Showing 39001 words to 42000 words out of 191031 words
ji, ganin haka yasa ta sake fa蓷in "Saleema, ki yi ha茩uri idan ba ki samu ba, kinga ni ma ban samu ba kuma ban damu ba, saboda na san akwai gaba kuma haka Allah ya tsara, kinga dayawa ma basu samu ba amma kowa ya ha茩ura, wannan shekarar jarabawa ta zubar da 蓷alibai dayawa, ki 茩warara kanki in sha Allah wata shekara sai ki ga kin samu."
A hankali ta rage kukanta jin ba ita ka蓷ai ba ce akwai dayawa, share hawayenta tayi ta mi茩e tsaye ta kalli budurwar tace" Nagode Chafa'atu, nagode sosai, Allah ya sa haka shi ya fi zama alkairi."
"Ameen." Ta fa蓷a tana murmushi, da sauri Saleema ta nufi hanyar fita ta samu dreba na jiranta ta shiga suka tafi, haka kawai ta ji zuciyarta ta bushe da tunanin hukuncin da mahaifinta zai mata, a ganinta idan ma duka ne ai ba yau ne farko ba, ya jima yana dukanta tun bata san ciwon jikinta ba, dan haka za ta 蓷auka idan ma dukan ne, ai dai ba zai 蓷auki ranta ba idan ba Allah ya nufi hakan ba, kyauta kuma ya ba wa su Hadeeya duk abin da ya mallaka bai dameta ba, in dai bai hukunta mahaifiyarta da laifinta ba to komai ya yi.
Cikin takon nutsuwa ta shigo falon, a hankali ta shiga bin kowa na 蓷akin da kallo saboda yanda ta ga sunyi zugum-zugum, babban abin da ya 蓷aga hankalinta shine ganin mahaifinta a gefen Alhaji Auwal zaune fuskarshi yanda kasan hadarin gabas, sai dai kuma a gefe da ta ga Nafissa dur茩ushe tana kuka 茩ashirban sai ta 蓷an murmusa kamar hankalinta a kwance yake.
Duk da arnan kallon da mahaifinta ke aika mata bai hanata 茩arasawa kusa da shi ba ta zauna 茩asa irin zaman tahiya tace "Abba ina kwana."
茒auke kanshi yayi daga kanta da mamakin ita yarinyar nan ba ta gane 蓳acin rai ne? Kusanshi fa ta zo bayan ta san zai iya tattakata, Alhaji Auwal ne ya dawo da shi daga tunanin da yake ta hanyar fa蓷in "瞥ata ya batun sakamakon?"
Kallonshi tayi sai kuma ta sunkuyar da kai a hankali ta girgiza kanta alamar ba magana, da sauri ya kalli Alhaji Yusuf da zai yi magana a zafafe ya masa alama da ido ya yi shiru, ha蓷ewa ya yi yana jinjina kai kamar zai tashi sama, a tsanake ya kalleta yace "瞥ata, kar ki damu kanki kin ji, fa蓷a min ya kike so? Kina son samun kanki a aji na gaba ne? Ko kuma kina so nan da awa 蓷aya ki ga sunanki a kafe a wata takardar?"
Kallonshi tayi tace "A'a Abba, nagode da karramawarka, amma na fi so na samu dalilin 茩o茩arina, idan akayi haka an zalunci dayawa wanda ba su da yanda zasuyi."
"Kuma har abada ba za ki samu ba indai da 茩o茩arinki ne." Cewar Alhaji Yusuf har da saka 茩afa 蓷aya ya tureta daga kusanshi, sai da tayi kamar za ta yi sujada dan abun bazata ne, gyara zamanta tayi sanda Alhaji Auwal ke fa蓷in "Ka ga kar ka kuma dukar min yarinya, karatun ba na Allah ba ne? Ko dabararta za ta bata ne?"
Cije le蓳en 茩asa Alhaji Yusuf ya yi kamar zai ciji iska, Alhaji Auwal kuma kallon Nafissa ya yi da ke ta sharar hawaye yace "Zan nemeki, ki bamu wuri yanzu."
Mi茩ewa ta yi ta nufi madafa, kallon Hajia Rabi da amarya yayi yace "Dan Allah ku bamu wuri za mu tattauna?"
A kasalance suka mi茩e musamman amarya da ta bi Saleema da harara, har yaran ma duka ya korasu sannan ya kalli Alhaji Yusuf yace "Bari na nuna maka wani abu game da 拼arka."
Kallon Saleema ya yi a tsanake yace "Matso nan Baby."
Mi茩ewa tayi ta koma kusa da shi ta zauna 茩asa, a nutse ya kalleta yace "Saleema, wannan yarinyar Nafissa ta zo min da wata magana yanzu, amma ban yarda da ita ba saboda na san 蓷ana..."
Gyara zamanshi ya yi yace "Ta fa蓷a min wai Yayanta ne ya ke so ya kashe min 蓷ana Mu'awwaz saboda ya gano akwai wata mummunar ala茩a tsakaninshi da ita Nafissa, kuma ta tabbatar da zai aikata saboda Yayan na ta 蓷an daba ne, shi ne ta tsorata take sanar dani wai na yi wani abu a kai, da fari ma 茩in fa蓷a ta yi sai da na yi da gaske ta fa蓷a min dalili, to magana ta gaskiya na 蓷an ta蓳a ganin abin da ya sani zargin Mu'awwaz, sai dai ba na jin zai iya neman 拼ar aikin gidan nan, to yanzu ke ya kike gani? Na tura Mu'awwaz wata 茩asar ne? Ko kuma na sanar da hukuma su shiga tsakaninsu."
Da sauri Saleema da dama komai shirinta ne ta kalleshi tace" A'a Abba, kar ka yi ko 蓷aya."
Da alamar tambaya ya tambayeta da" Me yasa?"
A nutse cike da hankali tace" Abba, ta min bayani akan Yayan nan na ta, 蓷an shaye-shaye ne da babu abin da yake sai zaman banza, ba ya da tunanin kansa bare ya yi tunanin rayuwar wasu na shi, a ganina idan ka shigar da maganar wajen hukuma, to kamar mun da蓳awa kanmu wu茩a ne, dan shakka babu za'a san abin da Mu'awwaz ya aikata, idan kuma ka fitar da Mu'awwaz 茩asar waje, to fa wannan 蓷an daban zai iya fallasashi da tunanin ya gudu ne saboda tsoron kar ya 蓷auki fansa, idan kuma har maganar ta fito fili, to hukumar kare ha茩茩in mata da yara 茩anana za su iya saka ido a kan lamarin, idan haka ta faru kuma za'a ce a gudanar da bincike, a 茩arshe kotu za ta shiga lamarin da 茩orafin Mu'awwaz na 蓷aya daga cikin ma su cin zarafin mata musamman marasa galihu."
A sanyaye sosai kamar za ta yi kuka tace" Abba, kuma ka san hukumar kare ha茩茩in mata ba ta wasa da lamari irin wannan, za su 蓳ata lokaci da ku蓷i har ma da iko wajen ganin sun kayar da mu wannan shari'ar, gwamnati ma ba ta ja da su Abba, dan su suna da goyon baya daga turawa ne."
Ta 茩arashe maganar da sigar dake nuna tana son tsoratar da shi, ai kam a tsorace Alhaji Auwal yace" Hakan na nufin mutumcin gidan nan zai zube kenan?"
Cikin ra蓷a kamar za ta yi dariya tace" Abba, ai har siyasarka ta shekaru ma lalacewa za ta yi, abokan hamayya sun samu abun tsokanarku da shi, gaskiya a duba wata hanyar."
Ri茩e ha蓳a Alhaji Auwal ya yi ya kalli Alhaji Yusuf da ya kafe Saleema da idanu da mamakin ina duk ta san wannan abubuwan? Wa ya bata wannan hikimar? Cike da jimami yace" Ya ka ke gani Alhaji Yusuf?"
茒auke idanu yayi daga Saleema yana 蓷an matse fuska yace" Gaskiya ne Alhaji, a duba wata hanyar daban."
Jinjina kai ya yi yace" To kenan ya kake gani?"
Kallon Saleema ya yi yace" Ke shiga ciki."
Jinjina kai tayi ta fara yun茩arawa a kasalance za ta bar wurin, inda shi kuma ya kalli Alhaji Auwal yace" Ina ganin a kira yaron sai a bashi ku蓷i ma su yawa da zai sa ya bar maganar kawai, kuma ma yarinyar ai ba fya蓷e ya mata ba, da son ranta haka ya faru tunda ba karan-kanta ta zo ta fa蓷a ba."
Da sauri Alhaji Auwal ya juya ga Saleema da ke tafiya a hankali tana jin me mahaifin na ta ke fa蓷a, ta na ganin idan 蓷aya daga cikinsu haka ta faru, shin haka zai fa蓷a? Kiranta ya yi yace" Dawo zauna."
Dawowa ta yi ta zauna yana kallonta yace" Kin ji me mahaifinki ya fa蓷a, ke me kike tunani?"
Saida ta saci kallon mahaifinta dake ta hararenta tace" Abba, mu fara tabbatar da gaskiyar maganar ta hanyar tuntu蓳ar Mu'awwaz."
Jinjina kai yayi yace" Wannan ma magana ce, amma yanzu ke mu 茩addara an tuntu蓳eshi kuma gaskiya ne abin da aka fa蓷a, me ye mafitar?"
瞥ar dariya tayi ta girgiza kai tace" Abba, gaskiya a wautar kasancewata 拼ar fari kuma mace mai rauni, idan a ra'ayina ne sai na ce mu aura masa ita, kunga kenan ko da daga baya maganar ta fito, to sai a 蓷aukeshi kawai soyayya ce irin ta masu 拼anci, tunda dukansu sun haura shekara sha takwas, dan idan ku蓷i mu ka bashi hakan zai iya sa wa ya dinga yaudararmu ta hanyar kar蓳an ku蓷i lokaci lokaci (blackmail), kunga kenan babu hutu kuma ko yaushe dai asirin zai tonu, amma idan ta zama matarshi babu mai 蓷aga maganar."
Bubbuga cinya Alhaji Auwal ya yi ya washe baki yana dariya yace" Wannan yayi, wannan shawara ta yi, hakan shi ne mafita."
Sai kuma ya kalli Alhaji Yusuf da mamaki ya sakashi zuba musu idanu kawai ya nuna mishi Saleema yace" Ka gani ko, abinda na ke so ka fahimta kenan, wannan ita ce *BAIWAR 瞥ARKA*."
Kallonta yayi yace" Tashi ki shiga ciki Baby, amma zan fara shawara da Baba na ji me yake gani game da hakan, dan yanzu bana komai sai da shawararshi."
Murmushi ta saki ta mi茩e kawai dan ta san ta wajen Papi ma ba za'a samu matsala ba, dan ta gama da shi tun kafin ma ta kitsawa Nafissa abin da za ta yi.
*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:41 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_17_
Tunda Papi ya fara magana bayan sun fa蓷a masa abin da ke faruwa Abban Saleema ke kallonshi kamar a tsorace, to sak shawarar da 拼ar 茩aramar 拼arsa ta bayar shi ma yake maimaita duk da ba su fa蓷a masa sun tattauna da kowa ba, har sai da Alhaji Auwal ya ta蓳oshi yace "Ka gani ko, ya kamata ka saka ido akan yarinyar nan, tunda ta zo gidan nan abubuwa masu kyau ke faruwa, sannan rayuwata da ta iyalina ta fara hawa kan saiti, wallahi babbar *kadara* Allah ya baka, ka kula da ita yanda ya dace, idan Allah yasa ba ta cikin wanda za su ci moriyar boko, to ka tambayeta abin da za ta iya yi bayan wannan, za ka sha mamakin yarinyar nan idan na fa蓷a maka watarana ni da kai za ta iya yi mana alfarmar da duk ikonmu da iliminmu ba za su sama mana ita ba."
Maida dubanshi yayi ga Papi yace" Baba, tunda kai ma abin da ka gani kenan, ina ga anjima sai mu je gidansu yarinyar, ko ba komai ni a ganina ya kamata Mu'awwaz ya shiga hankalinshi, dan abin da yarinyar ta zo da shi ya tabbatar min da zargina a kan shi, Baba kamar Mu'awwaz na kamashi da kororn roba (comdom) a motarshi, amma da na yi magana ya dinga min kame-kame, yanzu kam na yarda da abin da ke faruwa a gidan nan, tunda shi ya lalata mata rayuwa, to shi ya kamata ya aureta ko ba ya so, idan ta auri wani a haka za ta iya fuskantar tsananin rayuwa da 茩iyayya, idan mun yi sa'a auren ya yi 茩arko to za ta rayu cikin tsangwama, amma idan shi ne da ya fara, bai da bakin aibatata dan shi ya fita lalacewa."
Kallon Alhaji Yusuf ya yi dake tunani kan abin da Alhaji Auwal ya fa蓷a masa, a ganinshi me ye ya kamata a ce kamar Saleema na so bayan karatu? Ai sai dai in soyayya take, ko kuma aure take so? A gaskiya ba ya jin zai iya taimaka mata da komai in dai ba abin da ya shafi karatu ba, to me ya fi ilimi a duniyar nan? Idan ba ka da ilimin nan na boko wani ba茩auye ka ke zama, 茩aramin misali sau tari zai yi magana da yaran da harshen faransanci su mayar mi shi, amma ita ko ya yi niyyar yi mata sai ya dakata dan ya san ba za ta san me ya ce ba bare ya samu abin da yake so. Dafashi Alhaji Auwal ya yi yace "Muje ko?"
茒an zabura ya yi sannan ya mi茩e yana kallon Papi yace "Baba sai an jima."
Da haka suka fita farfajiyar Alhaji Yusuf na fa蓷in "Yanzu sai yaushe za'a turo min yaran? Ina bu茩atarsu a gidan nan wallahi, gaba 蓷aya mun yi kewarsu."
Nauyayyar ajiyar zuciya Alhaji Auwal ya sauke yace "Ka yi 茩o茩ari ka sama musu 茩annai mana, ka ga fa duk sun zama 拼an mata nan gaba ka蓷an aurar da su za ka yi."
Murmushi ya yi yana shafa wuyanshi yace "Alhaji ai... Ina ga sun isa haka, dama namiji ne muke ta fatan Allah ya bamu, kuma na fi so ya fito daga wajen mahaifiyar Saleema, amma Allah bai nufa ba har yanzu."
Murmushi Alhaji Auwal ya yi yace "Da alama kai kanka ka fi yarda da tarbiyar da Safiya ta ke ba wa na ta yaran?"
Sadda kanshi yayi 茩asa bai ce komai ba, murmushi Alhaji Auwal ya sake yi yace "Shikenan ba komai, zan turosu da yamma, akwai tsarabar da nake son ha蓷a musu ne, sannan da dare zan zo gidan na ka akwai maganar da na ke so muyi da kai a kan ita Saleema da kuma Hameeda."
Da sauri ya kalleshi yace "Lafiya dai ko? Ba wani abu sukayi ba?"
Girgiza kai yayi yace "Ba abin da suka aikata, idan na zo za ka ji ko menene."
Jinjina kai yayi yace "Shikenan Alhaji, Allah kaimu."
Musabaha sukayi ya bar gidan da tunanin wace magana kuma zai zo mishi da ita a kan Hameeda da Saleema? Da haka ya isa gida ya shaida ma Safiya Saleema ba ta samu ba kamar dai yanda tun farko ya je makarantar ya dubo musu, saida ta yi 茩walla na rashin jin da蓷i da fatan Allah ya nuna mata ilimin da ke cikin hakan.
Idar da sallah azahar 蓷inta kenan ta samu Hajia babba tace "Mama, dan Allah wayarku za ku ara min na kira Mamana."
Da fara'a ta nuna mata wayar da ke kan gado tace "Gata nan, idan kin ida kuma sai ki fa蓷awa su Hadeeya su shirya, Alhaji ya ce zaku fita tare siyayya."
"To Mama." Ta fa蓷a a ladabce tana 蓷aukar wayar, fitowa tayi daga 蓷akin tana 蓷ora wayar a kunne, jim ka蓷an Mamanta ta 蓷auka suka gaisa a tsanake, 蓷orawa tayi da "Mama lambar Khairat za ki duba min a wayarki, ina so zan yi magana da ita."
Numfashi Safiya ta sauke har tana jin sautinshi kafin tace "Shikenan, amma me zai hana ki bari har ki dawo, tunda anjima za ku zo."
A shagwa蓳e tace "Mama, magana ce ta gaggawa, kwana hu蓷u ya rage saukar makaranta, ina so na tambayeta wani abu ne."
"Shikenan." Ta fa蓷a tana cewa "Bari na duba na gani."
Har za ta kashe wayar Saleema ta yi saurin cewa "Mama."
Dakatawa tayi tace "Ina jinki."
Cikin ladabi tace "Abba bai miki fa蓷a ba a kan rashin samun jarabawata?"
Murmushi Safiya tayi tace "Bai yi ba Hajia, dake tun jiya ma kwance na ke ban da lafiya, amma yanzu da sau茩i."
Hankali tashe Saleema tace "Ayya! Mama baki da lafiya, ki yi ha茩uri jiya ban kiraki ba, ya jikin na ki?"
A tausashe tace "Da sau茩i sosai Saleema, kuma har da rashinki a kusa dani, amma yau na ji 茩arfi sosai da aka ce za ku dawo."
Cike da tausayin mahaifiyar ta ta tace "Zan zo Mama, shiyasa nake ta miki addu'a Allah ya sa ki min 茩ane, ko hakan zai sa ki sassauta soyayyarki a kaina."
Muryarta 蓷auke da sautin jimami da rawar murya tace "To ya na iya Saleema, ke ka蓷ai Allah ya bani, dole na tattara duka soyayyata na 蓷ora a kan ki, idan so samuna ne Saleema mahaifinki ya miki aure tun yanzu, ta hakane zan saka ran ganin jikoki daga gareki."
Kunya ce ta kamata kamar tana gabanta, rufe fuska tayi da tafin hannunta 蓷ay tace "Kai Mama, dan Allah ki daina ni bana so."
Safiya ma murmushi tayi daga inda take tace "To shikenan na daina, amma idan kika zo zamuyi maganar dan ki tabbatar ina bu茩atar hakan daga gareki."
茒an matse bakinta tayi tace "To Mama, karki manta lambar."
"To." Ta fa蓷a tana kashe wayar dan turo mata lambar, 茩arasawa tayi ga kujera ta zauna tana jiran shigowar sa茩o, kamar an ce 蓷aga kanki kalli 茩ofa sai kal suka ha蓷a idanu ita da Mu'awwaz dake shigowa falon da sauri kuma da alamar 蓳aci rai da tashin hankali. Kai tsaye ita ya nufo da mugun sauri, sai da ya zo gabanta ya tsaya, juyawa ya yi dama da hauni ya ga ba kowa sai ita ka蓷ai, maida dubnshi yayi gareta yace "Ke, me kika fa蓷awa Abbana?"
Wani kallo da take jifanshi da shi 茩asa da sama kamar ta ga abun 茩yama, 茩arshe ma 蓷auke kai tayi ta ta蓳e baki tace "Me ya ce masa na fa蓷a mi shi?"
Sunkuyowa ya yi kamar zai yi ruku'u yace "Na tabbata akwai abin da kika fa蓷a masa, yanzu yake tambayata wai me ye tsakanina da Nafissa."
Kallonshi tayi ta 蓷ora 茩afa 蓷aya kan 蓷aya tace "In tambayeka mana? Me yasa ka min 茩arya a waccen ranar?"
Rarraba idanu yayi yace "茦arya kuma? Yaushe na miki 茩arya?"
Nunashi tayi da yatsa tace "Ranar ka fa蓷a min shi ne farko, ashe wata uku kenan ka na anfanar 拼ar mutane kamar wata matarka, yanzu ka 茩addara kai ne mijinta ka sameta a haka, ya za ka ji?"
Ta蓳e baki yayi ya yatsina fuska cike da sha茩iyanci yace "Sam, ki ma daina kwatanta 茩azamar can da zamowa matata, kuma abin da ya faru ai biyanta na ke, ba dole na mata ba."
Cike da takaici Saleema ta mi茩e tsaye tana ri茩e wayar hannunta da kyau wacce ta ji shigowar sa茩o tana kallonshi tace "Ka sani al茩awarin Allah ba ya tashi, wallahi kai ba ka isa ka lalata rayuwar 拼an mata ba son ranka, sannan idan ka tashi aure kace kamila nutsatsiya ka ke bu茩ata, dole ka girbi abin da ka shuka, 蓳arnar da ka fara kuma kai ne za ka 茩arasata."
Sama da 茩asa ta dalla masa harara ta juya za ta bar wurin, cak ta tsaya saboda idanu da suka ha蓷a da Mu'az na tsaye a bayansu, ganinshi