Showing 126001 words to 129000 words out of 191031 words
za'a tura saida izinina, ki dai sake bincikawa."
Da mamaki a fuskarta ta mi茩e tsaye ta sake komawa kusan tagar ta 蓷aga labule tana le茩awa tace "To su *wanene* kenan?"
*Da* wani mugun sauri wayar hannunta ta su蓳uce mata ba tare da saninta ba sanda mutane hu蓷un dake tsaye kan mutanen dake zaune akan tabarmi suka cera da wani irin ki蓷a na sautin sarewar daya kara蓷e gidan a 茩an茩anin lokaci, busa ce irin ta gidan sarki mai mara蓷awa, busa suke kamar masu son tashin dabbobin dake bacci. Bata damu da wayar ba haka ta sake zura kanta tana hangen masu busar, da gudu Gaishata ta taso tana fa蓷in "Busar me a ke?"
Matsa mata tayi suka le茩a ta tagar, daga sama sama suka fara jin abun kafin ya fara shigo 茩o茩unan kawunansu har suka fara fahimtar abinsa san-茩iran nan yake 蓷aga murya da iya 茩arfinshi yana fa蓷in "Masha Allahu, Alhamdulillah, Allah ya kawomu lokaci ya riskemu, a wannan rana ta asabar da ta shiga tarihin masarautar mara蓷awa, aure ya 蓷auru tsakanin 蓷an sarki jikan sarki mahaifi ga sarki in sha Allah *sarki Abdus-samad Abdallah Wazir* uban marayu, gatan marar uwa, babanmu mai share kukanmu, Allah ya ja zamanin sabon sarki mai gadon mai mara蓷awa, tare da *拼ar baiwa* yarinya mai 茩ashin arzi茩i wacce ba ta duniyar sanda aka yi rabon tsiya, wato *sabuwar gimbiyarmu* uwa mabada mama amarya ga sarkinmu mai adalci *Haleematus-sadiya Yusuf Jiji*, aure ya 蓷auru akan sadaki ka蓷an domin samun albarkar aure."
Muguwar sarawa kanta yayi, ba ta da hawan jini a iya saninta, amma dai yau ta tabbatar ya kamata a nan takedan kuwa jiri ne ya 蓷ebeta ya kifar a 茩asa har ta kaiwa Gaishata karon da ita ma tayi tangal tangal za ta fa蓷i, da sauri Gaishata ta dur茩usa tana kiran sunanta, idanunta a bu蓷e kuma tana 茩yabtawa saidai kamar ba ta hayyacinta ba, tallabota Gaishata tayi ta tashi zaune suna kallon juna.
Har yau ba'a daina busar sarewar nan ba, inda hayaniya ta 蓷an 茩aru har suke iya jiyo maganganun maza a falonsu, tagumi Gaishata ta buga ta jingina a bango tace "Wai me hakan yake nufi? Anya kuwa gaskiya ne?"
Wuri 蓷aya ta kafe da idanuwa tana kallo, sam bata hayyacinta bare ta san me take, a da茩ile tace "Gaskiya ne, gaskiya ne muka ji!"
Kallonta Gaishata tayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Yanzu kenan duk wahalarmu ta tashi a banza? Ta auri wanda ya shallake tunaninmu kenan?"
A 茩ufule Ardiya tace "Haka ya nuna, na ce haka ya nuna."
Zunbur ta tashi tsaye tana matse fuskarta saboda jikinta da yaji ya 蓷auki ciwon fa蓷uwar nan da tayi a 茩asa, sa hanzari ta kama hanyar fita a falon hankali tashe, da sauri Gaishata ta bi bayanta har tana sakin gyalenta 茩asa. A falon suka samu wasu daga cikin dangin mijin nasu suna ma Safiya barka wacce ita kanta zulumin hakan ne yasa ta bin kowa da idanu kawai, ita ma kamar a mafarki ta ji ana shelantawa 拼arta Saleema ta auri sarki, sarki? Ba fa 蓷an sarki a ka ce ba, sarki gaba蓷aya?
Wuri Ardiya ta samu ta zauna saboda juyowa kanta da sukayi suna mata barka, murmushi nan ta saki mai kama da kuka gaya ta amsa da "Uhum! Barkanmu."
Shigowar Alhaji Yusuf ta saka ta zuba masa idanu da takaici kamar ta sha茩i wuyanshi ta kashe, yo ita zai yaudara haka? Ita zai ma rufa-rufa a rayuwar nan? Babbar rigarshi ya sa蓳a bakinshi har kunne ya 茩arasa inda Safiya take, cikin ra蓷a yace" Uwar Hajia, yanzu an daina hushin? 瞥arki fa yanzu *gimbiyar mara蓷awa* ce."
Maganar nan ce ta sakata fashewa da kuka tare da tashi zunbur ta juya ta kalli gabas a daidai inda Ardiya da Gaishata ke zaune, sujadar godiya ta yi ga Allah tana yi tana kuka kafin ta 蓷aga hannayenta sama tace" Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah Alhamdulillah, nagode maka da wannan babbar ni'ima, Allah nagode maka da ka nunawa ma茩iya da mahassada 茩arshensu."
Kamo kafa蓷unta Alhaji Yusuf yayi yana murmushi, Ardiya dake kallon Safiya idanunta a tsatsaye tamkar na mayyar da aka kama, wani gumi ya shiga wanke mata fuska tana kallon Safiyar kamar wacce aka firgita, cikin ra蓷a Alhaji Yusuf ya kalli Safiyar yace" Yanzu fa 拼ar babbar mace ce, ki gana da ita na 茩arshe, da sallah isha'i masu tafiya da ita zasu zo."
Kallon Ardiya yayi yace" Madame, dan Allah ki kula da komai, zan sa a kawo muku nama da za'ayi girki na musamman saboda ba茩i masu zuwa, mu zamu wuce fada ne yanzu dan kai gaisuwa ga sarki, kinsan yanzu aka yi na蓷in."
A 茩ufule, a hassale, rai 蓳ace, cike da guguwar hassada da 茩yashi ta rarako idanu tace" Ni ce m..." Sai kuma tayi shiru saboda duk mutanen falon uta suka kalla, bata so kuma a gane bata jin da蓷in lamarin nan ba, dan haka ta 茩yale kawai ta sadda kanta har ya fita a falon tare da takewar bayan 拼an uwanshi.
______________
A matu茩ar rikice uwar-gidan tsaka ta zazzaro idanunta tana kallon kanta a madubin da wayar dake kunnenta tace "茒an-galadima wannan wane irin abu ne? Me ye haka? Ya za'ayi na蓷i ba wanda ya sani sai kawai mu ji busar sarewar dake nuna mara蓷awa tayi sabon sarki?"
A matu茩ar gigice ya cire rawanin kanshi ya jefar cikin tashin hankali yace "Ranki shi da蓷e ba iya na蓷i akayi ba, harda fa aure aka 蓷aura masa, aure? Abdus-samad 蓷in?"
Ita ma maimaitawa tayi a razane da "Aure? Abdus-samad 蓷in? Amma ta ya haka... Wai kai kana ina duk haka ta faru?"
Wawan tsaki yayi sai kuma ya dafe gaban goshinshi dake sara mishi yace "Ranki shi da蓷e me ye abunyi yanzu? Ni fa malamin nan ya tabbatar min da babu ta yadda Abdus-samad zai yarda ya auri wata mace, ta ya yanzu za'a 蓷aura masa aure da wata? Wacece ma ita?"
A dake ta amsa da "Ni zan gano wacece ita, kai ka koma wajen malam ka sanar dashi abinda ke faruwa, idan zai yiwu kar ta shigo gidan, idan kuma har ta shigo to kar ta rayu, kuma a yi aiki da ilimi yadda babu wanda zai zargi mutuwar daga wani mahaluki ne."
Jinjina kai yayi a sanyaye yace" Angama ranki shi da蓷e."
Cike da siga ta mugunta ta sake sanyaya muryarta sosai tace" 茒angaladima, kada ka yi sanya kan lamarin nan, mu fara ji da yarinyar da har aikinmu baiyi tasiri akanta ba wajen hanata amincewa aurensa, daga baya zan san ta inda zamu 蓳ullowa lamarin har mu cimma nasara, a wannan karan na maka al茩awarin zama sarki ko ta wane hali, dama na tsaya maka ne har aka baka ri茩on 茩waryar mulkin nan saboda ina so ka ri茩eshi na wani lokaci har sanda 拼a拼ana zasu kai munzalin, amma yanzu..."
Ta kalli kanta a madubi sannan tace" Ka yi abinda na ce kawai."
Jinjina kai yayi yace" Shikenan."
Da haka sukayi sallama ta aje wayar tare da 茩ara gyara jikinta ta 蓷auki babbar alkyabbarta ta saka sannan ta fita a 蓷akin baccin na ta.
Abinda dama take gudu ne yake faruwa, dan kuwa mutane ta samu 蓷akin duk ba hayanuya suke ba, 茩arara alamu suke nuna yanzu fa ta fisu matsayi kenan, tunda 蓷anta ne sarkin, gashi dai ta shigo amma hadimai ne suka iya gaisheta da wannan girman da take burin ganin ya ci gaba da wanzuwa har abada. Zaune tayi kusa da gimbiya Ramlat dake kar蓳an gaisuwar matan liman da suka shigo, ba su gama gaisawa ba wata hadimar ta shigo da girmamawa ta zube 茩asa tace "Ranki shi da蓷e, yalla蓳ai gwamna ne da tawagarsu suke neman iso dan tayaki murna, mai martaba ne ya basu damar haka."
A sanyaye da sakin fuska tace "Ba matsala, za su iya shigowa."
Jakadiyarta ta kalla hakan yasa ta mi茩ewa tana fadawa matan. Dake nan cewa su zo ta nan, ta wata hanyar ta fitar da su daga falon Gimbiyar na kallon wannan ikon Allah yadda aka maidata kamar hoto.
Tana zaune suka shigo tana ganin irin gaisuwar da ake mata, sosai ta cika tamkar za ta fashe, sai dai tayi murmushin ya茩e kawai dan kar a ganeta, sai gashi sun kasa gaisawa a tsanake bare ta mata murna har ta san wacece yarinyar da ta kutso kai a daidai lokacin nan ta tayar musu da hankali, dole ta koma 蓳angarenta ba tare da sanin haka ba, saidai ta yi niyya za ta sani dan kuwa da ita za aje daukarta dan ta ga yanayin gidansu, idan wanda za'a ma barazana ne da ku蓷i sai ta gani, idan kuma masu bu茩atar jan kunne ne sai ta ja musu su kuma su ja ma 拼arsu.
*A* hankali ya sauke sanyayyan numfashin da babu wanda ya san yayi saboda fuskarshi da aka rufe da na蓷in farin rawani, sosai ya shiga damuwar al茩awuran da ya 蓷auka yanzun nan da nauyin jama'a da ya hau kanshi, shin zai iya saukewa? Shugabanci abu ne mai nauyi da kuma wuyar sha'ani, shin zai iya sauke ha茩茩in al'ummarshi? Ba ma wannan ba! Wani nauyin na daban da mahaifiyarshi ta jagoranta aka 蓷aura mishi, shima zai iya saukewa? Ta ya ma akayi baya jin wannan tashin hankalin kamar sauran lokuta idan za'a 蓷aura masa aure? Bai san komai ba game da yarinyar, fuskarta? Kamanninta? Sunanta kanshi bai sani ba har yanzu, abu 蓷aya daya sani shine *ita ta bashi magani*, hakan yasa a yanzun ya bata sunan *zam-zam*.
_Aunty Safiya ga fa sunan._
Ya gaji da zaman nan jama'a a cikin manyan kayan, sai dai har yanzu ba茩i ke shigowa, a haka wai wan蓷anda ke kusa ne da zasu iya zuwa, a bar maganar wanda zasu taso takanas dan tayashi murna da addu'a. A hankali ya sake lumshe idanu ya gya蓷a kanshi tamkar yana masa ciwo ya amsa gaisuwar mataimakin gwamna yana jin yadda fadawan ke amsa masa da cewa "Sarki ya amsa, sarki na godiya." Wannan sha'ani ne mai wuyar gaske, abun ne ya zamar masa biyu, ba gaira ba dalili yana zamanshi Ummi ta sakashi tunanin wacece ita? Ya za ta kasance? Fari' cikinsa ko ba茩in cikinsa? Fatanshi 蓷aya ne ta kasance tamkar ruwan da ta bashi ya sha, ma'ana zam-zam maganin kowace cuta. Yawan tunanin haka yasa shi jin 茩aguwa da duhu yayi ko a je 蓷auko masa *sirrinsa*, ba dan ya 茩agu ba sai dan ya ga wacece kawai.
______________
A hankali mutane suka fara cika gidan, dan abun a bazata ya zo ma kowa ba wannan tunanin, hakan yasa duk wanda ya ji sai ya hanzarta zuwa dan tabbatarwa. 茒ai蓷aikun mutanen dake 茩ofar gidan ne suka fara mi茩ewa kasancewar yamma tayi sosai tsaye suna kallon sarautar Allah, yadda motocin suka tsaya da yadda gimbiya *Kubra* ke fitowa jakadiyai na take mata baya, ga dogarai guda hu蓷u a gabansu sai 蓷aya dake ta faman shelantawa gimbiya ce da kanta ta zo 蓷aukar surukarta gimbiya, har falon suka dinga rakata saida aka mata nuni da 蓷akin maman Saleema ka蓷ai dogarai mazan suka jira da sauran hadiman, sai gimbiyar da jakadiyarta da kuma amintacciyar jakadiyar gimbiya Ramlat suka shiga.
Aunty Lubna da sauran matan dake 蓷akin ne suke mi茩e suna mata sannu da zuwa, kujera ta musamman suka nuna mata ta zauna cike da gadara da 茩arewa komai kallo ta 茩asan idanu, duk da har yanzu ba ta ga abinda za ta kushesu da shi ba, dan ta 蓷auka gidan 拼ar talakawa futuk za su shigo, jakadiyan ne suka zauna 茩asa kusa da 茩afafunta, a nutse cike da shan 茩amshi ta kalli Lubna da take 茩o茩arin ganin ta kar蓳esu yadda ya dace, a ta茩aice tace "Barkanmu ko?"
Da fara'a Lubna ta amsa da "Barkanmu ranki shi da蓷e."
Wani malalacin murmushi tayi tace "Umm...ke ce mahaifiy..." Sai kuma tayi shiru, gane tambayar yasa ta saurin cewa "A'a, gata nan."
Ta nuna mata Safiya da kanta ke sadde, 蓷an 蓷aga kai tayi alamar "Oho! Na gane." Cike da girmamawa Safiya ta sake cewa "Ranki shi da蓷e."
A da茩ile tace "Ina miki murna." Da fara'a ta amsa da "Nagode, nima ina muku murna."
Wani kallo ta watsa mata kafin ta 蓷auke idanunta ta mayar 茩asa inda jakadiyar gimbiya Ramlat take, da idanu ta mata alamar su gabatar da abinda ya kawosu, jinjina kai tayi sannan ta kalli Lubna tace "Ina gimbiyar take?"
Washe baki Lubna tayi ta nufi hanyar fita tace "Uhum! Bari na kirata."
Mi茩ewa jakadiyar tayi tace "Gyara kalamai akan gimbiya, mu zamu je inda take, ki kaimu gareta."
Da mamaki Safiya ta kalli jakadiyar inda Lubna tayi saurin fa蓷in "To, Allah ya huci zuciyarki, sake abun farko ne bamu san komai a kai ba."
Gaba tayi jakadiyar ta bita, suna fita a 茩ofar 蓷akin da Saleema take a nan jakadiyr ta yi alama da hannu biyu daga cikin hadiman da suka tsaya dan jiransu a nan suka nufota, tare suka shiga 蓷akin da Saleema take kwance ta 茩udundune hawayenta sun tsaya cak! Tunda aka ce an 蓷aura mata aure da sarki, sarki? Sarki fa? Ita? Ita a wa? Hmmmm! Ta rasa akan me za ta yi tunani, dan haka take kwance sakamakon ciwon da kanta ke mata.
A ta茩aice alwala da sallah magriba ka蓷ai suka barta tayi da kanta, hatta da cire zip na riga wata hadimar ce ta cire mata, tana ji tana gani amintacciyar jakadiyar nan ta mata 蓷aurin 茩irji da farin tattausan towel suka shiga ban蓷aki wai za ta tayata wanka, ko wankan me? Sarautar Allah.
A 茩alla dai sun 蓷auki awa 蓷aya da rabi a ban蓷akin, ba dan a ce 茩arya take ba sai tace har madara matar nan ta mata wanka da ita, bayan ta tambayeta zuma bata mata illar komai ta ce e, sannan ta shafe mata jikinta da ita ha蓷e da madara gari, hatta da turaren jiki na wuta a ban蓷akin ta mata kafin suka fito aka shiga shiryata. Tun yamma Hadeeya ta zo gidan amma tana zaune falo tana ta fama da cin dabino da 茩aramin cikinta ke sakata ga kuma 拼arta mai shegen la茩uwa bata yarda da kowa sai ita, tare da Hameeda wacce suka tafi Abuja da mijinta sai jiya suka zo suka taso dan zuwa su ga Saleema, shiri ne na gayu jikin Hameeda, amma suna dosowa 茩ofar za su shiga ba tare da su kula da hadimai biyun dake jikin 茩ofar ba suka tsaresu tare da fa蓷in "Kuyi ha茩uri ba zaku shiga ba, ana shirya sarauniya ne."
Da mamaki suka kalli junansu sai kuma Hameeda cike da sabuwar rashin kunyar data koya ta fitsara da jin yanzu tana auren mai ku蓷i tace "Sai me? Kunsan su waye mu? 茦annenta ne fa, su waye ku da zaku hanamu shiga duk inda muke so a gidan ubanmu?"
茒aya daga cikinsu ce ta ha蓷e fuska sosai tace "Ba zaku shiga ba, umarni aka bamu kuma dole mu cika."
Hadeeya ce tace "To nan ai ba gidanta bane, ku bari har ta je can 蓷in idan kun ga 茩afarmu sai ku mana iskanci."
A hassale Hameeda ta kama hannun Hadeeya tace "Zo muje dan Allah, can su 茩arata da da茩i茩iyar tasu da basu ma san w..."
A razane, a kausashe 蓷aya daga cikin dogarai dake tsaye ri茩e da bulala cikin 茩a茩茩arfan murya yace "Keeee! Gyara kimtsi 拼ar matsiyata, ki iya sarrafa harshenki ko jikinki ya gaya miki, sarauniya ba abar wasar uban kowa ba ce."
A tsorace Hadeeya ta ja baya tna kallonshi sai Hameeda da ta harareshi ta 茩asan idanu tace "Mu fa 茩annenta ne ba 拼a拼an matsiyata ba."
茒aga bulalarshi kamar zai tsala musu, amma tayar da sallah isha'i da aka yi kuma a lokacin ake son fita da matar sarki ba tare da kowace ijiya ta samu damar ganinta ba, sai kuma ya dakata daidai lokacin da aka bu蓷o 蓷akin da suke ciki.
*Alhamdulillah.*
20/06/2022 脿 22:07 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_42_
Jakadiyar gimbiya Kubra ce ta fito da sauri ta sanar da su sarauniya na fitowa, da sauri sauri hadiman suka isa bakin 茩ofar suka tsaya su kuma dogaran nan biyu 蓷aya ya fita da sauri dan dolenshi ya tabbatar babu kowa a kan hanyar wucewarsu kamar yadda a fada aka bu茩aci da a 茩ara wasu mintuna kafin tayar da sallah, ana so a lokacin da za'a shiga da ita gidan ya zama kowa na sallah a lokacin tunda ba za'a barta har dare ya tsala ba, 蓷aya dogarin dake magana da su Hadeeya 蓷aga bulalar yayi yana bubbugata gefe da gefe, da gangan, da saninshi ya tsala wa Hameeda dan 蓷azu ma ya so duka mata dan ta gane girman da Allah ya ba 拼ar uwarsu. 茦ara ta saki tare da dafe cinyarta da ya tsulama bulalar tace "Kammm!"
茒akin aka 茩ara bu蓷ewa jakadiya na gaba sai gimbiya Kubra sai sauran a bayansu, su Hadeeya dake tsaye dogarin ya daka ma tsawa da "Gwiwa 茩asa talakawan gimbiya, 茩arya kuke ku ha蓷a tsayi da uwar marayu."
A razane suka zube gwiwoyinsu 茩asa Hameeda da ta ji kalar bulalar nan harda sadda kanta tayi idanunta na cika taf da hawaye, wannan dogarin daya fita tare da hadimai biyun da suke jira suna jiran fitowarsu ne suka 茩araso, sula duk zagaye gabanta da bayanta sukayi, hakan yasa aka saka Saleema tsakiya wanda duk baza idanun Hadeeya ta kasa ganin ko da kayan jikinta bare ta ga fatar jikinta.
Gashi tafiya suke tamkar wa蓷anda basu da lafiya, tafiya kamar marasa kuzari, har ita kanta Saleema da kanta ke lullu蓳e cikin alkyabbar da aka rufe jikinta ruf da ita take ganin yaushe zasu kai da wannan tafiya? Ita kam da sun bata ma damar ganin Mamanta, dan rabonta da ita tun kafin sallah la'asar da suka sakata tsakiya ita da Abbanta suka mata nasihar da har yanzu haway take dan ji tayi tamkar za ta rabu da su ne na har abada. Suna kawowa daidai falo Gaishata na fito daga