Showing 162001 words to 165000 words out of 191031 words
yau gashi idan tana tafiya harda jami'an tsaro a bayan motar da take ciki guda biyu baya ga dogarawa.
Zafin da ta ji kan kumatunta ta tabbatar da hawaye ne take, hakan yasa ta a hankali ta sakala hannunta ga nashi hannun ta 蓷ora kanta a kafa蓷arshi ta 蓷an ja majina, a nutse ya le茩a fuskarta ganin hwaye sun sauke mata yayi saurin 蓷agota yana tallabo fuskarta cike da tsantsar kulawa yace "Matanmu, me ye faru? Fa蓷an namu ya kai hakane?"
Da sauri ta girgiza kai a sanyaye tace "A'a, ba shi bane."
"To me ye?" Ya fa蓷a yana sake tsareta da idanu, 茩ara jan majina tayi dan hancinta ke neman 蓷umewa sannan tace "Falalar ubangijina nake tunawa, yadda ya min *BAIWA* sai na ke jin tamkar ni ka蓷ai ce a fa蓷in duniyar, shiyasa na yi nasarar wawushe komai."
Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jawota ya 蓷ora kanta a 茩irjinshi yana 蓷an shafawa a nutse yace "Shiii! Ki godewa Allah."
Jinjina kai tayi a zuciyarta ta furta "Alhamdulillah." Haka suka ci gaba da tafiya ba da gaggawa ba har suka isa 茩ofar gidan, motar dake gaba mai gadin ya le茩a suka 蓷an yi magana jim ka蓷an ya shiga ciki ya wangale musu 茩ofar ya koma gefe yana kallon wucewar motocin guda uku, a farfajiyar sukayi fakin inda duk suka fiffito suka taru a daidai motarsu sai wata hadima dake tare da jakadiyar Saleema a motar dake bayansu ta yi azamar nufa cikin gidan dan sanar da su shigowar mai martaba da iyalinshi.
Kallonshi Saleema tayi tana jin kamar ta cijesu, to ita a ganinta gidansu ne sai an mata iso za ta shigo? Takurar banza kawai! Saida hadimar ta fito 蓷anbaka ya kama hannun motar ya bu蓷e yana fa蓷in "Takawarka lafiya mai mara蓷awa, giwa kake mai takon 茩asaita, zaki a dawa ma sarki kake, Allah ya taimaki mai taimakon talakawa."
A hankali ya fita a motar inda Saleema ta fita ta 蓷aya 茩ofar da jakadiyar ta bu蓷e mata, a nutse suka tako har suka sake ha蓷ewa kafin su ci gaba da takawa a hankali har suka haye 拼ar matakalar suka isa daf da 茩ofar shiga falon. Jakadiyarta tare da hadimar ce suka fara shigewa gaba sannan 蓷anbaka dake ri茩e da bulala ya shiga dan dolenshi ne ya tabbatar da zaman sarkinshi lafiya.
Safiya da fitowarta kenan bayan komawa da tayi ta 蓷auko hijabi sanda aka sanar da zasu shigo tsayawa tayi tana kallon 蓷anbaka dake gyara kujerar da kusan ita ce ta farko a layin kujerun sannan ya koma da sauri yana fa蓷in "Allah ya 茩ara maka lafiya da nisan, bismillah zaku iya shigowa."
Saleema ta fara shigewa kafin ya biyo bayanta, a tare suka yi sallama a cikin tausasan muryoyinsu musamman ma Abdus-samad da kamar baiyi ba. Alhaji Yusuf da ke tsaye tun 蓷azu yana mamakin wannan zuwa na safe haka da sauri ya matso yana amsa sallamar da yi musu barka da zuwa.
Carpet 蓷in dake gabansu wanda 茩aramin teburin ke gabansu yasa Saleema cire takalminta da basu da tudu sosai, a nutse cike da kamala da girmamasu da son nuna musu shi ma 蓷ane garesu ya sunkuya yana 茩o茩arin kwance zariyar ba茩a茩en takalminshi, da sauri Alhaji Yusuf yace "Ranka shi da蓷e ka barsu ba komai, ba sai ka cire ba ai bismillah ka zauna."
Kanshi kawai ya 蓷ago a hankali ya kalleshi ya girgiza kai sannan ya kwance duka ma蓷aurin ya mi茩e tsaye, cikin nutsuwa yasa 蓷aya 茩afar ya 蓷an take 蓷aya takalmen sannan yasa 茩afar dake sanye da safa fara tas tamkar shaddar dake jikinshi ya cire 蓷ayan sannan ya 茩arasa ya zauna.
A hankali Safiya ta 茩araso cike da dattako kusa da Saleema, shirin zubewa tayi 茩asa kamar yadda ta ga hadimar nan da jakadiya sun yi, hakan yasa Saleema yin zunbur ta ri茩o kafa蓷unta ta furta "Subhanallah Mama!"
Mi茩ar da ita tayi sannan ta zaunar da ita suka zauna tare tana sake ri茩o hannayenta, Alhaji Yusuf ma kusan Safiyar ya zauna hakan yasa shi da Saleema suka sakata tsakiya yana maida hankalinshi kan mai martaba yace "Ranka shi da蓷e..."
Kallon 蓳angaren da yayi inda suke yasa bai 茩arasa fa蓷a ba saboda umarnin da ya ga yayi ma jakadiyar da hannu, rusunawa sukayi suka amsa tare da mi茩ewa suna fadin sun barshi lafiya a fito lafiya.
Fitarsu a 蓷akin daidai da fitowar Ardiya tare da Hadeeya cikin shirinsu na tafiya gidan Saleema, wanda Ardiyar ce ta matsa sai dai su je tare da ita, kan wanda idanunsu suka sauka yasa kwarjini da tsananin haibarsa da shigarsa ta kamala data 蓳oye fuskarsa yasa Ardiya kallon inda mijin na ta yake sai dai dake hankalinshi baya kanta yasa ta 茩arasowa tana mai ci gaba da kallonshi sosai.
Saida ta zo kusanshi ne ya 蓷aga kai ya kalleta cikin ra蓷a yace "Zauna mana, mai martaba ne fa mijin Hajiata."
Wara idanu tayi ta sake kallon inda yake sai dai idanun da suka kusa ha蓷awa da Abdus-samad yasa ta saurin sadda kanta ta zauna kusa da Alhaji Yusuf din tana 茩a茩aro murmushin da ita dai bata shirya masa ba tace" Barka da zuwa... *ranka shi da蓷e*."
Hadeeya ma dake kallo tana mamakin yaushe suka shigo 茩arasowa tayi da wayarta a hannu da niyyar zama kusa da Ardiya akan kujerar, a nutse yasa hannunshi ya jaye glass din daya rufe mishi idanu duk da fari 茩ar ne, tamkar damisa haka Hadeeya ta ga ya watso mata wani kallo da bata ta蓳a sanin cewa akwai kallon da zai sa ka shiga hankali ba sai yau, da kallon nan da ya mata sai ta ji kamar za ta iya cewa ta fahimci me yake nufi, sai kuma ta sulale 茩asa tana sadda kanta ita ma tace "Allah ya taimaki yalla蓳ai."
茒auke idanu yayi daga kanta yana hango tsantsar raini a tare da yarinyar da kuma al'ajabi a idanun matar da ta fito yanzu, sai kuma dattako daga matar da ya samu tsaye tun shigowarsa. Yana jin su lallai suma iyalinshi ne, kamar yadda ta shiga rayuwarsa haka shima yake buri a yanzun, dan haka ma ya ri茩e glas 蓷in da hannu 蓷aya sannan ya sa 蓷aya hannun ya jaye rawaninsa daya rufe masa baki. Hakanne ya bayyanar da kamilallar fuskarshi dake da duhun fata da kyakyawan saje da ya mata 茩awanya.
Tunda Safiya ta sadda kai har suka 蓷an fara gaisawa ba ta 蓷ago ba, Alhaji Yusuf kuma yana 蓷agawa har su ha蓷a idanu amma na 蓷an lokaci, Ardiya ma da fari kallonshi take sosai har zuciyarta ta fara ayyana mata "Aikin banza, ta yiwu ma tsoho aka aura mata amma ake ta mana 茩aryar banza ita ta auri sarki."
Amma yanzu da ya fito da bakinshi hakan yasa fuskarshi fitowa taram, kula duk da alamu ya nuna ba yaro bane mai shekara ashirin da biyar zuwa talatin, sai ya zama a yanzu dai idanunta ba su ga wata makusa a tare da shi ba, tabbas ba茩i ne amma ba irin ba茩i 茩irin ba, gashi kuma hutu da ya bayyana a fatar sai ya zama mai 蓷aukar hankali, sai ta sake jin ta raina kanta da za蓳in 拼a拼anta. A dolenta ta sauke idanunta 茩asa dan da suka ha蓷a idanu a bazatar nan saida kayan cikinta suka ka蓷a.
*Alhamdulillah.*
29/06/2022 脿 15:29 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_53_
茒agowa daga jinginar da yayi a kujerar yana kallon tebur 蓷in dake 茩asa cikin sanyayyan murya da girmamawa ga wa蓷anda ke gabanshi yace "Dama jiya take fa蓷amin kunyi waya kuma kun ce za ku zo..."
Saida ya numfasa sannan yace "Shine na ce bari na fara zuwa na gabatar da kaina kafin ku zo, dan gaskiya ban ji da蓷i ba da ya zamana har wannan lokacin bamu san juna ba..."
Sadda kanshi ya sake yi yace "Ku gafarceni *iyayena*, hakan ya samo asali ne daga nauyin dake kaina."
Murmushi Alhaji Yusuf yayi cike da dattako yana 茩ara kallon Abdus-samad 蓷in yana 茩iyasta shekarunshi idan ma ya girmeshi fa ba dayawa bane sosai din nan da ya isa ya kirashi mahaifi, amma albarkacin auren 拼arsa da yake yau gashi sarki sukutum ya kirashi da mahaifi? Kai gaskiya yau yana cike da farin ciki.
Safiya ma cike da dattako da dattijantaka ta 茩ara sunkuyar da kanta tana murmushi tace "Ba komai wallahi, ai ina ga sai dai mu ba wasu labarin irin uzurirrikan dake gabanka, wannan zuwan ma da ka yi a yanzu da safen nan, ina ga ya wanke duka laifin da kake ganin kayi."
Fuskarshi 蓷auke da murmushi ya 蓷an kalli fuskar Safiyar yace "Nagode *Ummi*."
Alhaji Yusuf ma gyara zama yayi a sanyaye yace "Ai dake ni na sanka, dan tare da mu aka yi na蓷i, ita dai ce idan na ce ta je ta ga inda 拼arta ke rayuwa sai ta nuna a'a ba za ta je ba kunya take ji."
Murmushi ya 茩ara saki amma bai ce komai ba, shiru ya 蓷an ratsa 蓷akin kafin Alhaji Yusuf ya nuna masa Ardiya da har yanzu kanta ke sadde ta kasa 蓷agowa yace" Wannan ma mamanta ce, ita ta haifi wannan..."
Ya nuna Hadeeya da ita ma kanta ke 茩asa tana wasa da abun sauraren dake hannunta tare da waya tana ta jujjuyasu, sai kuma ya numfasa yace" Dama zuwan da zamuyi tare da ita ne za mu je, dan ita tana son ganin Saleema sosai..."
Tare Ardiya da Safiya da kuma Saleema suka kalleshi jin abinda ya fa蓷a, amma da ya dakesu ya ci gaba da fa蓷in" Saboda akwai wani abu da ya taso ne, shiyasa muka so zuwa da kanmu dan mu nemi alfarma a gurinka yalla蓳ai."
Kallonshi Abdus-samad yayi ya 蓷an kya蓳e baki yace" *Abhina*, dan Allah ku kirani da sunana ko kuma 蓷anku, hakan zai sa na ji nima na ku ne baku wareni ba..."
Sai kuma ya sunkuyar da kanshi yace" Na zo ne dan mu gana da ku, mu saba da ku, mu yi nisha蓷i da iyayenmu sannan mu ci abinci kari tare..."
Sai kuma ya sake kallonshi yana marairaicewa yace" A gida ta rabani da Ummina, ko ganina ba ta yi idan tana gabanta, na zo nan da tabbacin nima zan 茩wace na wa iyayen, dan Allah ku saki jiki dani ku ji tamkar 蓷anku ne da ya shekara ba tare da ku ba."
Kallonshi Saleema tayi tana turo baki shima kallonta yayi yana murmushi, Abba da ya ji da蓷in maganar sosai ya kalli Saleema ta wutsiyar idanu yace" In dai uwata ce ta saba shigewa zuciyoyin manyan mutanen da suka dace da halayenta na girma, amma wannan karan ta samu mahaifiya guda ne yayin da ta rasa biyu da kuma uba 蓷aya."
Le茩a fuskarshi Saleema tayi tace" Abba..."
Hararanta yayi yace" Me ye?" 茒ora kanta tayi a kafa蓷ar Mamanta tana turo baki, a hankali Safiya ta ture kanta tace" Ban sanki ba, wacece ke?"
茒agowa tayi ta yi takwaf takwaf da fuska kamar za ta fashe da kuka, sai kuma ta le茩a inda Ardiya take tana kallonsu wani hawa da sauka 茩irjinta keyi tsabar takaici, kuma tana so ta tashi daga wurin a fusace ama tsoron kar wannan mai shegiyar bulalar ya ganta ta window ya zo ya zabga mata tunda ba kunya ne da su ba dogarawan, hakan yasa dole take zaune tana kallon wannan takaici da wareta da aka yi kamar wata bare. Kamar daga sama Saleema ta kya蓳e fuska tace mata " *Mama*."
茒aga kai tayi ta kalli Saleema da mamaki, to ai tunda suke a rayuwa tsabar kowa harkanshi yake duka 拼a拼an kowa ba sa kiran 蓷aya matar da Mama sai dai aunty, hakan yasa da Saleema ta kirata yanzu sai ta ji abun har 茩asan zuciyarta tare da jin kuma me ye haka? Kafin ta gama tunanin komai ta mi茩e ta zauna kusa da Ardiya tare da 蓷ora kanta a kan cinyarta tana fa蓷in "Mama ai ke ba zaki juya min baya ba ko?"
Sororo duk sukayi banda Abdus-samad da bai san gaban lamarin ba sai ma dariya da yayi yana ayyanawa a 茩asan zuciyarsa lallai su sunyi sa'ar ha蓷a kawunansu, yo shi ko da wasa ya ta蓳a kwatanta yi wa 蓷aya daga cikin iyayensu haka idan ba wacce ta haifi ba? Ardiya da ta rasa yadda za ta yi murmushi ta 茩a茩aro ta shafa kanta tace "Hakane 拼ar gudaliyata, kowa ya juya miki baya amma ina tare da ke."
Gyaran murya Alhaji Yusuf yayi yana murmushi ya sake maida hankalinshi ga Abdus-samad yace "Amm... *蓷an arziki*, dama magana ce akan mijin yarinyar nan..."
Ya 茩arashe da nuna Hadeeya data 茩ara sadda kanta, shi ma 蓷an zuba mata idanu yayi da tunankn dama wannan tana da aure yanzu nan? Sai kuma ya 蓷auke idanunshi ya zuba kan yatsunshi da yake wasa da su yana sauraren Alhaji Yusuf na fa蓷in" Jiya da dare iyayenshi sun zo nan su ke fa蓷a mana abinda ya faru cewa..."
Saida ya gama bayaninsa tsaf Saleema ta kalli mahaifinta da rashin jin da蓷in wannan alfarma da ya nema, dan ita a nazarce ta kalli abun cewa suna kama 茩afa da ita kasancewarta matarshi suke wannan ro茩on, idan yayi musu ba tare da ya yi niyyar hakan ba, kenan ya dubi ala茩arsu ne ya yi hakan kuma ba daidai bane, idan kuma bai yi ba ransu zai 蓳ace su ji kamar baya martaba dangantakarsu Wata茩ila fushinshi ya shafeta. Dan haka tayi saurin Mi茩ewa tsaye tana shirin cire alkyabbarta tace "Mama, an gama abinci ne? Yunwa fa nake ji, muje mu ci abinci ko?"
Duk idanu suka zuba mata musamman ma Ardiya da ta 茩urawa cikin nata idanu da tunanin ba dai *cikin magajin masarautar take 蓷auke da shi ba*? A sanyaye Safiya da ita kunya ma ta kama gani 拼ar da茩i茩iyar 拼arta da ta sha hantara hannun mahaifinta ta zama wata babbar Hajia, a sati kusan uku kenan tayi wata kyakyawar 茩iba ta 茩ara haske da murjewa abunta, cikin sinne kai tace "Yana kan teburi."
Kama hannun Ardiya tayi ta mi茩ar da ita tsaye sannan ta nufo inda Abdus-samad yake zaune tana fa蓷in "Muj mu ci abinci daga baya ma tattauna."
Ganin yana shirin Mi茩ewa yasa Alhaji Yusuf Mi茩ewa yana fa蓷in "Hajiata har yanzu ba'a nutsu ba ashe."
Gaba sukayi wajen cin abinci inda Saleema ke tsaye kusa da shi har ya tashi, 蓷an sunkuyo kanshi yayi ya ra蓷a mata "Rufa min asiri ki maida babbar rigar nan, kinga na gaya miki kar muyi fa蓷a a cikin jama'a."
Ta蓳e baki tayi tace "A gidanmu za'a hanani sha茩at ne, duka iyayena."
Ta inda suka bi zasu wuce yasa ya 蓷auki alkyabbar ya mi茩o mata yace "Saka, ko wallahi mu tafi yanzu ba tare da an ci abincin ba."
Kar蓳an rigar tayi ta saka tana fa蓷in "Ni wallahi ina so na zo na wuni gidanmu."
Murmushi yayi yace "Saboda a can cizonki muke?"
Kashe mishi ido 蓷aya tayi tace "E mana."
Jinjina kai yayi ya bi bayanta suka nufi teburin dukkansu, a gaskiya za su iya cewa babbar sa'a suka taka da suke zaune tare da surukinsu kuma sarkinsu suna kari tare, duk da suna ji da sun san za su zo har haka ta faru? To fa da abincin sia dai su suyi daga masaukin ba茩i da ya fi kowane a garin nan dan muhimmin ba茩on da suke tare da shi. Shi kanshi cikin farin ciki yake, kuma dama yayi hakane dan gaskiya idan suka bar gidan bai kuma san ranar sa zai sake dawowa ba, duk da tunaninshi shine ya bar musu 拼arsu ta wuni tare da su, amma shi ganinshi zai iya sake musu wahala nan gaba musamman ma mahaifiyarta da ya ga alama ba lallai ita ta dinga zuwa inda suke ba. Abun da ya fi komai saka nisha蓷i shine da ya zama kowa ya saje ana hira sama sama cike da annashuwa, ta b'angare 蓷aya kuma ya ji da蓷i matu茩a da ta datse musu zancensu, dan alfarmar da mahaifinta ya nema abu ne da ko yayi to ba yadda zai yi ne, ba kuma ya so ya fara hakan a yanzu, dan in har za'a dinga yi wa wasu alfarma saboda matsayinsu to mulkin babu armashi kenan, za'a wayi gari kowa ma alfarmar yake nema 茩arshe kuma wanda ya dace a hukunta sai ya zo ba'a hukunta shi ba, hakan shi ya fi lalata kowace irin 茩asa ce kuma.
Suna kammalawa Abbanta ne ya fara mi茩ewa ya nufi gaban madubin dake bayan kujerarshi yana kurkure baki ga 茩aramin fanfon dake wurin, da sauri ita ma ta mi茩e ta matsa daf da shi cikin ra蓷a tace "Abba kar ku sake masa maganar nan dan Allah, nk zan masa bayani idan muka je gida."
Kallonta yayi da mamaki yace "Me yasa?"
Marairaicewa tayi tace "Dan Allah Abba?"
Ta蓳e baki yayi yace "Shikenan."
Murmushi tayi kafin suka dawo kusansu har ya mi茩e tsaye yana fa蓷awa Safiya "Ba komai Ummi, ta zauna tare da ku, da dare da kaina zan zo na 蓷auketa."
Sosai Safiya da Saleema suka ji da蓷i, duka rankayawa sukayi har falon kafin Saleema ta kalli Hadeeya tace "Hadeeya, jakadiya na 茩ofar 蓷aki, ki fa蓷a musu sarki na fitowa."
Wani kallo Hadeeya ta mata saidai suna ha蓷a idanu sai ta jinjina kai ta juya tana kumburo baki ita ce ma za'a kai shaidawa hadiman sarki na fitowa? Lallai ma! Ai kam har bakin 茩ofar falon suka yi tsaye cirko cirko suna kallon yadda jami'ai biyu dake ri茩e da bindigu manya suna ta kakkareshi da kuma dogarawa sai kirari suke ta mishi, sai dai banda Saleema da kallonshi ka蓷ai ya isar mata sa茩on kar ta fito mishi waje hakanan yasa tuni ta shige 蓷akin Mamanta ta fa蓷a kan gado tana lumshe idanu.
*Bayan Awa Uku*
Da sallama ta shigo 蓷akin Saleema dake kwance ruf da ciki Safiya na fa蓷in "Za ki sauke min 茩afafun da kika 蓷aga sama ko sai ranki ya 蓳ace?"
Ajiye 茩afafun tayi tare da turo baki saboda ganin yau Maman ta canza mata kowane motsi nata tana binshi da idanu da kuma lura sannan tana ta