Showing 48001 words to 51000 words out of 191031 words
bane yanzu.
*Washe gari*
Gidan Alhaji Auwal dai ba'a yi baccin arzi茩i ba musamman ma Alhaji da amarya, tunda ya fa蓷a musu Mu'awwaz zai auri Nafissa suka rikice ita da Mu'awwaz 蓷in, da kuma ta fara kawo masa hauka ya nunata da yatsa yace "Ke baki isa na fasa abin da mahaifina ya ke so baa, in ma za ki ha茩ura ki ha茩ura ki lallashi 蓷anki, da yake iskanci a garin nan kina ina? Ba kallon yaro kike masa ba? To ki nutsu daga ke har shi, idan har kuka ce za ku bijere min wallahi mataki zan 蓷auka a kanku da zakuyi mamakina a rayuwarku."
Bugu da 茩ari saida ya kalleta sama da 茩asa sannan yace" Kin fi kowa sanin ba tare muka zo duniya ba, sannan 蓷anki ba shi ka蓷ai na haifa ba bare na ji takaicin rasa me gadata bayan raina."
Cike da hauka da hargagi da kuma jin cewa ita ce hasken gidanshi ta cire 蓷an kwalinta ta jefar, yalo-yalon gashinta ba茩i mai tsayin gaske ya bayyana, cikin 蓷aga murya ta fara bubbuga 茩irji kamar wata dangin inyamurai take fa蓷in" Ahaji ni ka ke fa蓷ama haka? Akan me za ka yanke mana wannan hukuncin? Laifi muka maka ne? 茒an nawa za ka ha蓷a da mai aikin gidan nan 茩azamar yarinya saboda ka tsanemu, wallahi ba ka isa ba, Mu'awwaz Hameeda zai aura 拼ar Ardiya ko kana so ko baka so."
A nutse ya jinjina mata kai yace" To shikenan mu zuba, zan nuna miki na isa har na yi yawa."
Cikin bala'i da masifa tace" Ni dama tunda yaran nan suka zo na ga ka canja, wannan na san ba zai rasa nasaba da yarinyar nan da na ga kana wani shige mata kana mata kallon 茩auna, gwara ma ka fito fili ka fa蓷a mana gaskiyar abin da ka ke shiryawa, dan na san gaba ka蓷an za ka ce mana aurenta za ka yi."
A tsawace Alhaji Auwal ya kalleta yana nunata yace" Ke *Gaishata* (team amare) 馃槀ki san me bakinki zai dinga fa蓷a min, wallahi kika min hauka nan bar min gidana za ki yi, yarinyar da kike magana a kai ita ta zama fitilar da ta haska mana gidan nan shekara da shekaru, daga ke har Rabi cikinku wacece ta ta蓳a ce min na gyara tsakanina da mahaifina? To ki sani da zan iya samun wata kamar Saleema wallahi zan aura na ga idan kin isa ki hanani, shi kanshi 蓷an na ki da kike 蓷aga murya a kai ba dan shawarar da ta bamu ba da wata茩ila a kawo miki gawarshi 拼an iskan gari sun kasheshi."
Rara茩o idanu tayi tace" Saleema? Ita ce ta bayar da shawarar a aura masa 拼ar aiki? Na sani dama wannan yarinyar ce ta canza maka tunaninka."
Sai kuwa ta 茩arasa inda Mu'awwaz yake kanshi sadde ya ma rasa me ke masa da蓷i ta finciki hannunshi tana fa蓷in" Muje kai, in dai ni na haifeka bbu wanda ya isa ya aura maka wannan kucakar."
茒akinta suka nufa suna kusan shiga Alhaji Auwal yace" Ji ni da kyau, mahaifina lokaci 茩an茩ani ya 蓷ebo ma auren, ranar juma'a da za ta zo za'a 蓷aura auren a masallaci, idan ki ka ce ba za'ayi ba kuma kika kaini bango, to ki sani sa'ilin da surukarki za ta shigo gidan, lokacin ke kuma za ki tattara kayanki ki barmin gida. "
Mu'awwaz ya kalla da ya juyo ya kalli mahaifin na shi yace" Kai kuma ka sani ida har ka yi yun茩urin yin wani abu to za ka gami da 蓳acin raina, dan sai na rabaka da komai da yake nawa, duk wani da蓷i da kake ji da dukiyata sai na tabbatar ka kai 茩adamin da zaka iya yin barar abinci sannan zan ha蓷aka da hukuma su hukuntaka."
A fusace ya juya ya barsu tsaye sun shiga zulumi da ki蓷imar da basuyi tsamlanin zai yi ikrarin ambatar musu ita ba. Sakin hannun Mu'awwaz tayi ta kalli Hajia Rabi da ita dai tunda suka fara 蓷aga muryoyi ta ce su yi ha茩uri Gaishata ta daka mata tsawa ta zuba musu idanu, nuyya ce ta yi ko zai kafta mata mari ba za ta tashi ko da tsaye ba bare ta damu. A hassale Gaishata ta wurga ma Hajia Rabi harara sannan ta banka 茩ofar 蓷akin ta shiga har hawayen takaici da ba茩in ciki na ziraro mata da tunanin me za ta wa Saleema ta huce ma?
_____________
Wajen Saleema kuma maganar saukar da za'a yi ne kawai a gabanta, yanzu haka wayar Mamanta ce a kunnenta cikin nutsuwa tace "E malam ta kawo min, ga takardar ma a hannuna."
Daga 蓳angaren malamin yace "Yawwa Saleema, to kin gani yanzu kwana uku ya rage, kuma abinda kika bu茩ata za ki yi magana a kai ranar babban abu ne da ya dauki shafuka har uku, a haka ma a komai na saka miki ba, farkon za ki ga mu茩addima ne, na san wannan kin haddaceshi ba tun yau ba, abu ma fi mahimmanci shine ki haddace ko da rabin shafi na farko, tunda kinga minti biyar ne ake ba wa kowane 蓷alibi dan karatu."
Numfashi ta sauke tare da kallon Khairat dake gabanta tace" To malam, nagode sosai."
Kamar yana gabanta ya mata murmushi yace" Ba komai Saleema, kuma ina fata ba za'a samu matsala daga wajen mahaifinki ba?"
Ajiyar zuciya ta sauke tace" Malam ko da akwai matsala ma ni zan kar蓳eta, sanin lahirata ya fi min komai, idan na bi ta mahaifina zan tashi ne babu duniyar kuma babu lahirar, to idan haka ta faru wace riba na ci ta zuwana duniya?"
Cike da jin da蓷i da kuma jinjina nutsuwar yarinyar yace" Hakane Saleema, Allah ya miki albarka, Allah ya ma karatunki albarka, in sha Allah wata rana mahaifinki zai yi alfahari da ke."
A sanyaye tace" Allah ya sa malam, nagode."
Da haka suka rabu Khairat ta koma dan dama takardar karatun da zata gabatar ta kawo mata, Saleema kuma shiryawa ta yi ta fita kasuwa ta siyo kalar yadin hijabin da zasuyi anko uta da sauran 蓷alibai, ba ta dawo ba saida aka 蓷inko mata shi yanda take da bu茩ata sannan ta dawo. Ko da ta shigo ta samu Mamarta da 茩anwarta *Lubna*, gaisawa sukayi sosai cike da mutumtawa da kewar juna kafin tace mata "瞥ar mamanta kenan, gashi dai daga 茩arshe kela za ki yi saukar nan, burinki zai cika."
Murmushi Saleema tayi sannan ta kalli Mamanta tace "Mama, kar fa ki fa蓷ama kowa tunda kinga ba taro za'ayi ba."
Harara Safiya ta dalla mata tace "Kina tsoron ya sani amma ki ka dage sai kinyi?"
A ladabce tace "Mama ba tsoron ya sani yanzu ba na ke, wallahi ko da zai sani ne minti 蓷aya da gama karatuna a makaranta ban damu ba, na san dai ba zai wuce ya sake hanani wani abun ba ko kuma ya dakeni."
Dariya Lubna tayi tace "Ba ma zai dakeki ba yanzu tunda kin zama budurwa, kuma ai babu wanda ya sani a dangi, nima yanzu ne na sani data kirani ta bani ku蓷in nan da za'a miki wainar sadaka da kuma gallelen ragon da ta ce a siya dan a kai makarantar."
Cike da farin ciki Saleema ta rumgume Lubna tana fa蓷in" Kai amma na ji da蓷i sosai Aunty."
Da fara'a ta shafa kanta tace" Ai ke 拼ar Mamanta ce."
*Ranar Sauka*
Gidan shiru yake kamar ko yaushe babu alamar wani hidima, hatta da Saleema da abun ya shafeta ita da mahaifiyarta, a 蓷aki suke suna kitsawa da warwarewa saboda tsaro, inda lokaci lokaci sukan yi waya da Aunty Lubna suna jin yanda komai ke tafiya daidai daga 蓳angarenta. Wayar mahaifiyarta ce ta yi 茩ara da sauri ta 蓷auka da tunanin Khairat ce da take jiran ta kira ta bata malaminsu dan ta masa bitar haddata da ya ce yau da safe zai ji daga bakinta, ganin Hajia Rabi ce yasa ta mi茩awa Mamanta tace "Mama Hajiarsu Mu'az ce."
Cike da tsokana tace "Ki 蓷aga mana, sarakuwarki ce fa."
Turo baki tayi gaba tace "Maaaama."
Dariya Safiya tayi ta kar蓳i wayar ta 蓷ora a kunne da sallama, Saleema na jinsu suna gaisawa kafin daga bisani ta mi茩o mata wayar tace "Tana son magana da ke ne."
A ladabce Saleema ta kar蓳i wayar ta 蓷ora a kunne, a sanyaye sosai ta furta "Assalama alaiki, Mahmah."
Shiru aka yi ba amsa, da mamaki ta 蓷an 蓷ago wayar daga kunnenta ta duba sannan ta sake mayarwa tace "Hello!"
茦a茩茩arfan numfashin da ya sauke a cikin kunnuwanta ya sa ta kallon Mamanta da kyau da mamaki, cikin taushin murya kamar mai mata ra蓷a yace "Baby shine kika manta dani ko? Ina wayarki take? Tun da aka kawo miki nake ta kiranki amma bana samu, anya ma kin saka layin a wayar? Matata me yasa kike min wula茩anci ne haka?"
Gaba蓷aya sassan jikinta saida suka amsa, yanda yake maganar kamar zaiyi kuka da saurin da yake maganar sai ta ji wani abu mai kama da tausayinshi a zuciyarta, a hankali ta mi茩e tana satar kallon Mamanta har ta fice a 蓷akin kafin tace" Ni ban wula茩antaka ba, kuma ma ai...ni fa..."
Shirun da tayi yasa yace" Ke fa me? Har yanzu ba ki gama shawara da Maman ba ne? Saleema jiran amsar nan ta ki kinsan halin tashin hankalin da na shiga kuwa? Na rantse miki da Allah ko tashin hankalin da na shiga sanda na ke neman takardar wani aiki a wata Projet bai kai wanda na je ciki ba yanzu."
Cike da shagwa蓳a ta turo baki idanunta a rintse ita a dole kunya take ji kamar tana gabanshi tace" Malam ka mana shiru ko, kai bakinka ba ya gajiya da surutu? Ba na fa蓷a maka na amince ba."
Daga 蓳angarenshi da mamaki yace" Kin fa蓷a min? Yaushe kuma?"
Cike da yarinta da sangarta tace" Yanzu mana."
"Wayeeehuuuu!" Ya fasa mata kunnuwa da wata irin mahaukaciyar 茩ara, kafin ta ce wani abu ta ji muryarshi da alama ru茩um茩ume Hajia Rabi yayi yana fa蓷in "Ta amince wallahi Mama, wayyo da蓷i, Mama kasheni kar farin ciki ya min yawa."
A kunnenta tana jin yanda suke ta murna shi da Hajia har ta gaji da tsayuwa ta kashe wayar dan alamu sun nuna farin cikin da ya shiga ya mantar da shi waya suke. Kashe wayar tayi tare da nufa 蓷akin su Hadeeya dan kar蓳o wayar nan, sam ta manta da ita a rayuwarta, tun ranar wayar ke hannun su Hadeeya amma ba ta damu ba.
茦wan茩wasa 茩ofar 蓷akin ta yi tare da sallama, daga ciki Hameeda tace "Shigo."
Tura 茩ofar tayi ta shiga tana zuba idanunta a kansu, da alama tun da suka farka basu tashi a gadon ba, dama ba su karya tare da su ba, yanzu kuma gasu kwance da kayan bacci a jikinsu kawunansu a hargitse gashi a sake sai 蓷aukar hotuna suke, a ganinta me ye abun 蓷auka kuma daga tashi daga bacci? Shin hoton hauka da ake 蓷auka kowane lokaci? 茦arasawa ta yi ta tarawa Hadeeya hannu tace "Waya za ki bani?"
Da sauri Hadeeya ta kalleta tare da marairaicewa sai kuma ta kalli Hameeda, kamar za ta yi kuka tace "Dan Allah *aunty* Saleema ki bar min ita har a gama bikin murnar samun jarabawar 茩awata, gobe ne da an gama sai na baki."
A hankalce ta kalli fuskarta da mamakin ita ce yau Hadeeya ke kira da aunty? Aunty fa? 茒an ta蓳e baki tayi tace "To ke ba ga wayarki ba?"
Cike da sigar tausayi tace "Aunty wannan ba ta 蓷aukar hoto da kyau, wannan wayar fa babbar waya ce."
Hameeda dake zaune gefe ne tace "Wallahi aunty da ma zaki bar mana ita, kinga fa har ta bu蓷e tik tok, baki ga irin mabiyan da ta samu ba."
茦an茩ance idanu Saleema tayi tace "Dama abin da za ki yi da wayar kenan?"
Da sauri Hadeeya ta kalli Hameeda tana aika mata garga蓷in me yasa? Sai ka ce ta manta suna tare da ustazar gidansu ne, sai kuma ta kalli Saleema tace "A'a aunty, wa'azizzika nake 蓷orawa, tsaya ki gani."
Ta fa蓷a tana matsowa kusanta ta fara nuna mata wasu gajerun wa'azizzika tace "To kinga irinsu ne nake 蓷orawa, ba sa wuce minti 蓷aya zuwa second talatin, kinga ko ya mutum ya 茩aru da ni ai ke ma kin samu lada."
Jinjina kai Saleema tayi dan sosai abun ya kama hankalinta, numfasawa tayi tace "To ki bani kwalin wayar, da alama akwai layi a ciki."
Da sauri ta sauka a gadon ta 蓷auko ta kawo mata, har ta juya za ta fita Hadeeya tace "Aunty Saleema ko na baki wayata sai ki saka layin a ciki?"
Ba tare da damuwar komai ba ko jin ta yi asarar abu mai tsada ba tace "To ki bani ita duka mana, ke sai ki ri茩e wannan."
A tare suka rakata da idanu a waje Hadeeya har da safe 茩irji tace "Da gaske auntyna? Kin bar min ita duka?"
Yatsina fuska tayi tace "To me ye a ciki? Waya ce, dau蓷ar duniya, kina 拼ar uwata na kasa bar miki ita."
Da gudu Hadeeya ta sauko a gadon tana fa蓷in "Yeeeeeeee! Auntyna nagode, nagode sosai."
Rumgumeta ta yi Hameeda da ba ta ji da蓷in haka ba tunda ba ita aka bar ma ba kauda kai tayi tana 蓷an 茩aramin tsaki. 茒agowa tayi suka kalli juna Hadeeya ta sake sumbatar kuncin Saleema tace "Nagode auntyna."
Murmushi Saleema tayi ta 蓷an shafa kuncinta tace "Da ina da irin wayar nan guda dubu, to da na dinga baki ko dan na ji sunan aunty a bakinki tare da ganin 茩auna a tattare dake zuwa gareni, amma hakan ma nagode ma Allah."
Cike da kunya Hadeeya ta sunkuyar da kai tace "Ai daga yau aunty zan dinga cewa."
Murmushi kawai tayi ta tara mata hannu tace "茒auko min wayar?"
Juyowa tayi ta 蓷auki wayar a kan gado ta bata, yo ita fa dama tun ranar ta gama tura komai dake wayarta zuwa wannan wayar saboda ko jiya ta fita da ita ta dinga hura hanci ita a dole wayarta ce, kuma ta tura komai ne saboda sanin da ta ma Saleema ba mai damuwa da irin wannan abubuwan ba ce, a niyyarta da duk sanda za ta fita ta dinga ara tana fita, sai gashi 拼ar aljana kuma *ba茩auyar* auntynta da ba ta san da蓷in duniya ba ta mallaka mata wayar gaba蓷aya.
Tana fitowa daga 蓷akin sukayi kici蓳is da mahaifinta ya dawo 蓷aukar wani sa茩o, a ladabce tace "Abba sannu da zuwa."
A ta茩aice ya amsa "Sannu, ina Mamanki?"
Nuna masa 蓷akinta tayi tace "Tana ciki."
Jinjina kai yayi har zai wuce sai kuma yace "Ki gyara min 蓷akina, idan kin idar akwai naman talo-talo na nan an kawo ki yi girki da shi, zuwa rana zan turo a 蓷auka."
Farin cikin sakata aiki da mahaifinta yayi yasa ta sakin wani basaraken murmushi na jin da蓷i, har ya 蓷an wuce sai kuma ya juyo ya kalli fuskar, mamakin murmushin me take? Sai kuma ya juya ya ci gaba da tafiya da tunanin me yasa bai ga hushi a fuskarta ba kamar yanda yake gani a fuskar Ardiya idan ya saka aiki musamman idan ta dawo daga aiki ne ko za ta tafi sai ta ga duk ya takura mata kamar yana neman mayar da ita baya ne, saida ya kai farfajiyar gidan ya saki murmushi saboda tuna ai haka mahaifiyarta take ita ma, ba ranar aikinta ba amma kullum cikin hidima take da shi, to idan bai so Safiya ba wa zai so? Bai ta蓳a cewa ta yi ta nuna ba ta so ko ta ji ba da蓷i ba, da ya ce yi to kawai take cewa sannan ya samu abun akan lokaci.
Saleema kuma tqabar farin ciki yasa ta aje wayoyin a nan falo ta shige 蓷akin mahaifinta ta shiga gyaran ko ina a tsanake, ganin ta jima ba ta shigo bane yasa mahaifiyarta fitowa, wayoyin ta 蓷auka da ta gani a kan kujera sannan ta shiga 蓷akin na shi a nan ta sameta, ba ta kama mata ba sai ma bata wuri da ta yi ta ci gaba da aikinta, har ta kammala ta koma madafa, da taimakon mai aiki da mahifiyarta dake zaune ta gama wannan girki lokacin tafiyarta makaranta ya yi, dan 茩arfe 02:00 za'a fara saboda 蓷aliban na da 蓷an yawa, gashi kuma har karfe 03:04 ta na gidan.
*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:48 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_20_
A gaggauce ta shirya cikin doguwar rigar da Alhaji Auwal ya siya mata da kuma hijabinta pink wanda ya 茩ona ka蓷an, takalman nan ta sako ta 蓷auro ni茩ab ta fito, a falo ta samu Mamanta zaune tana cin salade, 茩arasowa tayi a ladabce tace "Mama na shirya, zan tafi."
Cike da nutsuwa ta cire hannunta a salade 蓷in ta kalleta tace "To Hajia, a dawo lafiya, Allah bada sa'a, Allah ya taimaka."
"Ameen Mama." Ta fa蓷a sai kuma ta yi shiru a nutse tace "Mama, ki yi ha茩uri."
Da mamaki tace "Akan me kuma?"
A marairaice tace "Mama zan gabatar da al'amari mai girma da ya shafi rayuwata, amma kuma ke ko Abba ba kwa wajen, haka ma babu 蓷aya daga cikin dangina."
Murmushi tayi tace "To ai Lubna za ta je, wata茩ila ma har ta rigaki isa."
Turo baki tayi gaba tace "Ni dai Mama ki yi ha茩uri."
瞥ar dariya tayi tace "Saleema, kin kai 茩adamin da ko kin koma wajen ubangiji zai tsayar dake ya tambayeki wajiban da suka hau kanki, indai akan wannan ne karki damu, ki je Allah ya tsare."
"Ameen Mama." Ta fa蓷a da fara'a tare da wucewa tana fa蓷in "Sai na dawo."
Da fara'a ta bita da kallo tace "A dawo lafiya."
Tana zuwa mai gadi ya mi茩e yana fa蓷in "Hajiar Alhaji fita za'a yi ne?"
Ba yabo ba fallasa ta amsa da "E, ba jimawa zan yi ba."
*Filin Makaranta*
茒alibai biyu sukayi karatu sai Saleema, kamar yanda kowane 蓷alibi na za蓳ar abin da yake