Showing 9001 words to 12000 words out of 191031 words

Chapter 4 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67963

rai b'ace zuciyarta na tafasa na k'arya da yanda k'aramar yarinya kamar Saleema ta yaudareta haka ta shiga labtawa jikinta bulala tana fad'in "Za ki k'ara daga yau? Ni za ki ma k'arya Saleema? Ni kika d'auka shashasha da ba ta san me take ba? Kin sake fita a gidan nan da sunan za ki je wajen d'inki ?"

Cikin kuka na bara-bara Saleema dake ta doka tsalle na azabar bulala take fad'in "A'a, A'a Mama, na tuba wallahi ba zan k'ara ba, na daina zuwa daga yau kar ki kasheni, wayyo ! Abba ka taimakeni."

Duk da shi ma ranshi a b'ace yake na turbar da Saleemar ke neman d'auka, amma kuma haihuwa ta fi gaban wasa, sai ya ji na shi b'acin ran ya fece inda zuciyarshi ta fara suya na yanda ya ga Safiya na dukanta. A sukwane ya nufosu ai kafin ya kai mata agaji Saleema da dama neman ceto take ta yi ram da k'ugunshi ta na lab'ewa bayanshi.

D'aga bulalar da Safiya ta yi za ta sake zuba mata yasa shi rik'e hannunta ram tare da jawota gaba d'ayanta ta fad'a jikinshi, tsit ! D'akin ya d'auka har Saleema dake kuka ma wacce ta tsura musu ido da tunanin kar dai dukan Mamanta zai yi? Ido cikin ido suka kalli juna duk idonsu sun yi jajir na mabambamta b'acin rai, sake damk'e hannunta ya yi sosai hakan ya tilasta mata sakin d'amarar ta na d'an rintse ido na zafin da ta ji, cikin tattausan murya yace mata "Dukan ya isa haka, kamar kin samu wata jaka za ki dinga narkar min 'ya a gabana, to kar ki k'ara."

Zamewa ta yi daga jikinshi cike da kunya tace "Ka ga ka mik'o min yarinyar nan na farfasa mata jikinta, gobe ba za ta sake min k'arya ba."

Harara ta dalla mata yace "Wallahi kika sake tab'a min yarinya ranki zai b'ace, ko ma me ta yi ai laifinki ne, shi ne za ki wani zak'alk'ale ki juye a kan ta dan kar na hukuntaki."

Kawar da kanta tayi gefe tana d'an gunguni, d'an k'aramin bakin na ta ya bi da kallo tare da lashe leb'enshi na k'asa, dafa kafad'ar Saleema ya yi ya mata alamar ta fita, dan ya kula yau Safiyar namansa take da fitina, har shi ne ma take ma gunguni haka? Cikin shashek'ar kuka Saleema ta ari na kare ta bayan mahaifinta ta fice a d'akin da gudu.

Bin ta da kallo Safiya ta yi tace ta nunata da yatsa cikin d'aga murya tace "Ai zan sameki d'akin dan ubankkkk...."

Tsit! Ta yi dan sai da ta tasan ma fad'a ta tuna irin sub'ul da bakan da ta yi, wato a gaban shi ta zageta. K'in juyowa ta yi a hankali ta fara jan jikinta za ta fice a d'akin da sauri ya nufeta ya k'ara jawota jikinshi, tsura ma fuskarta ido yayi yace" Sofee dama tsaurin idonki ya kai haka? Hajiar ta wa? Kuma a gabana?"

Marairaicewa ta yi tace" Ka yi hak'uri dan Allah, wallahi sub'utar baki ce na manta."

Jinjina kai yayi yace" Ni dai ko? Hajia ta kika zaga a gabana, ba komai." Ya fad'a yana sakinta tare da fad'in" Je ki yi shirin bacci ki zo, na gode Allah da ya sa ranar kwananki ne kika zagar min uwata, hakn shi zai bani damar d'aukar fansata."

Turo baki ta yi ta juya za ta fita dan zuwa d'akinta ta shirya ta zo kamar yanda ya ce. Da kallo ya bita kafin ya girgiza kai ya na murmushi ya zauna bakin gadon.


*Washe gari*


A ladabce ta shigo d'akin tana fad'in "Asaalama alaikum."

Safiya dake kwance da k'yar ta tashi zaune tana amsawa da "Wa'alaiki salam."

Kusan gadon ta k'arasa ta tsuguna tace "Mama, kin ga safiya ta yi kuma ba inda muke zuwa, yanzu kinga na fad'a miki gaskiya, zan iya tafiya wajen aunty Hafsatu?"

Harara ta watso mata tace "Saleema jiya ya mukayi da ke? Ban ce kar na sake ji ko gani ba?"

A shagwab'e Saleema tace "Dan Allah Mama ki barni na tafi."

A tsawace tace "Ke tashi, tashi ki bani wuri, kuma wallahi kika sake min maganar nan ranki zai b'ace."

Mik'ewa tayi ta juya za ta fita ta bita da harara ta na fad'in "Ka ga min yarinya, ina zaman zamana ki hassalani kuma ba daman na zageki yanzun nan ubanki ya sake titsiyeni."

Gyara kwanciyarta ta yi tunda dai yau ba aikinta ba ne tana fad'in "A bar ni na ji da abinda ke damuna mana."

Alhaji Yusuf da ke jinme take fad'a yana daf da shigowa ne yace "A ma sake kuskuren zagar min uwata wallahi."

Harara ya dalla mata yace "Yar rainin wayo." Da mamaki ta kalleshi tace "Ni d'in?"

"Ke d'in mana, ko akwai magana ne?" Girgiza kai ta yi alamar a'a, Saleema da ba ta yi nisa ba ya k'wala ma kira ta dawo d'akin, tana zuwa ta tsaya tana kallonshi, cike da gargad'i da jan kunne ya zaro mata ido yace "Kina ji na? Daga yau sai yau kar na sake jin kin yi maganar zuwa wajen koyon d'inki, idan ba haka ba kuma wallahi da kaina zan hukuntaki."

A tsawace yace "Kin ji me na fad'a?" Da sauri ta d'aga kai alamar e, nuna mata k'ofa ya yi yace "Wuce."

Juyawa ta yi jiki a sab'ule ta fita a d'akin ta na jin ba dad'i sam, saboda burinta ne ake neman hanata cimma shi, amma ya zata yi da ya wuce ta hak'ura kawai.


*Tafiya* ta yi nisa, amma har yanzu babu abinda ya canza daga rayuwar su, islamiya sun cire rai da sake komawa, saidai Saleema dake mai wayo ce har yanzu ta na d'aukar karatunta wajen kanwar malaminsu, wanda a shekarun nan ta k'ara sanin abubuwa dayawa, musamman da yanzu ta k'ara wayo da shekaru, sai ya zama har wayar mahaifiyarta take d'auka ta kira malamin su sake tattaunawa kan karatunta. A karatunta na boko ma har yanzu ba abinda ya sauya, duk yanda take son ta birge mahaifinsu ita ma wajen ganin ta yi k'ok'ari abun ya ci tura, sai ma k'ara lalacewa da lamarin ke yi saboda ta hak'ura ta d'auke hankalinta daga karatun na boko, tana yi ne kawai ba dan ranta na so ba sai dan mahaifinsu, hakan ya sa shekara biyu ta na maimaita wani ajin har Hadeeya ta risketa, shima kuma sai Hadeeyar ta yi gaba tana neman barinta, abinda Alhaji Yusuf bai tab'a yi bane ya yi a wannan karan, wato bayar da cin hanci da kuma neman alfarma aka izasu tare da Hadeeya dan baya so ta barta a nan.

Yanzu dai haka suna ajin zana jarabawar BEPC, ya ma ta k'wak'waran kashedi in har ba ta ci jarabawar nan ba to shi kad'ai ya san me zai mata, hakan yasa ta d'an sake maida hankalinta ta na son ganin bai mata abinda ya bar wa ran na shi ba, sai daia inda ta koyi abun a nan take tashi ta barshi, ta na shiga d'aki za ta nemeshi ta rasa.

*Farkawa* ta yi don yin fitsarin da ya addabeta, ta na tashi zaune idonta suka sauka kan Mamanta ta d'ora goshinta k'asa ta na kai kukanta ga sarkin sarakuna mai kowa mai komai, da alama ba ta kwanta ba kenan tun da suka rabu da sai da safe, dama kuma idan ba kwanan Mamanta ba ne d'akinta take kwana dan ta fi jin dad'in hakan. Sauko da k'afafunta ta yi ta na ci gaba da kallon mahaifiyarta wacce ta ke da yak'inin ita kawai take wa addu'a, dan watannin nan ta cika saka damuwa a kan ta wanda ba ta san dalili ba, haka kuma da ta ga tana yawan tsayuwar dare da azumin nafila sai ta ce ta na yi ne saboda ta na so ta yi nasara a karatunta ita ma mahaifinta ya yi alfahari da ita.

Mik'ewa ta yi ta shiga ban d'akin ta yi abinda za ta yi ta fito, zaune ta sake yi bakin gadon ta na kallon mamanta da sai yanzu kad'ai ta d'aga. Bayan wasu mintuna ta sallame sallar dan ta ji me ya sa Saleema ba ta koma ta kwanta ba? Kallonta ta yi murya a tausashe sosai saboda daren da ya tsala yace "Lafiya ba ki koma ki ka kwanta ba?"

Numfashi sosai Saleema ta ja kafin tace "Mama, ki kwanta ki huta mana, gobe za mu fara jarabawar, idan Allah ya k'addara zan samu zan samu."

Ajiyar zuciya Mamanta ta sauke ta na d'an murmushi na dattako tace "Ko da kun gama jarabawa Saleema ba zan daina yi miki addu'a ba, ina so na ga kema mahaifinki ya baki kyauta ko sau d'aya ne."

Girgiza kai Saleema ta yi tace "Mama, wai me yasa ni Abba ba ya so na ne? Saboda ba na da k'ok'ari a makaranta?"

Girgiza kai Mamanta ta yi tace "Ba haka bane, ya na so dai ya ga ke ma kina k'ok'ari ne."

Cike da damuwa a fuskarta tace "To amma Mama ilimi ba na Allah bane? Na yi iya k'ok'arina dan ganin nima na zama kamar su Hadeeya, amma abun ya gagara."

Cike da gasgatawa maman tace "Hakane Saleema, ilimi na Allah kula ya na ba wa wanda ya so, amma wasu lokutan idan ka sa wasa sai Allah ya bar ka da shirmenka."

Da tuhumammen kallo ta bita tace "Mama kina ganin ni ba na jajircewa ne? Ina fa k'ok'ari sosai, kawai dai abunda na sani na fi son karatun islamiyya saboda shi na fi ganewa a sauk'ak'e."

Murmushi ta sake yi cike da dattako tace "To shikenan, Allah dai ya bamu nasara wannan karan."

"Ameen Mama, zo ki kwanta to." Girgiza kai ta yi tace "A' a, ke ki je ki kwanta, ni zan ci gaba daga in da na tsaya."

Ita ma girgiza kai ta yi tace "A'a, ni ma bari in tayaki, ba zan iya bacci ba alhalin ki na tsaye a kaina."

D'an murmushi ta sake yi ta mik'e tsaye dan ci gaba daga in da ta tsaya, ba jimawa Saleema ta fito bayan ta d'auro alwala ta zo ta shinfid'a sallaya ita ma ta bi sahu a gefen mahaifiyarta.



*Saboda comment d'in da ku ke suburbud'awa*馃グ馃グ ga mai so ta yi magana dan shiga *grp d'ina*



*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:37 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_6_




*12:20* suka fito daga aji sun gama zana jarabawarsu, ranar da ake kwantsamawa ya sa ta nufi inda ke da ruwa dan sha ko ta ji sanyi saboda kakarewar da jarabawar ta mata a aji, dama dai ita ba wasu k'awaye gareta ba, to ta ya ma za su yi k'awaye? Bayan mahaifinsu ba kowace k'awa ya ke barinsu da ita ba sai mai ilimi irin na su, idan kuma ba ki da to ko kin zo wajensu zai sa mai gadi ya hanasu shiga, hakan ya sa ma tsakaninta da k'awa makaranta a gaisa a yi raha kawai a wuce wurin, ita ba waya gareta ba duk da shekarunta *goma sha takwas* a duniya, amma mahaifinta ya hana mata waya ya ce a haka za ta ji haushi ta yi k'ok'ari ita ma saboda ya ga yanda waya ke da tasiri a rayuwar matasan yanzu, hakan yasa ya siya ma su Hadeeya manyan wayoyi uta da Hameeda amma ban da ita, wai a dole sai ta ji haushi, amma abunda bai sani ba shi ne ko a jikinta, tunda dai ta na aiki da ta Mamanta ai shikenan.

Ta na zuwa gaban fanfon sai da ta aje yar jakarta k'arama sannan ta cire hijabinta ta zauna bakin dandamalin ta fara d'aura alwala, a iya saninta da ganinta dai ba kowa wajen, dan haka ma ta dinga alwalarta a tsanake har da ture d'an kwalinta ta shafa kai.
Ta na idawa ta mik'e ta na karkad'e hijabin na ta da ya d'auki lemar ruwa, a cikin karkad'eshin da take ne ta d'an juyo da kan ta kad'an. *Kwatsam* idonta su ka sark'e da na balagaggen namijin da ba ta tsammaci ya na wurin ba, da mugun sauri ta durmiya hijabinta ta juya bayanta cike da mad'aukakiyar kunyar da ta kasa misaltawa, gaban Mamanta kad'ai ta ke iya zama da yar rigar nan da ke jikinta, gashi yau ta yi saken da waccen *Alhudahuda* ya gama kalle mata jiki.


Da k'yar ta sunkuya ta d'auki jakarta ba tare da ta yarda ta sake kallon wajen ba, dan irin kallon da ta ga ya na mata abun ya bata tsoro, gashi ta na jin kunyarshi sosai, saboda wasu lokuta ana turoshi ajinsu ya kula da su idan babu malami, dalilinta na kiranshi alhudahuda kuma shi ne irin darasin da yake koya musu na lissafi mai matuk'ar wuya, hakan ya sa da an turoshi ajin za ka ga yan mata da samari kowa na kawo masa rub'abb'en lissafin da ya kakare masa a kwanya dan ya warware masa. Ita kam tsakaninta da shi ido ne shi ma a akasi idan sun sark'e, kamar yanda ba ta damu da shiga abinda bai shafeta ba, haka ta kula shi ma ba ya shiga sabgar da ba'a saka da shi ba, dalilin da yasa kenan ko sannu ba ta tab'a had'asu ba, kuma ta ji ma an ce shi ne shugaban matasa na makarantar.

Sum sum sum! Ta nufo hanyar wucewa wacce dole ta gefenshi za ta ratsa ta wuce, hakan yasa ta k'ara sadda kanta k'asa dan ba ta so su had'a ido, sai da ta zo daf da shi har ta d'an wuce kad'an *Huzeifa* da ya shiga halin d'imuwa da tashin hankalin da bai tab'a riskar kanshi ba ya yi k'arfin halin d'an matsawa kad'an da tunanin kar ta k'arasa warware masa alwalarsa ya na ambaton "A'uzubillah!"

Duk da ba ta tsaya ba amma sai da ta saci kallonshi ta gefen ido da son gano me ya ke wa a'uziyya? Ido suka sake had'awa dan shi mamakinshi bai wuce "Wai dama haka ta ke a cikin dogon hijabin nan?" Ba, shi ya na ganinta ba ruwanta ashe bama-bamai ne a cikin hijabi, tsakani da Allah da Annabi ya d'auro alwalawarsa ya zo da niyyar d'an tab'a karatu kafin 12:30 ta yi ya yi sallah, sai kawai ya wani sameta zigidir haka daga ita sai siket da k'aramar riga, anya kuwa ta san halin da ta sakashi a ciki? Shi fa idan ka cire matan banza da ya ke gani a tv wanda ya ke iya k'ok'arinshi wajen ganin ya kare kanshi daga kallonsu, da kuma ko da ya kallesu ba abinda yake ji, shi bai tab'a ganin irin haka ba, k'annan shi ma mummunan kashedi ya kirta musu kan zama haka a cikin gida. Yanzu ga shi yarinyar da ko sunanta bai sani ba ta gayyato masa da wata larurar da bai san ya na da ita ba.

Wannan kallon mamakin da Saleema ta hango a k'wayar idon shi ya sa ta tunanin ko dai ji yake shi ma malaminsu ne ? Nufinshi kuma ta gaisheshi? Sai kawai zuciyarta ta raya mata ai ba komai ba ne, gaishe shi ya ci albarkacin malaman. D'an tsayawa ta yi ta sake kallon inda ya ke amma ba ta kalli fuskarshi ba tace "Ina wuni."

Tsura masa ido ta sake yi ganin mak'walaton wuyanshi ya yi sama da k'arfi alamar ya had'iyi yawu sannan ya yi k'asa kamar wanda ya had'iyi kunama, da sauri ta d'aga k'afafunta za ta bar wurin ta ji rikitacciyar muryarshi mai bala'in sanyi da taushi wacce ta dace da yanayinshi na sahihin namiji mai sassauk'ar k'ira yace " *Ya sunanki*?"

Cak ta tsaya tare da juyowa a hankali ta sauke ido a kan shi, kamar ba za ta amsa mi shi ba sai kuma a sanyaye ita ma sosai cike da ladabi da kamun kai tace "Sunana kuma?"

Ido kawai ya iya lumshewa alamar e, d'an kawar da kanta tayi gefe sannan tace " *Haleematu Yusuf Saddi*."

A kan labb'anshi ba tare da ya san maganar za ta fito fili ba ya sake furta "Haleematu."

Kallonshi ta yi da kyau sai kuma ta juya ta ci gaba da tafiyarta, bai daina kallonta ba har said ya ji zuciyarshi na tambayarshi "Haba Huzeifa, wannan kallo ai ya wuce k'ai'da."

Da sauri ya d'auke kan shi yana jan d'an gemunshi da ya tara dan koyi da sunna tare da fad'in "Astagfirullah! Allah na tuba ka yafe min, a'uzubillah, shaid'an me ka yi haka? Ya aka yi ka samu nasara a kai na yau?"

Dab'as ya zauna a dakali ya na ci gaba da furta neman tuba ga mahaliccinshi kan ya gafarta masa, dan ya tabbata da shi ta ke fuskata da ta ji kallon ya fara cutar da ita, wanda kuma aka hana a shari'a cewa _" Bai halata ka dinga kallon musulmi ba kallo wanda zai cutar da shi, sai dai in ya kasance fasik'i ne, to k'aurace masa ya zama wajibi."_

In da a farkon karatun littafin Akhdari kuma aka lissafi a jerin abubuwan da baligi kuma ak'ili ya kama ya kiyaye shi ne _" Kallon ajnabiya (manisanciya-wacce ta ke ba muharramar ka ba), sannan ka kiyaye jin dad'in zancenta._


*Yau* kam suna cikin farin ciki na gama jarabawarsu, ko ba komai sun samu hutu su ma daga ranar da ake k'wlawa, musamman ma Saleema da take ganin wahalar banza take, sai dai farin cikin na ta ya koma ciki sanda mahaifin na su ya umarcesu da su shirya zai sa dreba ya kaisu gidan *Alhaji Auwal* wanda zai iya cewa mai gidanshi ne a fannin siyasa, dan shi ya kama hannunshi ya durmiya a cikin tafiyar, duk da a girme ya girmeshi nesa ba kusa ba, dan ko Yayan Alhaji Yusuf d'in ya girma amma suna mutumci da mutumta junansu.

A tsanake mamanta ta kalleta tace "Saleema, lafiya ki ke ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login