Showing 177001 words to 180000 words out of 191031 words

Chapter 60 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67995

baya ga hadda data samu ta Al茩ur'ani a yanayin da babu wanda yayi tsammanin za'a samu duba da a tarihi ita kanta ba ta san wani da ya samu karatu a yadda ta samu ba ba tare da ya dur茩usa gaban malami ba, hakan ma babbar *BAIWARTA CE*, ta san kuma Allah ya yassare mata lamarin ne saboda halin da ta samu kanta a ciki na matsi da takuran mahaifi wanda suka dinga samun sa蓳ani da mahaifiyarta game da hakan.

Sosai ta nutsu kafin ta fara zana zanen da take son gabatarwa kamar yadda Abdus-samad ya 茩arfafa mata gwiwa, saboda nutsuwar da take da bu茩ata yasa ba ma ta fara wa sai da dare idan Abdallah yayi bacci, dan yaron akwai rigima sosai musamman kukan dare wanda har yanzu suna fama da shi a kan haka, wasu lokuta ma jar shi kanshi sai yayi bacci ya barta zaune tana zanawa da gogewa da tsarawa. Haka ta 蓷auki sati tara tana aikin nan, bayan ta kammala ne ta ba wa Fareeda ta ce ta duba mata, ba komai ya sa ta yin haka ba sai dan ita ma mai 蓷inki ce wata茩ika ta gano mata wani kuskuren da ita ba ta hango shi ba, sannan bayan ta duba mata ta ce ita dai a nata ganin ba wani gyara tare da mata fatan alkairi, na gaba shine Huzeifa, shi ma ya duba mata kuma ba laifi duk da shi bai ta蓳a yin zanen kamar ita ba sannan ya 蓷inka, amma sai da ya nuna ma Fareeda wani gurin ya ce yana ganin da za ta gyara zai fi, daga Huzeifa ne sannan ta turawa wanda ya bata shaidar iya 蓷inki wanda dama shi mazaunin Niamey ne.

Cike da 蓷ar 蓷ar ta zauna jiran sakamakon sanda ya ce zai duba mata ta jirashi. Sosai ya jinjina mata da aikin nata, sai dai akwai inda ya 茩ara bata shawarwari hatta da irin kayan da za'ayi 蓷inkin a kai da kuma kalar matan da ya kamata su saka kayan dan tallatasu.


*Shagon* ta shigo hannunta 蓷auke da takardun, duk tsaye matasan suka mi茩e suna mata barka da shigowa, amsawa tayi da fara'a duk da fuskarta a rufe take da ni茩ab sannan ta ce su zauna, Iklim shine yaron da ta fi nutsuwa da shi saboda yadda ya fi girmamata da kuma yadda yake fa蓷a mata komai, dan ko ya zo da wani 蓷inkin daga 蓷aya shagon sai ya fa蓷a mata zai yi wani aiki ne, dan haka yanzu ma shi ta nufa kai tsaye ta 蓷an zauna akan kujera ta mi茩a mishi takardun tace "Ka ga aikin da na yi?"

Kar蓳a yayi yana dubawa yace "Masha Allah, amma Hajiarmu aikin nan ya yi, wannan hala 蓷inkin matar shugaban 茩asarmu ne?"

Murmushi tayi tace "Ba ka ga dinkunan sunyi na yara sosai ba, ai zan shiga gasar fitar da fitattun 蓷inkuna ne na 茩asa."

Zaro idanu yayi yace "Na 茩asa ranki shi da蓷e?"

Ba ta tanka masa ba sai sauran da ta kalla tace "Ku zo ku gani."

Tasowa duk sukayi suka duba suna ta yabawa sosai da cewa amma aikin yayi, murmushi tayi tace "Akwai Boyle da cotton swisse 蓷in da na bayar za'a kawo mana daga Dubai da wasu sauran kayan kwalliya, idan aka kawo zamu maida hankali mu ga mun fitar da 蓷inkin a jikin kayan tamkar yadda yake a zanen nan, dan haka nake so ku maida hankalinku sannan ku bani lokaci daga lokacin da zamu fara 蓷inkin har mu gama, dan wannan karan nima shago zan dinga wuni har sai mun gama aikin nan."

Jinjina kai sukayi suka ce" In sha Allah ranki shi da蓷e, Allah ya bamu sa'a." Mi茩ewa tayi tana amsawa da" Ameen."

Takardun ta fara tattarawa dan komawa ciki Iklim yace" Ranki shi da蓷e ki 蓷an bar mana su mana mu 茩ara dubawa da kyau, ni fa har na ji shau茩in aikin ya kamani kamar mu fara yanzu."

Wannan magana tashi ita tasa shi jin ba komai bane tunda ta yarda da shi, dan haka ta jinjina kai ta bar mishi 蓷in ta tafiyarta tare da fa蓷in" Idan kun gama dubawa ka kawo min ciki, zan sanar da su kana shigowa yanzu su barka ka wuce."

"Angama uwar marayu." Ya fa蓷a yana murmushi, *wannan* yarda da ta ma Iklim ita ta jawo mata asara da kuma wahalar banza, dan kuwa tsaf ya kwafe wannan zane a wayarshi ya turawa 蓷aya uban gidan na shi a waya tare da masa cikakken bayani, a lokacin shi sam bai ma san me ake ba, amma da ya ga zanen sai ya nemi hanyar da ake bi dan shiga kawai tare da ba wa 茩wararren wanda ya iya sarrafa computer ya maida mishi zanen a computer sannan suka fara shirin shiga gasar.

Duk wata kafa ta yanar gizo sanarwar gasar Mannequins (fashion designer) ake da za'a gudanar a ranar tallata al'adu ake, sai dai a wajen Saleema rana ta farko da ta gabatar da ta ta fasahar sai babu wani alamu da ya nuna an kar蓳i nata aikin sannan ba'a ce mata komai ba, hakan yasa ta shiga damuwa da zulumi har ta tuntu蓳i Abdus-samad ta fa蓷a masa, duk da shi kanshi yasan ko da ba zasu amsa bane dole dai zasu fa蓷a mata sannan su bata ha茩uri, to amma me yasa sukayi shiru? Hakan ne yasa bayan ya tashi daga nan da wayarshi ya shiga tuntu蓳ar wa蓷anda ya sani da kuma masu ruwa da tsaki na lamarin, amsar farko da aka bashi ita ce _"A yi ha茩uri yalla蓳ai, sanfurin da madame ta turo satar fasaha ne, dan an riga da an turo irinshi, a 茩a'ida kuma wanda ya taka mana doka ana cireshi ne a gasar tare da hanashi sake shiga sai dai ya tarbi wata shekara."_

Sosai hankalinshi ya so tashi, da ya tuna ita ya za ta ji kuma? Sai ya kwantar da nashi hankali ya nutsu sannan ya mata cikakken bayani. A ru蓷e ta kalleshi idanunta na cikowa da 茩walla tace" Amma...ta ya za'a ce...satar fasaha nayi? Ban ta蓳a ba wallahi, ban ta蓳a satar fasahar kowa ba, kai ma kuma ka sani ni ba..."

Rumgumota yayi jikinshi yace" Shiiii! Kwantar da hankalinki, ki nutsu kinji."

茒agota yayi daga jikinshi yace" Wa da wa kika nunawa zanen?"

Duka ta fa蓷a mishi wa蓷anda ta nunawa hr da Yayan Fareeda wato Huzeifa, saidai ta 蓷ora da" Na yarda da su ne, shiyasa na tura musu."

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon fuskarta yace" Ummu Abdallah, dama ai wanda ka ba wa yarda shi yake cutar da kai, baki ji an ce da 蓷an gari a kan ci gari ba? Wanda bai sanka ba ta ya zai samu damar zalintarka? Kiyi ha茩uri matanmu, mu 蓷auki a matsayin alkairin da zai riskemu a nan gaba, ko ma waye yayi hakan dan kanshi, wata shekara za ki shiga, sai dai mutum 蓷aya kawai za ki nunawa dan ya tabbatar miki."

Turo baki tayi tana neman sako da hawayen dake idanunta tace" Tom! Amma fa nasha wahala sosai wajen zanen nan, na 蓷auki sama da wata uku fa ina aiki ak..."

茒ora yatsarshi yayi a kan bakinta yace" Shiiii! Kar ki ce komai Babyyyyy, kiyi addu'a kawai hakan ya zama alkairi."

Daga haka ta ha茩ura da wahalarta ta farko ta shiga harin shekarar gaba, sai dai duk da haka tana bibiyar abinda ke wakana a gasar tare da tunanin a cikin mutanen nan waye ya ci amanarta, saida ta ji sunan wanda yayi nasarar hayewa zagaye na kusa dana 茩arshe a rukunin gasarar da kuma sunan kamfanin wato *KM fashion* ta fara zargin anya kuwa, dan ita dai ta san a shagonshi Iklim ke aiki, hakan yasa ta kirashi a waya take tambayar "Iklim dama mai gidanka ya shiga gasar nan amma baka fa蓷a min ba?"

Duk da a cikin waya ne amma sai ya dinga kame-kame yana murmushi da cewa "E..to, Hajiarmu dama, nima ban sani ba wallahi sai da suka bar garin ma."

Haka kawai ta ji bata yarda da shi ba sannan ta yarda lallai aikin Iklim ne dan a ranar shi ya ce ta bar musu zanenta su kara dubawa sannan shi ya maido mata da su. Murmushi tayi kamar tana gavanshi kafin tace _" Alhamdulillah, hakan ma nasararmu ce, tunda 蓷an garinmu ne kuma...fasaharmu ce."_

A hankali tace" Nagode Iklim, ka min hallaci." Daga haka ba ta 茩ara ganin Iklim shagon ba dan shi da kanshi ya kori kanshi, inda ita kuma ta maida hankalinta kan sauran ayyukanta dake ta sake bun茩asa a kullum sannan tana 茩ara samun gogewa a fannin.




*Alhamdulillah.*
02/07/2022 脿 10:42 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_57_




Sake dur茩usuwa tayi tamkar za ta yi sujada tare da daidaita wuyan rigar tana yankawa fuskarta 蓷auke da murmushi ta 蓷aga idanunta ta kalleshi tace "Allah ya huci ran sarkina Abu Abdallah, saura 茩iris fa na gama na bar maka 蓷akinka."

Sake tamke fuska yayi yace "Ki yi ta yi idan kina so, kika kaini bango za'a daina 蓷inki a gidan nan."

Da sauri ta 蓷ago ta kalleshi tana fa蓷a蓷a murmushinta tace "Haba dai, me yayi zafi haka? Idan na daina 蓷inki me zanyi?"

Saida ya sake mi茩awa Abdallah wayarshi sannan yace "Girki mana da kula dani, ko ba aiki bane?"

Ha蓷e murmushinta tayi tare da aje almakashin hannunta ta mi茩e tsaye ta tunkareshi, kawar da kai yayi yana sake ha蓷e fuska saboda kayan dake jikinta za su iya sakashi hasko wani abun daban alhalin tana halin rashin sallah, ba ta tsaya ko ina ba saida ta zauna kan cinyarshi sannan ta sagala hannunta a kafa蓷arshi tace "Abu Abdallah, fa蓷a min me kake so yanzu? Ka san dai 蓷inki ba shi zaisa na kasa baka lokacina ba ko?"

A hankali ya karkato kanshi har ya saka idanunshi a cikin nata a raunane yace "Da fari yunwa nake ji."

Da mamaki ta 茩an茩ance idanunta tace "Yunwa? Na 蓷auka tare muka ci abinci."

Yatsina fuska yyi yace "To ai yanzu ni sam duk yadda zan ci na 茩oshi idan ban...zam-zam, ki fahimta mana, idan fa ban jiki a jikina ba sai na ji ina kakkarwa saboda yunwa."

Waro idanu tayi sai kuma ta bushe da dariya ta 茩ara sagalo hannunta sosai ta jawo wuyanshi ta danna a 茩irjinshi tana fa蓷in" Rigima ko? To ai ka san bana sallah, ba dan haka ba ai kasan ni mai amsa kiranka ce a kowane lokaci."

茒aga kanshi yayi dake kwance a 茩irjinta yace" Na sani, yanzun ma tallafinki nake nema dan na samu bacci ya 蓷aukeni."

Murmushi ta sakar masa ta 蓷an juya ka蓷an ta kalli Abdallah dake zaune bakin gadon yana ta danna waya, kallonshi ta sake yi tace" Ya zamuyi da shi? Kafi kowa sanin rigimar Abbanmu."

Girgiza mata kai yayi yace" Ba dai Abbana ba, sai dai 蓷anki."

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta tace" A gafarceni to, 蓷anka."

茒agata yayi ya tashi tsaye tare da nufa wajen yaron yace" Bari na mi茩a shi wajen Ummi."

Rusunawa yayi gaban Abdallah yana son kar蓳e wayar yace" Yarimana, 蓷an Abbanshi, tashi muje wajen Mamie, za tabka alawa mai da蓷i."

Kallonshi yaron yayi sai kuma ya sake maida dubanshi ga wayar, Mi茩ewa yayi tsaye dan dama yasan ba saurarenshi zaiyi ba, cak! Ya 蓷aukeshi daga shi har wayar ya fita daga 蓷akin yana ci gaba da rarrashinshi.

Ganin sun fita yasa ta saurin tattara kayan data baza ta ajiye kan kujera da sauri ta fa蓷a ban蓷akin shi dan sake watsa ruwa a jikinta.



*Bayan Wata Biyu*



Da fara'a da kuma mamaki ya 茩arasa shigowa falon hannayensa biyu da ledoji, a tsakiyar falon ya aje yana kallon Safiya dake cin abinci saboda azumin da tayi yasa sai yanzu take ci yace "Umman gimbiya sa茩o ne daga 拼arki fa, duba mana ki gani me ye?"

茦o茩arin cire hannunta tayi tana fa蓷in "To, sa茩o kuma? Wa ya kawo yanzu a daren nan?"

Kujerar kusa da ita ya zauna yana fa蓷in "Baki ji an ce ana sallama ba? Ina fita na ga dreban can gidan..."

Sai kuma ya kalli Ardiya dake fitowa daga falonshi tana kwashe kwanukan abinci yace "Yawwa uwar 拼an matana. Zo duba mana..."

Ya fa蓷a yana kallon Safiya da har ta mi茩e yace "Zauna ma bari ta duba."

茦arasowa Ardiya tayi tana aje kwanukan bakinta har kunne tana murmushi ta dur茩usa tace "Tohh! Abban Hadeeya me muka samu? Ba dai kayan sallah ka 茩aro mana ba?"

Murmushi yayi yana kallon ledar da take kiciniyar bu蓷ewa yace "Ke dai bu蓷e mu gani."

A hankali ta fara ciro kayan ciki tana zazzaro idanu saboda dole ta nutsu wajen cirosu dan a goge suke a kwance, saida ta gama fito dasu gaba蓷aya ta aje kan ledojin sannan ta fara kallon kayan. Sak iri 蓷aya ne kayan, sai dai kowane an 蓷an li茩a wani 茩aramin kati mai 蓷auke da tambarin sunan *gimbiya Couture* 蓷aya an rubuta sunan *Mama Sofee*, 蓷ayan kuma an saka sunan *Mama Deeya*, sunan data karanta yasa ta sakin murmushin da bata shirya ba dan kuwa zahirin gaskiya daga zuciyarta ya fito, abu 蓷aya da ta kawo a ranta shine *tabbas aikin Saleema ne*, dan ita ka蓷ai za ta basu wannan darajar.

A hankali ta kai hannunta ta shafi lafiyayyar shaddar nan da ake wa la茩abi da *miel*, kuma tabbas ta ci sunanta dan kuwa haka take mai茩o tana 蓷aukar idanu ga mai kallonta, a dai yanzu a saninta nan kusa shaddar nan idan ba ita ce ta farko a farashin 茩arshe ba to ba zata gaza zuwa ta biyu ba. Ga kuma 蓷an uban leshen da ita dai ta san ku蓷inshi an ce mata dubu 蓷ari biyu har da sittin a haka fa wai daga Kano ma ba a nan garin ba. Ita yanzu abinda ba ta gane ba shine...

Sai kuma ta juyo da sauri ta kalleshi tace "Alhaji, kayan waye wannan? Wa ya aiko su?"

Ta蓳e baki yayi yace "Aka ce wai daga gi..." Wayarshi da tayi ruri ne yasa ya yi shiru ya shiga lalubenta a aljihu, yana ganin Saleema ce ya 蓷aga yace "Hajiata."

茒aga 蓳angarenta a nutse tace "Abba, ai an kawo sa茩on ko?"

"E an kawo, gashi kuma sai tambayata suke wa ya aiko?" Ya fa蓷a yana tsare Ardiya da idanu, a ladabce tace "Abba, na kune mana kai da su Mama da aunty, kowane da sunanshi a kai."

Numfasawa tayi kafin tace "Envelope 蓷in kuma, shi ya ce a baku tun kafin su tafi Saudia."

Da fara'a yace "Masha Allah Hajiata, yanzu ke kika musu wannan 蓷inkin? To angode sosai."

A nutse sosai kuma a sanyaye tace "Abba..." Sai kuma tayi shiru tayi saurin fa蓷in "Saida safe." Kashe wayar tayi duk da ta so ta ro茩eshi sa albarkarshi, wanda har yanzu take tsumayin ji daga bakinshi, tana so ta ji ya ce ina alfahari da ke kamar yadda ya dinga sakawa su Hadeeya a gabanta tana 茩arama, amma da ta tuna ai ro茩ane za ta yi kenan ba ta cancanta ba har yanzu? Sai kawai ba ta fa蓷a 蓷in ba ta 茩yalleshi da tunanin watarana zai fa蓷a dan ganin damarshi.

Tunda ta fahimci wayar da yake fa tana tabbatar da wannan kayan nasu ne yasa ta sake 蓷aukan wanda ke da sunanta tana dubawa, har Alhaji Yusuf ya taso ya kai hannu kan kayan ya 蓷auki envelope 蓷in bata san yayi ba, Mi茩ewa tayi tsayetana fa蓷in "Ikon Allah! Aaaa... Saleema ce ta aiko mana wannan kayan?"
Sai kuma ta aje nata ta 蓷auki na Safiya data koma ta zauna ko kallon kayan ba ta sake yi ba tunda ta ji suna waya ta mi茩o mata tace "Kin gani fa *Maman Hajia*?"

茒aga kai Safiya tayi ta kalleta jin sunan data kirata da shi, sai kuma ta kalli kayan ta yi murmushi tace "Masha Allah, Allah yasa albarka, idan na gama zan duba."

Dariya Ardiya tayi tace "To shikenan, bari na aje miki." Ta aje kayan kan 茩aramin teburi ta 蓷auki nata ta juya zata wuce 蓷akinta dan magana ta gaskiya ihu take so ta tsala, idan tana gabansu kuma ba zata iya ba, dan yanzu ma wannan fara'ar so take ta 蓳oye amma ta 茩i 蓳oyuwa, tana daf da wucewa Alhaji Yusuf yace "Ga ku蓷in ragunan layyarku ma sun samu."

Juyowa tayi tace "Kuma dai?"

Jinjina mata kai yayi alamar e, dariya tayi tace "Ina zuwa." Shigewa tayi shi kuma ya bita da kallo, yadsa ya santa da son ku蓷i ai ya 蓷auka za ta dawo ne ta tambayeshi nawa ne kafin ta yi 茩o茩arin rabashi da wani abu, hakan yasa ya tabbatarwa kanshi lalle abinda aka bata yafi wanda ke hannunshi yawa. Sake 蓷aukar kayan yayi na maza da Ardiya ko ta kansu bata bi ba, galleliyar gezna ce wacce daga 茩amshin ya gane haka, tasha babban 蓷inkin daya dace da ita ga kuma kwalin daya tabbatar masa da turare ne mai sunan 24h, murmushi ya saki a fuskarshi tare da furta " *Hajiata kenan, akwai sanin takamata.*" 茒akinshi ya nufa da nashi kayan su ka bar Safiya ita 蓷aya a falon a zuciyarta tana ta saka mata albarka tana kuma kara kallon kayan wanda alamu suka nuna tabbas hada na Ahmad, amma Ardiya da ta ci karo da wannan tsadaddi ta kuma tabbatar hada ita sai bata sake bi ta kan komai ba duk ta rikice.


Tana shiga 蓷akinta wayarta ta 蓷auka ta kira Agaishat, saidai tana 蓷agawa Agaishat 蓷in tace "Ba dai ke ma abinda kika kira ki fa蓷a min ba kenan?"

Da mamaki Ardiya tace "Me fa?"

Daga wajen Agaishat tace "Ko baki ji yarinyar nan ta haihu bane?"

Da jin haushi Ardiya tace "Wace yarinya kuma? Wai ya kike bani bayani a dun茩ule?"

"Khairat mana, kishiyar Hajia Iklima." Ta fa蓷a tana daga murya, tsaki Ardiya tayi tace "To me ya dame mu, kinga can fa matsalarta ce, ita ba ta nuna ba'a isa a mata kishiya ba? To ai gashi nan da ranta tana gani kishiyar na ta haihuwa, sai me kuma?"

Kallon kanta tayi a madabi tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login