Showing 30001 words to 33000 words out of 191031 words
bencin da ke cikin shagon ta zauna kamar yanda Nafisa ta zauna ta na fa蓷in "Ina wuni malam Huzeifa."
Taushin muryarshi da yanda ya amsa ba wani sakin fuska da irin rahar nan ta samari ya sa ta 蓷an saci kallon fuskarshi, kan gemunshi ta sauke ido da ke ba茩i-茩irin ya masa kyau a fuska duk da duhun fatarshi, ta na ji Nafissa na tambayar an ida, da sigar ban ha茩uri yace "Ki 蓷an yi ha茩uri ka蓷an Nafissa, shi na ke 茩arasawa yanzu, idan akwai in da za ku je za ki iya tafiya sai ki dawo."
"A'a zamu jira, ba in da za mu je." Ta fa蓷a tana gyara zamanta, jinjina kai ya yi yana rintse idonshi da 茩arfi sosai, to fa a dole zuciyarshi da she蓷an ke son fizgar idonshi ya kalli yarinyar da fitina ce kallonta a wurinshi, shiyasa ba ya so ya kalleta bare ya ji irin abin da ya ji ranar, dan ya fahimci abun a jikin *wannan ka蓷ai ya ke ji*, dan suna ha蓷a ido farkon shigowarta gabanshi ya fa蓷i tsikar jikinta ta yamutsa.
Shiru shagon ya 蓷auka, Saleema 茩arewa komai na shagon kallon take, ji take ina ma tana 蓷aya daga cikin ma蓷inkan shagon nan, garin kalle-kallen har ta juyo da kanta ta sauke a kan shi ya na 蓷inkinshi a nutse da tela ta lantarki da ko 茩ararta ba'a ji sosai. Ba tare da saninta ba ta saki baki cike da birgewa take kallon yanda ya ke 蓷inkin ta na jin kamar ta 茩wawa masa *BAIWARSA*.
Tunda ya lura shi take kallo jikinshi ya 蓷auki makyarkyata yake ji ina ma yana da 茩arfin halin da zai iya kallonta yace "Dan Allah sarara min haka, kawar da idonki a kaina."
Sai dai jikinshi 蓳ari yake sosai ta yanda idonshi suka fara disashewa yana neman yin abin da bai dace ba a 蓷inkin mutane, Allah ne ya ji tausayinshi ta hanyar jefo 蓷aya daga cikin samarin da ke zaune ya na fa蓷in" Sannunku."
Da sauri ta juyo sai kuma ta 蓷auke kanta jin Nafissa ta amsa masa har suna 蓷an hira yasa ta sake maida hankalinta gareshi ta na kallon aikin da yake, cike da tsokana matashin nan yace" Ustaza ba gaisuwa? Da alama sarauniyar jan aji ce ko?"
A hankali ta juyo ta kalleshi sai kuma tace" Sannu." Kawar da kai tayi tana yatsina fuska, hakan yasa matashin fa蓷in" Sai da na ro茩a? Wai me yasa 拼an matan yanzu ba ku san gaishe da mutane idan kun gansu?"
A take yanayinta ya nuna sam ba ta jin da蓷in takuratan da yake neman yi, ta nutsu tana kallon abin da ta jima ba ta yi ba kuma take kwa蓷ayi, amma sai wani canzen iska yake mata.
Cike da jin haushi tace "Ciwon kawunanmu ne mu ka fara sani, ta ya kawai za mu yi arhar da maza zaune a titi za mu wuce sai mun gaishesu? A cikin can akwai Yayana ne? Ko akwai Kawuna a ciki? Ko kuma Baffa na? Ba ko 蓷aya? To a kan me sai na bayyanar da al'aurata gareku dan na birgeku?"
Irin a 蓷an zafafen nan ta 蓷auke kanta daga gareshi, karaf! Suka ha蓷a ido da Huzeifa da ya dakata da 蓷inkin yana kallonta da mamakin dama akwai 拼an mata ma su irin wannan tunanin? Ganin sun ha蓷a ido a tare suka kawar da dubansu kowa na 蓷an 茩yafta ido, matashin ya kalla ya wanka masa harara mai cike da garga蓷in da ya fahimta ya kuma juya ya fice a shagon.
Kallonshi Saleema ta sake yi cikin nutsatsiyar murya da taushi sosai tace "Malam, am... Na ce, a nan kuna koyar da 蓷inki ne?"
Kallon fuskarta ya yi yana mamakin ashe dai ta ganeshi? Ya 蓷auka ta manta shi shiyasa shi ma yayi kamar bai ganeta ba, a hankali ya fara girgiza mata kai sannan ya maida dubanshi ga aikinshi yace "A'a, ba ma koyarwa."
Cikin sigar rarrashi tace "To amma ai kai ka iya 蓷inki, ba za ka koya min ba? Ina son koyon 蓷inki sosai."
Wani *sahibin* kallo ya aika mata yace "Kin ta蓳a koya ne a wani waje?"
Cike da zumu蓷i Saleema ta gyara zama tace "Na ta蓳a koya amma tun ina yarinya, amma kuma ban manta abubuwan da na koya ba, sai dai shekara takwas kenan yanzu, ina bu茩atar koyon irin 蓷inkin zamani."
Wani malalacin murmushi ya yi a ganinshi wannan 蓷in mai kama da 拼a拼an masu ku蓷i, ita ce za ta koyi 蓷inki? Ganin bai kulata ba ya ci gaba da abin da yake ya sa ta 茩ara cewa "Malam, ka fa蓷a min ko na wa ake biyanka sai na biya ni ma ka koya min?"
Kallonta ya sake yi ba ko 茩yaftawa, a kunyace ta sadda kanta 茩asa da mamakin kallon me yake mata haka? Nan ma dai bai amsata ba, dan haka ta 蓷aga idonta tare da wanka masa harara... Sai dai tana fara hararan na shi na jin haushin ya 茩i kulata caraf suka ha蓷a ido, da sauri ta juya kanta tana kallon titi cike da kunyar kamata da yayi.
Nafissa da tunda suka fara magana ba ta tanka mata ba cewa tayi "Haba malam Huzeifa, ba za ka koya mata ba?"
A hankali ya girgiza kai ba tare da ya kalleta ba yace "Ba na koyawa mata 蓷inki."
"To amma me yasa?" Cewar Saleema da sauri tana juyowa, satar kallonta yayi da tunanin wai me zai yi da za ta fahimci ba ya son suna doguwar hira ne? Ta kasa gane akwai wani abun al'ajabi a cikin nutsatsiyar muryarta wanda yake sa wa ga蓳蓳an jikinshi na amsawa zuciyarshi na dokawa da sauri, tsoro ya ke kar ya biyeta su dinga zancen ne har ya kauce 茩a'ida. 茦ura masa ido da tayi alamu ne na amsarshi take jira, a hankali ya 蓷auke dubanshi daga gareta cikin sanyayyar murya kamar wanda ba ya da lakka yace "...
*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:40 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_14_
A hankali ya 蓷auke dubanshi daga gareta cikin sanyayyar murya kamar wanda ba ya da lakka yace "Haka kawai."
茒an ta蓳e baki tayi ta kalli Nafissa da ke fa蓷in "To amma ai za ka iya fara wa da ita."
Ko kallon Nafissa bai yi ba ya ci gaba da aikinshi dan ba zai iya abin da suke bu茩ata ba, sun 蓷auki mintin da ya kai goma zaune wata mace ma ta zo kar蓳an 蓷inkinta, a mutumce ya gaishe da matar da kuma alamar sani a tsakaninsu, kujerar da ke gaban wata tela ya nuna mata yace "Zauna ko, bari a 蓷auko kayan."
Zaune tayi shi kuma ya le茩a ta tagar da ke gabanshi wajen samarin dake zaune yace "Kai zo nan."
Jim ka蓷an matashin nan na 蓷azu ya shigo yace "Gani."
Kallonshi yayi yace "Ka 蓷auko kayan Hajia."
茦arasa shiga shagon ya yi ya bu蓷a drower da suke aje kayan, a sau茩a茩e ya 蓷aukosu tare da 蓷aukar leda ya saka a ciki ya bata, godiya ta yi ta fita shi ma saurayin zai fita Saleema tace "Kai ma ka iya 蓷inki?"
Kallonta ya yi yana dariy yace "Sarauniyar jin kai, 蓷inki ai a jininmu ya ke, a nan shagon Babana ya rasu, yanzu haka idan kika shiga gidan can za ki samu 茩annaina suna yanka wasu 蓷inkuna ko suna gamewa, yayin da 茩anena ke saka mana duwatsu idan akwai bu茩atar hakan."
Kallon gidan da ya nuna mata tayi tace" Can ne gidan na ku?"
茒aga kai yayi yace" E."
Da sigar tausayi tace" Allah sarki, Allah ji茩an Babanmu."
Da fara'a ya amsa da" Ameen. "
Huzeifa kuma saida ya kalleta sanda ta ce *Babanmu*, ko a ina kuma ya za ma na su? Amma ko ba komai girmamawarta ga na gaba da ita ya birgeshi, uwa uba yanda ta kwatanta tsohon wasu da na ta, har matashin zai fita tayi saurin fa蓷in" Ba ka ji ba?"
Tsayawa yayi yana kallonta, a 蓷an kunyace tace" Dama ina da sha'awar koyon 蓷inki ne, ko zan iya koya a wajenku?"
Cike da lura ta fahimci ya kalli Huzeifa, sai kuma ya kalleta yace" To ki yi magana da babban Yaya, idan ya amince ba damuwa."
Da sauri Saleema ta juya ta kalli Huzeifa da za ka rantse ba ya gane yarensu, dawo da kallonta tayi ga matashin tace" Yayan ka ne?"
茒aga kai ya yi yace" E, shi na ke bi wa, shi kuma shi ne babba a gid..."
茒an gyaran muryar da Huzeifa ya yi ya ankarar da shi ya kalleshi, rufe baki yayi da tafin hannu yace" Yi ha茩uri Yaya."
Ficewa ya yi a shagon hakan yasa Saleema juyawa ta kalli Huzeifa ranta 蓳ace kamar ta ce" Wai me ye matsalarka?" Sai dai sam babu fuska a tare da shi bare ta yi maganar.
Yanzu kam ba wani jimawa ya gama ya mi茩e tsaye, cikin drower ya 蓷auko sauran an gogesu tsaf ya ha蓷a da wanda ya ida ya saka a leda, mi茩awa Nafissa ya yi yace" Gashi, dan Allah ki basu ha茩uri na jinkirin da aka samu."
Kar蓳a Nafissa tayi tace" Ba komai, ga ragowar ku蓷in." Ta fa蓷a ta na mi茩a mishi, kar蓳a ya yi ya sa aljihu yace" Ki musu godiya."
Mi茩ewa sukayi suka fita a shagon, Saleema ba ta sake juyowa ba bare su kalli juna, shi kuma yana tsaye har suka tsallaka titin suka shiga kwanar da mota ke jiransu yana kallon hijabinta da ke ta蓳a diga-diginta duk in ta 蓷aga 茩afar, saida suka 蓳ace mi shi ya koma ya zauna kan kujera yana godiya ga Allah da ya bashi damar cika al茩awarin da ya 蓷auka na 蓷inkin nan tunda ga shi har ya kammala ya bayar.
*Suna* isowa kai tsaye 蓳angaren suka tunkara, daf da za su shiga motar Alhaji Auwal ta danno kai cikin gidan, dakatawa Saleema ta yi yana gaba biyu daga cikin mutanenshi na bin shi a baya, tarbanshi tayi cike da ladabi tace "Sannu da zuwa Abba."
Da fara'a sosai ya amsa da "Yawwa sannu Baby, ya gidan?"
Cike da kunya ta amsa da "Lafiya lau Abba, ya aiki?"
Cikin jin da蓷i ya amsa da "Aiki da wahala yarinyata, amma tunda na dawo gida yanzu zan 蓷an huta."
Murmushi tayi tace "Allah ya baku ladar 蓷awainiya da mu."
Jim ya yi yana kallonta kamar mai son gano wani abu a fuskarta, sai kuma ya jinjina kai yana murmushi yace "茒awainiya da ku Baby ai dole, iyalinmu ne ku fa."
Ganin ba ta da niyyar shigewa ciki yasa ya nuna mata yace" Mu je ko."
Nuna masa hanyar bayan gida ta yi cike da son karkato hankalinshi tace" Abba zan je na ga Papi ne."
茒an zabura ya yi kamar wanda ya manta da tsohon, sai kuma ya mata murmushi yace" To shikenan, ni ma zan shiga yanzu na gansu idan na yi wanka."
Jinjina kai tayi alamar to ta juya ta nufi bayan gidan, shima 茩arasa shiga ya yi ya samu Hajia Rabi na mitar ina Saleema ta tsaya, shi ne ya bata amsa" Ta shiga wajen Baba ne za ta ganshi."
"Baba kuma?" Ta fa蓷a da mamaki kafin ta 蓷ora da "Me ya sa ba za ta zo ta huta ba?"
Ta蓳e baki ya yi alamar bai sani ba ya nufi 蓷akinshi, fitowar amarya daga 蓷akinta ne ta kalli Hajia babba tace "Kamar Alhaji na ji ya shigo?"
"E, ya shiga ciki." Ta bata amsa ba yabo ba fallasa, dan tsakaninsu ba wani sha茩uwa ba ce tsakaninsu da ake ma juna dariya ko sanin sirrin juna, ganin ta nufi 蓷akin yasa ta fa蓷in "Ga kayan nan an kar蓳o daga 蓷inki."
Da fara'a ta dawo da baya tana fa蓷in "Dukansu kuma?"
"Um." Ta amsa mata tana zama kan kujera, kayan ta bu蓷a ta shiga dubawa tana cewa "Kai! Gaskiya Huzeifa ya na da kirki, kin san ban 蓷auka zai gama aikin nan a 蓷an lokacin nan ba?"
茒an murmushi kawai tayi tace "Ai ya wuce haka."
"Gaskiya kam, kuma ga shi kamar dai yanda mu ka fa蓷a masa ya mana."
Kallon 蓷inkunan da hirar da suke ta蓳awa musamman kan bikin da za'a yi jibi wanda kayan shigar bikin ne na yasa har Alhaji Auwal ya fito ba ta sameshi da maganar da ta yi niyyar zuwa su yi ba, dan ba za ta bari ta yi sanya ba, dole ta daki 茩arfe da zafi-zafinshi.
Juyawa sukayi a tare suka kalleshi yana fitowa sanye da doguwar riga, cike da kissa da kwarkwasa amarya ta shagwa蓳e fuska tace "Baby, shi ne ka fito ba ka jirani ba? Gashi kuma ina son magana da kai."
茒an murmusawa ya yi yace "To ai ba guduwa zan yi ba, wajen Baba zan shiga, tun jiya rabona da su."
Hanyar fita ya kama ta bishi da kallo cike da jin 茩arfin gwiwar tabbas zai amince da abin da za ta zo mi shi da shi.
*Ya na* zuwa ya samu Saleema da mahaifinshi a 蓷akin suna ta hira da dariya, da mamakin irin dariyar da take ya 茩arasa yana zama bakin gadon yace "Me ki ke ma dariya haka?"
Wata dariyar ta 茩yal茩yale da ita ta nuna tsohon tace "Wallahi Papi ne ya ke ta cika min ciki da dariya, labari suke bani."
Murmusawa ya yi ya kalli mahaifin na shi yace "Baba, ya jikin na ku?"
Cike da tsantsar 茩auna da kulawa dattijon ya amsa da "Alhamdulillah Auwalu, ka na lafiya?"
A tausashe ya amsa da "Lafiyata lau Baba, ka ci abinci?"
Cikin sar茩a茩茩iyar murya yace "Ban ci ba, amma kai ka ci ne?"
Da alamar damuwa da tambayar mahaifin na shi yace "Baba, sai ka dinga min tambayoyi kamar wani 茩aramin yaro, hakan ya sa wasu lokuta bana son mu ha蓷u."
Shiru dattijon ya yi sai kuma a sanyaye sosai yace "To ka yi ha茩uri, na saba ne idan ban tambayeka ba bana jin da蓷i."
Da sauri Saleema ta katsesu ta hanyar dafa hannun dattijon tace "Papi, na kawo ma ka abincin ne?"
茒aga kai ya yi alamar e, mi茩ewa ta yi Alhaji Auwal yace "Ki ha蓷o da maganinshi."
Jinjina kai ta yi ta kama hanyar fita, ta na bu蓷ewa Nafissa na shigowa 蓷auke da abincin, kar蓳a ta yi ita kuma ta koma dan wasu ayyukan. Dawowa ta yi ta zauna ta zuba da kanta sannan ta 蓷ago ta mi茩owa Alhaji Auwal da ke shirin tashi ya tafiyarsa, kallonta ya yi da alamar jiran 茩arin bayani yace "Uhum?"
Saida ta yi takwaf-takwaf da fuskarta cike da sigar ladabi da biyayya a tausashe sosai tace "Abba, na yau kawai ka ba wa mahaifinka abinci da hannunka, a shekarun nan na shi zai yarda ka ciyar da shi ne ta hanyar bashi abinci a baki kamar yadda ya baka kana yaro, ba wai ta hanyar saka mai aiki ta dafa ba sannan ta kawo masa ya ci, na san an 蓷auki shekaru rabon da ka ji shau茩i na mahaifi na fizgarka, ka fizgo wannan shau茩in ko hakan ya sa ka tuna da mahaifinka na bu茩atar kulawarka, *kai ka蓷ai kawai* ya ke da bu茩ata."
Sadda kanta tayi 茩asa ta saki murmushi tace" Abba, ka na damuwa saboda yawan tambayarsu gareka, ba komai ya kawo hakan ba sai *soyayyar mahaifi ga 茩aramin 蓷ansa*, shi a wajenshi har yanzu kulawarsa ka ke bu茩ata, ba zai zama cikakken mahaifi ba idan har ya na nauyin baki wajen tambayar abin da ya shafi lafiyarka, harkokinka, farin cikinka da ma damuwarka, sannan abun farin ciki ne yau a rayuwa a ce kana da wanda ya damu da kai, Abba, wallahi duk soyayyar da iyalin nan na ka suke ta茩amar suna maka bai kai rabin soyayyar da bawan Allahn nan ya ke maka ba, hatta da 拼a拼an da ka haifa..."
Tunda ta fara maganar alamun komai na ratsashi ne ya bayyana a tare da shi, dan jikinshi yayi sanyi kuma kanshi a 茩asa yake sai dai wani lokaci ya kan 蓷ago ya kalli mahaifin na shi da alamar jin kunya, amma yanzu da ta ce wai har yaranshi sai yasa ya kalleta da mamaki, kamar ta san me kallon ke nufi sai kuwa ta ce "E Abba, soyayyar da yake maka ta fi wacce suke maka, sai dai idan muka kalla a zahiri shi ya na sonka ne saboda shi ya haifeka, su ma kuma suna sonka ne saboda kai ka haifesu, ba fata na ke maka ba Abba, a yanzu ba na jin akwai wata larura da za ta saka tsohon nan ya gujeka, amma yanzu Mu'az ko Mu'awwaz da za ka hanasu auren wacce suke so, to fa idan ba Allah ya shirya maka su ba, tsaf za su bijire maka a kan mace, kenan soyayyarsu ba ha蓷i da ta wanda ya kawoka duniya."
Burinta bai wuce kar ya ga za茩ewarta ba, ba ta so su ga ta cika shiga shirgin da ba na ta ba, sai dai kuma akwai kurakuren da take ganin ya kamata su gyarasu, saida ta 蓷an fa蓷a蓷a murmushi a ladabce tace" Dan Allah Abba kar ka fahimceni ba daidai ba, na yi magana ne saboda girma da mahimmancin iyaye garemu, idan har shi ka蓷ai ya rage maka a rayuwa, ya dace ka 蓳ata 蓷an sauran lokacin da ya rage maka wajen kula da shi, duk rayuwarsa ya 蓳ata ta ne wajen kula da kai, a yanzu da ya kawo 茩arfi yake kuma neman tallafi, kulawarka ka蓷ai yake bu茩ata, duk abin da ka ke nema da yake 蓷auke maka hankali daga nesantar mahaifinka, ba zai zama mai albarka gareka ba saboda mahaifinka ba ya farin ciki da halin da ka ke sakashi a ciki.."
Sai kuma ta kalli tsohon da ya 茩ureta da ido ya ma rasa akan me zai auna yarinyar, cikin kulawa tace" Papi, ko kana farin ciki da zaman wurin nan kai ka蓷ai?"
Da sauri Alhaji Auwal ya kalleshi da son jin amsar da zai bayar, shi ma kallonshi ya yi da tunanin ko ya masa kara? Sai kuma ya sunkuyar da kanshi 茩asa saboda ba ya so ya sosa ranshi ko ka蓷an, wani murmushi Saleema ta yi mai ciwo ta