Showing 6001 words to 9000 words out of 191031 words

Chapter 3 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67958

ta tsaya tare da juyowa a hankali tana kallonshi har ya k'araso, zagaya hannunshi yayi ta k'ugunta ya jawota jikinshi yana kallon kyakyawar fuskarta da ta firgice da tsoro, d'an jaye jikinta tayi kad'an saboda k'ofar falon bud'e take, kuma mai aiki da su Hadeeya na nan zaune suna aiki, sannan ga mai gadi dake rufe k'ofar wanda shi ma zai iya hangosu.

Jin ba ta ce komai ba yasa shi sake fad'in "Je t'茅coute (ina saurarenki)."

A duburbuce ta fara fad'in "Dama... Sani ne na ce ya d..uba min Sal...eema waje."

Kallon tuhuma ya mata yace "Ina Saleemar ta je?"

Hannunta ta kai ga wuyanta ta d'an shafo tace "Aiken ta na yi nan baya ta siyo min madara, ...shi ne fa...har yanzu ba ta..dawo ba."

Da mamaki a fuskarshi ya sake k'ura mata ido ya ja baya kad'an yace "Hajiar ta wa kika aika waje?"

Marairaicewa tayi tace "Ka yi hak'uri dan Allah."

A tsawace yace "Na yi hak'urin me? Ban fad'a muku kar wacce ta tura min yara waje ba idan ba makaranta za su tafi ba?"

Kamar za ta fashe da kuka ta sake fad'in "Ka yi hak'uri, ka kira ka ce na maka kunun madara ne, sai da na duba na ga babu madara a mangaza, kuma na fad'a maka amma ka manta, shine..."

A hassale ya sake fad'in "Shi ne kika aika min yarinya waje a wannan ranar? Ina mai aikin gidan take?"

A ladabce tace "Ka san yau girkin Ardayi ne, tana mata girki ne tunda ita tana wajen aiki."

A tsawace yace "To mai gadi fa? Shi ba mutum ba ne ?"

A sanyaye tace "To ai kai ka fad'a mana mai gadi iya aikinshi gadi ne kawai, kar wacce ta mishi aiken da zai sa ya bar bakin k'ofa."

Nunata yayi da yatsa yace "Wallahi idan wani abu ya samu 'yata kan ki zan huce."

Baki wangale tace "Kai na kuma? Dan na aike ta?"

Jinjna kai yayi yace "Kina wasa kenan?"

Saleema ce ta shigo gidan rik'e da leda a hannu sai Sani mai gadi a bayanta, da sauri suka nufeta in da Alhaji Yusuf ke duba duka jikinta yana fad'in "Uwata ba abinda ya sameki ko?"

Da mamaki Saleema ta kalleshi ta girgiza kai a hankali tace "A'a Abba."

"To me ya tsayar da ke?" Cewar Safiya na kallonta da kyau, sunkuyar da kai tayi tana rarraba ido, Sani ya kalla yace "Ina ka ganta?"

Cikin ladabi yace "Wani gida ne nan kusa da shagon da aka aiketa ta shiga shan ruwa."

Da mamaki Alhaji Yusuf ya kalli Saleema yace "...




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:37 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_4_




Da mamaki Alhaji Yusuf ya kalli Saleema yace "Me ya sa baki zo gida ki sha ruwan ba? Gidan ya na da tsafta ne?"

D'aga kai kawai tayi tana ci gaba da rarraba ido alamar rashin gaskiya, Safiya dake kallonta sarai ta fahimci gidan da ta je, wato ta tsaya wajen Hafsatu mai d'inki ko? Girgiza kai kawai tayi ta mik'o hannu ta karb'i ledar aiken ta shige ciki, cike da farin ciki Saleema jin Abbanta bai mata fad'a ba, Mamanta ma haka sai kawai ta shige ciki da zumud'in wayewar garin gobe dan ta je ta nuna wa Hafsatu d'inkin da ta yi kamar yanda ta buk'ata.


*Tana* idar da sallah azahar ta fito kai tsaye k'ofa ta nufa wajen mai gadi tace "K'awata ta zo?"

"A'a." Ya bata amsa, juyawa tayi za ta koma sai yace "Ga ta nan Hajia."

Da sauri ta juyo da farin ciki ta kama hannun matashiyar da ba za su wuce tsara ba, kai tsaye d'akin Mahaifiyarta ta wuce da ita kamar kullum, tana zama kan kujera ta fara ciro litattafan da suke karatu da su, d'auko na ta tayi ta zauna kusanta tace" Yau me malam ya koya muku?"

Nuna mata tayi tace" Gashi nan, shi ne zan koya miki ke ma, kuma malam ya ce wai ki maida hankali sosai."

Da fara'a ta jinjina kai tana jin dad'in yanda malamin na su ke nuna kulawarsa a kanta, tunda aka hanasu zuwa makarantar ya ke turo k'anwarsa tana d'ora mata karatun, ya yi iya k'ok'arinshi ma su had'u da mahaifin Saleema dan su yi magana kan kar a dagula mata karatunta amma Alhaji Yusuf ya k'i yarda su had'u, dan haka Saleema ta kawo wannan shawarar duk da yana tsoron abinda zai faru, amma dai gashi izuwa yanzu har an shekara d'aya ba abinda ya faru, alamu ne na mahaifin bai iya saka ido sosai a kan yaranshi ba kenan, dan da yana saka ido akan motsin 'ya'yan shi mata da yanzu ya fahimta duba da har bayan sallah isha'i a na zuwa a d'ora mata karatun.


*Washe gari*



Mik'ewar da ta yi daga kan teburin ya sa shi kallonta yace "Mamana ba dai kin k'oshi ba?"

"E Abba." Ta fad'a tana wucewa abun ta, da kallo suka bita har ta shige d'akin, jim kad'an ta fito daga d'akin da jakarta da ta b'oye a cikin hijabi ta nufi hanyar fita, Safiya ce ta kalleta tace "Ina za ki je kuma ?"

Littafin makarantar ta ta nuna tace "Mama wajen Khairat zan je ta koya min lissafin nan."

Harara ta wurga mata tace "Kuma shine sai yanzu da safiya za ki je musu ? Ki..."

Da sauri Alhaji Yusuf ya katseta da fad'in "Karatu fa ta ce za ta je, ki barta ta tafi."

Kallon Saleema ya yi yace "Uwata ta kaina, je ki kin ji sai kin dawo."

Ai da sauri ta wuce kamar za ta daka da gudu saboda farin ciki. Tana fita ba ta zame ko ina ba sai gidan Hafsatu, kayan da ta nuna mata yasa Hafsatu mamaki da ta tabbatar mata ita tayi duk da na yara ne, da mamaki ta sake kallonta tace "Amma ta ya kika d'inkasu?"

Cike da jin dad'in an yaba mata tace "Idan Mamanmu suka je karb'an d'inkinsu ne wajen tela sai na hau na yi."

Da fara'a a fuskar Hafsatu tace "Da gaske?"

Jinjina kai tayi alamar e, ita ma jinjina kan tayi tave "Masha Allah, kinga kam da Abbanki zai siya miki tela cikin sauri za ki iya d'inki."

Kallon fuskarta tayi tace "To amma za ki dinga koya min?"

"Sosai ma." Ta fad'a tana jinjina kai, dariya tayi tace "To zan fad'a masa."


*Ko* da ta dawo ta samu Mamanta d'aki take fad'a mata "Mama, aunty Hafsatu ta ce wai na fad'a ma Abba ya siya min tela za ta koya min d'inki."

Da mamaki Safiya ta kalleta tace "To, ke kuma yaushe kukayi haka?"

Cike da shagwab'a tace "Yanzu ai na biya can."

Kallon tuhuma ta mata tace "Kin tabbata karatu kika je ?"

Jim ta yi tana kallonta da tunanin kar dai ta fad'a mata ta hanata ko ta fad'awa Abbanta, sai kawai ta d'aga kai alamar e tare da fad'in "Allah ko Mama."

Jinjina kai tayi tace "Ni dai ba zan fad'a masa wannan shirmen ba, ki bari har ki fara koyon d'inkin tukuna, idan kika iya sai a siya miki."

Takwaf takwaf tayi da fuska tace "Amma Mama ai dama cewa ta yi idan na je can na koyo na dawo gida sai na dinga aiki da telata, ta hakane zan fi sauk'in zama *mad'inkiya*."

Girgiza kai Safiya tayi tace "Saleema, abun da mahaifinki ya ke so ki zama daban, abin da ke kike so daban."

Sake girgiza kai tayi tace "Allah ya zab'a miki ma fi alkairi."

Dariya Saleema tayi cike da yarinta tace "Mama idan na iya d'inki kinga faba sai kun kai ba, ni da kaina zan muku ke da aunty da su Hadeeya." Murmushi kawai tayi a ganinta shirmen Saleema ne kawai.


*Bayan Wata uku*



Duk girman farfajiyar gidan nan ta su cike yake da maza da mata, abun mamakin kuma yanda mata da mazan ke cakud'e wuri d'aya, kafatanin taron babu macen da ke d'auke da babban gyale bare hijab, dukansu shiga ce ta alfarma dake nuna matsayin kowace da kuma rayuwar da take ciki, kusan kowace riga da siket ne jikinta ta sagala mayafinta a kafad'a, mai d'an dama dama a cikinsu ce za ta d'orashi duka kafad'un biyu, inda fuskokinsu ke d'auke da rantsatsiyar kwalliyar da suka biya mak'odan kud'i aka cab'a musu ita, wasunsu ma har da zubo da gashi suke ya kwanta har kan wuyansu wanda aka kashe ma kud'i, jaka da takalmi masu sababin tsini kuma suka ce ja bani waje.

Ba wannan ne abun tsaya wa a kalla ba sai yanda gurin ba zaka gane ina matar wane ko waccen ba, saboda bariki da wayewa ya sa kowane namiji ya saki matarsa a wani wurin yana gaisawa da abokai da kuma matan abokan, inda su ma matan ke gaisawa da abokan mazan da kuma matansu.

Takon tafiyarta yasa dayawa daga cikin taron juyawa suna kallon mai tahowa, Ardayi ce cikin tsadaddar shiga wacce ta dace da yanayinta, kalarta da kuma jikinta, wanda hakan yasa ta sake haska wurin gwanin birgewa, iya d'an kwalin dake d'aure a kanta ne kawai, duk rabin wuyan rigar nan a waje yake yayin da siket d'in ya matse jikinta sosai, komai na jikinta ya bayyana ya fito mata da surarta. Alhaji Yusuf dake tsaye kusan abokanshi yana kallonta, murmushi kawai a saki ganin yanda abokanshi ke kallonta alamu ne na ta birge sai abun ya sa ya ji dad'i da jin cewa lallai ya yanko wulak'anci wannan wurin, duk da 'yar k'ibar dake gareta amma ba za ka ganta ka ce ita ta haifi su Hadeeya ba saboda iya d'aukar wanka.

Saleema na gefe zaune akan kujerar k'arfe mai zaman mutum biyu, daga nan take hangen irin bidirin da ake inda hankalinta ya fi karkata kan irin d'inkunan dake jikin mata, duk da k'arancin shekarunta amma tana mamakin yanda mahaifinta ya fi ba wa wannan rayuwa mahimmanci fiye da komai, ita dai a kan idonta ta ga ya kashe kud'in da suka ba million baya a kan abinda za'a tarbi bak'in nan kawai saboda su tayashi murna na girma da ya k'ara samu a wajen aikinshi kasancewarshi malamin kud'i, a iya saninta ita dai ba ta tab'a ganin wata bajinta da mahaifinta ya yi ba ga addininshi da zai nuna ya na kishin addinin na sa, dama dama ma idan azumi ya zo, a masallacin dake jikin gidan na su ya kan sa wa ana fitar da abun bud'a baki ga mabuk'ata, sai kuma abun sahur idan aka fara sallah tahajjud, wannan ne za ta iya cewa aikin alkairin dazata iya shaida mahaifinta na yi.

Maida kallonta tayi kan Hadeeya da ta shirya ko ta ce mahaifiyarsu ta shiryata cikin wata arniyar rigar kanti iya gwiwoyin Hadeeyar, ta yi kyau sosai dan ka rantse ma yar turawa ce, sai dai a ganin Saleema kamar ba ta dace ba, sam gani take yi shigar ba ta birgeta ba. A hankali ta sadda kanta kan takardarta fara tas sannan ta fara zana wuyan rigar da ta ga Mamanta ta saka d'azu ita ma da za ta zo wajen taron, dan wuyan ya burgeta sosai hakan yasa ta tsurawa rigar ido ta gama hardaceta a kan ta kafin Safiyar ta saka.

Kiran da aka masa a waya yasa shi d'agawa ya na d'an matsawa daga wurin ya amsa da "Ina jinka Abdul, ka zo ne ?"

Jim ya yi alamar ya na sauraren me maganar kafin yace "Ok ina zuwa."

Hanyar fita ya nufa yana fad'awa mai gadi "Bud'e k'ofa akwai wanda zai shigo."

Bud'e k'ofar mai gadi ya yi ya fita har k'ofar gidan yana dubawa, cikin wata tsadaddiyar mota bak'on ya fito tare da matarshi da ita ma ta gaji da had'uwa, gaisawa sukayi sosai kafin ya musu alama da su wuce gaba, suna shiga shi ma ya bi bayansu da niyyar shigewa muryar Hafsatu ta dakatar da shi daga niyyar shigewar tana fad'in "Ina wuni Abban Saleema."

Juyowa ya yi yana ganinta ganin dai ya d'an shaidata wasu lokuta Safiya na kai mata d'inki yasa shi d'an sakin fuskarshi ya amsa da "Lafiya lau, ina wuni ?"

"Lafiya lau, ina Saleema ?" Ta fad'a da fara'arta, ba yabo ba fallasa ya amsa da "Ta na ciki."

Murmushi ta yi tace "Saleema kenan, akwai k'ok'ari wallahi, idan ta yi wani abun ba za ka ce yarinya ce ba, shiyasa ma na ce ta fad'a maka a siya mata telarta, dan hakan zai fi kawo mata sauk'i."

Da mamaki da kuma rashin fahimtar inda zancenta ya dosa ya gyara tsayuwarsa yace" Tela kuma?"

Ba tare da tunanin komai ba tace" E, idan aka siya mata mai aiki da lantarki ma za ta fi gaskiya."

Har yanzu dai da mamakin ya sake cewa" Dama ta na koyon d'inki ne?"

D'an shiru ta yi sai kuma tace" E, ta yiwu ka manta dai, ai kusan wata uku kenan da ta fara zuwa, dan ma ba na koya mata wasu abubuwan saboda k'arancin shekarunta."

Wani kallo ya mata lokacin da idonshi suka fara yin launin ja na b'acin rai dan jin yaudara da ha'intarshi da Saleema da kuma mahaifiyarta sukayi, wato idan ya fahimta duk lokacin da Saleema ta ce mishi za tatafi karatu can ne ta ke zuwa? Jinjina kai kawai ya yi ya shige bayan ya furta "Nagode."

Ya na shiga inda ya hangi Saleema zaune ita kad'ai ta dasa kanta k'asa ta na zana abu a takarda ya nufa, ya na zuwa kam takardar ya fincika da k'arfi, hakan yasa rabi ta yage ta bi hannunshi rabi kuma a hannun Saleema da ta d'aga kanta tana kallonshi a tsorace. Kallon takardar ya yi ya ga ta zana sanfirin wuya, duk da bai gane komai ba amma ya fahimci dai abunda aka fad'a gaskiya ne dan ga shaida nan.

Tsaye ta mik'e tana zazzare ido ta na kallonshi, tsareta ya yi da ido yace "Me ye wannan?"

Rarraba ido ta fara yi na rashin gaskiya, kafin ta ce wani abu Safiya da ta hangesu ta kuma kula kamar ba lafiya ba ta taho tace "Lafiya Alhaji?"

Rai b'ace ya kalleta yace "Me ye wannan?" Ya nuna mata takardar? Kallon rashin sani da fahimta ta ma takardar sai kuma ta girgiea kai tace "Ban sani ba, me ye wannan d'in?"

Nuna kanshi yayi yace "Ni ma kike tambaya?"

Sai kuma ya jinjina kai ya nunasu da yatsa yace "Ku jira a gama taron nan zan ji daku dukkanku."

A fusace ya wuce ya barsu inda Safiya ta kalli Saleema tace "...




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:37 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_5_




A fusace ya wuce ya barsu inda Safiya ta kalli Saleema tace "Me kika masa kuma yanzu?"

A raunane tace "Ba abun da na yi, irin wannan zanen ne fa nake yi."

Ta fad'a tana nuna wuyan rigar Safiya, tab'e baki Safiya ta yi tace "Kin tabbata?"

Jinjina kai tayi tare da cewa "Allah ko."

Jinjina kai tayi tace "Shikenan." Juyawa tayi ita ma ta barta nan ta ci gaba da abinda take. Duk wannan shagali da abinci da aka shiga rabawa bai wani d'ad'a Saleema a k'asa ba, haka take abinda take ganin zai fisheta yayin da suma suke wanda ya fishesu, sai da dare ya yi sosai kafin su fara watsewa daga gidan.


*Mamakin* dalilin da yasa ya kirasu b'angarenshi take da kuma yanda ya taso Saleema a baccin ta, gashi ya musu tsaye k'erere har da wani rik'e d'amara a hannu alamar dai duka zai yi, sai dai ba ta san wa zai daka ba a cikinsu, ita ko Saleema ? Indai ita ce abun da bai tab'a faruwa ba ne, ko mari bai tab'a had'ashi da mace ba, bar shi dai ya rufeki da fad'a idan abu ya yi k'amari ya k'aurece miki, amma ban da duka.

Zuba masa ido ta yi tana jira ta ji me zai ce, sai da ya gama kumbura da kallonsu sannan ya kalli Safiya yace "Yaushe ki ka saka yarinyar nan koyon d'inki?"

Da mamaki ta kalleshi tace "D'inki kuma? Ni ban sakata koyon d'inki ba."

Wani kallo ya jefeta da shi yace "Amma ai da saninki take zuwa ko?"

Kallon Saleema ta yi da ta fara tsuru tsuru da idonta tana kakkame jikinta a sakan biyu kuma ta kalleshi tace "Ban gane ba? Me yake faruwa ne wai?"

A d'an fusace yace "Ni ne ma zan fad'a miki abinda yake faruwa? Safiya yarinyar nan wata uku kenan ta na zuwa gidan matar can mai d'inki, kina so ki ce baki sani ba ne?"

Sake juyawa tayi ta kalli Saleema da tsantsar mamaki tace "Saleema, d'inki kike koyo?"

Mik'ewa ta yi tsaye ta ja baya tana girgiza kai cike da tsoro tace "Mam...a, da..ma."

"Dama me ?" Ta fad'a a tsawace, zabura tayi ta fashe da kuka tace "Ki yi hak'uri Mama, ba zan sake muku k'arya ba."

Dafe baki Safiya tayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Saleema k'arya kika mana dama? Da kike cewa za ki tafi karatu, dama ba karatun kike zuwa ba?"

A mugun tsawace tace "Me yasa Saleema? Me yasa kika mana k'arya?"

Cikin kuka ta kalli Alhaji Yusuf dake kallon Safiya yanda ta hahhak'e ta saye bala'in ta kasa barinshi ya furta komai, da sauri ta girgiza kai tace "Kiyi hak'uri Mama, ba zan sake ba daga yau, na rantse miki da Allah."

A hassale Safiya ta yi kanta tare da fizgar d'amarar (belt) dake hannunshi, kafin Saleema ta ankara ta damk'o hannunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login