Showing 33001 words to 36000 words out of 191031 words

Chapter 12 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

68018

kalli Alhaji Auwal tace "Wani shirun ma amsa ce."

A hankali ta rusuna ta aje farantin abincin sannan ta mi茩e tsaye tana kallon Alhaji Auwal tace "Idan har ka yi ya茩i she蓷an kuma ka yi nasara, to na san za ka yi abin da ya dace kan lamarinshi, sannan za ka ci gaba da yi har sanda mai rabawa za ta rabaku kuna mai cike da alhini da 茩aunar junanku."

Idonta cike da hawaye ta matso kusa da Alhaji Auwal ta 蓷an ri茩e hannunshi tace" Abba, kafin kai ko shi wani ya bar duniya, ya kamata ya shaida arzi茩i da ikon da Allah ya baka ta sanadiyar jajircewarshi a kan ka har ka zama hakan."

Juyawa ta yi ta kalli tsohon da fara sharar hawaye saboda ta蓳o masa ciwon da ya jima yana gwaguyarsa, cike da tsokana ta marairaice ta kama kunnuwanta tace" Ayya! Papi ya na kuka saboda na ta蓳a masa 蓷an gudaliyarsa."

Da sauri ta ri茩e hannunshi 蓷aya tace" To a gafarceni ba zan sake ba, na barku lafiya."

Ta fa蓷a tana ficewa a 蓷akin da sauri-sauri, jiki a matu茩ar sanyaye tsohon ya bita da kallo yana mai saka mata albarka, ko ba'a samu canji ba a茩alla dai ta sauke nauyin da ya hau kanta na fa蓷in gaskiya da gyara kayanka, Alhaji Auwal kuma kanshi na sadde ya kasa 蓷agawa saboda tsananin kunya da nadama da kuma 茩udirin gyarawa da ya 蓷arsu a zuciyarshi yanzu yanzun nan.


Tsugunno ya yi a gaban mahaifin na shi ya ri茩o hannayenshi kanshi a 茩asa cikin muryar da ke 蓷auke da amon nadama yaxe "Baba ka yi ha茩uri ka yafe min, na tuba Baba ba z..."

Da sauri yace masa "Shikenan Auwalu, ya isa haka ka ji ko, ni dama ban ta蓳a ri茩eka a zuciyata ba, saboda na san illar hakan, bana so mutuwa ta riskeni ina mai hushi da kai, shiyasa duk yanda raina ya 蓳ace a game da halin ko in kula da ka ke nuna min sai na yi gaggawar yafe maka."

Hannayen mahaifin na shi ya 蓷ago ya sumbata har sau uku sannan ya dur茩usa gwiwoyinshi ya rumgumo tsohon na shi ya sumbaci wuyanshi, shi kuma da abun ya zo masa da rashin sabo sai ya ji kunya ta kama shi, rintse ido ya yi sai dai yana jin 茩aunar 蓷an na shi na sake narkuwa a cikin jikinshi, 蓳angare 蓷aya kuma soyayya yarinyar nan ya ji ta mamaye zuciyarshi da kuma saka mata albarka. Alhaji Auwal ma albarkar ya ke saka mata tare da ba wa kansa tabbacin wannan dole ma ta zama surukar gidanshi, wata zuciyar kuma na raya mi shi ba dan 蓷anshi ya rigashi ba ai da shi zai so samun wannan *zinariyar waliyiyar*, dan babu wanda ba ya son alkairi wa kansa? Amma a hakan ma idan har ta zama matar 蓷anshi, to shakka babu za ta ci gaba da 蓷orasu a sira蓷in rayuwa mi茩a茩茩iya.

Bai fita a 蓷akin nan ba sai da ya ba wa mahaifinshi abinci a baki ya sha maganinshi, wani abun farin cikin kuma yanda suke hira tsohon na ta蓳o yarinyar Alhaji Auwal wanda shi bai san ya yi ba, wani kuma ya sani amma ya manta saboda shekaru, sai ya sake yarda da abin da Saleema ta fa蓷a cewa har yanzu shi a 茩aramin yaro yake kallonshi tunda shi ya haifesa, to in ba haka ba har fa labarin lokacin da ya yi bayan-gari yake bashi daga makaranta, haka ya 蓷auki awa biyu suna nisha蓷i kuma har zuciyarshi sai ya ji kamar ya sauke wani nauyi mai girman gaske da ya jima yana dakonshi a kai.


A farfajiyar gidan suke zaune kowa ya na abin da ya fisheshi, motar Mu'az ce ta shigo gidan ya nufi inda ake aje motocin, da gudu Hamdeeya ta tunkareshi dan tarbanshi, kamar an kirata ita ma sai kuwa ta mi茩e duk da kayan da ke jikinta. Ta wutsiyar ido Saleema ta kalleta sai kuma ta maida dubanta ga gyaran persil 蓷in da take taimakawa Nafissa, har ya fito daga motar yana ri茩e da hannun Hamdeeya, ita ma Hadeeya ta na 茩arasawa ta ri茩o hannunshi tana kallon kyakyawar fuskarshi tace "Sannu da zuwa Yayana."

Kallonta yayi da fara'a ya amsa da "Sannu budurwata, kina lafiya?"

Farrr! Ta masa da ido alamar e, 茩are mata kallo yayi ya kanne mata ido 蓷aya yace "Uhum! Kin ganki kuwa? Gaskiya kin yi kyau sosai."

Murmushi tayi tace "Dama kai na yi wa."

Da mamaki yace "Da gaske?"

Jinjina kai tayi, 蓷an kallon Hamdeeya yayi ya mi茩a mata wayarshi yace "Je ki ina zuwa."

Kar蓳a tayi da farin ciki ta juya shi kum ya kalli Hadeeya ya saki hannunta ya ri茩e ha蓳a yace "To juya na gani in dai ni aka wa kwalliyar."

Rufe fuska tayi da tafukan hannaye alamar kunya, a haka kuma ta juya masa bayanta sannan ta juyo, daga sama har 茩asa ya 茩are mata kallo, irin 蓷an guntun siket 蓷in dake jikinta da rigar, ba 茩arya kayan sun mata kyau, matsowa ya yi kusanta sosai ba tare da ta ankara ba ta ji ya shafo mazaunanta cikin wani irin yanayi yace "Gaskiya 茩anwata ke babbar yarinya ce..."

Da sauri ta kalleshi amma yanda ya yi narai-narai da ido kamar zai yi kuka yace "Ba ki ban amsa ba har yanzu, ko dai..."

Sai kuma yayi shiru ya jawo hannunta gaba-蓷aya ta fa蓷a 茩irjinshi ya tsare fuskarta da kallo, kallon fuskarshi ita ma take tana ganin idan fa ta samu guyen nan ba 茩aramin kamu ta yi ba, masha Allah son kowa 茩in wanda ya rasa, ga wata 茩asumba da gemu irin na 拼an zamani da ya ma fuskarshi 茩awanya. Da sauri ta dawo hayyacinta sanda ya sake fa蓷in "Ina jinki mana cheri, ko dai ban miki ba ne?"

Lumshe idonta tayi tana tantance 茩amshin me ye bakinshi ke fitarwa? Inibi ko tuffa? Take she蓷an ya saka mata wani tunani cewa "To ai dan ya ta蓳ani ba wani abu ba ne, wayewa ce kawai, kuma da babu kyau ai da Mamanmu ba ta yi a gabanmu ba ita da Abbanmu, dan haka ba komai ba ne, kuma ma ai so na yake shine zai aureni, dan haka ba komai a ciki."

Ta na gama wannan tunanin ta bu蓷e manya kuma fararen idonta ta sauke a cikin na shi, ba tare da tunanin komai ba ta zubar da ajinta ta kai la蓳蓳anta a kan kumcinshi ta sumbata, sai bayan ta yi ne kuma she蓷an ya bijiro mata da wata kunyar 茩ara durmiyata halaka sai ta rufe ido da sauri ta jaye jikinta ta ruga a guje. Da kallo ya bita bayan ya 蓷ora hannunshi inda ta sumbata ya saki wani sha茩iyin murmushi, a zuciyarshi ya furta "Tukuna ma, sai ranar da kika fara tatso min madarar da ke addabata da bakinki."

A hankali ya shiga takawa har ya isa inda bai tsammanin samun mutane, amma sai ya samu su Saleema zaune suna aiki, Nafissa ce tace "Ina wuni Alhaji."

茒aga ido tayi ta kalli Nafissa cikin ra蓷a tace "Wai Alhaji, sun je makka ne?"

Ita ma Nafissa cikin ra蓷a tace "Ai har autan gidan nan ya je."

Ta蓳e baki tayi tace "Amm..." Zabura ta yi saboda sunkuyo kanshi da ya yi daf da wuyanta kamar zai ta蓳ata, 茩urawa juna ido sukayi Saleema na kallonshi cike da jin haushin wannan 蓷abi'a ta shi, murmushi ya sakar mata ya 茩yabta mata ido 蓷aya yace "Ina sonki."

Ra蓳ata ya yi ya wuce ta bishi da harara, tsaki ta ja sannan ta koma ta zauna, Nafissa kuma dariya ta yi ganin yanda Saleema ke ta kumbura kan wannan abu da ba komai ba ne a wajen samarin wannan gida.

Daga cikin falon Alhaji Auwal ya 茩wala ma Saleema kira, da sauri ta amsa da "Na'am."

Aje farantin dake kan cinyarta tayi ta mi茩e ta shiga, tsaye duk ta same su shi da matan sun sakashi tsakiya, tana zuwa 茩asa ta dur茩usa tace "Abba gani."

Ku蓷in da ke hannunshi ya mi茩o mata yace "Yawxa yar albarka, kar蓳i wannan kin ji, ku je 拼an kasuwa yanzu ku siyo labulen 蓷aki mai kyau da carpet, sannan ki siyo sababin kwanuka guda biyu da 茩aramin tebur na tsakar 蓷aki."

Ba ta tambayi komai ba ta jinjina kai tace "To Abba."

Saida ta mi茩e sannan ta rusuna tace "Abba zan iya tafiya tare da Nafissa? Saboda dreba baya nan."

Jim ya yi kamar mai tunani sai kuma ya kalli 蓷akin Mu'az sannan yace "A'a, ku je ke da Yayanki Mu'az, bana son hawa abun hawa na waje."

Tsammm! Ta kalli fuskarshi, ta ya za ta nuna masa ba ta son kusanci da *tantirin nan*? Bare har ta fita da shi waje, kamar ya san a kan me take tunani sai yace "Karki damu kin ji, ku je tare da shi kuma kar ku jima."

A sanyaye kawai ta jinjina kai ta nufi 蓷akinta dan shiryawa ta fito, tana ji Alhaji Auwal na fa蓷awa Hajia babba ta sanarwa Mu'az za su fita yanzu.




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:40 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_15_




A sau茩a茩e ta shirya kamar dai kullum cikin shigarta ta mutumci ta fito, Hajia babba ce ta mata nuni da 茩ofa tace "Mu'az 蓷in na zuwa, ki jirashi a waje."

Hanyar 茩ofar ta nufa inda amarya dake zaune kan kujera ta bita da uwar harara cike da takaicin wannan yarinya, ita gaba-蓷aya ma ta ga komai na gidan ya sauya tunda yaran suka zo, kuma Saleema ita ce silar komai, yanzu ma gashi Alhaji na wata banzar magana wai za'a gyarawa Baba 蓷akinshi, ga wasu uwayen dokoki da ya lafta musu cewa dole yanzu wacce ta yi girki ita za ta kai masa har 蓷akin da rana ko kuma a ba cikin yaran da ya haifa, na safe da dare kuma shi kanshi zai kai mishi, sannan wai kowace safiya sai sun je gaisheshi, abun da bai ta蓳a faruwa ba! To idan ba Saleema ba wa ye ua zigashi? 茦iri-茩iri ya 蓷auko ma茩odan ku蓷i ya bata ta siyo kayan 蓷akin bayan sai da ta ro茩i ya bata dan ta san sauran canji za su zama na ta amma ya 茩i. Dan haka ita gwara ma su gama kwanakinsu su bar gidan, idan ba haka ba za ta kasa 蓳oye 蓳acin ranta har ta fatattaki yarinyar nan ta koma gidansu, dan dama uwarta ma ba wani shiri suke ba, saboda ita ma dai kamar 拼ar take, amma abun mamaki uwar ma ta fi Saleema wayewa da 蓷an cakarewa, dan ita tana saka mayafi musamman bikin 茩awaye, sannan ta na kwalliya ga uya 蓷aukar wanka sannan ga ta kyakyawa ta fi 拼ar, amma ita sai fama da hijaban da suka fi 茩arfinta, da haka ta jinjina kai da tunanin za su ha蓷e idan ta sake kutse a rayuwarsu.


*Saleema* kam ta 蓷an jima a tsaye kafin ta hangeshi ya na tahowa, juya baya ta yi har ya 茩araso ta bayanta yana fa蓷in "Matata ki gafarceni na saka ki jirana."

Bu蓷e mata 茩ofa ya yi da kanshi yace "Shiga mu je."

Shiga ta yi ba tare da ta kula shi ba, dan niyya ce ta yi ba za ta biye mishi sosai ba bare har ya ga damarta ya kawo mata wargi, suna 蓷aukar titi ya kai hannu ga redio ya kunna pm3, take sautin tattausan ki蓷a ya kara蓷e cikin motar, sanyayyar wa茩a ce ta hausa ta soyayya ka rantse babu komai a duniya sai zallar soyayya saboda yanda baitukan suka fita. Hannu tasa ta na wasa da kuncinta saboda jin Mu'az na bin wa茩ar yana ka蓷a kai alamar dai da a tsaye yake zai uya taka rawa ma, dan yanayinshi ya nuna hakan ba ka蓷an ba, girgiza kai tayi a hankali yanda ba zai ji ba tace "Allah ya shirya."

"Ameen matata." Ya fa蓷a yana kallonta sannan ya 蓷ora da "Abinda na ke son ji daga bakinki kenan, ina ji a jikina addu'arki gareni kar蓳a蓳蓳iya ce."

Numfashi ta sauke ta kawar da kai ba ta tanka masa ba, le茩a fuskarta yayi yace "Matata, hushi kikayi ne?"

Kallonshi tayi sai kuma ta sake maida dubanta ga titi, cike da tsokana yace "Gaskiya ki saki fuskarki, yanzu idan na ha蓷u da abokina ta ya zan nuna masa ke da wannan ha蓷a蓷蓷iyar fuska? Ya 蓷auka satoki na yi?"

A hankali ta furta "Ya Allah." Waro ido yayi yace "Lahhh! Wai har na dameki hakane?"

Yatsa biyu ya sa ya dam茩e la蓳蓳anshi yace "Shikenan na yi shiru, idan na sake magana ki mari fuskata irin na jiya."

Da sauri ta kalleshi dan ita kam ta ma manta da ta mari fuskar nan ta shi da alamu suka nuna yana kula da ita, sunkuyar da kai tayi cike da jin kunya, dubanta yayi da kyau yace "Hajia kin san da marin nan ko ka蓷an ba zafi? Shin tausayina ne ya hanaki marina da kyau? Ko kuma dai iya 茩arfinki ne?"

茦ala dai ba ta ce masa ba, dogon numfashi ya ja yana kallon titi yace "To! Mu'az ka yi ha茩uri, ita dama soyayya haka take, fatana bai wuce wanna. Babyn ta so ni kamar yanda na ke sonta, idan kuma ba haka ba..."

Da sauri ta kalleshi da 蓷an jin haushin takura mata da surutu tace "Idan ba haka ba fa?"

Da hannunshi ya yi alama a wuyanshi kamar wanda zai yanka ma茩ogoronshi ya 蓷an zuro harshe waje kamar wata dabbar da ta yi mummunar mutuwa yace "茦itttt! She茩awa zan yi."

Me Saleema za ta yi? Sai kuwa ta bushe da dariyar da za ta rantse tun da suka zo gidan nan ba ta yi ba, dariya sosai take shi kuma yana kallonta cike da birgewa yanda ha茩oranta ke jere reras farare tas, cikin dariya ta dafe ciki tace" Wallahi ka na da abun dariya."

Cike da 茩warin gwiwa yace" Na sani Matata, dan ma baki sakin jikinki da ni, da ba ke ba zama gum."

Wani kallo ta masa tare da 蓷an tsagaita dariyar tace" Ka ta蓳a ganin inda aka ba kura ajiyar nama?"

Tsammm! Ya yi yana kallonta, tabbas magana ta fa蓷a mai kyau, sai dai bai ji haushi ba tunda gaskiya ta fa蓷a, sai kawai ya bushe da dariya ya nuna kanshi yace" Ni ne kura?"

Wata yar harara ta galla masa tace" Ni dai ban ce ba."

Hannunshi ya kai da niyyar talla蓳o ha蓳arta dan ta kalleshi, wanda sabo ya jawo masa hakan ya manta da wacece ya ke tare, yana daf da zai kai hannun sai kuma ya tsaya cak yace" Oh! Yi ha茩uri, na tuba Allah."

Sai kuma ya 蓷ora da" Kin san wani abu, al茩awari na ma kaina zan daina duk wani abu marar kyau, saboda ke."

Ha蓷e fuska tayi idonta har sun 蓷an rarako tace" Saboda ni? Me yasa sai ni?"

Saida ya cire duk wasa ya mayar gefe cike da kamala sannan yace" Saboda ke kika tunasar da ni mahimmancin sallah, hakan yasa na fara bibiyar wa'azizzikan malamai, hakan kuma ba 茩aramin tasiri ya yi gareni ba, dan na 茩ara jin tsoron ubangijina."

Wata nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi tace" A ta茩aice dai tsoron ha蓷uwarka da Allah yasa za ka daina?"

Jinjina kai yayi yace" 茦warai."

Sanyayyan kallo ta masa mai ban sha'awa tace" Allah ya 蓷oraka a hanya madaidaiciya, Allah ya baka ikon gyara duk wani kure da ka san kana yi a rayuwarka, Allah kuma ya baka lada a kan ya茩i da zakayi da tsohuwar 蓷abi'arka wajen 茩ir茩iro sabuwar 蓷abi'a."

"Ameen, nagode matata." Ya fa蓷a yana kallonta da 茩auna kamar a ce an 蓷aura musu aure ne.

Da mamaki ta sake kallonshi tace "Me yasa ka ke kirana da matarka? Bayan kuma ka san ba haka ba ne."

茒aga gira yayi yace "To ai ina sonki, kuma na fa蓷awa su Abba sun san da maganar, har ma ya min al茩awarin zai je ya ga Abbanki, kin ga kuwa kin zama matata."

Hankali tashe ta marairaice tace "Dan Allah Yaya Mu'az ka rufa min asiri, aure da soyayya, ni sam ban ma san su ba, dama-dama ma auren tunda ta hanyarshi aka haifeni, dan Allah kar ka ruguza min burina, sannan ka ga ina karatu kuma Abba ma ya ce ba yanzu zai aurar da mu ba sai mun cimma wata 茩wa茩warrar matsaya a rayuwa."

Yana tu茩i yana kallonta da mamakin dama tana dogon surutu haka wanda bai shafi nasiha ko karatu ba? Sai kuma ya 蓷auke kai ya ta蓳e baki yace" Matata kar ki damu, idan mukayi auren za ki ci gaba da karatunki, burinki kuma ki zayyane min shi yanzu, ni zan cika mi shi da yardar Allah."

Girgiza kai tayi tana kallonshi tace" Ni dai dan Allah ka dakatar da almarar nan da ka ke rerawa, sam bana son aure a yanzu saboda wasu dalilai na."

Ba alamar wasa ya kalleta yace" Fa蓷i biyu na ji."

Rumgume hannaye tayi tace" Ba na sonka, sannan ina da burika."

Da hannu ya mata alama ya 茩an茩ance ido yace" Fa蓷a min buri 蓷aya na ji."

Wani murmushi tayi mai kama da kuka amma ba tace komai ba, cikin kulawa ya kalleta sosai yace" Uhum! Ina jinki?"

Iska ta feso daga bakinta ta ha蓷e kukan da ya taho mata tace" Babban burina shine nima mahaifina ya yi alfahari da ni, ko sau 蓷aya ne ina so ya furta min cewa *ina alfahari da ke*, zan so ya dafa kaina ya saka min albarka, sai dai ban sani ba ko zan cimma haka, dan na yi iya 茩o茩arina wajen koyawa kaina fahimtar karatu amma abun ya gagara, ban san me yake damun kaina ba, gashi yanzu za..."

Shiru tayi ta kalli Mu'az kamar a tsorace, dan gani take ta yi su蓳ul da baka sosai wajen fa蓷in abinda ke ranta ga wanda ba wata sha茩uwa ba ce tsakaninsu, goge hawayenta tayi ta 蓷aure fuska a dole ita ba komai kawai, lura da haka yasa Mu'az bai ce mata komai ba saboda a karatunshi ya karanci l'homme et le monde (mutum da duniyarsa) yasa ya bata damar hucewa kafin ya ce mata komai.

Ba wanda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login