Showing 129001 words to 132000 words out of 191031 words
蓷akin Ardiya za ta tafi gida sai Ardiya dake bayanta zata rakata, sun wuni suna gulmar suna jajanta lamarin, ga takaicin Kabil wanda da ta fa蓷a masa ma Saleema fa tayi aure ya ja mata tsaki a wayar ya kashe bai tanka mata ba, ranta ya 蓳ace sosai da abun nan da ya mata, da gudu 蓷aya daga cikin dogarawan ya shiga bu蓷e babbar rigarshi yana zazzaro musu idanu yana fa蓷in "Kawuna 茩asa, 茩asa, maza."
Jikinsu ne ya fara rawa basu san sanda suka dur茩ushe 茩asa ba Gaishata gaba蓷aya ma zaune tayi tana sadda kanta 茩asa jikinta sai rawa yake, dan tsawar da ya musu ta tsorata ta, Ardiya ma kanta na 茩asa sai "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Take karantawa.
Saida suka ga fitarsu suka 蓷aga kawunansu, take abinda Ardiya ta fa蓷a kwana biyu da suka wuce ya dawo mata, wato izgilin da ta yi ne take ganin ai abu ne da ba zai faru ba, sai gashi yana faruwa da uta yanzun nan, Saleemar da suka rayu tare, ita ce yanzu har ake kakkarewa idanunta ma suka kasa ko da hango suturar jikinta in ba sanyayyan 茩amshin da ta bar masu a 蓷akin ba.
Gyara zamanta tayi dangalgal tace ma Gaishata "Je ki kawai, munyi waya daga baya."
Harara Gaishata ta watso mata tace "In fita wa蓷ancen mahaukatan su zaneni, shela fa na ji suna yi kar wanda ya fito wai gimbiya za ta fita."
Sai kuma ta ta蓳e baki tace "Humm! Da bari mukayi ma ta auri Mu'az 蓷in, ko ba komai ba zata mana wuyar gani ba."
A hassale Ardiya ta mi茩e tana fa蓷in "Ki tafi kawai, ni har yanzu ba da蓷in jikina nake ji ba."
Gaishata ma mi茩ewa tayi tana 蓷aukar jakarta data saki ta ta蓳e baki tace "Hawan jini ma kamaki zaiyi idan baki cir..."
A zabure ta matsa kusan Ardiya suna neman 茩amkame juna saboda busar sarewar da akayi daga waje wacce ke nuni da fitowar sarauniya waje, a haka aka bu蓷e mata mota ta shiga ita da gimbiya Kubra sai jakadiyar gimbiya Ramlat da ke gaba zaune, a nutse motocin sukayi jerin gwanonsu suka fita a gidan saleema ba ta ko ji motsin Mamanta ba bare auntynta Lubna da har lokacin tana nan ita ma.
Su Hameeda ne suka taso daga inda suka dur茩usa ranta 蓳ace na bulalar nan da aka tsula mata, kusan Mamanta ta tsaya tace "Momma ni na tafi gida, wallahi da na san kayan takaicin da zan tarar kenan da ban zo gidan nan ba."
Juyawa tayi za ta fita tace "Aikin banza kawai."
Da kallo suka bita har ta fita, Hadeeya ma 蓷akin Mamansu ta nufa tana fa蓷in "Nima dai bari na kirashi ya zo ya 蓷aukeni, banga anfanin zaman ba."
Da kallo Ardiya ta bita tace "Ke shikenan abinda kika za蓳a ma rayuwarki kenan, ciki ne fa da ke."
Da sauri tace "To wai Momma ya zanyi, tunda yana son abunshi ba shikenan ba."
Da mamaki ta ri茩e ha蓳a tace "Kuma dan yana so shikenan sai kiyi ta biye masa? Shikenan rayuwarki ce."
_______________
Sanda suka iso masarautar anyi tsakiyar sallah isha'i, hakan yasa gidan ke shiru sosai, tunda aka ce ta fito ta zuro 茩afafunta da addu'ar shigowa gida "Bismillahi wa'lajna, wa bismillahi karajna, wa'alallahi Rabbina tawakkalna."
Kamata sukayi suka shiga ta 茩ofar sirrin da sarki ke kai kawo a cikin suka dinga kutsawa har suka isa falonta na biyu a sabon wurin da ya zama mallakinta yanzu, gimbiya Kubra ce ta kamata ta zaunar da ita tare da cewa" Zauna ko."
Saida ta zauna sannan hadiman suka zauna a 茩asa.
Shigowar gimbiya Ramlat yasa hadiman suka rage yawa a falon, sam ta kasa yarda da irin wannan shigewa da gimbiya Kubra take musu, hakan yasa ta mi茩ewa ba tare da tayi maganar da take son yi da Saleema ba ta kalli jakadiyarta amintatta tace "Jakadiya, kinsan abinda ya dace kiyi, zamu baku wuri ki shiryata, idan kun ida sai ki jira umarnin mai gado."
Cike da ladabi ta amsa da "Angama ranki shi da蓷e."
Kallon gimbiya Kubra tayi da bata da niyyar tashi, amma da ta kalleta da idanu ta nuna mata mu tafi, dole ta mi茩e tana murmushi suka fice jakadiyarta na binta a baya tana ayyana "Idan ba yau ai akwai gobe."
Suna fita jakadiyar ta taso ta rufe 茩ofar sannan ta dawo wajen Saleema, a nutse ta fara cire mata alkyabbar nan, kamata tayi ta tashi suka shiga wani 蓷aki, kan wani gado gado mai shinfi蓷e da leda ta zaunar da ita ta juya bayanta ta cire mata zip 蓷in rigarta. Tana ji tana gani ta sake tu蓳eta zigidir kafin a saka mata wata yar riga ba茩a wace aka fara yi mata darzar fatar jikinta da ita, 蓷akin wani irin 蓷umi ne yake da wanda da farko ta ringa zufa sosai sai daga baya zufar ta tsane a jikinta a lokacin da ta ke mata wata irin lindar da ta kusan fitar da ita daga hayyacinta.
Sosai take bin duk wani sa茩o na jikinta tamkar wanda zasu canza mata fatarta daga ba茩a zuwa fara, ruwa mai 蓷umin gaske mai ha蓷e da ruwan turaren nan mai tsadar gaske suka wanke mata jikinta tas, babban towel 蓷in da ta bata ta 蓷aura yasa Saleema kallonta a nutse tace "Mama, ina so zanyi sallah isha'i."
Jnjina mata kai tayi tace "Shikena, kiyi alwala idan kin idar sai mu ida."
Da kallon son tambayar har yanzu ba'a gama ba kenan? Ta bita kafin ta 蓷aura alwala ta fito ta bata doguwar riga ta saka sannan ta kabarta sallah. Daga yadda dattijuwar ke zaune ya nuna mata kamar ita take jira, dan haka da ta sallame ba ta samu damar 茩arasa Azkhar 蓷in da ta saba ba ta tashi suka koma 蓷akin.
Rigar ta sake kamawa za ta cire mata, kamar za ta fashe da kuka ta kalleta tace "Mama, yanzu ma cirewa za'a yi?"
Murmushi dattijuwar ta mata tace "Da alama ba sai na koyar dake tausasa harshenki ba, dan alamu sun nuna kin iya magana da babba, sai dai yalla蓳ai sarki ne, sarkinki, idan zakiyi magana da shi idanunki a 茩asa, sannan muryarki ta fi haka kwanciya, idan zai yiwu ki dinga magana tamkar muryarki na 蓳arin kuka dan tsoro, amma fa ba kowane lokaci ba, haduwarku ce ta farko wannan, ki kula sosai wajen magana da yalla蓳ai, ki sani wata maganar ma ba da baki zaki furta masa ba, ido kawai sun isa su sanar masa da sa茩onki, matar sarki kike yanzu, dole ki koyi wannan sarauniyata, musamman idan kuna tare da mutane, ya dace ki fa蓷a masa abinda kike son fa蓷ane da idanunki da kuma yanayin fuskarki."
Zaunar da ita ta sake yi bakin gadon ta zagaya bayanta, kanta da suka kwance mata tun a gida ta shiga warwarz mata yalwatacciyar sumarta tana rabata, wani dandanan man kai ta dinga shafa mata tare da dun茩ule mata shi tamkar kitso, saida ta gama ta zagayo gabanta tana kallon fuskar Saleema da uta dai ta 蓷ora hannayenta ta rufe 茩irjinta sannan tace "Motsinki, tafiyarki, yanayin gudanar da duka lamuranki, dole a samu nutsuwa da aji a ciki, ko daga ke sai yalla蓳ai ne, ba kowane lokaci zaki bu茩aci bu蓷a bakinki ba, tambayarsa kawai zakiyi da idanu kuma ya fahimci me kike nufi, haka idan kina son ganar da shi wani abu ne dake kusa dashi, zaki iya yin fari da idanunki na sai kin ce uffan ba."
A sanyaye ta sake fa蓷in " A yanzu ke 蓷in kin zama uwar talakawa, nauyi mai girma ne ya hau kanki tare da nauyin da ya hau kan yalla蓳ai, akwai bu茩atar ki zama hutunsa a cikin gida, ke ce za ki tarbeshi idan ya 蓷au zafi saboda nauyin al'umma, ke ce zaki tarbesa a duk halin da ya shigo miki, mulki babban lamari ne da idan Allah ya baka ba yana nufin ya fi sonka bane a cikin bayinsa, alamu ne na babbar jarabawa ake maka, akwai abubuwa dayawa na tashin hankali da zasu faru da shi a waje ya dinga shanyewa, amma ke matsalarki, ba lallai ne ya iya shanyeta ba, damuwarki 茩arara za ta bayyanar da tasa damuwar har ta fara shafar mulkinsa, dan kuwa a gabanki ne zai iya fitar da 蓳acin ran da ya wuni yana sha茩a, a gabanki ne zai iya fitar da yanayi na tausayi, tsoro, da firgicin da yake zagaye ga talakawansa wanda hakan ke kassara nutsuwarshi da farin cikinsa, to kinga a nan dole ki zama mai nutsuwa, hankali, da sanin ta kamata, dan kuwa ke ce zaki zama mai shanye damuwarsa, akwai yiwuwar a gabanki ya zama tamkar yaron goye, idan baki lalla蓳ashi ba sai ya 蓳aude har a kan kujerarsa ma, ki zamar masa kwanciyar hankalin cikin gida, yadda ko yana zaune a kujerarsa damuwa ta sakoshi a gaba da gajiya, ya zama ke ce kawai za ki zo masa a tunani a wannan lokacin, hakan kuma ba zai faru ba sai kin kasance mai tsafta, mai girmamashi da tausasawa a gareshi."
Kasko dattijuwar ta 蓷auka tana hura huta tana ci gaba da fa蓷a mata" Ki zama mai *ladabi* 拼ata, idan ya ce yi, to kiyi indai bai sa蓳a umarnin Allah ba, idan kuma ya umarceki akan wani abu ne da bai dace ba sakamakon 蓷aukar zafi irin na maza wasu lokutan, to a lokacin kada ki ce a'a ba haka ba, ki bishi da angama ranka shi da蓷e, ki fara 茩o茩arin sama masa nutsuwa, idan kin tabbatar hankalinsa ya kwanta sai ki nuna masa hukuncin da ya yanke akwai tsauri a cikinsa, idan kuma ya zama mai kawo miki damuwar da ta shafeshi, kada kiyi 茩asa a gwiwa wajen bayar da hankalinki kanshi, ki nutsu sosai ki bashi hankalinki tamkar baki ta蓳a bawa wani abu mahimmanci ba sai lokacin, hakan zai bashi zummar fa蓷a miki damuwarsa, idan ya fa蓷a kuma ki kasance mai bin labarin daki-daki har ki fuskanci irin shawarar da za ki bashi game da lamarin, kinga kenan anan akwai bu茩atar ki zama mai hangen nesa da kuma kaifin 茩wa茩walwa."
Tana kallo ta yaye karpet 蓷in dake bayan 茩ofar 蓷akin sai ka rame mai zurfi ya bayyana, kujerar tsugunno ta aza mata sannan ta kamota ta zaunar kan kujerar, kwa蓳in da tayi na garin musawul ha蓷e da turare na ruwa ta fara shafe mata jikinta da shi, sosai take murza mata shi a jiki har tana rintse idanu, bayan ta aza kaskon da sanyayyan 茩amshi ya fara tasowa tare da haya茩i ka蓷an ka蓷an yadda ba zai cutar da ita ba, tana zaunawa ta kawo bargo mai nauyi ta rufe mata jiki dashi ruf sai iya fuskarta kawai.
A ka蓷an ta yi minti ashirin kafin ta tayar da ita suka nufi ban蓷aki kuma har lokacin shawarwari take bata yadda zata fuskanci sabuwar rayuwarta, wani wankan ta sake yi da sabulun da aka ha蓷a da zallan mayuka da basa saka haske sai gyara jiki ga kuma garin magarya da kuma man zeitun da sauran mayuka. Maclean da brush ta bata bayan ta ida wanka ta wanka bakinta sosai sannan ta fito.
Tun ruwan jikinta basu tsane duka ba ta bata wani ha蓷a蓷蓷iyar farar humra da aka wa la茩abi da *Deeja* (akwai fa humrar nan mata, sai ki jaraba za ki gane) ta shafe jikinta har saida ta umarceta ta 蓷aga towel 蓷in ta shafe duka cinyoyinta zuwa mararta da kuma 蓷uwawunta, wata irin lallausar doguwar rigar bacci har 茩asa ta 蓷auko mata kalar pink, pant 蓷in rigar ta fara bata ta saka sannan ta saka riga wacce ta mata 蓷as a jiki, sunkuyawa tayi ta aje mata wasu sau茩a茩茩in silifas masu taushi sosai kalar pink ta saka, kwalli ta mi茩a mata tace "Shafa."
Kar蓳a tayi ta kalli madubi ta shafa sannan ta bata farin man le蓳e shima ta shafa, rufaffiyar alkyabba mai taushin gaske ta saka mata ta sake rufe mata kanta da rigar, zaunar da ita tayi bakin gado ta nufi 茩aramar fridge 蓷in dake falo, tana zuwa ta bu蓷e sanyayyar tattaciyar masarar shanu ta bata tace "Shanye duka."
Da ta kar蓳a ba dan ta shanye bane dan bata da ra'ayin komai, amma tana kifa kai sanyin madarar nan ya dinga ratsata sai kuwa ta shanye tas ta mi茩a mata robar, 茩aramin kofin tasar dake hannunta da cokali 茩arami ta cikashi da zuma ta debo ta nufi bakinta da shi, bu蓷a bakin tayi tare da sake yin bismillah ta kar蓳a, ta sake 蓷ebowa za ta kai bakinta aka 茩wan茩wasa 茩ofar 蓷akin. Sadda kai Saleema tayi san ta fara 蓷aukar darasin matar, ita kuma ta aje tasar ta nufi 茩ofar, saleema ta dai hangi hadimar suna magana 茩us茩us, dawowa tayi ba tare da ta rufe 蓷akin ta tallabo Saleema tace "Ranki shi da蓷e an zo tafiya da ke."
Kallon fuskar Saleema tayi tana mata murmushi tace "Zaku je tare da ita, jakadiyar sarki ce, ki kasance mai ha茩uri, kada ki zama mai raki."
Saleema ba ta ce komai ba ita dai tana kallo har aka mi茩a bakin alkyabbarta ga 蓷aya jakadiyar ta shiga janta tamkar makauniya.
Gaf da 茩ofar shiga 蓷akin baccin ta dakata a sanyaye tace" Sarauniyata, bakin tafiyata dake iya nan ne, bani da hurumin wucewa ciki, ki shiga ciki."
A hankali Saleema ta 蓷aga kanta ta juya ka蓷an ta kalli falon a 拼an sakanni, ya fi 茩arfin ta faslta kyawunshi a 蓷an kallon nan na da茩i茩u, irin 茩amshin da falon ke fitarwa ya fi tsaya mata a rai har take jin anya kuwa duk 茩amshin nan da jikinta ke yi ba sai ta gaza gamsar da ma'abocin 蓷akin ba? Ganin har yanzu jakadiyar na inda ta rusuna yasa ta kama hannun 茩ofar ta mur蓷a a nutse sannan ta zura 茩afarta da yau tsabar darzar sa suka gani har sukayi wani taushin alhaki, saida ta shige gaba蓷aya ta maida 茩ofar ta rufe sannan jakadiyar ta bar wurin.
Tsaye take wuri 蓷aya tana 茩arewa 蓷akin baccin kallo, tun daga gaban madubin dake sha茩e da mayuka da turaruka kala kala, zuwa kan kyakyawar drower kaya kan ha蓷a蓷蓷en gadon Hunkar da ya 茩awata 蓷akin, ga wani sabon 茩amshin da yayi daban da na falon, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da matsawa 茩a蓷an ta zauna kan kujera tana ci gaba da kallon ko ina, wanene shi? Ya zai kasance gareni? Mai tausasawa? Ko mai kausasawa? Ya Allah.
Ta fa蓷a tana dafe gaban goshinta tana lumshe idanu, ta gaji matu茩a yau da wannan al'amari, kanta har yanzu yana mata ciwon lamarin daya ba茩unceta, hakan yasa ta 茩ara gyara zamanta ta mi茩ar da 茩afafunta ba tare data cire silifas 蓷in 茩afarta ba ta buga tagumi tana ta lumshe idanu saboda sanyin dake ratsata ya gama kashe mata jiki bacci ke neman 蓷aukarta.
Baccin da ya fara fizgarta ne yasa ta bu蓷a idanunta da sauri da kuma 茩arfi sakamakon 茩ofar da aka rufe, 茩ofar a gabanta take can gefen gado, hakan ya bata damar ganin mai shigowar da kyau, ido cikin ido suka kalli junansu, kowane fuskar da yanayin dake nuna tsantsar mamakin ganin 蓷anuwansa, duk da bata ga alamu da ya nuna mata ban蓷aki bane, ama kuma ya fito jikinshi sanye da doguwar farar riga tas tas tamkar madara, saisanyayyan 茩amshin turarenshi na Brand 69 ya fara kai mata karo a hanci.
A hankali ta gyara zamanta har ta mi茩e tsaye fuskarta ba ta daina mamakin ganinshi da tunanin ko dai shine mijin nata? Mutumin da ke fama da ciwon 茩afafu ko tafiya baya yi da kyau? Mutumin da idan ma wani tsautsayi yasa ta tuna da shi take kiranshi da sunan da ya dace da shi saboda kwalliyar data ta蓳a ganinshi cikinta da kuma takonsa na 蓷ai蓷aya, tuna haka da wannan tunanin a ranta yasa da sigar mamaki da kuma 蓷an tsoron da ta ji na ganinshi tace "Kaiii! *茒AWISU* Kai ne?"
馃槀 _Wato Saleema ta 茩ware a wajen sakawa kowa sunan da ya dace da shi, mai mara蓷awar namu? Huzeifa Alhudahuda, Mu'az Akhu, sarkinmu kuma shine 茒awisu?_ ba ruwana, ki fanshi kanki. 馃槍Kwate ga sabuwar majinyaci nan, a bata gado a asibitin da aka kwantar da 茩awata Aminatu.
*Alhamdulillah.*
20/06/2022 脿 22:07 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_43_
Rashin sanin waye shi har yanzu da kuma tunanin kar dai a ce shine sarkin yasa ta sauri rufe bakinta ta sadda kanta 茩asa tana wala-wala da idanunta alamar rashin gaskiya, cike da kunya take wasa da yatsun hannayenta tana ci gaba da jujjuya idanu.
Tsaye yake cak! Wuri 蓷aya yana kallon fuskarta, 茩yallin da fuskarta ya ga tana yi ne yake bashi mamaki, ba dan kar ya zuzuta dayawa ba sai ya ce tamkar *jaririn wata* yake kallo, idan baiyi 蓳atan lissafi ba kenan wannan marar kunyar da bata iya gaishe da manya ba ce Ummi ta aura masa? Gashi yanzu ta sake tabbatar masa hada fitsara ma ta iya, yarinyar da ta gaisheshi da *Barka dai*! Hmmmm!
Da wani masifaffen yanayin da茩ilewa ya shiga takowa gabanta, hakan ya haddasa mata faduwar gaba tare da kowane takonshi 蓷aya mai kama dana gajiyayyar mai tsohon ciki, tuni ta kuma sadda kanta ta rintse idanu ta gama yanke 茩auna da kifeta zaiyi da mari sannan ya mata hargagin kan me za ta shigo masa nan 蓷in da har yanzu ba ta san 蓷akin waye ba. Saida ya zo kusa da ita kawai ya ra蓳ata ya fita a 蓷akin, wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tare da kmawa kan kujerar ta zauna tana fa蓷in "Wallahi dole na iya bakina, wannan idan ya mareni sai na ga taurari."
Sai kuma ta ta蓳e baki tace "Hmmm! Kamar wata mace yayi ta abu da sanyi."
Sai kuma ta yatsina fuska tace "Ba kazar-kazar irin na maza, sam *baka min ba*."
Ba jimawa aka sake shigowa, wannan karan ba ta motsa ba saida ta kalli mai shigowar ta 茩asan idanu,