Showing 78001 words to 81000 words out of 191031 words
na farmakarsa a sallar ta hanyar bijiro masa da tunani akan halin da take ciki yanzu. Yana idawa ya mi茩e ya dawo mota, sa茩on Hadeeya ya sake gani kamar haka _"A ganinka ita 蓷in saliha ce ba, to kura ce da fatar akuya, ban da zubar mana da mutumci ba abinda take yi."_
A gajarce ya maida mata da _" Ki fara yin mutumcin mana, kafin ki yi 茩orafin an zubar."_
Sosai sa茩on nan na shi ya sosa ranta, me kenan yake nufi? Shi ma kuma ya tura mata ne dan ranshi a 蓳ace yake kumaya fahimci kamar 蓳atanci take so tayi ga 拼ar uwarta, da wannan yanayin ya isa gidan kuma kai tsaye shiga ya yi har farfajiyar, mai aiki ce ta sanarma da Safiya yana magana, a lokacin ita kuma bata yanayin farin ciki ta ce kawai a ce ya shigo.
Daf da zai shiga suka game da Hadeeya wacce ke ri茩e da waya tana 蓷aukar hoto, harara ya watsa mata ya 蓷aue kai ita kuma ta yi saurin tare gabanshi, rai a jagule yace "Hadeeya kauce min a hanya?"
Fari ta masa da idanu cike da salon shegantaka tace "Me ya kawoka? Ai ban ce ka zo ba ko?"
Rai 蓳ace yace "Ke gusa min daga nan kafin na takaki. Ke ce za ki fa蓷a min abinda zan yi?"
Tsaki ya ja ya sake 茩o茩arin ra蓳ata ya wuce ta sake tareshi, wayar hannunta ta nuna mishi tace "Ka ga ka saurare ko kuma wannan hoton yanzun nan ka ganshi a manhajar tik tok, ka san dai labari ne mai zafi? Kuma ka yi tunanin abinda zai iya faruwa."
Da yanayin mamaki yace "Hadeeya, 拼ar uwar ta ki? Za ki iya mata haka dama?"
Ta蓳e baki tayi tace "Ita da take son rabani da kai fa, bata san ina sonka bane?"
Girgiza kai yayi yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Saboda ni yanzu sai ki tona mata asiri haka? Hadeeya har jikinta fa ya fito."
Irin kallon nan qna kai ka sani, ka yi ka gama take kallonshi alamar dai ko oho! Ba alamar wasa yace "Kinga bani wayar nan."
Da sauri ta ja baya tace "Ka 茩wata mana."
Sai kuma ta soka wayar a cikin aljihunta na bayan dogon wandon dake jikinta sannan ta juyo masa 蓷uwawunta tace "Ka 蓷auka mana, wurin ai ba ba茩onka bane."
Rintse idanu yayi wata kunya ta kamashi, sai yake ji da fa bai fara mata iskanci ba da ba ta yarda ta masa haka ba, kenan ya zai yi yanzu? Bu蓷a idanu yayi ya sauke numfashi yace "Yanzu me kike so?"
Nunoshi tayi da yatsa tace "Kai, kai na ke so."
Girgiza mata kai yayi yace "Me yasa kike sona? Jikina ko wani abun?"
Kanne masa ido 蓷aya tayi tace "Duka ma..." Sai kuma ta 蓷aga masa gira tace "Kuma ma ai kai ka fara, ni ina sonka kuma zan aureka."
Da yanayi na rarrashi yace "Hadeeya, ke yarinya ce, ba zan iya auren mai 茩asa da shekara sha takwas ba, sannan ina son Yayarki da aure."
Da yanayi na rashin wayo tace "To ka fasa aurenta mana, ni sai ka aureni."
Ajiyar zuciya ya sauke ya sassauta murya yace "Hadeeya, ki goge hoton nan dan Allah, Saleema ba ta cancanci haka daga gareki ba, dan Allah Hadeeya."
Harara ta wanka masa tace "Sai ka yi kuma, ni kaga tafiya tunda ba za ka yi abinda na ce ba."
Da sauri ya taka 茩afarshi zuwa gareta yace "Kinga Hadeeya..." Juyowa tayi tana kallonshi, a nutse yace "Kar kiyi komai dan Allah, ki bari zuwa gobe sai muyi magana."
Murmushi ta masa tare da watso masa sumbata tace "Shikenan rabin rai."
Shigewa tayi 蓷akinsu shi kuma ya 蓷an jim na wasu da茩i茩u kafin ya nufi 蓷akin su Saleema, yana shigewa mai aikinsu da ke shirin shigowa falon tana tsaye ta ji komai kuma ta ga komai, da mamakin da ya so kasheta ta shigo ta aje jug 蓷in a inda ya dace ta juya zuciyarta cike da tunani.
Tsaye yayi 茩ofar 蓷akin bayan yayi sallama, sau biyu Safiya na fa蓷a masa ya shigo, Saleema na jin haka ta tashi daga sallaya ta shige ban 蓷aki tana rintse idanunta, dan ra蓷a蓷in jikinta 茩aruwa yake ba raguwa ba, saida ya zauna kan kujerar dake daf da 茩ofar shiga ita kuma tana zaune bakin gado suka gaisa, bayan gaisuwar kuma shiru ne ya biyo baya na wasu mintoci, numfasawa yayi cike da girmamawa ba tare daya kalli fuskarta ba yace "Mama, me ya faru haka? Me Saleema tai wa Abba?"
A 茩ufule cikin 蓳acin ran dake ta azalzalarta kuma jiran dawowarshi gidan take ta amayar da abinda ke ranta tace "Fin 茩arfi mana, daga yarinya ta nuna ga abinda take so ta yi shikenan sai ya rufe min 拼a da duka, na gaji wallahi zai zo ya sameni gidan, na gaji da 茩iyayyar da yake nuna mata."
Shi kanshi Mu'az ya fahimci zuciya ce ta kai mata wuya, yau da gobe kuma sai Allah, a ladabce yace" A yi ha茩uri Mama, komai zai wuce."
Sai kuma ya 蓷an 蓷aga kanshi yace" Ina Saleema?" Nuna masa 茩ofar ban蓷akin tayi tace" Yanzu ta shiga ciki, ba ta son ka ganta ne a halin nan."
Cike da tausayi yace" Mama ba ta bu茩atar ganin likita?"
Ha蓷e abunda ya tokare mata ma茩ogwaro tayi tace" Nima na so mu tafi, amma ta ce ba ta jin komai."
Ajiyar zuciyar ya sauke ya 蓷an yi shiru, da茩i茩u ka蓷an suka shu蓷e ya mi茩e yana mata sallama, dan ya san Saleema ba zata yarda ta ganshi ba, har ya fita sai kuma Safiya ta bi 茩ofar da kallo, a kan la蓳蓳anta ta furta" Amma wa ya fa蓷a masa? Ya akayi ya sani?"
Ta 蓷auki wasu sakanni tana wannan tunanin ssai kuma ta share ta hanyar kiran Saleema ta fito daga ban蓷akin, tana fitowa kan gado ta kwanta tana sauke numfashi idanunta na tara mata hawaye musamman hannunta da ya fi mata zugi.
*Ardiya* na dawowa Hadeeya ta sanar da su abinda ya faru har da 蓷aukar hoton ta nuna musu, tsaki Ardiya tayi dan lokacin ba茩i maza ne a gidan sun zo kayan lefen Saleema, dan haka ita abun bai wani dameta ba kamar yadda kawo kayan nan ya fi damunta, gashi irin kawowar nan aka yi hatta da Safiya ba wani 蓷an uwa nata dan ba wanda ya san a yau 蓷in za'a kawo. Ardiya ba ta ji ranta ua sake 蓳aci ba saida 茩anen Alhaji Yusuf ya shigo da ku蓷in da aka kawo ya nunawa iyayen mata dan su shaida tare da goro da kuma fa蓷a musu an tsayar da rana sati hu蓷u kawai garesu. Hadeeya na kan kujera gefe tana jin sanda basu ku蓷in, harara ta dinga galla masa tana yatsina baki tana ayyana ina ma Saleema za ta yi wannan sa'ar, ai wannan milyoyin da ita suka dace ba Saleema ba.
*Washe Gari*
Kiran Hadeeya ne ya tasheshi a baccin da yake na farin cikin jiya an sake tabbatar masa da Saleema za ta zama tasa, tunda ya ga lambarta bai so 蓷auka ba da fari, saida ta sake kira na uku ka蓷ai ya 蓷aga, bai ce mata uffan ba saida ita ta fara da "Ya yi kyau Yaya Mu'az, kaga kenan yanzu sai na tura wannan hoton kowa ya gani, tunda ba ka damu da wanda zasu ganta ba."
Tashi zaune yayi da sauri yace "A'a dakata!"
Gyara zamanshi ya 茩arayi yace "Hadeeya, me kike nema ne gareni? Dan Allah ki fa蓷amin abinda kike so, daga ku蓷i, matsayi, aiki da sauransu, zan tsaya miki na ga kin samu, amma ban da maganar nan Hadeeya."
Wata lalatacciyar dariya tayi tace "Yaya Mu'az, duka abin nan da ka zana iyayena za su iya tsaya min na sameshi, ba dole sai kai ne za ka tsaya min ba."
Numfashi ya sauke yace "Shikenan, zan kiraki muyi magana."
Da yanayi na raini tace "Ka ga ni fa ba sakara bace, jiya ma haka ka fa蓷a min zamuyi magana, amma ba ka kirani ba bare muyi maganar, wallahi idan ka kuma shareni sai dai ka ga hoton tsiraicin matar da zaka aura a manhajar nan."
茒if! Ta datse kiran shi kuma ya jefar da wayar ya shiga hautsina gashin kanshi kamar zai yi hauka, zuciyarsa abubuwa d dama take raya mishi game da yarinyar nan, ba tare da tsayar da abinda zai mata ba ya tashi ya shiga wanka.
*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:50 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_29_
Tun jiya Saleema ke lalla蓳arta amma ta 茩i ko kulata, yanzu haka ma da take zaune har yanzu jikinta kayan jiya ne, a tsanake ta kalleta da ladabi tace "Mama, dan ki manta da abun nan, Mama ni fa na masa laifi, bai kamata a ce na kai 茩ararsa gun wani ba, shi fa mahaifina ne, dan Allah Mama ki daina hushi da shi, kinga fa bai dace ba sam, jiya sa in sa kikayi da shi."
Wata uwar harara ta wurgo mata a kausashe tace" Ke! In zaki kama min bakinki ki kama min, in ba haka ba zan ha蓷a dake, wato ke ko kishin kanki ma ba kya yi, ya dakeki kamar jaka amma kina bani ha茩uri, dan ya haifeki halittarki ya yi? Baiwarsa ce ke? To ba zai yiwu ba, na fa蓷a masa sai ya sakeni na bar masa gidansa."
A razane Saleema ta furta" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Mama saki?"
Nunota tayi da yatsa tace" Kar ki kuma tanka min."
Hawaye ne suka gangaro mata tace" Dan Allah Mama kar kiyi haka, Mama a kai..."
Tattausar sallamar da ya yi tasa ta ha蓷e sauran kalaman ta kalli 茩ofar, jikinta har 蓳ari yake ta sadda kanta tace" Abba ina kwana."
茦urawa fuskarta idanu yayi yana kallo, irin yansa fuskarta ta fa蓷a lokaci 蓷aya, da irin taushin yarinyar gareshi, ha茩i茩a sai a kanta ne yake sanin shi ma ubane, ba tare da wani ya tanka masa ba ya sauke ajiyar zuciya tare da kallon *rigimammiyar matarshi*, a rayuwarshi kaf bai ta蓳a sanin haka ta iya masifa da tijara ba sai jiya, wai shi Safiya ta ma tsaye ta tara hannu sai ya saketa? To ya saketa shi kuwa ya shiga gidan uban wa a duniyar nan? Ai wallahi mutu ka raba takalmin kaza, mutuwa ce ka蓷ai za ta rabashida Safiya, amma ko larura ta gidan duniya baya jin za ta iya sakashi rabuwa da ita.
茦ara takowa yayi a nutse ba tare da ya amsa gaisuwar Saleema ba ya kalli Safiya yace "Maman Hajia ina kwana?"
Kamar yadda tun shigowarshi ba ta 蓷aga kai ta kalleshi ba, haka yanzu ma kamar ba ta san yayi ba, wayarta kawai take ta latsawa, 蓷an kallon Saleema yayi da gefen idanu, hakan yasa ta saurin saukowa daga kan gadon tana saka hijabinta ta fice ta basu wuri, saidai ba ta 茩arasa falon ba ta tsaya a iya corridor dan gaskiya tun jiya kunyar fita take.
Ganin Saleema ta fita ta mi茩e za ta ra蓳ashi, da sauri ya sha gabanta tare da ri茩o hannunta, da sauri ta fizge ta kalleshi tace "Ka daina ta蓳ani."
Marairaicewa yayi yace "Soffee, dan Allah kada ki bari damuwa ta samu muhalli a gangar jikinki ma bare ruhinki, kin fi kowa sanin illar da hakan zai haifar mana."
A gatsalce ta kalleshi tace "Me wai? Cikin jikina? Kai ma ai kasan ba mai zama bane, kamar yadda ba茩in cikinka na baya ya yi sanadiyar zubewarshi, yanzu ma haka ce za ta faru, da haka na gane ba sona kake ba, rayuwata kake nema *Isuhu*."
Kecewa ya yi da dariya ya 蓷an ja baya ya nuna kanshi yace" Isuhu? Ni?"
Ba alamar wasa tace" E 蓷in, ko 茩arya na yi ba sunanka bane, na fa蓷a Isuhu."
Gumtse bakinshi yayi yana dariya yace" Shikenan na ji, yanzu dai dan Allah kiyi ha茩uri, ke ma kinsan abinda ta yi bata kyauta ba, ni fa ubanta ne, ta ya za ta kai 茩arata ga wani? Kenan ni ban isa na yanke hukunci a kanta ba?"
Fashewa tayi da kuka ta ja baya har saida ta zauna bakin gadon tace" Shine sai ta wannan dukan za ka nuna mata kuskurenta, wallahi ban yarda ba, haka kawai za ka dinga narkar min yarinya kamar wata jaka."
Dur茩usawa yayi gabanta yace" Shikenan na ji, daina kukan to, fa蓷a min ya kike so na yi? Na miki al茩awarin zan yi amma bana son damuwarki."
Kallonshi tayi tace" Ka amince ta koyo abinda ranta yake so."
Ha蓷e fuska yayi tare da kawar da kai yace" Ban da shi, ki nemi wata alfarmar."
Ha蓷e kukanta tayi tace" Shikenan, amma ka manta da nima matarka ce."
茒an 茩aramin tsaki yayi ya kawar da kai yace" Soffee, bana so fa, ki daina irin haka kamar wata yarinya, ta ya zatayi laifi na hukuntata kuma ki dinga hushi dani? Dan kinga ina damuwa ne da damuwarki?"
Mi茩ewa yayi tsaye ya karka蓷e rigarshi yace" Ki ci abinci a kan lokaci, kada ki ci 蓷an蓷ano dayawa, sannan ki sha magungunanki a kan lokaci, ki samu isashen bacci, dan Allah ki min wannan alfarmar ko dan abinda ke cikinki."
Har zai tafi sai kuma ya tsaya cak, ba tare da ya juyo ba yace" Kada ki sake ki harareni idan na juya."
茦eyarsa ta kalla dan magana ta gaskiya har tayi haramar hararen tashi, amma jin haka sai ta kasa binshi da hararar, saida ya fice ta daki gadon da hannu tace da fa蓷in" Ba zan yi 蓷in ba, ba zanyi ko 蓷aya da ka fa蓷a ba."
*08:20 na dare*
Kiranta yayi ya ce su ha蓷u a gidan cin aminci na *Kebab*, ba gardama ta ce masa za ta zo yanzu, duk da ta san dare ne kuma mahaifinta na gidan, amma a ganinta da ta ce masa za ta je kar蓳an wasu takardu an wuce wurin, addu'a zai mata har da guzurin ku蓷in adaidaita. A gaggauce ta shiga shiryawa, Ardiya dake zaune da na'ura gabanya ana ta faman lissafi ta kalleta tace "Wai ina za ki je na ga kina ta shiri? Ko ba茩o kikayi a waje?"
Turaren da take murzawa a hannayenta ta shafa a wuyanta sannan ta juyo ta kalleta tace "A'a, fita zanyi."
"Ina?" Ta fa蓷a tana 茩ura mata idanu, saida ta 蓷auki wayarta a hannu da jaka ta rataya tace "Mama Yaya Mu'az ne ya zo na zo mu ha蓷u yanzu."
A hassale Ardiya tace "Ke saurara bana son iskanci, wai me ye tsakaninki da shi? Ke baki da zuciya ne? Ba ki ga kayan Yayarki ya kawo jiya ba?"
Sassauta murya Hadeeya tayi sosai ta zauna kusa da ita tana daddana wayarta tace "Momma kinga, wani abu nake shiryawa, ban san ko zaiyi aiki ba, amma dai na tabbata zai kawo tsaiko a auren nan."
Kar蓳an wayar ta sake yi tana kallon videon Hadeeya kuma na fa蓷in "Ba na nuna miki ba jiya, to ai shima na tura masa kuma na ce masa zan 蓷orashi a tik tok, shine ya tsorata ya ce kar na zubar mata da mutumci, nafa蓷a masa idan bai amince da aurena ba sai kowa ya ga tsiraicinta, shi ne ya ce zai kirani muyi magana."
Zuba mata idanu tayi na wasu da茩i茩u, sai kuma ta washe baki da yanayin jin da蓷i ta nunata da yatsa tace" Kinga anfanin boko kenan, 拼ata mai basira."
Hannu ta bata suka tafa hakan yasa suka fashe da dariya, tsagaitawa Ardiya tayi tace" Kin san me? Ba za ki je ba yanzun, Hadeeya ke yarinya ce, dan a haufe Mu'az ya haifeki dan baiyi aure da wuri bane, na tabbata akwai abinda ya shirya miki, shiyasa ya nemi da ku ha蓷u."
Da mamaki tace" To Momma ya zanyi kenan? Idan fa amincewa zai yi?"
Girgiza mata kai tayi tace" Ba ma haka bane, zai yi wuya ya amince a sau茩a茩e haka, kinsan me?"
Ta fa蓷a tana mi茩o mata wayar tace" Tura masa sa茩o cewa ba za ki samu damar zuwa ba, da sauri Hadeeya ta shiga yin abinda ta umarceta da shi, tana turawa tace "Yawxa na tura."
Kar蓳ar wayar Ardiya tayi ta kasheta gaba蓷aya sannan ta kalleta tace "Kada ki kunna wayar nan har sai gobe da safe, kuma idan ya kiraki karki 蓷aga, idan ya turo miki sa茩o ki duba amma karki mayar masa."
Da mamaki Hadeeya tace "Amma Momma me yasa? Idan ya yi zuciya ya shareni fa? Ni fa gaskiya Momma ina sonshi."
Da fara'a tace "To ai auren na shi nake son jawo miki, idan ya ga kina rawar 茩afar nan zai ji haushinki, sannan zai ga kin fi shi matsuwa, amma idan kika shareshi bayan ke kike ri茩e da wannan makamin, dole zai ci gaba da nemanki, dan ba zai so ki tona sirrin future iyalinshi ba."
Tintserewa sukayi da dariya suka kuma tafa hannu, jinjina kai Hadeeya tayi tace" Shiyasa nake sonki Momma."
"Nima haka." Ta fa蓷a tana mi茩a mata wayarta, kar蓳a tayi ta fita a 蓷akin zuwa na su dan dama kayan kwalliyar mahaifiyarta yasa ta shigowa 蓷akin, tana ganin fitarta ta ri茩e ha蓳a da yatsu biyu ta jinjina kai tace "Mu'az kenan, in kana tunanin yi mata wayo, to ai ni na girmeka, ka ga ba zaka min wayo ba, ka jira ka蓷an, lokaci zai ha蓷aka da matarka."
Sai kuma tayi murmushi ta ci gaba da aikinta zuciyarta fari tass tana jin sun gama samun abinda suke so.
*Mu'az* na ganin sa茩onta da sauri ya shiga aika mata kira amma take ake fa蓷a masa wayar kashe, ranshi da yayi 茩ololuwar 蓳aci jefa wayar yayi kan kujerar mai zaman banza ya taka birki, ri茩e ha蓳a yayi yana tunanin duk yadda aka yi akwai mai taimakawa yarinyar nan kan lamarin nan, amma yarinya kamar Hadeeya da wuya ta iya haka, shi da ya so su ha蓷u sai sun ci abinci a hanyarsu ta komawa ya kakkafta mata marin da zai gigita tunaninta sannan ya kar蓳e wayar gaba蓷aya, dan dama bar mata wayar da Saleema tayi bai mata ba, dan ta fara masa rigima ne kawai ya rabu da ita,