Showing 36001 words to 39000 words out of 191031 words
sake magana har suka isa kasuwa shagon Alhaji Ibrahim, wanda Saleema ce ta san shi a nan suke siyan duk wank abu da ya shafi atamfa, leshi, shadda da sauransu, zaune take kan benci daga baki-bakin shagon, shi kuma ya na tsaye ya rumgume hannaye yana kallon duk wani motsinta, ita kam hankali na kan kayan da ake ta fito mata da su tana dubawa dan za蓳en wanda ya mata. Mu'az da ya kula da wani matashin da ke yawan kallon Saleema gyara tsayuwa ya yi yace "茦anena, sassauta mata kallon nan haka ka j, ka yi ha茩uri ka bar min ita ta wa ce, ka ga ni ma ba kulani take ba bare kai."
Tunda ya fara maganar ta 蓷aga kai tana kallonshi tana kallon matashin, sai da ya gama ta girgiza kai ta kalli yaron shagon da kunya ta kamshi yana ta sosa 茩eya tace" Yawwa wannan na ke so."
Nuna masa duk wanda ta za蓳a ta yi sannan ya jinjina kai yace" Bari na fa蓷awa Alhaji."
Shigewa ya yi ciki ita kuma ta kalli Mu'az tana sauke numfashi, shi ma kallonta yake da fara'a a fuskarshi yace" Ban san me yasa ba, amma dai haushi na ke ji idan wani na kallonki."
Fuskarta a ha蓷e tace" Ka daina wasar nan mana, na fa蓷a maka komai fa yanzun nan, sam ni da kai ba mu dace ba."
Sam babu alamar ya ji zafin maganarta ko makamancin haka, sai ma murmushi da ya sakar mata yace" A gaba za ki so ni, lokaci kawai ki ke bu茩ata na baki, kuma na baki daga nan har a 蓷aura mana aure."
茒auke kai tayi ta kalli mai shagon dake fitowa yana mata murmushi suka gaisa, nuna masa kayan ta yi ya lissafa ya fa蓷a mata tare da mata ragi sosai saboda sanayya, godiya ta masa bayan ta biya ku蓷in yaronshi ya 蓷auki kayan ya na saka mata a mota. Ba su yi nisa ba aka fara kiraye-kirayen sallah magriba, faka motar ya yi gefe ya kalleta yace "Matata, za ki iya jirana na yi sallah?"
Bu蓷a baki ta yi za ta yi magana sai kuma ya langa蓳e kai yace "Dan Allah madame, kar ki hanani, ke ce fa ki ka nuna min mahimmancin sallah kan lokacinta, shiyasa na ke 茩o茩arin kamantawa yanzu."
Sakin fuskarta tayi daga 蓷aurewar da ta mata ta saki murmushi tace "To shikenan, a sakamu a addu'a."
Bu蓷a motar ya yi zai fita yana fa蓷in "Tunda na ganki na ke addu'ar samunki, kar ki damu matata, addu'ata ta ki ce."
Saida ya rufo mata 茩ofar kawai ta saki wani sanyayyan murmushi tana girgiza kanta, gyara zamanta tayi sosai tana hangenshi bakin 茩ofar masallacin yana alwala, irin yanda yake sauri saboda an kusa tayar da sallah, amma kuma a nutse yake kamar ba jikinshi ke kazar-kazar 蓷in ba, ba ta gushe tana kallonshi ba har suka kabbara sallah.
______________
Da sallama dattijuwar ta shigo 蓷akin, a sanyaye ya amsa yana tashi zaune, cike da ladabi ya kar蓳i kwanon hannunta yace "Mama da kan ki? Ina su Fareeda?"
Saida ta zauna tana fuskantarshi kafin tace "Suna can suna aikin da aka saba, ka san asabar 蓷in nan uta ce ta farkon hutun makaranta da aka shiga, dan haka akwai bukukuwa da dama."
Jinjina kai ya yi yace "Hakane, amma Mama ai da ba ki kawo min da kanki ba."
Irin kallon nan na manya ta aika masa tace "Na kawo maka da kaina ne saboda a gabana na ke so ka ci ka bani kwanon."
Cike da kunya ya sosa 茩eya yace "Mama, Allah za..."
Dakatar da shi tayi da hannu tace "Ka ga Huzeifa, ka ci abincin nan yanzu ko ranka ya 蓳ace."
Sunkuyar da kanshi 茩asa ya yi tare da talla蓳e ha蓳arshi, bai san ta ya zai kwatanta ma mahaifiyarshi ba ya sha'awar cin komai ba? *Allah sarki, Allah ji茩an Babanmu*! Wannan zazza茩ar murya ita ke masa amsa-kuwa a kunnuwa, sahihiyar fuskarta mai cike da kamala da haiba, tsintar kanshi ya yi da murmushi shi ka蓷ai a zaune.
Mahaifiyarshi da ta 茩ura masa idanuwa ta na jiran ya ci abincin ta ga shiru, a 茩arshe sai ganin ta yi ya 蓳ige da murmushi shi ka蓷ai, cike da kulawa tace "Huzeifa."
Zunbur ya kalleta dan ya manta a gabanta ya ke, da sauri ya kalleta ya 蓷an rarraba idanu yace "Ah...ahhh, na'am Mama."
A tausashe tace "Me ya ke damunka?"
Girgiza kai yayi kanshi 茩asa yace "Ba komai Mama."
茦ara gyara zama ta yi sosai tace "Huzeifa, kada wannan jarabawar ta sa ka illata kanka, ka daina cin abinci gaba蓷aya, kullum karatu ba ka da lokacin hutu, 蓷an lokacin da ba karatun ka ke ba kuma 蓷inki ka ke yi, kana ganin hakan ya yi dai-dai? Ba ka tsoron ulcer 蓷inka ta tashi?"
Kallonta ya yi a ladabce yace" Ki yi ha茩uri Mama, in sha Allah zan kiyaye, ai komai ya zo 茩arshe tunda an gama."
Cike da tabbaci tace" An gama, amma jiran tsammanin sakamakon shi yake jefaka a halin tunanin nan, me zai hana ka bar wa Allah za蓳i, idan ka yi nasara ka gode masa, idan ba ka samu ba ka gode masa ka kuma duba wata hanyar ka bi."
Ajiyar zyciya ya sauke ya jinjina kai yace" Hakane Mama, in sha Allah zan yi yanda ki ka ce."
"Allah yasa." Ta fa蓷a tana kallon kwanon abincin tace "Maida hankali ka ci abincin."
"To Mama." Ya fa蓷a yana jawo kwanon dan ba ya son yin musu da ita, saida ta ga ya fara jefa abincin ka蓷ai ta bar 蓷akin tana sake jadadda masa za ta zo 蓷aukar kwanon da kanta, maza ya cin ye duka kafin ta dawo.
茦arar da wayarshi ta yi yasa ko amsa mata baiyi ba ya du a wayar, wani iska ya feso daga bakinshi ganin Sharhasila ce, 茩urawa lambar idanu yayi da tunanin ya 蓷auka? Dan tun da ya fara zana jarabawar nan bai kirata ba saboda zafi da kanshi ya yi, yau ne ya gama yake tunanin zai je gidan dan su ha蓷u saboda 茩ara 茩aratowar lokacin bikinsu, gashi kuma ta kira bai san dalili ba.
茒auka ya yi ya kara a kunne yana sallama, a ta茩aice ta amsa wa "Alaika salam, Baby shine ka manta da ni ko kirana ba ka yi?"
Lumshe idanu yayi kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya numfasa cikin nutsuwa yace "Ban manta da ke ba, zan zo gidan yau."
Cike da shagwa蓳a da kuma sakarci tace "Ka ga ni zan zo, zan zo gidan na ku, ina son ganinka ne."
Waro idanu yayi a sau茩a茩e yace "Gidanmu kuma?"
Turo baki tayi ta amsa da "E, gidanku, na yi kewarka Baby."
Dafe gaban goshonshi yayi yace "Ba sai kin zo ba, ni zan zo anjima, kin ji?"
Cikin shagwa蓳a tace "Ka yi al茩awari?"
"Na yi." Ya fa蓷a a tausashe, murmushi tayi wanda saida ya ji sautinsa a kunnuwa tace "To Baby ka taho mana da ice cream, ni zan ba ka wani abu idan ka zo."
Rufe idanu yayi yana mamakin wauta irin ta Sharhasila, "To." Kawai ya fa蓷a yana 蓷auke wayar daga kunnenshi ya aje ya ci gaba da cin abincin.
*Ga mai son shiga grp 蓷ina ya tuntu蓳i wanda ke musu post zai samu kanshi a ciki in sha Allah.*
*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:41 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_16_
Fitowarta kenan daga wanka tana tsane jikinta da babban towel, su Hadeeya ta samu suna ta mitar aikin da sukayi na gyaran 蓷akin Papi wanda har kayan abinci sai da Alhaji Auwal ya sa aka canza musu wuri aka maidasu madafa, Ummee haushi kamar zai kasheta da tana aikin, yanzu haka duk a gajiye suka kwanta har 茩arfe 11:00 ta yi.
Kayan baccinta ta saka ta zauna bakin gado tana addu'o'in da ta saba yi, ta shafe jikinta kenan za ta kwanta aka 茩wan茩wasa 蓷akin, mi茩ewa tayi da niyyar bu蓷ewa dan Hameeda tsaki ta ja tana fa蓷in "Daren ma ba za'a bari mu huta ba."
Ta kai hannu za ta 蓷auki hijabinta aka turo 茩ofar, ido hu蓷u sukayi da Mu'az da yayi turus yana kallonta daga 茩asa har sama, bakinshi bu蓷e ya kasa furta ko a, hankali ya lalubi idanunshi ya rufe dan in ba haka ba zai mutu a tsaye. Sa'a 蓷aya ta yi saurin rarumo hijabi ta rufe jikinta ba tare da ta sanya ba, sosai kunya ta kamata ta sadda kanta 茩asa, riga da wando ne jikinta na bacci, rigar ta na da hannaye iya damatsenta, saidai ta fito mata da surarta, haka ma wandon duk da bai kamata ba, amma tsayinshi iya bakin gwiwoyinta ne.
Hadeeya da ta mi茩e zaune ce tace "Yaya, lafiya?"
Bu蓷a idanunshi ya yi ya kalleta sai kuma ya yi gyaran murya yace "Ughym! Umm..ammm...! Dama jarabawarku ne ta fito, na zo na ji lambobinku ne dan na duba muku."
Da sauri Hadeeya ta taso tana fa蓷in "Yawwa, Yaya ni lambata 4452..."
Saida ya saci kallon Saleema da ta wanka masa harara ta ja tsaki ta koma ta zauna kan gadon kafin ya turawa abokin na shi lambar da sunan Hadeeya ya duba masa, cikin 茩an茩anin lokaci aka fa蓷a masa Hadeeya da Ummee sun samu har ma da Hameeda da ita ta zana jarabawar ne kawai amma ba ta kai ga ajin ba (candidate libre), cikin 茩an茩anin lokaci 蓷akin ya hargitse da ihu da shewa na 拼an matan, da gudu suka fita dan sanar da iyayen da har yanzu suke zaune a falo suna kallo suna hira.
A hankali ya tako ya zo gabanta cikin sanyin murya kamar mai tsoronta yace "Saleema, lambarki?"
A zafafe tace "Ba na bu茩ata malam, ka ga shigo mana 蓷aki da ka yi ma ba tare da an baka izini ba ya isa, dan haka kar ka hassalani dayawa."
Kawar da kai tayi tana sake ha蓷e fuska sosai ita dole ya 蓳ata mata rai, dur茩usawa ya yi niyyar yi dan ci gaba da bata ha茩uri, haka kawai ya ke jin ranshi ba da蓷i saboda ranta ya 蓳ace, da sauri ta jaye 茩afafunta dake kusa da shi tana 蓷an galla masa harara, mi茩ewa yayi tsaye yace "Ki yi ha茩uri Saleema, na shigo ne dan na ga baku jima da shigowa 蓷akin ba bare a ce har kun kwanta, amma ai na 茩wan茩wasa 茩ofa, kuma sai da na 蓷an jinkirta kafin na shigo, tunanina hakan ya ba wa wacce ke farke damar kimtsa jikinta."
Sake marairaicewa ya yi yace" Saleema, ni fa ba kowace mace ke birgeni ba, ba kuma kowane tsiraici na ke son gani ba, tunda na ke a rayuwata ban ta蓳a jin ina son wata 拼a mace ba sai ke, ke ce mace ta farko da na ji ina so na yi rayuwar aure da ita, ke ce macen da na ji ina sha'awar ta zama uwar 拼a拼ana, Saleema..."
Yanda ya kira sunanta yasa ta 蓷aga kai ta kalleshi, ci gaba ya yi da cewa" Tabbas 茩arya na fa蓷a idan har na ce surarki ba ta birgeni, amma ki sani na yi tarayya da mata da suka fi ki kyau da wayewa, sai dai ba su min ba saboda sun rasa *aji*, a gareki ne na fahimci duk wata mace mai aji, to tana tare da *kamun kanta*, wallahi abu 蓷aya ya sa na ke sonki da aure, wannan abun kuma shine *tarbiyya*, ina da ya茩inin tarayyata da ke za ta zama tsanin hawana hanya madaidaiciya, kamar yanda na ke da tabbacin zuri'ata indai ta tsatsonki za su fito, to za su zama abun alfaharin kowa, sannan na zama uba ma fi dacen 拼a拼a a duniya."
Da sauri ya dur茩usa gabanta yayi tsugunno irin na maza yana kallon fuskarta kamar yadda ita ma take kallonshi da 茩yar take 茩yaftawa yace" Saleema, ki nemi za蓳in ubangijinki a kan lamarina, kar kiyi gaggawa dan ni ma ba zan yi ba, duk da kuwa ina matu茩ar son yin aure saboda wani babban dalili, idan har kika ji kin gamsu za ki aureni, to ki sanar da ni a ko da yaushe, ni kuma na miki al茩awarin fa蓷a miki komai a game da ni, har da ma wanda iyayena kansu ba su sani ba, dan bana so mu fara zama na gaskiha ba tare da kin san wannan abun ba, dan gaskiya ba na jurar matsala daga abun da na ke so, musaman ma..."
Saida ya yi 茩asa da kanshi kafin yace" Musamman ma ke, wallahi zan iya miki kuka idan kina hushi dani."
Da sauri ya 蓷ago ya kalleta yace" Kin gane? Ni kwata-kwata ban saba da rayuwar wahala ba, ban ta蓳a jin abu ya birgeni lokaci 蓷aya ba kamar yadda kika shiga raina, an reneni cikin gata da bani duk abin da na ke so, dan Allah Saleema kar ki hana min kanki a karon farko na rayuwata."
Bu蓷a ido tayi da kyau tana kallonshi, 蓷an jan hijabinta tayi ta 茩ara rufe 茩afafunta da take jin ta kamar a tsirara, ba tare da ta 蓷auke dubanta gareshi ba tace" *Aku*, aku sarkin surutu."
La茩ace mata hanci yayi yana dariya yace" Ke ma da kin aureni za ki koyi surutu."
Da sauri ya mi茩e tsaye yana sake fa蓷in" Yanzu bani lambar ta ki kema na sa a duba miki?"
Girgiza kai tayi tace" Gaskiya a'a, ina ji a jikina ma ban ci ba, ba sai ka wahalar da kanka ba."
Da mamaki yace" Me yasa? Ya za ki cire rai haka?"
Cike da jimami tace" Ka share kawai, nagode da kulawarka."
茒aga kafa蓷a ya yi yace" Shikenan, bari na canza kaya sai na je na dubo miki."
Da mugun sauri ta mi茩e tsaye har tana sakin hijabin ya zube 茩asa ta yi ram da rigarshi tana fa蓷in" A'a, a'a dan Allah kar k..."
Sai kuma ta saki rigarshi ta ja baya tana dur茩usawa ta 蓷auki hijabin kanta 茩asa cike da kunyar abun da ta aikata, ganin ta yi shiru babu ma alamar za ta ce 茩ala sai kawai ya fita shima ya na ji a ranshi lallai lallai dole ya dinga nisantar yarinyar nan dan gudun samun matsala, dan in dai zai dinga ganinta a haka, sannan har wani dalili ya sa su ha蓷a jikinsu, to fa tabbas komai na iya faruwa a yadda yake tsananin son yin aure dan ya ci halalinsa.
Da farin ciki Hameeda ta shigo 蓷akin tace "Abba ya ce ki zo."
Ba ta amsa mata ba ta mi茩e bayan Hameeda ta fita a 蓷akin, zane ta 蓷aura a kan wandon sannan ta saka hijab 蓷in ta fito, falon ta samesu suna ta murna inda ta ji Ummeeta na fa蓷in "Gaskiya Abba ni dai 茩aton sa za'a yanka min, 茩awayena su ci nama su 茩oshi."
Tana 茩arasowa ya kalleta yace "Saleema ke ba ki fa蓷a mana sakamakonki ba?"
A sanyaye tace "Abba da safe zan je da kaina na dubo."
Da mamaki yace "A'a, me yasa to? Gashi a sau茩a茩e Yayanku na diba muku."
A ladabce tace "Abba na fi so na duba a can."
Kallon Amarya ya yi yace "Ai ina tunanin 拼an Bac ma gobe ake fito musu da sakamako?"
Saida ta yatsina fuska ta kalli Saleema tace "Haka ake saka rai."
Jinjina kai yayi yace "To shikenan, Allah kaimu goben sai ki je tunda haka kika fi so."
Juyawa tayi ta koma 蓷aki ta kwanta gaba蓷aya take ji a jikinta kawai ba ta samu ba, amma dai za ta je dan ta samu tabbacin haka.
*Washe gari*
Ta jima wajen Papi suna hira tana fa蓷a masa wani abu da ya zo kanta daren jiya kafin bacci ya 蓷auketa, ganin ta samu goyon baya 蓷ari bisa 蓷ari sannan ta fito daga 蓳angaren na shi ta nufo falon dan 蓷aukar jakarta ta tafi makaranta dubo sunanta. Kai tsaye madafa ta nufa ta samu Nafissa da amarya suna aiki, 蓷an kama musu tayi saboda Nafissa take so ta ma magana, tana ganin Amarya ta bu蓷a mangaza ta ra蓷awa Nafissa abu a kunne, kallonta tayi da mamaki tace "Kin tabbatar?"
Lumshe ido tayi alamar e tace "Ki yarda dani, ki 茩warara kanki."
A tsorace ta furta "Gaskiya ina jin tsoro."
Girgiza mata kai tayi ta ri茩e hannubta tace "Ki ji tsoron Allah kawai, yana tare da mu kuma zai taimakemu, saboda niyyarmu mai kyau ce."
Jin amarya na fitowa yasa Saleema raba hannunta da na Nafissa tace "Yawwa ni na tafi, sai na dawo."
Jinjina kai tayi tace "A dawo lafiya."
Da harara amarya ta bita tana ayyana "Allah raka taki gona, na san ma ba samu zakiyi ba tunda ba karatun ne a gabanki ba."
Amarya na idar da girki ta kira Ummee, tana zuwa ta bata abincin Papi ta ce "Ki kaiwa Baba 蓷akinshi."
Wani yatsina fuska tayi tace "Papi kuma? Ba ga Nafissa nan ba."
Rai 蓳ace amarya tace "Ke in za ki kar蓳a ki kar蓳a, doka ce kuma ubanki ya 蓷orata, in ba za ki kai ba na kira Mu'az ya kai sai na fa蓷a masa ke kin 茩i."
Da sauri ta finciko kwanon ta juya kamar za ta cira bakinta tana bubbuga 茩afafu ta nufi 蓷akin cike da takaicin me ye sai ita za ta kai masa abinci, tana shiga 蓷akin ba sallama dan ta nuna bata so ba fa, ajewa kawai ta yi ba ko ina kwana duk da yana zaune falon haka ta juyo ta fito, da kallo ya bita kawai ya girgiza kai a ranshi yace "Allah ya shiryaku."
Tare da dreba suka tafi makarantarsu, a kam ta samu 蓷alibai da dama da suma suka zo duba na su sunan, ba ta ;ata lokaci ba wajen fara duba sunayen da suka fara da harafin H, shiru babu alamar na ta sunan, haka ta dinga dubawa daga farko har 茩arshe amma babu, jiki a sanyaye ta koma gefe 茩ofar wani aji ta zauna ta tangale kanta da ginshi茩in wurin, sannu sannu ta ji idanunta sun fara kawo mata ruwa, kamar an daketa sai kawai ta fashe da kuka.
Cikin 拼an ajinsu ne wata ta dafa kafa蓷arta tace "Saleema."
茦in 蓷agowa tayi saboda ita ka蓷ai ta san me take