Showing 180001 words to 183000 words out of 191031 words

Chapter 61 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

68017

"Kinsan wani abu? Yarinyar nan fa..."

Sai kuma shiru kamar mai tunani kafin tace "Yaushe ta haihu?"

"Ta ce min 蓷azu da yamma ne." Cewar Agaishat, murmushi Ardiya tayi tace "Rana kamar ta yau suna kenan? Bikin matar gwamna, duk da tenure ta kusa 茩arewa, amma dai nasan za'a tara manyan mata, dan haka na fasa fa蓷a miki abinda yasa na kiraki, ranar sunan idan mun ha蓷e kin gani."

Da mamaki Agaishat tace "Za ki je kenan? Bayan kisan haihuwarta ta farko ma da muka je muka dinga wula茩anta dangin amaryar saida ran Hajia I茩lima ya 蓳ace a wajen shi excellency?"

Yatsina baki tayi tace "Sai me? Zamu je, kuma babu abinda za'a fasa, kinsan me? Ita Iklimar nan ba tana ganin tafi kowa saka abu mai kyau da tsada ba? To za ta gani ranar sunan nan, ai na so ma ace ita ce ta haihu wallahi ta ga rashin mutumci, da ta ga yadda zan jera kafa蓷a da kafa蓷a da ita tsabar ha蓷uwa."

Dariya Agaishat tyi tace" Ga dukkan alama akwai babban kamun da kika yi, zan zuba idanu na ga wannan shirin naki."

"Zaki gani." Ardiya ta fa蓷a cike da tabbaci kafin tace "Saida safe malama, yau da gobe duk nice aiki, gyaran nama na can na jirana, dan ma na sa mai aiki ta fara kafin na fito."

Da dariua Agaishat tace "To sai da safe, ni ai nayi sa'a yau na saki, amma a banza tunda waccen uwar shishigin da matar Mu'az sune ke mata aikin ita tana zaune."

Dariya Ardiya tayi tace "To ai ta haifa ne, kinga dole ta huta."

Ta蓳e baki Agaishat tayi tace "Hmmmm! Ke dai saida safe." Da haka sukayi sallama kowa da abinda ke zuciyarshi.



_______________



Yadda duk suka zama 茩awaye yasa Nafissa fitowa cikin ha蓷a蓷蓷iyar atamfarta da ta sha 蓷inki a hannun Saleema wacce anko ce sukayi duka 茩awayen Khairat din har da Fareeda, kallo 蓷aya Agaishat ta mata tare da 蓷aukewa, sai dai da sauri ta sake maido dubanta gareta, a wula茩ance tace mata "Ke zo nan."

茒an waigawa Nafissa tayi ta kalli Mu'awwaz dake ri茩e da hannun yaronsu sai kuma ta tafi amsa kiran, bin bayanta yayi suka tsaya a gabanta, kayan jikinta ta sake 茩arewa kallo sannan tace "Wannan ba ita ce ankon Khairat ba?"

A ladabce tace "E Mama, ita ce."

Kallon Mu'awwaz tayi da ya tsareta da idanu yana jira ya ji me za ta ce, cikin hushi tace "Ka ce min 茩aramar atamfa ce jaka takwas ka siyo mata?"

"E, hakane." Ya fa蓷a yana gyara tsayuwarsa, da yanayin 蓳acin rai tace "茦arya kake, wannan atamfar ko makaho ya gani ya san babba ce, gashi nan kuma an mata babban 蓷inki."

Da sauri Nafissa ta marairaice tace "Wallahi Mama jaka takwas ne turmi 蓷aya, ki tambayi kowa ma ki ji zasu fa蓷a miki, kuma 蓷inkin nan ni kyauta ma Saleema ta min, kuma shima shaida ne..."

Ta fa蓷a tana juyowa ta kalleshi tace "Ko?" Cike da tabbatarwa yace "E, bata amshi komai ba, ni na je na amso kayan ma jiya."

Girgiza kai tayi tana ta蓳e baki ita dai sam bata yarda ba, irin 蓷inkin nan ne lafiyayye mai shigewa a jikin abunda aka 蓷inka, 蓷inki ne mai duwatsun nan manya da suke mayar da abu babba sai ka ga tamkar mai tsadar gaske ne saboda duwatsun manya ne, da hannu ta mata alamar ta tafi kawai tare da 蓷ora 茩afarta kan 蓷aya tana sake aikawa drebansu kira dan ya zo ya kaita wajen bikin, kawai ba ta son tafiya tare da Nafissae ne da ta ce Mu'awwaz 蓷in ya kaita.



*Gidan Biki*



Wani sahihin murmushi ta sake saki ta 蓷aga kanta sama cike da kuri da hura hanci ta fara jijjiga 茩afarta, Agaishat ma dake sake duban Ardiyar ha蓷e fuska tayi ta kawar da kanta a ranta tana ayyana "Na tabbata tijara kika wa Yusuf kafin ya iya siya miki shaddar nan, idan kuma ke kika siya to nasan tanadin aikinki ne na gaba蓷aya rayuwarki."

Hajia Rabi dake mamakin yadda Ardiya ke ta wani 茩afafa ita ta sako kayan da babu mai irinsu a wurin hatta da Iklima ma, ita kayan data saka ba sune a gabanta ba kamar kwalliyar da ta ca蓳awa fuskarta kamar wata 茩aramar yarinya, Iklima ma daga 蓷an nesa take kallonta tana yatsina fuska, a ganinta me ya sa Ardiya za ta 蓷auki wannan shirin a bikin kishiyarta? Gashi irin wankan da ta 蓷auka da kayan jikinta ka rantse da Allah ita ce matar gwamnan ba su ba, dan ko uwar bikin sai ta yi.

茒aya daga cikin matan da suka zagayeta ne ta sake buga tagumi tana kallon Ardiyar tace "Gaskiya Hajia ba 茩arya wankanki ya wanku, kuma fa shaddar naga kamar babbar ce ko?"

Wani yatsina fuska Ardiya tayi tace "Kama ce ma kika gani? A ganinki zan saka 茩aramar ne?"

Murmushi tayi tace "Ba haka nake nufi ba, gaskiya Hajia kin kashe masu gidan rana a wurin nan, irin wannan wula茩anci da kika koro ai ko matar gwamnan ta baki waje."

Wani murmushi tayi na jin da蓷i tare da 蓷an kawar da dubanta wajen Iklima a sanyaye tace "Anfanin nema kenan, da baka da abun yi ne sai a ce ka mallake miji."

Sai kuma ta gyara zamanta tana ha蓷e fuska tace "Ko da yake, ko aikinmu bai siya mana ba ai muna da surukai da aka sansu a gar..."

Tsaf! Ta ha蓷iye maganarta sakamakon ido hu蓷u da sukayi da Safiya da ta shigo falon dake cike da hamsha茩en mata suna ta raharsu, tabbas saida gabanta ya fa蓷i ganin Safiya a wurin dan ita dai ta san ta barota gida ta ce bata jin da蓷in jikinta, hakan ya 茩ara mata 茩arfin gwiwar tahowa da kayan nan tayi birgimarta yadda ta so. Ba wai ganin Safiyar ka蓷ai ba sai ya zamana sanye take da leshen nen wanda Saleema ta musu iri 蓷aya, matsalar ita ce ranar sallah shi ta saka kuma ta 蓷ora kanta a statu, dayawa 茩awayenta sun dinga ta蓷in leshen saboda kyawunshi da 蓷inkin da ya samu ga kuma tsadarsa, a yadda ta ce musu shine mahaifiyar Kabil ta ba sautu ta kawo mata shi daga Dubai.

Tuni ta gyara zamanta tana sadda kanta 茩asa kamar mai son 蓳oye kanta daga ganin Safiyar, ita kuma bata damu ba sai ma 茩arasawa da tayi suka dinga gaisawa da wa蓷anda ta sani kafin t kawo inda suke ta kalli Ardiyar tace "Kin ganni na zo ko? Gidan ne ya min shiru ba kowa kuma na ji dama dama shiyasa kawai na taho."

Murmushin ya茩e tayi tace "Ohooo! Ai dake nima ban jima da zuwa ba na ce musu ba kya jin da蓷i."

Murmushi kawai Safiya tayi ta karasa wajen Hajia Rabi suna gaisawa. Ardiya ba ta tsure ba sai da ta ga mata biyu sun shigo a tare da sauri sauri suna kula da hanyar shigowar tare da kirarin da ya tabbatar mata Saleema ce za ta shigo falon.

Duk tsarguwa tayi tare da tunanin asirinta ya tonu kawai, dan a ganinta Saleema za ta nuna ai ita ta mata wannan 蓷inki da kuma siya mata kayan ma, sai dai me? Saleema tabbas ta ga kayan jikinta kuma ta san wanda ta basu tare da mahaifiyarta ne, amma kamar yadda ta gansu ga mahaifiyarta farin ciki tayi da kuma godewa Allah da ta kai matsayin da ta fara taimakawa iyayenta tun suna da ransu, haka yanzun ma da ta ga Ardiya ta ji wannan abun a ranta bayan ta gaiseshu hadiman nan na gaba tana baya tare da jakadiyarta a bayanta suka shige 蓷akin mai jegon, da mamaki Ardiya ta bi bayanta da kallo yadda ba ta ko yi alamar ta gane kayan ba.

Haka abubuwa ke ci gaba da tafiya har lokacin da ta fara shirye shiryen sake shiga wata gasar, sai dai dalilin rashin lafiyar gimbiya Ramlat yasa ta dakatar da komai dan sosai ta yi jinya har saida aka fita da ita, daga 茩arshe ba ta samu damar shiga wannan gasa ba a wannan shekara ba, hakan yasa shekara biyu kenan tana rasawa.


*Yau* ma suna wayar gari Allah ya ma gimbiya Kubra rasuwa wacce jikin nata dama ba wani lafiya yake ba tun waccen faduwar da tayi, haka suka gama jimaminsu kwana uku kafin kowa ya koma rayuwarshi kamar da. Yanzu ma ta gama shirinta na komai dan tun waccen shekarar da bata samu ta shiga ba ta 茩arasa duk abinda za ta yi ta aje, dan haka wannan lokacin 茩arasawa ne tayi kawai tana jiran lokaci ya cika, amma sai laulayi ya sakota gaba wanda ya sa dolenta ma ta aje dan har ranar ta zo bata san ta zo ba sai Abdus-samad ne idan yana son tsokanarta yake tuna mata.



*Wata shida*



Ihun daya kara蓷e gidan ne yasa Alhaji Yusuf da Safiya dake zaune falon suka tashi a tsorace suna waigawa 蓷akin Hamdeeya da suka jiyo abun, da gudu suka nufi 蓷akin suna rige-rige, dake 茩ofar 蓷akin a bu蓷e suka sameta turus suka ja suka tsaya suna kallon Ardiya da tayi zaman 拼an bori akan tiles 蓷in idanunta kakkafe akan Hamdeeya.

Waro idanu sukayi da matu茩ar firgici suka sake kallon Hadeeyar dake kwance kan gado tamkar gawa ga kuma jinin daya wanke tsakanin cinyoyinta har kan gadon yayi jagab da jini.


Da mugun gudu ya 茩arasa ga Hamdeeya data jima da somewa ba ta san inda kanta ya ke ba ya jijjigata yana kiran "Hamdeeya, ke! Ke Baby! Babyna..."

A gigice ya juyo ya kalli Safiya data matsa kisanshi tana duban Hamdeeyar da yanayin firgici yace "茒auko min makullin mota mu kaita asibiti."

"To." Ta fa蓷a da sauri ta fita a 蓷akin da gudu, ta dauko suka ci karo ya 蓷auko Hamdeeya har farar rigarshi ta 蓳ace, hankali tashe ta kalleshi tace "Ita ma na ga kamar ta some?"

Da gudu gudu ya fita da Hamdeeyar yana fa蓷in "茒aukota in za ki iya?"

Zaro idanu tayi sai kuma ta bi bayanshi da gudu ita ma, saida ta ga fitarsu sannan ta dawo 蓷akin ta samu Ardiya kamar yadda ya fa蓷a, a haujace Ardiya ta kalleta bayan ta mi茩e tsaye tace "Ina take? Ina Hamdeeya? Me ya samu 拼ata???"

Ta 茩arashe fa蓷a da 茩arfi, nuna mata 茩ofa tayi tace "Ya tafi ya kaita asibiti, ki kwantar da hankali ya ce mu sameshi a can..."

Da sauri ta bi bayan Ardiya data fita da gudu, ta manta bata da mayafi, sam bai ma zo gabanta a lokacin, haka ta fita Safiya na kiranta ita kanta bata samu damar aiwatar da komai ba sai mai aiki ta barwa sa茩on ta kula da gidan suna dawowa ita ma ta bi bayan Ardiya da gyalen mai aiki da ta kar蓳a dan ta bata ta yafa ko ya ya ne.

Asibitin ku蓷i da suka tabbatar can zai je suka nufa, da isarsu wata malamar asibitin ta nuna musu saman matakalar suka haye inda aka kwantar da Hamdeeya, suna shiga suka sameshi tsaye sai kai da kawowa yake, suna ha蓷a idanu a tare suka jefawa junansu tambayoyi mabambamta, shi yana tambayarta "Wai me ya sameta ne?"

Ita kuma tana tambayar "Ina take? Me aka ce yake damunta?"

Ba wanda ya amsa ma kowa tambayar sai fitowar likita daga 蓷akin da yanayi na hanzari yana tsaresu da idanu, Alhaji Yusuf ya kalla sosai a 蓷an ki蓷ime kuma murya a tausashe yace "Alhaji, muna bu茩atar jini da za'a 茩ara mata, domin ta zubar da jini dayawa, komai zai iya faruwa idan ba'a saka mata jinin nan da gaggawa ba."

A rikice Ardiya tace "Me ya samu 拼ata likita? Me ya sameta haka da take bu茩atar jini? Mutuwa za ta yi kenan?"

Kallonta yayi a nutse ya girgiza mata kai yace "A'a, muna dai bu茩atar jinin."

Ra蓳asu yayi zai wyce sai kuma ya dakata ya kalli Alhaji Yusuf yace "Sai dai fa kuyi ha茩uri, domin an rasa abinda ke cikinta."


Dammmmmmm! 馃槀Kai wallahi na gaji jama'a馃槥gashi ba kazi a kusa.



*Alhamdulillah.*
02/07/2022 脿 10:42 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_58_



Tangal tangal yayi yana shirin kifewa a gaban likitan yayi saurin ri茩oshi inda Safiya ta zabura tana fa蓷in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"

Tallaboshi tayi ta baya duk da ya mata nauyi, irin kakkafewar da yake neman yi idanunshi tsaye kan likitan bakinshi na har蓷ewa da 茩yar ya furta "Ta....ya...ya? 瞥at..."

茒iffff! Idanunshi suka rufe ya 茩arasa neman zubewa Safiya da likitan suka ri茩eshi da kyau likitan na 茩wala kiran malamar asibiti.

Ardiya data jingina da bangon tana kallon komai dake faruwa a idanunta sai dai hankalinta baya jikinta, tana gani aka kamashi zuwa wani 蓷akin sai Safiya da suka dakatar da ita a 茩ofar 蓷akin.

Da sauri ta 茩araso wajen Ardiya da ta bata tausayi gaba蓷aya saboda yadda ta yi wani iri sai idanun kawai, dafata tayi a nutse tace "瞥ar uwa, kiyi ha茩uri ki nutsu, dan Allah ki saki ranki ki barwa Allah komai, kar ke ma wani ciwon ya sameki."

Luf! Ta lumshe idanunta wasu hawaye masu zafin gaske suka kwaronyo mata a fuska, a hankali ta bu蓷e ta kalli Safiya sai kawai ta fashe da kuka daga 茩asan zuciyarta tana fa蓷in" Safiya 拼ata fa, 拼ata wai ciki, a ina? Yaushe? Wa? Garin ya ya? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"

Ta fa蓷a da sake fashewa da wani matsanancin kukan ta sulale 茩asa, binta Safiya tayi ta dur茩usa ita ma tana rumgumota jikinta tana fa蓷in" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Tabbas akwai tashin hankali, amma mu kwantar da hankalinmu mu jira komai ya daidaita sai mu ji ta bakin Hamdeeya, sannan ma zan 茩ara magana da likitan ya tabbatar mana."

Girgiza kai Ardiya tayi tana kuka tace" 瞥ata fa duka shekararta sha hu蓷u, yaushe ma ta zama macen da har za'a ce an mata ciki? Kai! Kai! Kai! Wallahi ba zan yarda ba, ko uban waye sai na yi shari'a da shi."

Mi茩ewa tayi tsaye tana shirin fita wata malamar asibiti ta fito daga 蓷akin da Hamdeeyar take ta tsaresu da idanu tace" Kunga ana bu茩atar jini da za'a 茩arawa yarinyar nan, a gaggauta dan Allah."

A 茩agauce Safiya tace" Dan Allah idan akwai na siyarwa a siya a saka mata zamu biya, idan kuma nawa zai dace muje a gwada sai a 蓷iba a saka mata."

Kallonta likitar tayi tace" Baki da ciki?"

Girgiza mata kai tayi, 蓷orawa tayi da" Hawan jini fa?"

Nan ma girgiza kai tayi tace" Sai dai ulcer."

茦asan matakalar ta nufa tana fa蓷in" Biyoni muje."

Ardiya na tsaye ta rasa ina ma za ta nufa me kuma za ta yi har Safiyar ta dawo ba tare da an 蓷ebi jinin ba saboda basu dace ba, 茩arshe dai siyowa aka yi aka shiga dan saka ma Hamdeeyar. Hankali tashe Hameeda ta shigo asibitin kai tsaye wajensu ta nufa, tana zuwa ta kalli mahaifiyarta tace "Momma! Lafiya? Me ya samu Hamdeeyar?"

Kallonta kawai Ardiya tayi ba ta ce komai ba, Safiya ce ta kalleta tace "Hameeda ya aka yi kika san muna nan?"

Da saurin magana tace "Na je gida ne mai aiki take fa蓷a min, na san kuma wannan asibitin za ku zo, ina Hamdeeyar?"

Numfashi ta sauke tace "Tana ciki, jini ake 茩ara mata."

"Abba fa? An ce tare kuke." Ta fa蓷a tana zazzare idanu tana dubashi, 拼ar 茩walla ce ta silalowa Safiya a sanyaye tace "Fa蓷uwa yayi da ya ji halin da take ciki, ban san me ya sameshi ba..."

Kuka ne ya 茩wace mata Hameeda kuma ta zaro idanu tace "To me yake damunta? Na ga jiya ma sun je gidana tare da 茩awarta."

Saida ta kawar da kanta tace "Wai ciki ta zubar."

Da 茩arfin gaske Hameeda tace "Me? Ciki? Hamdeeyar?"

Sai kuma ta kalli Ardiya data fashe da kuka, a sanyaye ita ma tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ciki?"


Da sauri ta lalubi wayarta ta soma kiran Hadeeya, ba jimawa ita ma ta ji abinda ke faruwa ta kuma garzayo asibitin tare da Zeid, ganin duk sun taru kuma har lokacin ba'a fito aka fa蓷a musu jinkunan marasa lafiyarsu ba yasa Safiya ta kalli Hameeda tace "Hameeda, na ce ki kira Saleema mana ki fa蓷a mata."

Saida ta 蓷auke kanta ta 蓷an yatsina baki sannan tace "Uhum!"

Wayar ta fara dannawa sai kuma ta kalli Hadeeya tace "Kina da lambarta ne?"

Da sauri Safiya ta kalli Hameeda da mamaki tace "Na 蓷auka Saleema na fa蓷a min kuna waya?"

Juyar da kanta tayi dan ba za ta iya ce mata e Saleema na kiranta ba amma bata ta蓳a saka suna a lambar ba, wani lokacin ma gogewa take dan haushinta take ji sosai yadda ko gida zasu ha蓷e da Saleema sai dogarai da jakadiya sun dinga wani nuna musu su ba kowa bane, wani lokaci ma sai sun fara shigowa sun sanar wai za ta shigo kafin zata shigo, gani hakan take kawai a matsayin wula茩anci irin na Saleemar da samun dama, shiyasa ba ta shiga sabgarta kwata kwata. Da mamaki ta kalli Hadeeyar da take zayyano mata lambar Saleema a kai da alamar ta hardaceta tamkar ruwan sha, sai dai ita Hadeeya ta fita wayon zaman duniya, takanas ta Kano ma tana kiran Saleema su gaisa, hakan yasa ta fi Hameeda cin moriyar kasancewar Saleema Yayarsu, dan sallah ma da ta wuce da yan kwanaki 蓷inkin sallah ta aiko ma yaranta 拼an mata harda takalmi sannan ita Hadeeyar ta bata ku蓷i har da cewa tanyi ha茩uri ka蓷an, ranar kwana tayi tana zumdumawa Saleema albarka.

Jin wayar na 茩ara yasa ta mikawa Hadeeya tace "Ke kiyi magana da ita."

Kallonta Safiya ta sake yi sai kawai ta girgiza kai ta 蓷auke kanta tana ayyana "Akwai ranar 茩in dillanci."

Saleema na 蓷aga wayar Hadeeya ta gaisheta da girmamawa hakan kuma na 茩arawa Hameeda 蓳acin rai kafin daga bisani tace "Aunty dama Mama ce ta ce a kira a fa蓷a miki Hamdeeya na asibiti, idan da za ki zo wai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login