Showing 45001 words to 48000 words out of 191031 words
zuba miki 茩wandala da sunan karatu, dan haka ba ke ba sake fita a gidan nan da sunan za ki tafi makaranta, *na dakatar da ita daga yau*."
Duk zuba mishi idanu sukayi har Safiya dake tsaye, sai kuma ta girgiza kai tana lumshe idanunta, Saleema ma idanunta cike da hawaye ta kalleshi sai kuma ta kalli mahaifiyarta da tunda ta zo ta fahimci kamar har yanzu jikinta ba ta jin da蓷inshi, abin da take son fa蓷a masa tsoro kuma ya hanata dan kar ya bigeta, sai kwatsam mahaifiyarta ta yi tambayar cewa "Amma Alhaji ka hanata zuwa islamiyya shekara takwas da suka wuce, ka hanata 蓷inki tun tana 茩arama, yanzu kuma ka dakatar da bokon ma, toe za ta yi idan ta zauna a gidan?"
Kallonta yayi a zafafe yace "Wannan hukuncina ne kuma na gama yankewa, ta zauna a gidan ta dinga kama muku aiki har ta fito min da wanda ta ke so nan da wata biyu na aurar da ita."
Da sauri Saleema ta furta "Aure Abba, amm..."
Kallon da ya mata ya sa ta yi shiru, 茩wafa yayi tare da fa蓷in "Idan la ba ki da saurayin ni zan miki, kuma ma ai ba zaki rasa ba tunda har kika 茩i maida hankali ga karatu, na san soyayya ce ke hanaki."
Ardiya da take jin da蓷in haka cike da kissa tace "Ai shekarunta sun isa na aure, ba ka ga duk wata wahalar da take sha kafin ganin al'adarta ba?"
Kunya ce ta sa Saleema du茩ar da kanta, inda Hadeeya da Hameeda suka yi dariya a tare, Safiya kuma kallon Ardiya tayi tace "Me yasa kike min hakane? Dan ba 拼arki ba ce?"
Ta蓳e baki Ardiya tayi tace "Kowa dai na gidan nan ya san gaskiya na fa蓷a, na tabbata soyayya ke hana Saleema karatu har sha'awarta ke 茩ara tunzura, idan ba'a aurar da ita yanzu ba wata rana abun kunya za ta 蓷auko..."
Cokalin da take zuba miyar da shi dake hannunta ta buga a kan teburin da 茩arfi tana rintse ido tace" Ya isheki haka."
Duk kallon Safiya sukayi da tayi kwaratsin, nuna Ardiya tayi da cokalin za ta yi magana, da sauri Alhaji Yusuf ya mi茩e tare da jawo Safiya jikinshi ya 蓷an rumgumata, ba ya so ta 蓷aga murya sosai, ba ya so ta yi fa蓷a da Ardiya, ba ya so ta 蓷aga hankalinta kamar yadda likita ya fa蓷a masa a kiyaye duk wani tashin hankali da 蓳aci ranta saboda cikin dake jikin na wata uku. Yun茩urawa ta yi za ta tashi tana sake fa蓷in "Wallah..."
Hannu ya kai kan bakinta ya toshe cikin ra蓷a yace "Ya isa haka Sofeena, rabu da ita kinji uwargidana."
A hankali ta dinga sauke numfashi tana 茩ara tusa kanta a 茩irjinshi, shafa bayanta ya dinga yi yana kallon fuskar Ardiya dake kumbura tana musu wani mugun kallo. Saleema kunya ce ta sake kamata a ranta ta ayyana" Tofa! Mun dawo kenan, wai Abbanmu ba ya girma ne shi?"
茒ago kai Safiya tayi ta kalleshi idanunta taf da hawaye tace" Dama ina son magana da kai."
Cike da kulawa da guje duk abin da zai 蓳ata mata rai ya tallabo ha蓳arta yace" Ina jinki, ko sai mun shiga ciki?"
Turo baki tayi cike da shagwa蓳a ta 蓷an saci kallon Ardiya da har yanzu ke kallonsu tana mamakin mijin na su, mamakinta bai wuce yadda in suna tare yake nuna ba wata sai ita ba, ko aikace wasu lokuta ya na nuna mata ta fi Safiya mahimmanci, amma duba yanzu yanda yake ta nani茩eta a gabansu wai dan tana da ciki, hmmmm! Ta fa蓷a tana ayyana "A haifeshi mu gani."
Safiya da ta fahimci haka cikin shagwa蓳a tace "Dama ku蓷i na ke so, kuma ka ga watan da ya wuce ba ka bani komai ba."
Ajiyar zuciya ya sauke jin matsalar ta ta ba wata babba bace, dama dan bata aiki ya 蓷auki al茩awarin bata jaka saba'in kowane wata, duba da Ardiya tana aiki kuma tana 蓷aukar albashi, dan kar abun ya mata yawa ya shi 蓷aukar wannan matakin, duk da wasu lokuta idan ya bata ma sai ta ce ba ta bu茩ata ko kuma ta 蓷auki rabi, wani lokaci kuma shi yake mantawa kamar dai yanda ya yi watan da ya wuce.
Cikin sassauta murya yace "Shikenan, zan ganki anjima, yanzu je ki huta 蓷akinki ina zuwa, bana son hayaniyarki."
Jinjina kai tayi alamar to tare da nufa hanyar 蓷akin na ta, da kallo duk suka bita har Hadeeya ta ta蓳e baki, dan ita ba ta ta蓳a ganin haka ba sai yau, Saleema kuma zaman ne ta ji zai isheta tunda babu mai tsaya mata a wurin, mi茩ewa tayi za ta bi bayanta ba kunya ba komai Alhaji Yusuf yace "Kar ki sake ki takura min mata da matsalolinki, ciki ne da ita kuma bana son abin da zai 蓷aga mata hankali."
Rufe idanu Saleema tayi sai kuma ta girgiza kai tace "Ba wajenta zan je ba, falo zan zauna."
Tana wucewa Hadeeya ta kalleshi cike da wauta da ga蓳anci tace "Abba, ka ga ni dai irin wayar da na ke so ka siya min, ta ya ma Saleema za ta ri茩e wannan wayar ni ina fama da wannan Samsung."
Ko kallonta bai yi ba yace "Um um! Ban da arzi茩in da zan siya miki wayar nan."
Turo baki tayi ta kalli Ardiya tace "Momma..."
Da yatsabta nunata tace "Kar ma ki fara, ubanki bai iya sai ni ce zan iya?"
茒an kallon Ardiya ya yi sai kuma ya girgiza kai ya ci gaba da cin abincinshi, Ardiya dake kallonshi tana ta hassala ne tace "Shi ne ma ba zaka kulani ba."
茒agowa yayi yace "Me ya faru?"
Cike da masifa da harshenta na hausa da baya fita da kyau tace "Shi ne zaka wula茩antani a gabanta? Ka yi ta wani rumgumeta dan na gane ita ma mowa ce a wurinka."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ki yi ha茩uri to, ba dan ranki ya 蓳ace na yi ba, na fa蓷a miki yanda likita yace game da lafiyarta, dole mu kiyaye 蓳ata mata sannan mu lalla蓳ata."
Jinjina kai tayi tace "Shikenan to ya yi, sai ka yi ta lalla蓳atan ai."
Mi茩ewa tayi a hassale ta nufi 蓷akinta, da sauri ya tashi ya bi bayanta dan ba zai so ita ma ta yi hushi ba, dan wallahi al茩awari ya la kanshi cewa ba zai kuma kusantar Safiya ba sai ya ga cikinta ya girma, dan yanzu gani yake motsi ka蓷an zai sa ta yi 蓳ari.
*09:00* Safiya ta sameta 蓷akinta har ta yi shirin bacci tana zaune kan gado tana karatu, da fara'a ta 茩araso ta zauna kusanta ta mi茩o mata ku蓷i, da sauri ta amsa tana murna ita ma, 茩idaya ku蓷in tayi ta kalleta tace "Mama duka wannan ne suka bayar?"
Da murmushi ta jinjina mata kai alamar e, ita ma jinjina kan tayi ta fa蓷a jikinta tace "Nagode Mamana, gaskiya Abbanmu yana sonki."
Murmushi kawai ta sake yi amma ba ta musa mata ba, dan gaskiya ne ya na sonta kuma yana yawan fa蓷a mata haka, sannan a aikace ma yana nuna mata, duk irin yanda take da sani kan ya auro Ardiya ne saboda iliminta da wayewa, sannan ya na sonta da kuma 拼a拼anta kyawawa, amma tana da tabbacin soyayya ta gaskiya yake mata, dan kuwa ba ta nemi komai ta rasa a wajenshi ba, duk abin da zai ma Ardiya shi zai mata, idan zai kashe ma Ardiya million 蓷aya to ita ma haka, matsalar Saleema ce ma kawai ta sa wasu lokuta yake fa蓷a mata magana mai 蓷aci ko a gaban yaran, wanda hakan take 蓷aukarsa a matsayin sa蓳ani na ma'aurata. Amma ko daren jiya da suka je asibiti aka fa蓷a masa tana da ciki, kai tsaye wajen cin abinci suka wuce ya kashe mata ku蓷i sosai a kan abinci kafin su zo gida, jimawar da sukayi yasa Ardiya rufeshi da masifa har saida ya fa蓷a mata dalilin ka蓷ai.
茒agata tayi daga jikinta ta kalli fuskarta tace "Kin san me? Ba茩i mukayi a gidanmu."
Da mamaki tace "Ba茩i kuma? Su wa ye?"
Irin kallon tuhuma da tsokana ta mata tace "Alhaji Auwal ne da mahaifinshi, sai kuma... Yaya Mu'az 蓷inki."
Ta 茩arashe tana mata dariya, waro idanu tayi tace "Mu'az kuma?"
Da sauri ta nemi saukowa daga kan gadon tace "Mama mama, na ro茩eki Mama kar ki bari Abba ya biyewa haukan Mu'az, shi fa sam ba ya da hanakali."
Dariya ta 茩yal茩yale da ita tace "Zamu gani dai waye mahaukacin, yanzu tashi ki je Abbanki na nemanki."
Kya蓳e fuska tayi kamar za ta yi kuka tace "Maaamaaa."
Ita ma kya蓳e fuska tayi tace "Na'aaaam.." 茒aure fuska tayi tace "Tashi ki je."
Jiki a sanyaye ta mi茩e ta 蓷auki hijabinta iya gwiwa ta saka sannan ta fice cike da fatan ba abin da take tunani ba ne zai faru. Dan in kuwa hakane to tabbas Mu'az bai da sanya a lamura kuma ya mata shigar sauri, amma fa hakan ba ya na nufin za ta amsa bu茩atarshi ba ne, duk da kuwa bayan dawowarsu ta yi tunaninshi sau 蓷aya, dan sosai kalaman nan na shi a ha蓷uwarsu ta 茩arshe suka tsaya mata a zuciya da ma 茩wa茩walwarta.
Tashin muryar Alhaji Auwal yasa ta nutsuwa sosai ta sadda kanta sosai duk da fa蓷uwar da gabanta ke yi ta 茩wan茩wasa 茩ofar tare da sallama a sanyaye sosai, ba tare da ya amsa ba Alhaji Yusuf ya bata umarni da "Shigo."
Tura 茩ofar tayi a hankali ta shiga takawa a nutse ba tare da ta 蓷aga ta kalli kowa ba, ita dai kawai ta ji idanun mutane a jikinta suna yawo, sannan daga 茩amshin turaren one million ta gane kusurwar da Mu'az yake zaune dan shi ke anfani da turaren, daga kallon 茩afafu ta gane inda mahaifinta yake, a kusa da shi ta zauna a ladabce tana fa蓷in "Ina wuninku."
"Lafiya lau Saleema." Alhaji Auwal da Papi suka fa蓷a a tare sai Alhaji Auwal da ya 蓷ora da "Baby kin ga har na fara kewarku tun yanzu, ina ma za ki koma gidana da zama?"
Sai kuma ya yi dariya yace "Ko da yake abinda ya kawomu kenan, amsarki ita za ta bayyana mana shin za ki rayu da mu ko akasin haka, dan babu wanda ya isa ya miki dole in dai ina raye."
Wani kallo Mu'az ya watsa mishi ta 茩asan idanu da tunanin "Za ko kaga abin da zan yi, a cikin gidan nan zan 蓷irka mata ciki in ya so kwa shafa mana fatiha bayan ra蓷awa 蓷anmu suna."
Maida dubanshi ya yi ga surukin na shi dake kallon Saleema yana fa蓷in "Mu'az ne dama ya ce yana sonki, kuma ya ce kin san da maganar, yanzu haka sun zo neman aurenki, kin amince a bashi aurenki?"
Alhaji Auwal ne ya katseshi da cewa "Ba ta amince a ba da aurenta ba, ta amince ta na sonshi?"
茒aure fuska Alhaji Yusuf yayi dan shi wannan sa'a ta Saleema a ganinshi ba sai an tuntu蓳eta ba, dan kawai Papi da Alhaji Auwal 蓷in sun matsa ne, wanda ya tasa dalilin da ya sa suke wani ririta yarinyar, alamu ma nuna masa yake Alhaji Auwal zai iya yin komai dan Saleemar, kamar dai wacce ta aikata masa wani babban abu da ba wanda ya ta蓳a kwatanta yi masa. Maida dubanshi yaui ga Saleema yace "Muna jinki, kin amince?"
Daga cikin hijabi ta zuro hannunta ta share gumin da ya ji茩a mata goshi har zuwa dogon hancinta, rawa jikinta ya kwasa da tunanin mafita, duk 茩o茩arinta na satar kallon Mu'az ta kasa ganin fuskarshi saboda tsayinshi sannan ya shige cikin kujerar da yake zaune sosai, tana so ko ya ne su ha蓷a idanu ta aika masa kallon "Ya za ka min haka? Haka kwatsam?"
Saidai rashin nasarar ganin fuskarshi yasa ta 蓷auki sama da minti 蓷aya ba ta amsa ba har ma ta manta a ina take saboda tashin hankalin da take ciki, ba ta san me ye so 蓷in ba kanshi, ba ta san wane irin zama za ta yi da shi ba, hasalima ba ta jin komai a game da shi, sannan abubuwan da ya dinga mata farkon haduwarsu ya saka mata shakku a kanshi, idan fa bai da 蓷abi'ar 茩warai? Za ta rayu da ba茩in ciki kenan har abada?
A kausashe Alhaji Yusuf yace "Malama ke fa muke jira, ya zaki wani yi mana shiru kamar yaranki."
A gigice ta 蓷ago kanta, hakan ya ba hawayen da suka taru a idanunta damar zirarowa suka sauko kan kutatunta, a ki蓷ile ta girgiza kai sai kuma ta kalli inda Mu'az yake, suna ha蓷a idanu ya jefo mata kallon" Ki min rai Saleema."
Inda ita ma ta bishi da kallon" Ba zan iya ba Mu'az." Alhaji Auwal ne yace "瞥ata."
Kallonshi tayi saidai suna ha蓷a idanu ta fashe da kuka, cikin kulawa ya taso daga inda yake ya zo kusanta ya tsuguna, cikin tausasawa yace" Baby, kina ji na? Idan ba ki shirya ba ki fa蓷a mana, kamar yadda na fa蓷a miki da farko babu wanda zai miki dole, fa蓷i ina jinki?"
Sadda kanta tayi 茩asa cikin muryar kuka tace"...
*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:48 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_19_
Sadda kanta tayi 茩asa cikin muryar kuka tace" Abba ni ban san komai ba, ina so zan yi magana da Mamana..."
Ta 茩arashe tana fashewa da sabon kuka, murmushi yayi ya dafa kanta yace" Shikenan ba komai, ki je sai ku tattauna da mahaifiyarki, zamu tafi yanzu zuwa gobe sai mu ji amsarki."
Mi茩ewa yayi yana fa蓷in" Kuma duk wanda ya takura miki ki sanar da ni, ni zan 蓷auki matakin da ya dace."
Ha蓷a idanu sukayi da Alhaji Yusuf dan ya san da shi yake, shi ma kuma ya kalleshi ne dan ya san ya ji kuma ya fahimta, mi茩ewa tayi a rikice ta juya ta bar falon na mahaifinta. Mu'az da ya bita da kallo tana fita a 茩ofar ya kalli Alhaji Yusuf yace" Abba zan iya magana da ita?"
Jinjina masa kai kawai yayi dan takaicin na Saleema ya hana shi magana, shi kawai gani yake yarinyar nan kamar ma sauya masa ita aka yi a asibiti, sam yarinya kamar wacce ta zo a zamanin Kakarshi Hajia Zarah.
Tana kaiwa tsakiyar falonsu ta tunkari 蓷akinsu ta ji muryarshi a bayanta yace "Saleema."
Cak! Ta tsaya jikinta ya 茩ara 蓷aukan kyarma, ba ta juyo ba har saida ya zo daf da ita ya tsaga gabanta, kallonta yake sosai kamar zai ha蓷iyeta, kamar an mintseneshi sai kuma ya dur茩usa gwiwarshi 蓷aya a 茩asa yana kallonta yace "Saleema, ban san me kike so na fa蓷a miki ba bayan wanda na fa蓷a miki a gida, kamar yadda na fa蓷a miki ke ce mace ta farko dana fara jin ina so, Saleema kwana uku ka蓷ai kukayi a gidanmu, amma rayuwar gidan gaba蓷aya ta canza, a wadanan kwanakin na maida komai na wa zuwa ga Allahn da ya halicceni, kwana na ke ina neman gafararsa akan abin da na aikata a baya, Saleema na kasance..."
Saida ya sadda kanshi sannan yace" Ina biyan bu茩atata da duk macen da ta birgeni, amma fa ba zina na ke aikatawa ba..."
Baya Saleema ta ja ka蓷an tana kallonshi da kyau, hakan ya sa shi mi茩ewa da sauri kamar zai ri茩ota yace" A'a ba yadda kike tunani ba ne, ina nufin ba na jima'i da mace, amma dai mu kan yi...wasa da junanmu har bu茩ata ta biya, Saleema ina ganinki na ji na aje komai gefe ina kuma so na yi aure da wuri."
Tafin hannunshi yasa shima ya 蓷an shafe gumin da ya fara tsatsafo mishi gaban goshi yace" Yanzu idan ki ka 茩i amince ya zanyi? Saleema ba zan iya auren macen da bana so ba dan kawai maganin sha'awata, idan ba ki amince dani ba kamar kin yerje na ci gaba da aikata 蓳arnar da nake aikatawa a baya."
Duk da hawayen da ke mata anbaliya saida ta kalleshi tace" Kenan nima *auren sha'awa* ne za ka yi da ni?"
Girgiza kai tayi ta ha蓷e hannaye tace" Ka ga dan Allah ka janye 茩udirinka a kaina, ka sake tunani ka bincika za ka samu wacce ta yi daidai da kai, ni...ni fa na sani wannan 蓷in ha茩茩ine dake hawa kan duka ma'aurata, amma yanda ka ke nuna min ya sa ni jin tsoron lamarin fiye da yadda kake tunani."
Numfashi ya sauke cike da sacewar gwiwa yace" Shikena Saleema, ba zan tilastaki ba, amma kamar yadda kika ce kiyi shawara da Mama, zan ji daga gareki zuwa gobe."
Ra蓳ata yayi ya wuce ya barta nan tsaye, saida ta ji ya rufe 茩ofar sannan ta 茩arasa ita ma 蓷akin ta samu mamanta zaune bakin gado tana shan magungunan ta. Ganin alamar ta ci kuka yasa hankali tashe ta aje kofin hannunta ta jawo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita, cike da kulawa ta kalleta tace "Hajia, me ya faru? Me ya sameki kike kuka? Wani abu ya miki?"
Girgiza kai tayi ta kwantar da kanta kan cinyoyin mahaifiyarta tana ci gaba da rusa kuka, dadda蓳ata ta fara yi ta sake cewa "Fa蓷a min me ya faru? Dukanki ya yi ne?"
Girgiza kai tayi cikin kuka tace "Mama ki tayani da addu'a, maganar aure Abba ya min kuma da Mu'az, bana jin komai da ya danganci a game da shi, ina tsoron kar Abba ya tilasani na auri Mu'az."
Girgiza mata kai tayi tace "A'a Hajia, Abbanku bai da wannan tsarin a rayuwa, ba zai tilastaki ba in sha Allah, amma ki zauna ki nutsu kiyi tunani, idan kin ga ya miki sai ki amince, idan bai miki ba ba wanda zai miki dole."
Share mata hawayen tayi tace "Yanzu tashi ki wanke fuskarki ki zo ki ci gaba da karatunki."
Jinjina kai tayi tana shashe茩ar kuka ta shiga ban 蓷aki, da kallo ta bita har ta shige cike da tausayinta da kuma fatan kar ya mata auren dolen, dan bata san me yasa yake hassala akan lamarin Saleema ba wasu lokuta? Mi茩ewa tayi ita ma ta fita daga 蓷akin dan ba lokacin baccinta