Showing 108001 words to 111000 words out of 191031 words

Chapter 37 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67981

na fa蓷a ba, amma hanaki zuwa makarantar boko, sannan an hanaki zuwa ta islamiyya tun tsawon lokaci, burin da kike da shi ma a hanaki fuskantarsa, anya kuwa hakan ba yana nufin ci gaban rayuwarki ne ba'a so ba? Idan kuma ana ganin ana yi ne dan martabarki, ina ganin babban gatan da za'a miki shine a barki da za蓳inki, *Saleemah*, rayuwarki taki ce, ke ya kamata ki tashi dan ingantata, idan baki mata komai da zai sa ta gyaru a yanzu ba, to fa bayan kin sake shiga hannun wani mai iko dake, ba lallai ki iya wata hwan蓳asawa ba, dan kusan duk maza tunaninmu iri 蓷aya ne. Da wannan nake shawartarki ki daure ki fara koyon 蓷inkin nan, idan Allah ya dafa miki watarana mahaifinki alfahari zaiyi da ke, ina tabbatar miki sai ya zubar da hawayen farin cikin ganinki a inda bai yi tsammani ba, kuma ta dalilin 蓷inki kika samu hakan."

A sanyaye sosai kamar mai ra蓷a ya sake cewa" Ki 茩warara kanki, zamanki a gida ba karatu ba aiki shine babban tazgaron da zai ruguza rayuwarki, mahaifinki bai fahimci haka bane, idan kuma ya fahimta bai 蓷auki mataki bane kamar dai yadda mafi yawan lokuta iyayenmu su suke 蓷oramu a hanyar da bata 蓳illewa da tunaninsu ita cigabanmu."

A 蓷an da茩ile yace" Kiyi shawara da mahaifiyarki, sannan kiyi tunanin rayuwarki ta gaba."

Sosai maganganunshi suka ratsa Saleema, jiki a mace ta lumshe idanu tace" To, nagode sosai."

Da haka sukayi sallama, ba ta kuma 蓳oyewa mahaifiyarta ba saida ta sanar da ita komai, sai dai wannan karan abinda ya fito daga bakin Maman nata shine" To, Allah yasa alkairi, amma fa ki sani babu ruwana idan ta kwa蓳e, dan ni dai Allah na gani nayi iya 茩o茩arina na hanaki amma kin 茩i fahimta, ba zan hanaki ba dan wata茩ila anan abincinki yake, amma idan mahaifinki ya gane ba hannuna a ciki."

Daga wannan rana Saleema ta fara kar蓳an horo a hannun Fareeda na, ta kan zo sau uku a sati, ranar litinin, alhamis da kuma juma'a, duka ranaku ne da Fareeda ba ta zuwa islamiyya da rana, dake kuma Saleema ta 茩ware a irin haka tamkar dai yadda ta samu karatunta na boko a 蓳oye, haka yanzu ma take koyon aikinta cike da zala茩a da son abun a ranta sa kuma za茩uwa, hakan ya sa Fareeda kullum da mamaki take komawa gida, dan yadda ta na nuna lata take hardacewa, da yadda yanka abu komai wuyarsa baya mata wahala sai take jinjina lamarin har tayi tunanin ko dai tana da aljanu a kanta ne da suke sakata 茩warewa lokaci 蓷aya. Shi kanshi Huzeifa da take zuwa yana 蓷ora mata duk ranar lahadi mamakin take bashi, har wasu lokuta ya zuba mata idanu yana kallo, idan ta zo ko awa bata yi take komawa, dan kuwa 茩arara Huzeifa ke nuna jin haushin kasancewarta a shagon sanda ke da kwai maza a ciki, sai ya yi ta ha蓷e rai yana harare harare, sau茩inta 蓷aya tana da saurin fahimta ba ta jimawa, sannan kullum da hijabinta take mai hannu wanda ko hannayenta ba sa fitowa waje.

*Yau* ma kamar sauran lahadin zuba mata idanu yayi da mamakin ya zata raina masa hankali haka? Irin fa yankan da shi kanshi bai fi watanni da koya a wajen wani babban ma蓷inki dake Kano take cewa ya koya mata, ban da rigila yaushe ta fara koyon da za ta jawo wannan babban aiki? Gyara tsayuwarsa yayi ya nunota da almakashin hannunshi yace "Kinga, idan ba koyon kika zo ba yau ki tafi gida kiyi bacci, ni ina da ayuka da dama."

Ba alamar wasa tace "Wallahi koyo na zo, ka koya min malam, idan na ga da wahala saina ha茩ura a gaba na koya."

A kausashe yace "Kinga ba zai yiwu ba, idan 蓳ata lokacin kike so muyi a shirme kinga kayan can, 蓷auki fara ha蓷emin su, anjima mai su za ta zo kar蓳a."

Cike da rigima ta rumgume hannaye tace "Ban iya taka tela ba."

Da wani kallon mamaki ya bita da tunanin yau bala'i take so su yi, kuma daidai yake da ita shi ma, banda haka taka tela fa shi dai a saninshi a wuni 蓷aya ta koya kuma ko 拼ar gajiyar nan da wasu ke mita ma shi dai bai ji ta yi ba, kai a halin da ake ciki yanzu shi bai shakkar bata 蓷inki na 蓷aya daga cikin shahararrun matan dake kawo masa, a dai yanda zahirin ya nuna ya san yarinyar nan za ta iya, tunda yana bata yanka ta je da shi gida tayi ta kawo masa duk da masu sau茩i yake bata. Dade 茩ugu yayi yace "Kinga, ina rabaki da tsokanata, dan Allah muyi abinda ke gabanmu."

Wani farrr ta masa da idanu ta murgu蓷a baki tace "Na ce fa ban iya ba, to ni baiwarka ce da zaka sani aikin nan? Bayan na ce ka koya min yanka 蓷inkin da ake yayi yanzu, sai ka ga mace ta sa riga duk tattarar tayi sama tamkar an saka mata 茩afara gwanin sha'awa, shine zaka ce wai ba yanzu ba."

Da ma蓷aukakin mamaki ya nuna kanshi yace" Ke! Wai ni kike ma wannan kayan?"

Jujjuyawa ya fara yi yana neman abun awon da zai bata su fara koyon dan ya ga iya gudun ruwanta, ta 蓷auka abun bugu yake nema da gudu ta fita a shagon ta tsallaka titi da sassarfa ta shige gidansu tana 茩yal茩yala dariya. Ri茩e ha蓳a yayi yana kallonta, sau kuma ya saki murmushi yana girgiza kai, wato ka samu macen da za ta san ita macen ce ma rahama ne, duk buhun 蓳acin ran da zai fito da shi daga gidan can inda aka ce lahadi ya zo shagon nan to an gama, dan tsaf yarinyar ke 蓷orashi ta hanyar hassalashi sannan daga 茩arshe ta mayar da sakarai, yanzu nan na tafi kenan sai kuma ta tashi tafiya ta shigo ta masa sai anjima.


Da irin haka take ci gaba da 茩ara 茩warexa a abinda ta saka gaba, yanzu haka ta 茩ulla 茩awance da wayarta saboda dabarun da Huzeifa ya sake nuna mata, kullum cikin bibiyar rayuwar ma蓷inka take da kuma kallon sanfiri na salon 蓷inkuna daban daban, a haka har yanzu ta kan siyi atamfa dan ta 蓷inkawa kanta, kuma bata ta蓳a nunawa Huzeifa ya ce bai yi ba saidai ya 茩arfafa mata gwiwa, idan tana son yin mai wahala ne wanda hannunta bai gama fa蓷awa ba sai ta zo shagon ta yanka gabanshi ya gyara mata wasu abubuwan, da haka har ranar ta matsawa Mamanta ta bata atamfarta 蓷aya a cikin wanda zatayi shigar biki ta kai shagon ta 蓷inke ta kawo mata. Tayi farin cikin ganin 蓷inki sosai da mamakin ita ta yi har da 茩wala, dan duk da zaka iya 蓷an koyo yayi amma a lokacin da ta fara gaskiya dole a jinjina mata. Duk shagalin nan da aka yi Alhaji Yusuf bai da labari kamar sauran lokuta, dan kuwa lokacin da Fareeda ke zuwa gidan baya nan, ita kuma da take fita duk lahadi baya wani zarginta tunda satin na iya kamawa ya 茩are bata fita ba sai lahadin kawai, wani lokacin kuma yana ma bacci za ta fita har ta dawo bai fito cikin iyalin ba bare ya san me ke faruwa, Hameeda ce hankalinshi ya fi karkata kanta dan ita ce ta fi yawan fita yawon biki da gidajen 茩awayen, rashin yawo sosai ya taimaki Saleema daga kauda idanun mahaifinta a kanta har yanzun ta fara jiyo 茩amshin cikar burinta.


*Bayan Wata Uku*



Tunda ta shigo 蓷akin asibitin take ha蓷e fuska da yatsina baki, kallon Alhaji Yusuf take kamar ta wanwaka masa mari, da alama ma ya tare asibitin ne shima, kwanansu biyu yau a asibiti Safiya na na茩uda, gashi yau aka ce za'a mata tiyata da yamma dan ciro abinda ke cikinta, dan kumburi tayi sosai da 茩yar take motsa jikinta ma, tunda suka zo asibitin ita dai sau 蓷aya ma ta ganshi gidan shi ma a gaggauce. Yanzu haka gashi nan ba kunyar mutanen dake 蓷akin yayi wani zama gaban Safiyar kamar mai ro茩onta gafara sai tattausa mata 茩afafunta yake da suka zama sumtuma sumtuma, wato duk son ta haifa masa namiji ne ya kawo haka? To sai me? Ita ma ta na son cikin nan dan dai tana duba cikas 蓷in da yake kawo mata a aikinta ne, amma ko yanzu ta ga dama za ta iya samu ita ma.

Saleema da ta gama salla ne ta kalli auntyn nata tace "Aunty ina wuni."

Yatsina baki tayi tace "Lafiya, ya mai jikin?"

Da fara'a ta amsa da "Sau茩i."

Juyawa Alhaji Yusuf yayi ya kalleta yace "Saleema zo ki zuba wa mamanki abinci."

A wahalce Safiya dake ta kanta ta girgiza masa kai, bakinta ta motsa da 茩yar tace "Um um, ba yanzu ba."

Kallonta yayi yace "Na'am."

Da 茩yar muryar ta ta ke fita, dan haka da ta sake maimaitawa bai ji ba, 蓷agawa yayi ka蓷an ya kai kunnenshi kusan bakinta yace "Ban ji ba."

A wahalce tace "Ba yanzu ba." Da rashin jin da蓷i ya kalleta yace "Za ki ci anjima?"

茒aga kai kawai tayi alamar e, harara Ardiya ta wurga masa ta mi茩e cike da jin haushi ta kalleshi tace "Alhaji zamu iya yin magana?"

Kallonta yayi sai kuma ya kalli Safiya, tashi tsaye yayi yana fa蓷in "Ina zuwa Maman biyu."

Fitaa tayi ya rufa mata baya yana jin shi fa takura masa take so ta yi, Allah Allah yake yammar nan tayi a yi aikin nan cikin nasara ya ga baiwar Allahn can ta samu lafiya, kai shi fa bai ma ta蓳a sanin haka yake son Safiya ba saida cikin nan ya canza mata halittarta gaba蓷aya, wani tausayinta ke 蓷awainiya da shi kullum, baya son gusawa nan da can sai ya ga kamar wani abu zai faru da ita.

Lubna dake 蓷akin kallon 茩anwar mahaifiyarsu tayi da ita tana dai zaune ne 蓷akin amma kunyar Alhajin take ji tace "Ikon Allah, mata tayi ta gatsinar fuska tamkar tana gaban kashi."

Ta蓳e bakin 茩anwar mahaifiyarsu tayi wacce ita ta rage musu a wanda dai zasu iya kira na iyayensu tace "Ita ta sani, in sha Allah Safiya lafiya za ta haihu."

"Allah yasa." Lubna ta fa蓷a suna kallon Saleema da ta zauna kusa da Mamanta tace "Mama na kawo miki madara?"

Girgiza mata kai kawai tayi, a shafwa蓳e Saleema ta 蓷ora kanta a kafa蓷ar Safiyar dan kuka ke son kwace mata, halin da Mamanta take yana bata tausayi sosai, ita ma a asibitin take kwana dan ba za ta iya zama a gidan ba babu mamanta, ri茩o hannun Safiyar tayi tana murzawa tana fa蓷in "Allah ya baki lafiya Mamana, in sha Allah za'ayi aikin nan lafiya."

Murmushi kawai Safiya tayi ita dai tana zaune kan gadon 茩afafunta na 茩asa, zaman ma ba da蓷inshi take ji ba bare kuma kwanciya. Shigowa Alhaji Yusuf yayi da alamar 蓳acin rai tare da shi, wanda Ardiya ce ta 茩unsa masa wai wula茩antata yake ko gidan ma baya zuwa, ya so kwatanta mata a tsanake 拼ar uwarta na bu茩atar kulawarshi, amma har take masa tsaki tace wai idan yana so su dawwama a asibitin sannan ta juya ta barshi, shi ga sakarai ba?

Kusan Saleema ya tsaya a sanyaye yace "Wai ke baki ga halin da take ciki bane za ki wani hayeta?"

Kamar jira take a mata magana kawai ta tusa kanta a kafa蓷ar Mamanta ta fashe da kuka, tsugunno yayi irin na maza ya ri茩o hannun Saleema yace "Haba Hajia, saboda Allah me ye irin haka yanzu? Ni ne kike so kiga ina kuka?"

Girgiza kai tayi amma ba ta daina kukan ba, ganin yadda take turmusa kanta a jikin Safiya kamar ma nema take tayi kwance yasa shi juyawa ya kalli Lub'a dake fa蓷in "Saleema kiyi ha茩uri mana, ki mata addu'a kinji."

Zaune yayi inda ya tashi 蓷azun ya jawo hannun Saleema ya zaunar da ita kusa da shi, karo na farko a rayuwar ta da dai wayonta da haka ta faru, kanta da ya jawo ya 蓷ora a 茩irjinshi yana shafa kanta yana fa蓷in" Shikena to Hajajjuna ya isa, ki yi ta mata addu'a kinji, ba fa abinda zai sameta in sha Allah, aiki ne kawai za'a mata a ciro miki 茩aninki, ba kina so ki ganshi ba?"

Cikin shashe茩ar kuka ta rufe fuskarta da hannu tana jin kunyar yau ita ce jikin Abbansu, 蓷aga kai tayi alamar e, murmushi ya saki mai sauti yace" To kula shine zakiyi kuka? Ke dai ki jira ta haihu lafiya ki gani, har ku蓷i zan baki masu yawa kiyi biki kema, ki tara 茩awayenki ki gwangwaza shagalin da har a tv sai anyi labarinshi, kinji ko Baby."

Shashe茩ar da take saukewa yasa dariyar da ta saki ta fito cikin sigar da ta sa duka 蓷akin suka kwashe da dariya, 茩anwar Mamansu Safiya kam tashi tayi ta fita dan ita gaskiya bata son rayuwar nan ta Alhaji Yusf da babu kunya a ciki, yo har ina za ta iya da wannan ita?


Cikin farin ciki aka fito musu da santalelen yaron da aka ciro bayan aiki cikin nasara, riga-riga ake wajen kar蓳anshi tsakanin Saleema da mahaifinta da saida yayi sujada ga Allah da wannan babbar kyauta, tunda ya 蓷ora idanunshi a kan yaron wasu hawayen farin ciki suka lullu蓳eshi, sumbatar yaron ya shiga yi kafin ya kalli Saleema da sigar tsokana yace "Hajiata sai dai kiyi ha茩uri, amma daga yau na yayeki ni dai, bayan shekara sha takwas an miki 茩ane, lallai ke *拼ar baiwa ce*."

Dariya tayi a ranta tana ayyana "Dama ni 拼ar Mamana ce, na san ai ba za ta yayeni ba ita."

Ku蓷i dai ba wata tsiya ba Alhaji Yusuf kashesu yake dalilin wannan 茩aruwa da ya samu, wanda hakan ke 茩ona zuciyar Ardiya ka rantse ita ke bashi ku蓷in, saida sukayi kwana biyar a asibiti kafin a sallameta jikinta yayi sau茩i sosai, nan suka koma gida ana jego mai cike da nutsuwa, inda Saleema ta zama tamkar ita ma kishiyar Safiyar ce, san kuwa uta ke tsaye kan girkin gidan, dan takaici yasa Ardiya 茩ara sammakon zuwa wajen aikinta, bata dawowa sai bayan magariba, idan ka ga ta le茩a wajen mai jego to dare ne yayi ba kowa a lokacin. Ba wanda ya damu da tsiyarta tunda ba abinda aka ce dole sai ita za ta yi, kamar yadda babu wanda ya damu hakan, dan iya kulawar da Saleema ma ke bawa Mamanta ka蓷ai ya isheta ta rayu cikin aminci. Dan kuwa takanas Saleema ta 蓷auki hutun zuwa wajen koyon 蓷inkinta, sai Fareeda da ta zo ganin jariri tare da Mamanta.




*Alhamdulillah.*
13/06/2022 脿 17:25 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_37_



Zaro idanu Safiya tayi ta shiga 蓷aga 茩afafunta da sauri tana fa蓷in "Na shiga uku ni Safiya! Saleema wa ya sa ki yi mishi wanka? Ko ni kinga ina mishi?"

Saleema kam da ta ta茩ar茩are ta 茩wala yaron a cikin robar wanka da ruwan masu 蓷umi murmushi tayi tace "Mama na iya fa, gani nayi Mama Bilki tana wani aiki ke kuma kina wanka, kuma har mutane sun fara zuwa."

Tsaye tayi tana kallo, kuma wallahi wankan take masa ta tallabe yaron da hannu 蓷aya tana goga mishi lallausan sosonshi da sabulu a jiki, sala sala take bi tana wanke mishi ko ina, da mamaki ta yi zaune kan gado tace" Wa ya koya miki Saleema? Ni fa ban iya ba wallahi, ko ke dana haifeki sai da kika fara zama na fara miki wanka."

Dariya tayi tace" Abinda gabana Mama Bilki ke mishi, kullum ina so inyi dan nasan hanani zakuyi ai, Mama ba wuya fa."

Shigowar Mama Bilki ne yasa ta ita ma rarako ido ta taho a guje tana fa蓷in" Sallalahu alaihi wa sallam! Safiya kina kallo?"

Dariya tayi tace" Mama ki barta ta iya fa."

Dakatawa dattijuwar tayi sai ta ga kuma babu kuskure, ri茩e ha蓳a tayi tace" Ikon Allah, tun kina budurwa kin iya wanka jariri? Lallai."

Ba ta kulasu ba sai 蓷aga yaron da tayi daga cikin ruwa ta 蓷auki lallausan towel 蓷inshi ta na蓷eshi ciki, bushe masa kunnuwa da idanu tayi kafin tayi zauna gaban garwashin da Mama Bilki ta zauna tana jiran ta mi茩a mata yaron, saidai da kanta ta dinga 蓷ora hannunta bakin kaskon idan yayi zafi saita danna masa cibiyarsa wacce ta fita kwana biyu kenan, haka ta dinga tausa mishi jikinshi da 蓷umin wutar nan, hatta da kwalli da mai saida ta shafawa yaron sannan ta saka mishi pempers wacce dama ita ke saka mishi kullum dan Mama Bilki ta ce iya ba ta iya 蓳alla wannan jaraba ba. Tsaf ta fito da 茩anenta cikin shirin riga da wando na kanti masu kyau ta shafa mishi turare na su na jarirai sannan ta mi茩e ta bawa Mamanta shi tace "A bashi yasha."

Juyawa tayi ta shige ban蓷aki ita ma dan yin wanka yau suna, da kallo Safiya ta bita tana murmushi, uta ka蓷ai ta san me take hangowa a tare da 拼arta, idan ta ce 拼arta za ta zama abar alfahari babbar mace nan gaba za'a iya cewa dan ita ta haifeta, amma ita ka蓷ai ta san me take gani a tare da ita, tana ji a jikinta za ta taka matsayin da ba lallai a samu mai kwatankwacin irinshi a danginta ba dana Babanta.

An gudanar da biki cikin farin ciki da kwanciyar hankali, yaro ya ci sunan *Ahmad* sai fatan Allah ya raya kan sunna. Kwana biyu da yin biki Saleema ta koma bakin aikinta, ma'ana Fareeda ta ci gaba da zuwa tana koya mata abinda ta iya, ranar Lahadi kuma sai ta je ga Huzeifa dan 蓷orawa, sai dai ta canza lokacin tafiya daga zuwan safiya da take, dan yanzu sai ta kai azahar bata tafi ba, kuma hakan ya faru ne sakamakon Abbansu da ya daina baccin safe, yana ida sallar asuba zai zo 蓷akin ya 蓷auki Ahmad, haka rana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login