye."
Da fara'a a fuskarta tace" Allah ya miki albarka."
"Ameen." Ta fa蓷a tana rusunawa sannan ta juya ta 茩ofar da suka shigo ta nan ta bi dan ta hakane za ta iya gane na ta 蓳angaren.
*Alhamdulillah.*
20/06/2022 脿 22:08 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_47_
Jakadiyar dake gabanta ta kalla a nutse bayan ta aje littafinta tace "Madafa nake son shiga, za ki iya yi min jagora?"
Rusunawa ta sake yi tace "Yadda kike so uwargijiyata."
A nutse ta mi茩e tsaye hakan yasa jakadiyar take mata baya, daga nan take nuna mata hanyar har suka isa madafar, ba kowa a ciki dan lokacin girkin rana bai yi ba, kula an riga da an gama na safe, hakan yasa Saleema kallonta tace" Ko zan iya ganin wa蓷anda suke iya shigowa madafar nan?"
Rusunawa tayi tace" To ranki shi da蓷e."
Gaban wayar tangarahon dake ajiye ta 茩arasa, Saleema na kallonta tayi kira ta kuma fa蓷i ta茩aitaccin kalmomi cewa su shigo madafa sarauniya na son ganin masu ruwa da tsaki a madafar, bayan ta aje wayar da kamar sakkani talatin mace uku namiji 蓷aya suka shigo.
茦are musu kallo tayi ta nunasu tace "Ku ka蓷ai ne a gidan nan ke iya shigowa nan?"
茒aga kawunansu sukayi suka amsa da "E, ranki shi da蓷e."
Matse bakinta tayi ta zama irin ba wasar nan sannan tace "Ku kuke dafa abincin da gimbiyoyi ke ci kenan?"
Wata babba a cikinsu ce tace "E ranki shi da蓷e, yanzu kula hada na sarki ma."
" *To ya isa.*" Saleema ta fa蓷a tana juyar da kanta gefe, duk tsura mata idanu sukayi suna kallo, a hankali ta sake kallon inda suke tace "Daga yanzu abincin masu gidan kawai zaku dinga dafawa, amma banda na *sarkina*, ni zan dinga shigowa madafar ina girka masa da hannayena."
A da茩ile ta furta "Kun fahimta?"
Kallon juna sukayi jin wani sabon tsari, su fa shiyasa lamarin sarautar na yanzu ma ke basu haushi, kawai yara ne 拼an boko ke mulkarsu, a sai蓳ance suka 蓷aga kawunansu suka ce "E ranki shi da蓷e."
Jakadiyarta ce ta 蓷an matso kusanta ta ra蓷a mata "Ranki shi da蓷e, ba girmanki bane shiga madafa bayan ga mu, ki umarcemu da komai kike so a dafa za mu iya."
茒aga mata hannu tayi tace "Ba bu茩ata, ni aura ba ku ba, akan me ku ne za ku kula da abincinsa?"
Maida dubanta tayi ga masu girkin tace "Zan iya samun makulli nima?"
Da sauri namijin nan ya laluba aljihunshi hannaye na mishi rawa ya ciro ya mi茩o mata, yadda hannayenshi ke rawa da ru蓷ewar da yayi har ya mi茩o mata makullaye dayawa haka yasa ta kallonshi sosai 蓷in nan, da sauri ya shiga cire 茩waya 蓷aya sannan ya mi茩o mata, 蓷an waiga kanta tayi ka蓷an inda jakadiyarta take, hakan yasa ta saurin kar蓳an makullin, a hankali ta fara takawa za su bar madafar.
Saida ta kai bakin 茩ofa ta juyo a nutse ta sake kallonshi ta nunoshi da yatsa tace "Ga bata makullayen, daga yanzu ita ce me alhakin bu蓷ewa da rufewa."
Wacce ta nuna suka kalla wato matar nan da ta fi su shekaru, 茩ura mata idanu yayi kamar dai yana son 茩arin bayani, hakan yasa Saleema 蓷aga girarta 蓷aya ta masa kallon "Me ye?"
Da sauri ya kalli matar ya bata makullayen ya sunkuyar da kanshi 茩asa, rusunawa matar tayi tace "Nagode ranki shi da蓷e."
Kallon ki shiga taitayinki ta mata tace "Ba haka kawai na dam茩a miki ba, sanin wanda ya shiga da wanda ya fita ne aikinki, ya zama duk wanda zai shigo nan to da saninki."
Jinjina kai tayi tace "Angama uwargijiyata."
Ficewa tayi a madafar ta barsu da zulumi da kuma tunanin me ye haka? Suna fita daga ciki matashin nan kai tsaye 蓳angaren gimbiya Kubra ya wuce. Ba wanda ya masa shamaki da shiga 蓳angaren har cikin falonta, dake tana waya sadda ya shigo, hakanne ya sa ta tashi ta shige 茩aramin falon tana sauraren 茒an-galadima da yace "Ranki shi da蓷e, yanzu haka gani gaban malam na sake dawowa, ya ce na baki za ku yi magana."
A nutse tace "Uhum!" Bakin gado ta zauna tana kallon kanta a madubi, inda malamin ke magana ta wayar yana fa蓷in "Allah ya taimaki gimbiya, uwar marayu gatan marasa gata, ranki shi da蓷e aiki fa ya tunkaroku."
Yatsina fuska tayi ta kya蓳e baki tace "Muje ga gundarin magana."
Ci gaba yayi da fa蓷in "Ranki shi da蓷e tun da aka 蓷aura aure da 蓷an-galadima ya zo min da bayani nake aiki akan lamarin nan, wallahi ranki shi da蓷e yarinyar nan *ba yadda zamuyi da ita*."
Da yanayin jin haushi tace "Kamar ya? Ita ta halicci kanta ne? Aljana ce ita? Ko mala'ika?"
A nutse yace "Ba ko 蓷aya ranki shi da蓷e, sai dai *baiwar Allah ce* ta gari kamar sauran salihan bayi, gimbiya! Duk wani 茩ulunbotona da 茩o茩arina akan yarinyar nan mun rasa hanyar da zamu tarwatsa ruhinta da gangar jikinta, ranki shi da蓷e tunda nake aikin nan ban ta蓳a cin karo da wanda ya gagareni ba, tunda nake a harkar nan ban ta蓳a ganin wata halitta da ake ba wa kariyar yarinyar nan ba, sannan..."
A 茩ufule tace " Ba wannan nake son ji ba malam, ta ina zamuyi nasara a kanta? Shi kawai nake son ji."
Numfasawa yayi yace" Ranki shi da蓷e a gaskiya ba wata dama daga yarinyar, sai sai dai akwai mafita."
A da茩ile tace" Me ye mafitar?"
茒orawa yayi da" Idan da zamu san abinda ke faruwa tsakaninta da sarki Abdus-samad, sannan mu samu zanin da suka kwanta a kanshi...ba wai kwanciya bacci ba, ina nufin zanen da sukayi mu'amular aure a kanshi, to zamu iya yin wani abu a kai, sannan..."
Shirun da yayi yasa ta fa蓷in" Sannan me?"
茒orawa yayi da" Akwai rubutun da zan turo miki anjima a dinga sakawa shi sarki a abun sha, da sannu zamu sake samunshi, idan mun jaraba ta waccen 蓳angaren bamuyi basara ba, to ta 蓳angarenshi sai mu samu tazgaron da muke bu茩ata."
Dogon numfashi taja tace "Duka abubuwan daka lissafa masu sau茩i ne gareni in dai bu茩ata za ta biya, saidai ina so ka bani tabbacin tasirin aikin, dan bana son tsaiko dayawa saboda rashin isashen lokaci."
Cike da bata tabbacin da shi kanshi bai da tabbaci a kai yace "Ai wannan karan aikin nan idan muka samu nasara a kai bana tunanin ko mala'ika ya sakko daga sama zai iya gano bakin zaren (wal'iyazubillah), bare wata 茩aramar yarinya da ko tafasa batayi ba bare ta 茩one."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Shikenan, ka bani nan da gobe, zan sa a samo mana zanin gadon, dan na fa蓷a maka yarinyar nan ba haka take zaune ba, a daren ranar da aka 蓷aura musu aure a ranar ya je gareta, shiyasa bana so muyi sanya."
"In sha Allah ranki shi da蓷e, zamu nuna mata mu a tafiye muka kwana." Da haka sukayi sallama ta aje wayar ta fito ta samu matashin nan da har yanzu yana zaune yana jiranta, tana fitowa ya 茩ara rusunawa yana mata barka da fitowa, zaune tayi cike da gadara tana kallonshi ta yatsina fuska tace" Uhum, me ya faru?"
茦ara sadda kanshi yayi yace "Ranki shi da蓷e, Allah ya taimaki gimbiya, dama wani labari ne ke yafe dani."
A ma茩oshi ta sake amsawa da "Uhum." 茒orawa yayi da "Ranki shi da蓷e akwai matsala, wannan sarauniyar za ta bamu matsala, dan kuwa nema take ta ruguza mana tsare-tsarenmu, yanzu haka daga madafa nake, kuma ita ce ta bu茩aci da mu je, ta kar蓳e makullin hannuna na madafar ta ba wa Mariya, sannan ta ce ba za'a sake fiddawa mai martaba abinci, ita da kanta ce za ta dafa."
Da sauri ta 蓷ago daga jinginar da tayi cikin 蓷aga sauti tace" Me? Ita ce ta fa蓷i hakan?"
Rusunawa yayi yace" Ita da kanta Allah ya ja zamaninki."
Girgiza kai tayi tace" Ba zai yiwu ba, wacexe ita? Yaushe ta zo gidan da har aa ta nemi canza mana tsari?"
Wani huci ta dinga saukewa tamkar ta yi gudu tace" Shikenan, gimbiya uwar mai gado ta san da maganar?"
Girgiza kai yayi a hankali yace" Bana tunanin ta san da maganar."
Jinjina kai tayi tace" Shikenan, ka je zan sake nemanka."
茒a hannu ya mata jinjina irin ta sarakai kafin ya fita a falon. Ita ka蓷ai ta dinga cika tana batsewa tana ayyana" Ina! Ba zai yiwu ba, wallahi 茩arya kike, ni nan sai na sa ki zama tamkar hoto a gidan nan, ba iko shine burinki ba? To zai gagareki sai dai kiyi kallo."
______________
Saleema kuma na falonta aka ma mai 蓷inkin iso, 茩asa ta zauna tana kwasar gaisuwa, saleema kuma duk sai ta ji ba da蓷i yadda babbar mace ke gaisheta haka, jakadiyar ce ta nuna matar tace" Alkah ya taimaki *uwar magaji*, mai 蓷inkin matan fada kenan, gimbiya uwar mai martaba sarkina ce ta ce na mata iso zuwa nan dan ta aunaki, saboda za ta tafi da kayan 蓷inkinki."
Gyara zamanta tayi a nutse tace" Shikenan, bismillah."
A nutse matar ta mi茩e tana aje jakar dake rataye a kafa蓷arta, mikewa Saleema ma tayi ta cire hijabin dake jikinta dan ta bata damar yin abinda ya kamata, sunkutawa tayi ta bu蓷a jakar ta ciro al茩alami da 茩aramin littafin da take rubuta awon sannan ta matso ri茩e da abun aunawa. Cikin nutsuwa ta dinga aunata tana rubutawa a littafin har ta kammala sannan ta kalleta a nutse tace "Ranki shi da蓷e ko akwai irin kalar da kike so a miki?"
Girgiza kai Saleema tayi tace "Ki yi kawai, ban da za蓳i."
Rusunawa tayi alamar girmamawa sannan ta shiga maida kayan a jakarta, cikin nutsuwa Saleema tace "Ko zan iya samun almakashi wurinki idan za ki sake dawowa?"
Kallonta tayi sai kuma ta ciro na cikin jakarta tace "Ga wannan ranki shi da蓷e."
Girgiza kai tayi tace "A'a, wannan ai na aikinki ne, ki kawo min wani dai."
Murmushi tayi tace "Ba komai wallahi, indai anfani zakuyi da shi ki ri茩e."
Kar蓳a tayi tace "Nagode." Fita sukyi a falon jakadiyar ta mata rakiya har zuwa 蓳angaren Gimbiya Ramlat.
茒akin baccinta ta shiga ta bu蓷a drower kayanta sabi da aka zuba jiya bayan an nunawa iyayenta, wata kyakyawar atamfa ta 蓷auka ta dawo kan gado ta aje hijabinta, a hankali ta shiga warware zanin atamfar sannan ta 蓷auki almakashi ta fara yankawa, komai tana yi ne a nutse ba hayaniya, haka take abun ta wani sa'ilin sai ta tsaya ta zubawa atamfar idanu tana jin kamar fa ta manta yankan sai kuma ta yanka har ta samu ta yanka riga irin doguwar nan dake saukowa zuwa gwiwa, sai dai tana jin dole ta aje idan mai 蓷inkin nan ta sake dawowa sai ta bata ta duba mata, dan ta san dole a samu kurakurai duba da ko can ma ba ta kammala abinda ta fara ba aka samu matsala sannan yanzu haka rabon da ta ri茩e almakashi da sunan yanka shekara sama da uku kenan.
*FADA*
Sosai ya rintse idanu yana sauraren jawabin tsohon dake neman adalci ido rufe, ba tare da ya tsagaita da kukanshi ba ya ci gaba da fa蓷in "Wannan ki蓷e-ki蓷en ba komai suke haddasa mana ba sai masifa, domin kuwa idan aka saka ki蓷an nan mata suka fara rawa, ko kiran sallah basa ji bare su tuna kiran ubangijinsu, a matsayina na babba mai hankali yasa na musu maganar ya kamata a kashe haka kowa ya je yayi sallah, duba da su kansu mawa茩an maza ne majiya 茩arfi, amma sun saka matayen mutane gaba suna kallo suna ti茩ar rawa, kawai yaran nan marasa mutumci suka dinga min ihu a kunne har wata fitsararriya ta dinga zagina wai ni magulmaci munafiki ina ruwana? 茦arshe fa yarinyar nan jifana tayi da takalminta ta watsa min ruwan leda a jiki...tunda na ke ba'a ta蓳a cin mutumcina irin haka ba sai yau, shiyasa na garzayo na zo wajen uba mai share kukanmu, baya