Showing 63001 words to 66000 words out of 191031 words

Chapter 22 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67968

kai da kawowa, ita dai Saleema na biye da ita duk wanda ta ji matashiyar ta ma magana sai ta gaisheshi da girmamawa, saida suka isa gaban mahaifiyarsu matashiyar ta tsuguna ta na fa蓷a mata sa茩on aiken da ta mata, ganin ita tana tsaye dattijuwar kuma na zaune sai ta ji ba da蓷i, due茩usawa tayi kamar yadda yarinyar tayi tace "Ina wuni Mama."

Cike da kulawa ta kalleta fuskarta 蓷auke da murmushi mai cike da kamala tace "Lafiya lau 拼an mata, muna lafiya?"

"Lafiya lau." Ta amsa da shi tana sinne kai sakamakon kallon da dattijuwar ke mata, mi茩ewa matashiyar tayi tace "Mama riga ce ta kawoma Yaya za'a gyara mata , kuma kinga shi ko yana nan baya da dama, shine zan gyara mata."

Da fara'a ta amsa mata da "To shikenan, amma ki hanzarta kinga yanzu an fara kiran sallah magriba."

"To Mama." Ta fa蓷a tana juyawa ta kalli Saleema tace "Muje."

Bayanta Saleema ta bi har suka shiga wani 蓷akin da ya tabbatar mata lallai 蓷inki kawai ake ciki, cike da so da 茩auna da kuma sha'awa Saleema ta zauna tana kallon duk wani motsin matashiyar komai na sake birgeta tana jin ina ma a ce ita ce, kasa ha茩ura tayi sai da tace "Ya sunanki?"

Da fara'a ta amsa mata da "Fareeda."

Murmushi Saleema tayi tana kallon hannayenta da take tashin waccen 蓷inki da reza sannu sannu saboda 蓷inki ne mai wahalar gaske a shiga tanan ne a fita ta can, idan tayi garaje za ta iya ha蓷awa ta tashi har 蓷inkin inda ba bu茩ata, cikin sanyayyar murya Saleema tace "Za ki iya koya min 蓷inki?"

Da murmushi ta kalleta tace "Kina son koyon 蓷inki ne?"

"Sosai ma." Ta fa蓷a tana. Jinjina mata kai, 蓷orawa tayi da "To ai da Yaya kika gani tunda duka gareshi muka koya."

Kya蓳e baki tayi tace "Kai! Wannan 蓷in? Ranar fa da ina tambayarshi ya koya min cewa ya yi ba ya koyawa mata."

Dariya tayi tace "Ya dai fa蓷a ne, amma shi ya koya mana har ma da wasu cousins 蓷inmu."

Marairaicewa Saleema tayi tace "Ni dai ke nake so, sai dai in kema ba zaki koya min ba, kuma fa da ku蓷i nake so ba kyauta ba."

Kallonta tayi tace "Allah ba haka bane, amma tunda kin ce hala shikenan, zan koya miki."

Zunbur ta mi茩e tsaye ta 茩arasa gabanta d farin ciki tace "Da gaske? Kai amma na ji da蓷i sosai, nagode Fareeda Allah ya biyaki."

"Ameen." Ta fa蓷a kafin ta 蓷ora "Yanzu dai mu samu a gama wannan, sai na baki lambata daga baya muyi magana."

Jinjina kai tayi tace "Hakan ma yayi, nagode sosai."

Kiran sallah magribar da aka fara ya ba Saleema damar fitowa ta 蓷aura alwala ta koma 蓷akin Fareeda ta nuna mata sallaya ta shinfi蓷a ta kabbara sallah, har ta ida Fareeda na zaune kan telar, saidai yanzun bata jima ba ta gyara rigar daga jirketa da tayi ta kakka蓳e sannan ta mi茩a mata "Allah yasa haka ya yi?"

"Za ma tayi in sha Allah." Saleema ta fa蓷a tana ninke rigar ta saka cikin leda, bu蓷a 茩aramar jakarta tayi ta ciro jaka ta bata tace "Gashi ki sha ru..."

Tun bata gama fa蓷a ba tace "A'a wallahi, ai an biya ku蓷in 蓷inkin tun farko."

Da fara'a Saleema tayi tace "Kyauta ne na baki wannan."

Da fara'a ita ma tace "To ki bari watarana kin bani, amma yanzu da na amsa sai na ji kamar na aikin da na miki ne kika biya."

Tare suka taho da Fareeda da buta a hannunta za ta 蓷ebi ruwa a fanfo dake daf da 茩ofar shiga, saidai samarin da suka shigo yasa Saleema raku蓳ewa dan basu damar shkga sannan ta fita, da zumu蓷i Fareeda tace" Yaya sannu da zuwa."

Wannan sarkin surutun Saleema ta kalla daya 茩ura mata idanu duk da ba haske sosai yace" Sarauniyar jin kai, ke ce a gidanmu?"

Ba ta tanka mishi ba saboda Fareeda dake fa蓷awa Huzeifa" Yaya dama wajenka ta zo, amma har na gyara mata."

Sai kuma ta kalli Saleema tace" Ga alhudahudan ya zo."

A tsorace Saleema ta kalleta tana rarako idanu, sai kuma ya 蓷an sadda kanta ka蓷an tana satar kallon Huzeifa da ya kalli Fareeda da mamaki sannan ya kalli 蓳aren da Saleema take, da 茩yar da lahaula ya cira bakinshi yace" Huda-huda?"

Da sauri Saleema ta 蓷aga kai ta kalleshi tana girgiza kai tace" Ni ban fa蓷a ba, kawai dai..."

Shiru tayi saboda kallon da yake mata irin na kana jiran 茩arin bayani ne kawai, ledar hannunta ta sake tamkewa sosai ta kalli saurayin nan tace" Zan wuce, sauri nake."

茦in matsa mata yayi yace" Wai waye alhudahuda? Yayan na wa? Saboda iliminshi ko? Ai ya cancanci sunan, shi fa haka yake, yana ganin abu sau 蓷aya yake shiga kanshi, yanda kika san wata na'ura haka yake, kuma kinga a haka fa yake da..."

Wani kallo ya watsa mishi yace" *Kabeer*."
Tsittt! Ya ja bakinshi ya tsuke, Fareeda dake dariya ce tace" Yaya, 蓷inki take son koya dan Allah ka koya mata idan an gama sabgar nan."

Kallon da ya ma Fareeda yasa ita ma ta ja na ta bakin tayi shiru, kallonshi Saleema tayi da mamakin wai shi dodon ina ne? Sai kuma ta shagwa蓳e fuska tace" Dan Allah malam Huzeifi ka da ka hanata koya min, ka ga kai ka ce baka koyawa mata, shiyasa na ce ita ta koya min."

Saida ya ji ta dasa aya kafin ya juyo da dubanshi gareta, tsaf ya dire idanunshi kan la蓳蓳enta da suka furta sunan *Huzeifi*, me ye kuma Huzeifi? Ya tambayi kanshi, da sauri ya 蓷auke idanunqhi a kanta saboda jin she蓷an na neman tuna mishi ranar can da ya ga sirrin da take 蓳oyewa cikin hijabi. Dake gidan ya 蓷an yi shiru saboda tafiyar wasu matan wasu kuma suna 蓷akuna wajen sallah, da mugun sauri ya dinga cira 茩afafunshi zai bar wurin, Saleema da ranta ya fara 蓳acewa game da halin ko in kula na shi yasa ta gyara tsayuwa tana sake ri茩e ldar hannunta da kyau tace "Kai malam! Wai me ye matsalarka ne? Na ce ka koya min ka ce a'a, ita tace za ta koya min shima ka hanata ta hanyar bata umarni da idanunka, me kake nufi to? Ba ka so na koya ne? Ko ku蓷i ne matsalarka? Idan su ne ka fa蓷a min nawa zan biya sai k..."

Juyowa yayi a hassale jin tana neman kawo mishi zafin kai irin na Sharhasila dake ta茩amar za ta iya siyan komai da ku蓷in mahaifinta, da wani mugun kallo ya fara takowa zuwa gareta. Sam Saleema ba ta yi 茩asa a gwiwa ba wajen saurin la蓳ewa bayan Kabeer tana fa蓷in "Ka ga magana ce fa ta fatar baki, me ye sai ka dakeni kuma? Allah baka ha茩uri *sarkin ma蓷inka*."

Cak! Ya tsaya tare da shafa goshinshi yana sakin murmushin da har ga Allah su蓳uce masa ne yayi, kawai abin da yake dubawa shine su yara ba ruwansu da damuwa, inba wauta ta yarinyar nan ba ta ya za ta yi tunanin zai daketa ne? Fa蓷a蓷a murmushinshi yayi ya juya zai ck gaba da tafiyar sai kuma ya tsaya ya sake juyowa ya kalleta tana fitowa daga bayan Kabeer dake ta she茩a dariya, cikin sakakkiyar muryar da shi kanshi yayi mamakin tsintar kanshi cikin farin ciki yanzu yanzun nan yace "Shikenan, za ta koya miki, abinda ya fi 茩arfinta sai na koya miki."

Farin cikin da ta tsinci kanta a ciki yasa ta takawa da sauri ta 茩arasa gurin Fareeda ta rumgume tana 茩ara mata godiya, ba tare data raba jikinta da na ta ba ya ra蓳asu ya wuce ta bi 茩eyarshi da kallo duk da yana sanye da hula da kuma manyan kaya na farar shaddar da ta sakashi fitowa a matsayin ango.

Ya bu蓷e 蓷akinshi kenan zai shiga Saleema data 蓷ago ta kalleshi tace "Allah ya sanya albarka a gareka, kuma ya yi maka albarka, kuma ya ha蓷a tsakaninku da alkairi."

A hankali ya juyo da mamakin jin addu'ar da ake yi wa wanda yayi sabon aure ko abun hawa a bakinta, a tausashe daga inda yake ya amsa mata da "Jazakhillaha khairan."

Murmushi ta sakar masa da ya sakashi waro idanu sai kuma ya lumshesu kamar zai suma, 蓷agawa Fareeda hannu tayi kafin ta juya bayan ta kalli Kabeer tace "Aku sarkin surutu sai anjima."

Da dariya ya bita da kallo yana fa蓷in "Wa ye akun wai? Ni? Zan kamaki."

Da farin ciki marar misaltuwa ta isa gidan mai kwalliyar, nan Nafissa ta saka kayan sannan suka tafi bayan Saleema ta biya ku蓷in, bata gushe ba har saida aka sada Nafissa da 蓷akinta wanda Mu'az na cikin 拼an 蓷aukar amarya kuma musamman saboda Saleema y zo kuma a motarshi suka tafi. Ganin dare yayi kowa na tafiya yasa ita ma sukayi sallama da Nafissa, har ta juya za ta fita Nafissa tace "Hajia Saleema."

Juyowa tayi ta turo baki tace "Hajia ko? Zan yi zuciya na tafi Hajj nan na huta, kinga sai na amsa sunan Hajiar."

Dawowa tayi ka蓷an tayi tsaye tace "Ina jinki? Wani abu kike so?"

Fuskarta da alamar damuwa tace "Tsoro nake ji..."

Cike da kulawa ta dafa kafa蓷arta tace "Keeee! Tsoron me kuma? Ai yanzu zai shigo gidan, kuma ba su Mama da aunty amarya suna nan ba?"

A rikice Nafissa tace "Ai shine matsalar, dubi fa yadda ta kar蓳i 拼an uwana, na tabbata basu ji da蓷i ba kawai sunyi shiru ne."

Girgiza mata kai tayi tace "Kar wannan ya fara 蓷aga miki hankali Nafissa, a gidan nan kina da goyon bayan Abba da kuma Papi, duk wanda ya sa蓳a miki kawai ki fa蓷a musu, na tabbata ba zasu bari a tozartaki ba, sannan ke kika fi kowa sanin Mu'awwaz, karki yarda ya bu蓷e miki ido na banza da wofi, ke da shi kar ta san kar ne fa."

Jinjina kai tayi tace" Hakane, in sha Allah zan 茩warara kaina da 茩arfin gwiwar da na samu daga gareki."

Murmushi ta sakar mata ta sake dafata tace" Ni zan tafi saida safe."

Har ta juya ta ji Nafissa ta ri茩e hannunta, juyowa ta sake yi ta zuba ido a kanta, mi茩ewa Nafissa tayi tsaye ba ta 蓳ata lokaci ba wajen fa蓷awa jikin Saleema tana fa蓷in" Nagode 茩awata, kin 茩wato min 拼ancina, ha茩i茩a da kowane mai lalata 拼a拼a mata yana samun hukuncin daya dace da shi, da izuwa yanzu sun shafawa rayuwarmu lafiya."

茒agota Saleema tayi tana kallon fuskarta tace" Hakane, amma ki sani ba kowane lokaci bane irin wannan hukuncin ke daidai da mai keta haddin mata, Nafissa wani she蓷anin hukuncin kisa ne ya fi dacewa da shi, amma mun bar hukuncin Allah shiyasa musibu suka kewaye rayuwarmu."

Sai kuma ta sauke numfashi tace" Kinga ni zan tafi dare na yi, kuma Yaya Mu'az na jirana a waje."

Da haka sukayi sallama Nafissa na jin kewarta sosai kamar ta zauna suka ci gaba da rayuwa, saidai ta wani 蓳angaren ta ji da蓷i tunda ita ma za ta auri Mu'az ta tare a gidan nan.



______________



A tsanake ya shiga ma茩ala machete 蓷in hannun rigar mai kalar maroon wanda ido ka蓷ai zai nuna maka mai tsada ne, yana gama sakawa ya 蓷auki agogon dake zagaye cikin ba茩in soso cikin wani 茩aramin akwati kamar na sar茩ar mata, ma茩ala agogon yayi sannan ya 蓷auki kyakyawar al茩alamin da take zuwa tare da sauran kayan ya saka a gaban rigarshi wacce alkyabbar da ya 蓷ora sama ta 蓳oyeta, gilashin dake tare da kayan ya 蓷auka siriri fari ya rufe idanunshi da shi sannan ya 蓷auki 茩aramar carbin dake da duwatsu masu 茩yalli 拼an mul-mul ya ri茩e a hannunshi, juyawa yayi a hankali ya fara cira 茩afafunshi dake rufe cikin maroon 蓷in takalmin sak kalar kayanshi wanda duka wannan kayan 茩awar tafiyayyi ne daga kamfanin *Diamond Bleu*, ha蓷a蓷蓷in turaruka kala biyu ya fesa, *Aman dior* ya fara fesawa a kayan dake ciki, sannan ya 蓷an fesa *chairman black* sama sama saboda ya 蓷an fi 茩arfi.

Yana mur蓷a 茩ofar 蓷akin fadawan da jiran fitowarshi suke duk suka dur茩usa aka kwashi kirari, takun nutsuwa da 茩asaitarsa yasa duk suka sadda kawunansu saida ya yi gaba sannan suka mi茩e, wasu ne suka shiga gaba suna kula da duk wanda zai taho daga gaba, inda uku ke baya suna take masa baya ana masa firfita da wani sakaran mafici da ana yi ne kawai dan isa. Suna fita a falon nan ma wasu dandazon masu jiran fitowarsa ne, nan take masu busa dake gefe su uku suka shiga busa wacce ke nuni da sarki mai mara蓷wa ne ke tafe, da wannan takon na alfarma wanda kowa dake bin bayanshi da gabanshi haka suka dinga tafiyar har suka isa fadar inda aka tanadi wajen zamanshi dan na蓷i kamar yadda suka bu茩ata.

Manyan ba茩in da suka halarci wurin masu matsayi da iko na fa蓷a-aji duk suna zazzaune a kujerun da aka tanada musu, inda wurin ya cika da mabiya kala kala kowane da na shi shugaban da yake bin umarninshi, busar sarewa kuma har yanzu tana tashi, ga kuma kirari da zigar da kowane san-茩ira ke yi wa wani babban dan samun abinda zai saka bakinshi. 瞥an jarida na gefe 茩asan carpet 蓷in da aka shinfi蓷a kowane hannunshi ri茩e da abinda zai 蓷auki rahoto da shi, lokaci kawai suke jira a basu dama su fara gabatar da abinda ya tarasu a wurin.

Tunda ya yi haramar zama kan kujerar suka rufeshi da manyan rigunansu suna ta gyara kimtsi tare da shaidawa kowa kanshi 茩asa, sun yi ka蓷an su ga zaman sarki, a nutse ya zauna kan kujerar tare da rufe idanunshi ruf saboda jin kamar ana caccakarshi da tsini wu茩a da allura daga 茩asa, wani irin masifaffen zafi ne jikinshi ya 蓷auka lokaci 蓷aya fiye da na mai zazza蓳i da ake yayyafawa ruwa, take hankalinshi ya gushe, nutsuwarshi ta gudu ta barshi, ya gigice ya ki蓷ime lokaci 蓷aya.

Sanda kowa ya gama zaunawa duk an zuba mishi idanu sai wanda zai yi na蓷in, kamar da wasa sai gani sukayi mi茩e tsaye cirrr! Kamar wanda ya ha蓷iyi ta蓳arya yana zazzare idanu daga cikin gilashin, waziri da sauran fadawa ne suka tashi tsaye suna kallonshi da tambayar lafiya a nutse? A rikice ya kalli limamin fadar tasu cikin muryarshi da ta nuna tashin hankalin da yake ciki yace "Liman, *an 蓷aura auren ne*?"

Da mamaki Liman ya kalleshi cike da tausasawa y dubi agogon hannunshi yace "Ranka shi da蓷e a yanda muka tsara tafiyar da komai, ina ga nan da minti biyar za'a 蓷aur..."

Bai dire kalmar da kyau ba mai gadon kamar yanda dayawa ke kiranshi yace "A dakatar da shi, a dakatar yanzun nan."

Yanzu kam kowa da mamaki a fuskarshi ya kalleshi saboda 蓷aura auren ne fa zai bashi damar zama sarkin d zai mulki al'umma, to idan ya ce a fasa bayan haka aka tsara, me yake nufi kenan? A gigice Liman ya kalleshi yace" Amma ranka sh..."

Bai jira fa蓷ar kowa ko masu take mishi baya ba kawai ya shiga takawa da mugun saurin da tunda Allah ya halicceshi bai ta蓳a sanin yana da shi ba sai yau, irin yanda zuciyarshi ke bugawa ga wani zafi da take masa tare da ga蓳蓳an jikinshi, yanayi ne da yawancin lokuta ya ke shiga idan aka masa maganar aure, to gashi yanzu har kujerar da mahaifinsa ma ya bari tana neman gagararshi hawa.

*Tunda* ya ficedaga fadar ya bishi da kallo daga cikin ba茩in gilashin dake idanunshi, rawanin daya rufe mishi baki ya hana ganin murmushin da yayi a zuciyarshi ya ayyana " *Ba sai ka yi auren ba sannan za ka zama sarki*? To ka yi mu gani, in dai ina raye haka ba zata faru ba *Abdus-Samad*."

Galidimomi har ma da waziri da liman duk suna bi bayanshi, dan tashin hankalin d zasu shiga idan aka fasa auren nan Allah ka蓷ai ya san shi, dole ne ma a hura musu wuta daga sama dan su tsayar da wanda zai hau kujerar nan, amma idan ba haka ba lokaci yayi da zaman kujerar babu sarki zai zo 茩arshe. Falon mahaifiyarshi da ya shiga kai tsaye yasa duk suka ja birki, dan duk haukansu basu da damar shiga wurinta kai tsaye haka.

Duk saurin da yake sai gashi labarin ya rigashi isowa wajen mahaifiyar tashi, saboda tazarar dake tsakanin fadar da kuma falon na ta, da ya bi ta sassau茩ar hanya da ya iso da wuri, sai dai hankalinshi baya jikinshi da 茩yar ya kawo kanshi nan, shigowarshi tasa hadimai biyun dake tare da ita suka rusuna sosai suna gaisheshi, baida 蓷abi'ar wula茩anta na 茩asa da shi, sai dai har ga Allah idan ya ji gaisuwar nan to tabbas wanda ya mutu ma yana jin kira, da sauri suka fice a 蓷akin suka barshi daga shi sai ita. Sarauniya da hannayenta biyu ke tallabe da kyakyawar farar tasar da take dama mishi fura a duk lokacin da baya azumi kasancewarshi mai irin azumin *Annabi Dawud*, yau ya ci abinci gobe ya sha ruwa, tunda ta ji labarin ta dakatar da komai ta shiga 蓷imuwar da ta kasa kwatantawa.

Har ya zube gwiwoyinshi 茩asa kusa da 茩afafunta ya rirri茩e 茩afafun, idanu kawai ta zuba mishi tana kallonshi kamar bata gane shi ba, kallon fuskarta yayi da idanunshi da sukayi jajir alamar bala'in da yake ciki shi ka蓷ai yasan shi yace "Ummiiiii! *Ummina ki lamunce min na bar 茩asar nan*?"

茦ara 茩walalo idanunta tayi waje, sai kuma ta zabura da sauri ta aje tasar furar gefenta wacce ita ka蓷ai ke dama masa ita a duk duniyar nan, hannayenshi ta 蓷an 蓷agoshi yayi irin zaman nan daya tokare yatsunshi na 茩afafu duka 茩asa. Hawaye ne suka fara biyar kumatunta cike da dattijantaka tace "Babana, me yake faruwa ne? Me ya faru? Me ya sa ka ce a dakatar da 蓷aurin auren? Yarinyar ce bata maka ba da ka ga hotonta? Ko kuma ahalinta ne basu maka ba?"

Girgiza kai yayi da sauri da alamar ro茩o yace "Ko 蓷aya Ummi, ni dai dan Allah ki min rai ki amince na bar 茩asar nan, Ummi zafi nake ji ta ko ina, idan na ci gaba da zama a nan mutuwa zan yiiii."

Ya 茩arashe da kwantar da kanshi kan cinyoyinta, dafa kafa蓷arshi tayi a sanyaye tace "Babana me yake damunka? Ka fa蓷a min mana, ni fa mahaifiyarka ce, yanzu fa sau uku kenan sai za'a 蓷aura maka aure sai ka ce ka fasa, shin 拼an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login