Showing 165001 words to 168000 words out of 191031 words

Chapter 56 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67994

kaffa-kaffa da ita, wuri ta samu ta zauna tace "Aunty Saleema dama na zo muyi magana ne?"

Kallonta tayi, ko da ta ji ta ce aunty ta san bu茩ata ce da ita, dan haka ta tashi zaune ta maida hankalinta kanta tace "Ina jinki Hadeeya, me kike so?"

Da jin kunyar tambayar da ta mata ta sunkuyar da kanta, ganin tayi shiru Safiya ta mi茩e tace "Bari in baku wuri ko?"

Da sauri Hadeeya tace "A'a Aunty za ki iya zama."

Girgiza kai Safiya tayi tace "A'a, ke dai bari na baku wuri, magana ce ta yan uwa ai."

Ficewa tayi a 蓷akin lokacin Hadeeya ta 茩ara kallon Saleema tace "Aunty, kin ji komai da Abba ya fa蓷a a gaban yalla蓳ai mijinki, amma ban ji ya ce komai ba, dan Allah aunty ki taimaka min ki masa magana ya sakoshi, kinga fa ina son komawa gidana kuma ga su *Saudat* a hannun kakaninsu suke sam ba sa jin da蓷in zaman can din 蓷in, dan Allah aunty ki taimaka min."

Zuba mata idanu tayi tana kallo na tsawon lokaci kafin ta girgiza kai tace" Ki yi ha茩uri Hadeeya, gaskiya ba zan iya hakan ba."

Marairaicewa tayi tace" Saboda me aunty? Ni fa 茩anwarki ce, kina jin da蓷in ganina a gidan nan haka ni ba mai aure ba kuma ba bazawara ba."

A sanyaye ta girgiza mata kai tace" Bana jin da蓷i gaskiya, sai dai ba abinda zan iya yi miki Hadeeya."

Fashewa tayi da kuka ta tashi da gudu ta fita daga 蓷akin tana fa蓷in" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! 茒an uwa ba zai iya taimaka maka ba?"

Da murmushi Saleema ta bita da kallo sannan ta ta蓳e baki ta sauko daga kan gadon ta nufi shiga ban蓷aki dan gabatar da abinda Mama ta sakata, shigarta kenan ta cire rigarta tana 茩ara kallon lallen da Maman ta kwa蓳a na hausa da ruwa ruwa ta ji sallamar Ardiya, towel ta 蓷auka ta rufo a jikinta sannan ta fito tana amsa sallamar da cewa "Aunty."

Wani washe mata baki Ardiya tayi tana fa蓷in "Ranki shi da蓷e wanka ne ma za ki yi ko?"

Murmushi tayi ita ma tace "E Aunty, lafiya?"

Kallonta tayi a sanyaye tace "Saleema 茩anwarki ce gata can tana ta kuka ta ce ta miki magana amma kin ce ba abinda za ki iya yi mata, shine na ce tsaya na zo na ji ko me yasa kika ce haka?"

Sai kuma ta kamo hannun Saleema ta 茩arasa fito da ita daga ban蓷akin ta zaunar da ita bakin gado sannan ita ma ta zauna, ita fa bata so sai maganar Zeid ta kaisu ga zuwa fadar nan ne, dan haka take so a yi maganar tun nan gida a 茩are, gashi ganin Hadeeya a gida kullum suna fa蓷a ita da Hamdeeya abun na bata haushi dan gani take Safiya dariya kawai take musu tana yama蓷i蓷i da su a gari, dan haka za ta sauko ta zubar da ajinta da wayewarta ta ro茩i wannan yarinyar a karon farko na rayuwarta.

Zaunawa tayi ita ma suna kallon juna cike da rarrashi tace "Saleema, kinga a gidan nan ke ce babba, kuma dukanmu muna saka rai ko bayan ba ranmu za ki iya tsayawa kan 拼an uwanki, ki yi ha茩uri ki manta da duk abinda ya faru, kinga 拼ar uwarki tana ta zama gida haka ba da蓷i, idan kika masa magana na san tasirin da kike da shi a rayuwarsa zai sa ya mana wannan alfarmar, dan na fi ki sanin irin muhimmiyar rawar da mace ke takawa ga rayuwar da ta shafi mijinta."

Ajiyar zuciya Saleema ta sauke tace" Aunty, na san da haka nima kuma na san zai iya yi min komai idan na nema, sai dai ku gane inda matsalar take, aunty bana da hurumin shiga abinda ya shafi mulkinsa, wannan hukunci ne da ya zartar bai kamata ni ko wani nawa ba mu masa katsalandan a ciki, yin haka fa kai tsaye shine cin hancin da yake lalata mana al'umma..."

Numfasawa tayi tace" Aunty ba wai ba zan iya yi ma Hadeeya wannan alfarmar bane, zan fi kowa farin ciki a ce tana gidan mijinta kuma cikin farin ciki, sai dai gaskiya ba zan nemi alfarma a gurinsa wacce na san idan ya min ita to zai sa蓳a a茩idarsa tare da tauye kansa saboda jin naiyina dana ahalina ya mana ita ba, kuyi ha茩uri aunty idan na 蓳ata muku rai."

Ta 茩asan idanu ta fara aika mata harara kafin ta saki murmushin ya茩e tace" Kin gane 拼ata? Ba wai kai tsaye za ki masa maganar ba, ke fa mace ce mai kissa da 茩walisa, idan kika so lamarin nan ta 茩wayar idanunki kawai za ki aika masa da sa茩on abinda kike so ya isar miki, kuma fa ba wani babban laifi suka aikata ba, fa蓷a ne tsakanin mata su kuma suka shiga dan rabasu."

茦ara ri茩e hannunta tayi gam-gam tace" Dan Allah Saleema ki taimaka kinji kisa baki, kuma ke ma ai gimbiya ce kin isa yanke hukunci a masarautar nan."

Fuskarta ba yabo ba fallasa tace" Hakane aunty, amma fa ina da damar hukunci ne akan abinda nake da hurumi, ba wai yanke hukunci akan hukuncin sarkina ba, idan ni ce na yanke hukunci da fari zai iya yankewa a karo na biyu saboda ya isa ta kowane fanni, sarki ne shi kuma shugabana ne shi, amma ni kam ban da wannan damar gaskiya, kuyi ha茩uri aunty."

Ta 茩asan idanu ta sake hararenta sannan ta mi茩e tsaye tace" Shikenan, na san ai da ciki 蓷aya kuka fito da kin sa an saki mijinta, da kuma ni na haifeki da ban isa na zauna a nan ina miki magiya amma ki kasa saurarta ba, nagode."

Da kallo ta bita har ta fice a 蓷akin sannan ta girgiza kai dan ta san dama ba zasu fahimceta ba bare har su mata shaidar arziki, saidai akan haka ba fa za ta ta蓳a shiga hurumin da ba nata ba gaskiya, shi kanshi ba zai ji da蓷i ba idan ta yi, idan kuma ya zo ya musu kafiya to ribar me suka ci, sun zubar da mutumcinsu sannan basu samu biyan bu茩ata ba? Ba riba kenan.

Tun aurenta za ta iya cewa yau ka蓷ai ta kasance cikin walwala saboda sakewar da tayi a gidansu, tayi farin ciki tare da mahaifiyarta da 茩aninta, dan Ardiya fita tayi daga gidan haka ma Hadeeya, hakan yasa gidan ya musu da蓷i ba kadan ba. Sai dai duk da haka kewar mutumin nan ta addabeta, hakan yasa duk sanda ya samu sarari to suna ma茩ale a waya, sai dai kuma rabin wayar tasu fa蓷ansu ne suke 蓷orawa, dan kiran farko ma da ya mata tana 蓷auka cewa tayi "Uhum! Rashina na wasu mintuna har ya sa ka fara kirana ne?"

Sai kawai ya buga kai ga kasa yace shi fa sam ya kirata ne dan ya tambayeta ko zai samu abinci daga wajenta? Yanzu ma da ya kirata cewa tayi dan fa yana shine ta 蓷aga, tund aya ce ba 茩aunar ta yake ba me ye kuma na kiranta a kai a kai? Shi ma ya ce dan Ummi ta ce ya dinga kiranta ne shiyasa ya ke kira. Haka dai har dare ya mata a gidan bayan ya nutsu ya shirya ya zo 蓷aukarta.

Saida ta shigo motar kafin ta lura da kayan dake jikinshi, waro idanu tayi ta 蓷aga murya tace "Wai da kayan nan ka fito daga gida?"

Tsareta yayi da idanu yace "E, me ye?"

Rumgume hannaye tace "Ba komai, ina mamaki dai ne."

Murmusawa yayi ya tayr da motar suka bar gida, kallonta ya sake yi bayan sunyi nisa yace "Matanmu, zamu iya zuwa cin abinci? Yunwa fa nake ji, kuma kinga yau haka kika manta dani gaba蓷aya."

Da sauri ta kalleshi tace "A'a gaskiya, ni ban ta蓳a zuwa cin abinci ba wani wuri, kuma ma ko zan je ba da wannan babbar rigar ba."

Kallonta yayi yace "Ban gane ba? Ba dai nufinki sai kin cireta ba?"

茒aga masa gira tayi alamar e, girgiza kai yayi yace "A'a wallahi." Ci gaba sukayi da tafiya ba jimawa ya faka motar a gidan abinci na Rosario kasancewar sun fi kusa da nan, bai fita a motar ba sai ma wayarshi da ya shiga daddanawa kamar ya manta a inda suke, ita kuma tana kallon motocin dake laye a wurin da alama su ma suna cikin gidan cin abincin.

Mutum biyu ta ga sun fito daga gidan cin abincin 蓷auke da runfar nan ta kakkauran leda mai kwalliya, a kusa da inda ake faka motocin taga sun aje suna 茩o茩arin yi mata masauki, a nutse suka kafa ginshi茩anta har runfar ta tashi tsaf, da sauri suka koma gidan abinci 蓷aya na 蓷auke da kujeru biyu farare 蓷aya na 蓷auke da teburin shima fari 茩ar na roba, suna komawa ciki mace 蓷aya da namiji 蓷aya suka fito da farantai a hannayensu suka 茩awata wurin da abinci da abun sha, a daidai lokacin manager wurin ya fito kai tsaye motarsu ya tunkaro.

Fita yayi daga motar bayan sun yi musabaha taga suna magana kafin ya koma ciki shi kuma ya zagayo ya bu蓷e mata ta fito.

Yanayi mai da蓷i tare da wanda zuciya ke so, hakn yasa duka fuskokinsu 蓷auke suke da 茩asaitaccen murmushi dake kwantar da hankalin junansu, sake kallonshi tayi a karo na adadi tana murmushin daya fito da ha茩oran makarta tace "Nagode *mijina*."

Ba tare da murmushi ya bar fuskarshi ba yace "Ba komai matanmu, kin cancanta ai, ya kamata ke ma kisan kina aure, ba kullum a takure a fadar masarauta ba da kuma alkyabba."

Wani farrr tayi da idanu tace "Gaskiya kam, na ji da蓷i sosai."

A haka suka kammala cin abincinsu ba hayaniya kuma babu hasken fitila cike da nisha蓷i kafin su bar nan su koma gida.

Kwana biyu kenan amma har yanzu bai sake tada mata maganar da Abbanta ya mishi ba kuma ba ta ji labarin ya sakesu ba, dan haka ta ba maganar baya kawai, shi kuma ya yi shiru ne kwana biyu ya ga ko za ta masa maganar, amma kuma sai ya ji shiru hakan yasa shi 茩ara girmama lamarinta, har yau da yake zaune gaban mahaifiyarshi cike da ladabi yace "Ummina, kin san da yarinyar nan 拼ar aljanna ce ko?"

Duk da ta gane da wa yake, amma sai ta share ta kalleshi tace "Wace yarinya kenan Babana?"

茦asa yayi da kanshi yace "Ummi wace yarinya kuwa face wacce ta kafa mana tarihi."

Da sauri tace "Ohhh! Saleema wai? Ai sosai ma, shiyasa na za蓳a maka ita."

A sanyaye yace "Ummina, me kika sani game da ita? Ina so na tambayeta amma kunya ke hanani."

Da mamaki ta kalleshi tace "Kunya kuma? Akan me?"

Ajiyar zuciya ya sauke yace "Sai nake ganin kamar ba za ta ji da蓷i ba idan na tambayeta labarin rayuwarta."

Murmushi tayi tare da ci gaba da damun furarta tace "Ban san abu dayawa a kanta ba, saidai bayan zuwanta nan muna hira sosai, a nan ne na san abunda na sani a rayuwarta ta baya, Saleema dai ta taso a gidan..."

A ta茩aice ta bashi labarin rayuwarta har zuwa wayarsu da Saleema ta 茩arshe wacce take fa蓷a mata mahaifinta zai mata auren dole, dalilin da yasa kenan suka shirya da yayanta da kuma 蓷an uwan mahaifinshi aka nema mishi aurenta a 蓳oye saboda kada masu hana ruwa gudu su shiga lamarin.

Sake kallonta yayi ya saka hannayenshi biyu ya fara matsa mata 茩afafunta wanda ya jima bai mata haka ba sai Saleema ce ke yi yace "Ummina, amma dai kinsan wallahi Allah ne ya ceceni ya wanke yarinyar nan ya bani, yanzu fa da ta auri waccen na farkon da aka saka musu rana?"

Sai kawai a zuciyarshi ya ayyana "Rabona."

Dariya tayi tace "Ai dan tana taka ce shiyasa ma lamarin ya wargaje."

A hankali ya ci gaba da matsa mata 茩afafun ita kula tana damunta yace "Ummina, ranar ma fa haka na sameta ta gama yanka wai ita 蓷inki take yi, Ummi ba kya ganin ya kamata muyi wani abu game da burin nan nata?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi tace "Nima na yi tunanin haka, amma kasan gidan nan da kuma matsayinka, zai sa a yi ta 茩ananan maganganu, shiyasa ma ban maka maganar ba, ni dai karatu ne dama na ke cewa zan fa蓷a maka ina so mu fara da ita."

Shi ma fuskarta ya kalla yace "Ummi makaranta za ki kaimin iyali?"

Murmushi tayi tare da hararenshi tace "Tun farkon zuwanta gidan nan fa na fa蓷a maka, ina so ta dinga koya min karatu."

Murmushi yayi ya sadda kanshi yace "Ba damuwa Ummi, za'ayi, za'ayi komai da kike so, kawai ki mana addu'a, amma bai kamata mu bari burinta ya ruguje ba."

Zumar dake gefenta cikin kwalba ta 蓷auka ta tsiyaya a cikin furar sannan ta 蓷auki gorar dake 蓷auke da kakkaurar madarar ta zuba sannan ya juya ta mi茩o masa, kar蓳a yayi tare da gyara zama ya aje tasar gabanshi sosai ya fara sha da bismillah.

Lumshe idanu yayi yana murmushi yace "Ummi, wato a duk duniya har yanzu ban samu wacen ta kaiki iya damun fura ba."

Murmushi tayi tace "Har *瞥ar Baiwa*?"

Zuba mata idanu yayi kamar da mamakin ya take son 茩ureshi haka? Sai kuma yayi murmushi, hakan yasa ta dungure mishi kai ta 茩yal茩yale da dariya tace "Ja'irin yaro, wato na kamaka?"

Dariya yayi ya sunkuyar da kai yace "Ummi, da na gama shan furar nan gyara 茩afafu za ki yi na kwanta na yi bacci, na jima ban samu haka ba ina so kuma yau hutun nan da na samu in yi shi a tare da ke."

Da farin ciki da kuma jin da蓷in hakan tace "Karka damu yarona, ka samu ai."


*Ba ta* san shirin me yake ba a kan ta, ita dai ya tsareta gabanshi ya dinga tambayarta me da me ta koya game da harkar 蓷inki a farko? Sannan me ta fi iyawa? Wata nawa ta yi? Ta iya kaza da kaza? Haka duk ta amsa mishi kafin ya tura cikakkun bayanai wa mutumin da yake son 蓷orata a inda ta tsaya. Yau kuma da ya bata babbar wayar tablet dole ya fa蓷a mata ya biya ku蓷i ne a koya mata 蓷inki, dan haka ta kula ta maida hankali dan ta waya ne za'a 茩arasa koya mata kamar yadda mai dinkin ya ce in sha Allah ba zasu jima ba tunda duk abubuwan da ya tambaya ta ce ta koya kuma ta iya wasu ne take cewa ka蓷an ya rage ta koya aka samu matsala ta dakata.


A tafiyar mulkinshi kuma saida aka 蓷auki cikakken sati biyu kafin ya nemi jin ta bakin Inspecteur 蓷in da tun farko ya sa a kawosu Sharha gabanshi, bincike yasa aka yi mishi gale su idan suna da wani tsohon case a ofishin 拼an sanda ko babu? Hakanne yasa Zeid da biyu daga cikin 拼an matan da kuma biyu a cikin mazan aka sallamesu ya zama sai su hu蓷u ne aka mi茩asu hannun jami'an tsaro aka ce a kaisu kotu kawai, musamman 蓷ayan ma da aka ce an kamashi da laifin siyar da 茩waya ne sai Sharha kuma da aka sameta da laifi har biyu na yi wa wasu mummunan rauni har yake sa ana rufeta. Babban abinda ya sake 蓷aga masa hankali da tunzurashi game da lamarin Sharhasila har ya umarci da lallai a gaggauta kawar dasu daga gabanshi kafin ya ari takobin 蓷anbaka ya cire kanta shine, a takardun case 蓷in da aka kawo 蓳aro-蓳aro ya ga sunan Haleematu Yusuf da kuma sukan Alhaji Yusuf Jiji wanda alamu suka nuna mishi su ma dai daga 茩arshe rufe case 蓷in aka yi. *Tabbas* ba zai manta ranar da suke kwance da ita ba dake bras ce ka蓷ai a jikinta ya ga 蓷an shatin ciwo a cikinta kusa da cibiya ya tambayeta ta ce ciwo ne kawai, wato wannan she蓷aniyar ce ta so halaka masa mata.

Da kakkausan yanayi ya kalli Inspecteur 蓷in sannan yace "Ba dan iyalina ba, sai dai sauran al'umma, wannan yarinyar za ta iya zama gobara a cikin mutane, ko waye ubanta, ko wa ye ke tsaya mata, wannan karan da kaina zan ja shari'ar daga nan har duniya ta tashi, amma sai na tabbatar da ta kar蓳i hukuncin da ya dace da laifin da take aikatawa."

Wannan magana ta sarki ta toshe duk wata 茩ofar da mahaifin Sharhasila zai bi dan ku蓳utar da yarinyar, duk inda ya nufa sai a ce ai sarki ya sa baki a maganar ba abinda za'a iya yi masa, dan harka ce ta iko kuma sarakunan gargajiya na da tasiri sosai a al'ummarmu sannan suna da ikon fa蓷a-aji, hakan yasa babu yadda ya iya da ya wuce ha茩uri da lamarin da kuma zubawa sarautar Allah idanu, sai dai kam ya yarda wannan karan Sharha ta ta蓳o *ubansu* daga ita har shi 蓷in.




*Alhamdulillah.*
29/06/2022 脿 15:29 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_54_




*Bayan Wata Uku*: Da hanzari ya 茩araso yana aje babbar envelope 蓷in dake hannunshi ya dafa kafa蓷arta yace "Subhanallah! Matanmu lafiya? Me aka miki kike kuka?"

Ture hannunshi tayi daga kafa蓷arta ta mi茩e tsaye tana kallonshi tace "Abdul kana sona ko a'a?"

茦an茩ance idanu yayi ya gyara zamanshi a hannun kujerar yace "Me ya kawo wannan maganar kuma?"

Jinjina kai tayi ta juya bayanta ta 蓷auki gyalenta tace "Na zan zauna 蓷in ba, ai dama cewa kayi muna zuwa nan zaka fa蓷a min komai dake ranka, shine da kaga ka raboni da 茩asar iyayena za ka wani yi banza dani."

Juyawa tayi kamar za ta fita daga falon gidan da suka sauka a Niamey saboda 茩arasa shirinsu na tafiya Umra, fizgo hannunta yayi da karfi har ta fa蓷a kanshi ta saki 茩ara, ido cikin ido suka kalli juna yace" Me ye? Dole ne sai na fa蓷i abinda bana ji? 茦arya kike so nayi?"

Turo baki tayi ta kawar da kanta tace" Ni ban damu ba, ko ma 茩aryar ce ka yi min dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login