Showing 105001 words to 108000 words out of 191031 words
da zagina, kuma Momma..."
Hankali tashe tace" Kuma me? Zeid 蓷in ne ya zageki?"
Cikin kuka tace" E Momma, ni dai ki fa蓷a min yadda zanyi kawai."
Ajiyar zuciya ta sauke dan wasu lokuta Hadeeya mamaki take bata, shin soyayyar Zeid ce ta mata yawan da ga damuwa 茩arara amma take 蓳oyewa? Ko kuma dai wata muguntar yake mata da take mugun tsoronshi? Cikin nutsuwa tace" Ki kira Ummeeta mana ta je ta kama miki, ko kuma wata daga cikin 茩awayenki, Hameeda dai ba iyawa za ta yi ba dan kinsan ita ko jikinta ba son tashi take ta gyara ba, idan ma na tura miki ita aikin banza ne saidai ku taru ku lalace."
Hankali tashe Hadeeya ta sake fashewa da kuka tace" Allah ya sawa茩e min na kira 茩awayena, Momma ni yanzu ma na hana kowace 茩awa zuwa min gida, dan in suka zo sai Zeid ya yita kallonsu yana musu hira da basu kyauta idan zasu tafi, Momma ranar fa Ummeeta ke fa蓷amin ta ga lambarshi a wayar wata 茩awarmu Habiba, ni kawai ba zan kira kowa ba."
Rintse idanu Ardiya tayi a ranta ta furta" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" A zahiri kuma sai tace" To ita Ummee a ina ta san lambarshi da har take iya ganewa a wayar wasu? Hadeeya dama mijinki 蓷an iska ne?"
Ranta ne ya sosu matu茩a dan duk lalacewarshi a haka dai ta koyi sonshi kuma tana masa fatan shiriya, rai a jagule tace" Mommaaa! Ni dai ki taimaka min."
Ta蓳e baki tayi tace" Hadeeya bana so ki zama sakaryar mace da namiji zai dinga juyawa, wallahi ki murje idanunki ki nuna masa ke fa ba kanwa lasa ba ce, kada ki yarda yayi anfani da yarintarki ya dinga cuta miki, ki zage dantse in zaki iya idan ba haka ba wata rana kukan jini zaki yi nake fa蓷a miki."
Numfasawa tayi sannan tace" Ban san wa zai aika miki ba kuma sai dai in ni zanje mu yi aikin tare."
Da sauri Hadeeya tace" Ke fa Momma?"
Banza ta mata dan ta gama 蓳ata mata rai, kamar wata wacce ba ta yi karatu ba? Kamar ba wayayya ba za ta zauna tana wani shan wahala a hannun namijin da gasu nan birjik a gari, tana cikin tunanin haka kawai tayi saurin cewa" Yawwa kina ji?"
A sanyaye Hadeeya tace" E." 茒orawa tayi da" Bari na kira Autynku (Safiya) sai na sa ta tura miki wannan 拼ar zaman banzan da ba komai take a gida ba sai shiga madafa."
Cike da jin da蓷i Hadeeya tace" Yawwa Momma ya ma fi, tunda ita 拼ar uwata ce ai ba zai kalleta ba ma."
Ta蓳e baki Ardiya tayi tace" Hummm!" Sannan tace" Kina zuwa makarantar kuwa? Ko ya hanaki?"
Da sauri tace" A'a Momma ina zuwa, ai bai isa ya hanani ba tunda al茩awari ya muku zan yi karatuna har na samu aiki."
Jinjina kai tayi cike da garga蓷i tace" Kuma ki kula da kyau, ina sake jadadda miki kada ki kuskura ki 蓷auki ciki yanzu, wallahi kina yin wannan kuskuren kin gama ta蓳ewa yarinya, dan laulayi ba zai barki karatunki ba, idan kika haihu reno ya hanaki ta蓳uka komai, kafin ki farga Hadeeya kin zama matar gida mai ciki da haihuwa kawai, wannan jar fatar taki da 茩walisa duk zasu zama labari."
Shiru Hadeeya tayi ba tace komai ba, yo ta ya za ta yarda ta fa蓷a mata yanzu haka ciki ne jikinta, kuma akan ta nuna bata so ne tun jiya yake daddaga mata bala'i, duk iskancinshi da lalacewarshi yana son haihuwar, saida ya yi kamar zai cinyeta 蓷anya dalilin haka har ya ce mata idan ta cika 拼ar iska ce ta cire cikin dan Allah ta gani, shi kuma da ba ita ba har uwarta sai ya yi shari'a da ita daga nan har duniya ta na蓷e. Ba ta san ya zatayi ba yanzu? Ta yi shiru ne kar Mamanta ta ji? Ko kuma ta fa蓷a mata duk fa蓷an da zata mata dai ba zata daketa ba ai. A qanyaye ta amsa mata da "To Momma." Sukayi sallama dan bata so maganar ta yi tsayin da za ta sakata fallasa kanta.
Da zuciya 蓷aya Safiya ta tura Saleema gidan Hadeeya dan ta taimaka ma 拼ar uwarta, saidai tuni Safiya ta sa ma ranta cewa Hadeeya ciki ne da ita, dan ko zuwanta na 茩arshe gidan ta kula da 蓷an dabinon dake bakinta tana ta tsutsa, to amma tunda komai nasu a 蓷aki sukeyi ba'a bari kowa ya ji, sai ba ta nuna ta sani ba kawai tana mata fatan in ma shine to ta sauka lafiya, dan cikin na yanzu wanda ya ta蓳a yi ma ya suka 茩arata da haihuwar nan bare sabin shiga. Haka Saleema ta isa gidan a adaidaita sahu, tun shigarta take cin karo da abubuwanda basu kwanta mata a rai ba har ta shiga falon.
Hadeeya na kwance kan kujera da waya tana latsawa, kusa da ita daga 茩asa kuma ledoji ne ba茩a茩e da kallo 蓷aya ba zaka san me ye a ciki ba, 茩arewa falon kallo tayi sannan ta 茩arasa shiga da sallama, da sauri ta tashi zaune da fara'a a fuskarta saidai bata amsa ba, tashi tayi ta fito farfajiyar ta tofar da yawu kafin ta koma, kallonta Saleema ke yi kamar ba ta ta蓳a ganinta ba, yadda jar fatar nan ta wani ko蓷e ita ba dan ace ta zuga abun ba sai tace kamar yaushi yaushi ta gani a jikinta na rashin gyara da kula da kai, sam jikinta ba alamar tana kula da shi, haka kuma yanzun haka ba alamar da ta nuna ta yi wanka, idan ma tayi to jikinta bai ga mai ba bare maganar kwalluyar da aka 茩ware wajen 蓷aukarta a gida.
Gaisawa sukayi a sama sama dan ba wani sakewa ne dama a tsakaninsu ba, hakan ba dan babu soyayyar 拼an uwa ba ne, kawai daga iyayensune ne matsalar, hakan yasa har yau babu sha茩uwa idan ba su da suka fito ciki 蓷aya ba. Ledojin dake gabanta ta nuna mata tace "Aunty Saleema kin ga naman nan yanzu ya kawo, sai ko duba ki ga me ya dace muyi? Bayan la'asar ne zasu zo."
Mi茩ewa Saleema tayi ta dur茩usa wajen ledojin ta fara dubawa, nama ne har kala uku, kayan ciki, naman rago, da kuma naman zabi, kallon Hadeeya tayi tace" Me kike so a yi?"
Turo baki tayi tace" Aunty ai wannan aikin ya mana yawa mu biyu, ki 蓷auki wanda kike son yin aiki da shi, sauran sai a saka a fridge a ajiye, na dinga aiki dashi daga baya."
Kallonta Saleema tayi tana mi茩ewa tsaye tace" Haka ya gaya miki?"
Girgiza kai tayi a hankali tace" A'a."
A sanyaye tace" Dan haka zamu iya, in sha Allah."
Cire hijabinta tayi ta aje kan kujerar sannan ta kwaso ledojin ta fito da su waje, madafa ta shiga ta 蓷auko kayan aiki da duk abinda za ta bu茩ata, a tare ta 蓷ora silalar naman ragon da na kayan ciki bayan ta saka musu komai da ta ga mahaifiyarta na yi, kafin ta shiga gyara zabin nan ba tare da ta yanyankasu ba ta cire wuya kawai da wajen yatsun, wankesu tayi sosai kafin ta aje dan su tsane.
*Alhamdulillah.*
13/06/2022 脿 17:25 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_36_
Silalar kayan cikin ta sauke ta tsane ruwan ta aje kayan cikin daban dan bata bu茩atar ruwan, naman ragonta ma daya dahu saukeshi tayi a wuta sannan ta 蓷ora silalar zabin nan guda uku bayan ta saka musu dafaffen 茩wai a ciki da albasar data yanka da fa蓷i tare da tarugu babba guda ba tare da ta yankashi ko sa蓳awa ba, sannan ta yanka dankalin turawa kamar za ta soya sai ta saka a ciki shima, hakan yasa zabin suka zama 茩osassu tamkar girmansu ne a haka sannan ta 蓷inki bakinsu da zare da sabuwar allura, komai na kayan 茩amshi ta saka musu tare da 蓷an蓷ano, basu jima a wuta ba ta sauke dan bata bu茩atar su silala su ragargaje, Hadeeya dake 蓷aki kwance 茩afafu a mi茩e tana kallo tana shan iska ta samu tace "Hadeeya wurin gashinki yana yi?"
Waro idanu tayi tace "Kai! Ban ta蓳a aiki da shi ba aunty."
Juyawa tayi cike da takaicin abubuwan da take ta gani a gidan 茩anwar ta ta da kuma mamakin kiranta Aunty da take wanda ba ta haka idan ba wani abu take so a wurinta ba, ko da ta bu蓷a wurin gashin 茩ura ce bajaja, hakan yasa ta dagewa ta shiga gyara wurin ta wanke duk abubuwan na gashi, kafin su tsane ta shiga soya miyarta ta kayan ciki ba tare da tayi aiki da ruwan silalar ba, dan sune suke 蓳ata miyar ka ga tayi kauri sosai har mai tsantseni ya kasa ci, sannan su yi mai茩o gana ci hannunka na daskarewa tsabar mai. Ta na zuba kayan cikin ta shiga 茩o茩arin gasa zabinta data sake linde jikinsu da ha蓷in mai da da 蓷an moutarde da jajjage, ta kunna oven 蓷in dan 蓷orawa kawai ya 茩i yi, haka ta yi juyin duniya amma ya 茩i yi, 茩arshe ha茩ura tayi dan ta san rashin aiki da shi ne ya kawo haka. Tukunya kawai ta 蓷ora a wuta ta zuba mai isashe dan ta soya.
Shigowarshi kenan ya ji gida ya gauraye da 茩amshin girki, abu ne da bai ta蓳a ji ba tunda ya ke, dan ko girkin amarya da aka yi na kwana biyu shi dai bai ji haka ba, da mamakin me ya samu Hadeeya wa kuma ya canzata ya nufi masafar, saidai daga bakin 茩ofar ya tsaya cak! Yana kallon sarautar Allah, she蓷an la'ananne ba inda ya ja idanunshi sai kan 茩ugunta, har hakan ya jefashi tunanin to "Wai kakarsu ta wajen uba ke da mazaunai haka?"
Shi dai ya ga hatta 拼ar 茩aramar nan Hamdeeya haka take da dan茩areren 茩ugu, kuma abun fa kamar mataki mataki ne da ke aiki da shekaru, Saleema ta di Hadeeya, Hadeeya ta di Hameeda da dai saurensu, cije le蓳enshi yayi har yayi nasarar ha蓷e le蓳enshi a cikin bakinshi yana lashewa inda ya kai hannunshi na hagu kan hantsar wandonshi ya ri茩e yana hango wani abu daban da ba wanda zai iya hasasowa sai shi.
"Shhhhhhhh!" Wannan mummunar 蓷abi'a ta jan yaji da yayi yasa Saleema saurin juyowa a tsorace, dan tunda ta fara aikin Hadeeya ba ta le茩o wajen ba bare a yi zancen kama mata, ganinshi tsaye a gabanta sai wani mayen kallo yake mata yasa ta ha蓷e fuska tace "Hadeeyar ta na 蓷aki."
Ta 茩arashe da wurga masa harara amma ba ta juya ba, ganin ya tsurawa 茩irjinta idanu kamar wanda baya hayyacinshi yasa ta 茩walawa Hadeeya kira, da sauri ya dawo hayyacinshi tare da juyawa yana kallon 茩ofar yace "Sannu da aiki, ashe auntynmu ce."
Harara Saleela ta wanka masa a ranta ta ayyana "Auntyn uwarka ba, maye."
Ciki ya shiga Hadeeya ta bi bayanshi, gaba蓷aya ta gane me yanayinshi yake nufi, dan haka suna shiga a marairaice tace "Yayata ce, ba ka ce mata komai ba?"
Wani kallo ya mata yace "Wai ke me kika 蓷aukeni?"
Girgiza kai tayi tace "Ba komai."
Juyawa yayi zai shige 蓷akinsu sai kuma ya dawo da baya, yana zuwa yaja 茩ugunta ya ha蓷a da na shi yayi niyyar kai bakinshi cikin nata, tsammm! Ya dakata tare da tureta gefe yace "Je kiyi wanka, ina jiranki."
茒akinshi ya shige ita kuma ta bishi da kallo, 蓷an kakkawar da kanta tayi gefe tana so ta shinshino abinda ya ji da ya sa yace lata ta je ta yi wanka, sai kuma ta ta蓳e baki kawai ta nufi 蓷akinta dan ba damar cewa a'a, idan ma ta ce har gaban Saleemar zai tausheta kuma ya mi茩e ba ruwanshi shi kam.
*Har* Saleema ta gama aikin nan tas ta 蓷auki kwanukan da suka dace ta zuba abincin nan ba ta jin motsinsu, ita dai abun bai dameta ba amma har suka fara saka mata tunanin abinda ke faruwa a 蓷akin, dan kar ta zauna shiru sai kawai ta shiga kiciniyar share madafar da goge komai saida ta ga ta yi 茩yalli, amma har lokacin shiru kuma gashi tana tsoron shiga 蓷akin, sai ta shiga share farfajiyar ma ta yi ta gyaran da ba'a sakata ba.
Ana kiran sallah magriba suka fito da wasu kayan a jikinsu ba na 蓷azu ba, Saleema ba ta kula da tsiyarsu ba sai alwala da tayi ta shiga 蓷akin ta kabbara sallah, har ta idar Hadeeya na zaune, tana idawa ta kalleta a gaggauce tace "Ba茩in da aka ce zasu zo da la'asar gashi magriba tayi."
Murmushi Hadeeya tayi tace "Ya fa蓷a min wai sai anjima."
Ta蓳e baki Saleema tayi tace "To ni dai na miki mai wuyar, kinga Mama cewa tayi kar na kai magriba, ga abincin nan sai ki 茩arasa abinda ban yi ba."
Jakarta ta 蓷auka mai wayarta a ciki ta kama hanyar ficewa, da sauri ta mi茩e ta biyo bayanta tana fa蓷in "Ki tsaya ko abincin ki ci mana."
"Um um." Ta fa蓷a dan gaskiya sun gama 茩ular da ita daga shirun da sukayi suka shareta tamkar wata banza a gida, duk da dai ta san akwai uzurin da zai iya kawo hakan, amma ai kawaici ma na da da蓷i, da sauri Hadeeya ta ri茩o hannunta tace "To dan Allah ki jira ya dawo sai ya kaiki gida, masallaci ya tafi."
Girgiza kai tayi tace "A'a ki barshi nagode." Ganin ba yadda zatayi da ita yasa ta fa蓷in "To dan Allah ki jirani, dan Allah."
Tsayawa tayi tana basarwa ranta duk a jagule, jim ka蓷an Hadeeya ta fito da ku蓷i a hannunta ta mi茩a mata, girgza mata kai tayi tace "Mama ta bani ku蓷i, ki barshi kawai nagode, ni dan Allah na zo na taimaka miki."
Game fuska Hadeeya tayi tace "Nima dan Allah na baki ba dan kin min aiki ba."
Sake girgiza kai tayi tace "A gaskiya ba zan iya kar蓳a, amma idan kin matsa gwara ma ki 蓷an 蓷eba min 蓷aya daga cikin abincin na kai wa Mama ta ga shaida."
Har zuciyarta ta ji da蓷in hakan, da sauri ta juya tace "To shikenan ina zuwa." Ba ta fi minti 蓷aya ba ta dawo da kwano ta zubo mata romon kayan cikin da ta ce su take bu茩ata, dan ita naman tsintsaye ba wajen kukanta bane (馃槦baki da wayo ashe? Ba ki san da蓷i) abincin ka蓷ai ta amsa ban da ku蓷i ta mata sallama ta bar gidan.
Tunda Zeid ya dawo gidan gaba da gaba ya nuna mata bai ji da蓷in barin Saleema ta tafiyarta ba da tayi, ta nuna masa ba laifinta bane amma ya ce 茩arya take, kawai kishinta ne na banza da wofi dan ta ga Saleema ta fita komai, ba茩in ciki uya ba茩in ciki ya kama Hadeeya, ta yi kuka kamar za ta mutu tare da kallon kanta a madubi ta ga da me Saleema ta fita? Le ye ya gani a jikin Saleema da zai fa蓷a mata haka? Kenan 拼ar uwar ta ta ma bata tsira ba? Ya gama kalleta tas kenan, haushi sosai ya kamata tare da cin alhwashin duk aikin da zatayi sai dai ta yi abunta amma ba za ta nemi kowa taimako ba.
______________
Tana zaune ita ka蓷ai da littafinta a hannu tana karantawa lambar 蓷azu da safe ta sake kiranta, saida ta yi kamar za ta tsinke kafin ta 蓷aga bayan ta ga rashin dacewar 茩in 蓷gawar, a 蓷an kakkauce suka gaisa kafin shiru ya biyo baya, sai kuma ya nisa yace "Me yasa kika kashe kiran 蓷azu?"
A sanyaye ita ma tace "Me yasa ka kirani?"
Ta蓳e baki yayi yace "Tambaya kan tambaya, hakan 蓷abi'arki ce?"
Da sauri tace "A'a malam, kayi ha茩uri."
A dake yace "Ki kirani da alhudahuda mana, ko kuma ki ce Huzeifi."
Murmushi ta saki ta sinne kai tace "Ka yi ha茩uri."
A nutse yace "Na kiraki ne dama dan na tambayeki, idan kina bu茩ata ki tsayar da lokaci Fareeda za ta je ta dinga koya miki 蓷inkin har gida."
Zabura tayi ta gyara zamanta, cike da rashin gasgatawa tace "Da gaske kake malam? Gida fa?"
Cike da tabbaci yace "E, na ji tana fa蓷a ba zaki samu damar zuwa nan ba."
"Ahhhhhhhhhh! Wayyo! Mama, Mama, Mama zo ki ji, Mama? Wayyo Allahana da蓷i." Duk ihun nan da take tana nufa hanyar fita daga 蓷akin, kamar yana gabanta ya dafe gaban goshinshi ya furta "Aouchhhh!"
Tsit! Tayi dan sai lokacin ta tuna waya fa take, a sanyaye tace "Ah, ka yi ha茩uri fa."
Cikin sigar zolaya yace "Bana tsammanin kunnena yana nan."
Dariya tayi sai kuma ta tsaya daga inda take tace "Malam, a gaskiya kana da kirki, ban ta蓳a tsammanin hqka daga gareka ba, nagode sosai da taimakon nan da za ka min, idan ka min haka ka cika min burinq na gidan duniya, nagode sosai."
Kamar ta tuna da wani abu kuma sai ta numfasa tace "Amma Abbana, ban san ta ya zan yi haka ba izininsa ba? Bana so na sake 蓳ata masa rai."
Da sauri kuma tace "Amma karka damu, ko gobe ma ta fara zuwa, tunda ai shi ya ce bani ba zuwa wajen koyon 蓷inki ne, kaga sai na koya kamar yadda na yi karatuna."
Kamar kuma wacce aka ragewa sauti sai ta sauke numfashi tace "Kashhh! Dan Allah ka tayani addu'a mahaifina ya fahimceni."
A sanyaye sosai Huzeifa daya kasa kunne yana saurarenta cike da tausayi yace "Ana samun irin haka dama a wajen iyayenmu, sau da dama iyayenmu suna 蓷aukar burikanmu a matsayin zubar mutumcinsu ko kuma 茩as茩anci a garemu, da fari ki bi maganar mahaifinki, sai dai ki sani abinda kikayi na karatu yayi daidai, dan babu biyayya ga ababen halitta wajen sa蓳awa mahalicci, a nan kuma zamuyi duba da yadda kika 蓷auki burinki, da kuma yadda ake neman tauyeki, da fari idan mukayi duba da rayuwarki ta yanzu zamu iya cewa akwai cutarwa a ciki, kiyi ha茩uri idan baki ji da蓷in abinda