Showing 168001 words to 171000 words out of 191031 words
na ji da蓷i mana."
Yatsarshi yasa yana share mata hawayen data 茩a茩aro 蓷azun yace" 茦arya haram, in yi kuma ki zo ki yayatani."
Tsura masa idanu tayi a matu茩ar sanyaye tace" Yanzu kai Abdul baka jin ya dace ka min adalci? Me ye a cikin kalmar to da ba za ka iya fa蓷a ba?"
Murmushi yayi yana sake ri茩e 茩ugunta da kyau yace" Idan hakane to fara fa蓷a?"
茒auke idanunta tayi daga kanshi tace" To ai ni bana sonka ne, da ina sonka dana fa蓷a maka tuntuni."
Ha蓷e fuska yayi yace" Oho! Hakane?"
Jinjina kai tayi tace" E mana, hakane."
Tureta yayi daga jikinshi yace" To ni na fa蓷a miki ina sonki 蓷in ne da kike son tursasani? Bana sonki malama wuce 蓷akinki."
Ya fa蓷a da nuna mata 茩ofar 蓷akin na ta, dafe 茩irjinta tayi sai kuma ta dinga 蓷an bubbu蓷a hancinta kamar tana sha茩ar wani abu, yatsina fuska tayi tace" Nima bana sonka Abdul kuma bana son 茩amshin turarenka mai kama da... "
Sai kuma tayi shiru saboda tasowar da yayi ya sake ha蓷ata da kugunshi yace" Uhum! Me kama da me?"
Sadda kai tayi tace" Wallahi gaskiya zan fa蓷a maka, turaren nan yadda kasan kayi wanka da Gwanda."
Tintsirewa tayi da dariya ta ja baya daga ri茩on da ya mata saboda mamakin da ta bashi, sau uku kenan yana canza turare tana cewa bai mata ba, wannan 蓷in fa ma da tsada ya siya amma wai kamar yayi wanka da Gwanda, girgiza kai kawai yayi ya ra蓳ata ya 蓷auki envelope 蓷in da ya shigo da ita yana fa蓷in "Ba dai sarkin naki kika raina haka ba, ci gaba *Sadiyayye* akwai ranar da zan rama, kuma na fasa miki albishir 蓷in da na zo da shi."
Da gudu ta bishi saboda 蓷akin da yake neman shigewa ta ri茩o hannunshi tace "A'a yalla蓳ai, ni wallahi iya gaskiyata ce na fa蓷a maka, amma tunda baka so ba zan sake ba, fa蓷a min me ka zo min da shi?"
Mi茩o mata envelope 蓷in yayi yace "Shaidar kammala koyon 蓷inkinki..."
Duk da ya kai 茩arshe amma ihun da tayi tare da ma茩ale masa a wuya yasa dole ya 蓷auke wuta, sumbatarshi ta shiga yi a fuska har saida ta kunna masa caji ya shiga mayar mata da martani, da sauri kuma ta nemi zillewa ya fa蓷a da ita kan gado yace" Baki isa ba Salee baby, ke kika tsokanoni fa."
Daga nan suka sauya wata tashar aka mata da duk wata rigimar wa ke son wani wa ye ba ya son wani, sai dai suna mantawa idan suka shiga wannan falin na daga babu wanda baya fa蓷awa 蓷an uwanshi kalmar kna sonki ina sonka ina 茩aunarki ina 茩aunarka, amma idan suna duniyar mutane sai suyi ta zare idanu su a dole sai 蓷aya ya fara fa蓷a kafin 蓷ayan ma zai fa蓷a.
*02:43 na dare* ta dadda蓳ashi, ko bu蓷a idanu bai yi ba dan ya san me zaiyi ya mi茩e idanunshi rufe yace "Muje."
Tsaye tayi wuri 蓷aya tace "Shine kuma ko kallona ba za ka yi ba, kenan na fara takura maka ko?"
Bu蓷a idanu yayi da tunanin ya rasa me ke damunta da yanzu ita abun magana baya mata ka蓷an, haka kawai tayi ta masifa tana nemanshi da rigima, kama hannunta yayi ya 茩akaro murmushi yace" muje matanmu."
Suna isa bakin 茩ofar ban蓷akin ya bu蓷e mata ta shiga yayi tsaye kamar yadda yake yi kullum, saida ta gama ta fito ya dawo ya kwanta, ruwan data 蓷auka a cikin gora za ta sha yasa shi fa蓷in" Dan Allah karki sha, kinga ba na sake tashi rakaki ba sai dai ki yi shi a gado."
Marairaicewa tayi tace" Ma茩oshina ne fa sai ya bushe sosai idan ban sha ba."
茦wafa yayi yace" Ni dai na fa蓷a miki, kina sha ki nemi mai rakaki."
Kya蓳e fuska tayi ta bu蓷a bakinta da yanayi na jin rigima da koma waye tace" To dan All..."
Da sauri ya ha蓷e hannayenshi alamar ro茩o yace" Na ji, na ji sha Hajian Abbanta, zan rakaki."
Turo baki tayi ta 蓷aga gorar ta kifa kai cike da jin ta fa kai mafa蓷aciya ita ma, saida ta sha rabin robar sannan ta aje, matsowa tayi daf da gadon ta 蓷ora hannayenta, wara 茩afarta 蓷aya tayi ta saka nashi 茩afafun tsakiya, bu蓷a idanu yayi ya kalleya yana jira ya ga ta 茩etara amma ba ta yi hakan ba sai ma 蓷ora kanta a 茩urjinshi dake yana kallon sama, rufe idanu tayi tace "Yalla蓳ai dadda蓳ani bacci zanyi."
Girgiza kai yayi ya 茩ara rumgume da kyau a jikin nashi yana ayyana "Allah ka sa wannan bala'in nata ya zamar min alkairi."
A zahiri kuma cewa yayi "To shikenan sarauniyar mara蓷awa."
A sanyaye tace "Um um! Kai ne sarkin mara蓷awar ai."
A sanyaye shima yace "A'a na bar miki, a duk garin Mara蓷i da kewayenta wa kika ta蓳a gani na raka ban蓷aki? Ko kuma kin ta蓳a ganin wacce ta hayeni hakane kamar dai ke 蓷in nan?"
Da sauri ta 蓷ago kanta ta kalleshi fuskarta da alamar tuhuma tace "Ban gane na ta蓳a gani ba? Yo dama kana hakan ne a 蓳oye ban sani ba? Inna lillahi wa'inna ilaihi...!"
Ganin tana niyyar sauka kuma har ta bu蓷e baki kamar za ta fashe da kuka yasa shi saurin ri茩eta gam yace "Shiiii! Baby ba fa abinda na ke nufi kenan ba, kinga kwanta dan Allah ki yi bacci kinji, da safe zan miki bayani."
Ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana fa蓷in "Ta蓳! Idan abinda nake tunani ya zama gaskiya ko? Hmmmm! Yalla蓳ai ina kishinki fa."
Sai kuma ta sake 茩am茩ameshi tace "Ina so...na yi ta zama a haka har abada."
Dariya kawai yayi shima ya sake rumgume a jikinshi yana addu'ar bacci ya kwashe mishi ita yanzu yanzu, shiyasa kwanakin nan baya son farkawar nan ta ta fitsarin dare saboda kafin wani baccin ya 蓷aukesu ba sai asuba ta kusa yi.
*Washe gari*: Hannun yasa zai figi ri蓷in da take ta ci hankali kwance ta yi saurin janye hannunta tace "A'a fa."
Kallonta yayi yace "Kinga fa ba茩o ne zai shigo, idan ba zaki daina cin abun nan ba ki koma 蓷aki to."
Mi茩ewa tayi ta nufi 蓷akin tana cin abunta ya bita da kallo, haka kawai fa ta sashi tsayawa a hanyarsu ta zuwa ya siyo mata shi mai yawa, shi wallahi ya 蓷auka tsaraba ce za ta yi, amma gashi nan sai ci take kuma ya nemi hanawa ranar wuni tayi tana kuka da fa蓷a dashi a gidan, 茩arshe Ummi ta fa蓷a ma ita kuma ta ce ya bata ai baya komai dole ce ta sa haka, da ya nemi sanin dolen sai ta bashi bayani a ninke cewa yarinyar da aka sani da kunya da zurfin ciki, amma harbta iya buda baki ta ce a mishi magana ya bata abunta ai ko abun babba ne, to shi dai har yanzu bai gano komai ba bai kuma ga dalilin da zai sakata cin waccen abun ba mai za茩i da 蓷aci 蓷aci.
Kar蓳an sakamakon gwaje gwajen da aka yi musu yayi sannan ya sake maida hankalinshi ga likitan dake fa蓷in "Sannan yalla蓳ai akwai 拼ar matsala dangane da tafiyar taku tare da uwar-gida."
Tsareshi yayi da idanu yace "Wace irin matsala kuma? Ta ta蓳a tafiyar nan fa."
A ladabce yace "E yalla蓳ai, ba wai daga takardun bane ko wani abu daban, kasan wannan sabuwar gwamnatin ta aza sabuwar dokar hana masu ciki tafiya aikin Hajjd ko umra saboda wasu wahala ta kan sasu 蓳ari musamman idan cikin 茩arami ne, to kuma a gwajin da muka ma madame ya tabbatar mana tana 蓷auke da juna biyu har tsawon sati goma sha biyar, shine dai kawai 拼ar matsalar, amma idan kuna so za'a iya goge rahoton dan..."
Mi茩ewa yayi tsaye hannunshi dafe da 茩irjinshi yana kallonshi yace" Ciki? Da gaske ciki gareta?"
Jinjina kai yayi yace" Tabbas yalla蓳ai, dake gwajin 茩wa茩wafi mukayi daga jini muka gano hakan."
Rintse idanu yayi wasu zafaffan hawaye suka silalo masa daga kurmin ijiyarshi ta dama yana furta" Alhamdulillah, Alhamdulillah, tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai, Allah kaine Allah kuma kaine abun godiya."
Aje takardun yayi akan 茩aramin teburi ya fuskanci gabas yayi sujadu shukr ya kara 蓷aga hannu yace" Allah nagode maka, Allah ka sauketa lafiya, Allah ka raya mana abinda za ta haifa, Allah ka bamu ikon tarbiyarshi bisa tafarkin addininka."
"Ameen." Likitan ya fa蓷a yana gyara zama da murmushi a fuskarshi, tashi yayi ya juyo ya kalleshi yace "Ka zama shaidata ko da na mutu, na yi al茩awari tsakanina da ubangiji zan yi azumin wata 蓷aya bayan watan nan da muke ciki na gode masa akan wannan babbar kyauta da ya min."
Envelope 蓷in ku蓷i ya ciro daga aljihunshi guda biyu, niyyarshi dam zai ba wa likitan 蓷aya ne dayar kuma zai fita ne yanzun, amma sai ya mi茩a mishi duka yace" Goron albishir 蓷inka."
Kar蓳a yayi ya rusuna yana godiya har ya bar gidan bai bar godiya ba na jin da蓷in wannan kyauta. Yana komawa ciki ya zauna bakin gadon yana kallonta wai har bacci ya 蓷auke hannunta ri茩e da ri蓷in nan, murmushi ya saki tare da 蓷an jan rigar atamfarta sama ka蓷an ya tsurawa mararta idanu, dur茩usawa yayi kasa ya sumbaci daidai cibiyarta sannan ya gyara mata rigar ya tashi tsaye ya sumbaci goshinta, a sanyaye yana kallon fuskarta yace " *Ina sonki rayuwata.*"
Juyawa yayi ya fita a 蓷akin yana ayyana "Bari ta tashi ta min list na duk abubuwan da take da bukata na ci in siyo mata, idan babu a nan kuma zan sa Ummi ta turo mana."
Yana jin kunya sosai na fa蓷a mata wannan magana dan shi dai bahaushe ne ta wajen uba, ama da ya ce Ummi ta baro fada ta zo ta dage ba za ta zo ba haka kawai dole ya fa蓷a mata an fasa tafiyar ne da Saleema, kuma baya so ta koma gida ita ka蓷ai ya fi so su tafi tare da Ummin, dan barin masarautar ba shi ba Saleema kuma ba Ummi akwai matsala, hankalinta ta so tayarwa me yasa aka fasa tafiyar da Saleema? Shine kawai a ta茩aice yace mata "Ummina an ce ba ita ka蓷ai ba ce ba fa, kuma yanzu an hana tafiya da masu wannan abun..."
茦itt! Ya yanke kiran wanda ya sa Ummi mi茩ewa a rikice ta aniya sake tura masa kira, saida wayar ta tsinke sannan ya sake kiranta a take tace "Da gaske an tabbatar maka, dama ni nayi wannan tunanin, amma dai da ban tabbatar ba sai nayi shiru, ina take? Ba ni 拼ata na ji muryarta dan Allah."
Murmushi kawai yayi yace "Ai daga cin ri蓷in nan bacci ya 蓷auketa."
Da zumu蓷i tace "To shikenan, Babana ka ga dai yarinyar nan ka kula min da ita dan Allah, kuma banda hushi dan kasna ba ita ka蓷ai ba ce sai a na ha茩uri."
Murmushi ya sake yi kawai bai ce komai ba har suka gama wayar a haka bayan tabbacin da ta bashi safiyar gobe d izinin Allah za ta 蓷auko hanyar zuwa. Cikin yardar Allah kam washe gari gimbiya Ramlat ta zo nan, sai dai basu koma ba har saida jirgin Abdus-samad ya 蓷aga sannan suka juyo cike da masa fatan alkairi da sauka lafiya. A ranar suma suka baro Niamey suka dawo Mara蓷i, sai dai kamar yadda Abdus-samad ya sani ne indai basu nan dole wani abu zai faru, suna zuwa suka samu labarin rasuwar mutumin da ya farmaki Abdus-samad 蓷in a masallaci wai an bashi guba a abinci ta hanyar wani dogarin, dan tunda aka rufeshi sarkin bulala ka蓷ai ke zuwa inda yake kuma yake bashi abincin.
Sam wannan bai damu Saleema ba kamar ta corridornta da ta ga an bu蓷a wata hanya ana gyara, ba ta san me ake ba dai saidai yawan hayaniyar da ake wurin yasa ta za蓳ar zama wurin Ummi, idan sukayi karatunsu da safe sai ta yi zamanta can tasha bacci wani lokacin sallah ka蓷ai take tashi yi akan lokacinta.
*Bayan sati uku*
Duk kallon kallo suke ma juna a falon kowa na son sanin dalilin wannan taro na gaggawa haka, shi kanshi fa Abdus-samad 蓷in dirowarshi kenan garin, amma ya wani kirasu a babban falonshi ya kuma zuba musu idanu yana ta kallo 蓷aya bayan 蓷aya. Gimbiya Kubra da a yanzu bata da damuwar komai, dama mutumin nan ne kuma sun san yadda sukayi suka gama da shi, dan haka take ganin bata da wani sauran fargaba a yanzu, dan su a yadda suka 蓷auka tunda har mutumin nan ke gidan horo to fa taurin kai yayi ya 茩i fa蓷an wanda suka aikoshi kamar yadda akayi al茩awari, dan haka ma da suka kasheshi suke ganin sun 蓳atar da shaidar da ta rage ma sarki. Ita a yanzu Saleema ce a gabanta, bayan shiga hancinta da tayi a du茩un茩une ta hanata rawar gaban hantsi, sai ya zamana yanzu ta lura da wasu canje canje a jikin yarinyar, haske take 茩arawa sai kuma kyau dake fito mata ga 茩iba da take 茩arawa, ma'ana indai cikine da ita to wanda ya kar蓳i jikinta ne ya kara mata kyau? A karo na ba adadi kenan ta 茩ara kallon Saleemar da zaman ya fara gundurarta ta 蓷an yatsina fuska tare da fito da 茩afafunta daga lan茩washewar da ta musu, a tare Ummi da Abdus-samad suka kalleta dan dukkansu motsinta akan idanunsu yake, tsaye ya mi茩e yana 茩ara tamke fuske ya maida hannayenshi baya.
Sadda kai 蓷angaladima yayi da waziri da kuma liman da Sheikh Mukhtar kowanensu da mamakin mahimmancin abinda ya sa shi tarasu a falonshi na musamman sannan fuskarshi ba ko rawanin, ba ma maganar rawani ba kanshu ko hula babu, yana dai sanye da riga tazarce, da yanayin zafi zafi da kuma kaushi domin rikita magautashi ya kalli 茩ofar shigowa yace "Na samu labarin mutuwar 蓷an kurkukuna tun ina 茩asa mai tsarki, abun mamaki a nn shine..."
Sai kuma ya kalli galadima yace "Ta ya akayi haka ta faru?"
Sai kuma ya saki murmushin gefen la蓳蓳a yace "Ko da yake, wa蓷anda suka turoshi suna tunanin zai fallasasu ne, shiyasa suke ganin sun 蓷auki ranshi kafin na san komai dangane da su, in ba hauka ba ta ya za'a yi tsammanin mutumin da ya 蓷auki sama da wata uku hannunmu a ce bamu samu wani bayani a gunshi ba? Mutumin da yake 蓳ari saboda tsoro, hakan yasa tun ranar da abun ya faru ya sanar dani komai... Hummmm!"
Sai kuma ya girgiza kai yana kallon kowa na 蓷akin yace" Allahn da ya halicceku shi ka蓷ai zai muku hisabi, talalar da ya muku kuna cin karanku babu bakakka ita ta bani tabbacin Allah yana son kamaku da kanshi ne, duk u茩ubar da zan muku ba za ta kai wacce ya tanadar muku ba daidai da cikin cokali, dan haka na barku ku rayu da abun kunyarku, sai dai ku sani..."
Ya fa蓷a yana nuna sama da yatsarshi manuniya alamar rantsuwa zai gitta, a kasashe sosai muryarshi a sama yace" Wallahi tallahi idan kuka sake shiga rayuwata ko ta ahalina, na rantse muku da Allah sai na aje rigar sarautar zan gicciyeku a tsakar gari yadda kowa zai ga gawarku, wannan rubutacciyar kalmata ce."
Sai kuma ya sake maida hannunshi baya ya goya ya kalli sheikh Mukhtar yace" Kawu, a rufe mana da salatin Annabi."
Dariya ce ta so kubxewa Sheikh, wato lamarin Abdus-samad sai Allahn da ya halicceshi, ta ya ma zai rikuta musu lissafi haka ya hautsina musu kayan ciki, sannan ya ce a rufe da salatin annabi? Sai kawai ya sake murmushi yana sadda kanshi tare da satar kallon mutanen. Tabbas gimbiya Kubra na bu茩atar ganin likita da gaggawa, dan jikinta rawa yake matu茩a inda idanunta ke ta kakkafewa tamkar wacce ke zanzana.
Haka ma galadima da waziri a matu茩ar ru蓷e suke dan sai kallon kallo suke suna 茩ara sadda kawunansu, bai ce su ne ba, yayin magana bai kallesu ba bare kowa ya gane, amma su da suka san kansu duk firgici ya bayyana a tare da su. *Tiiiiff!* Gimbiya Kubra ta 茩arasa kai wa kwance ta fa蓷i, hakan yasa yaran suka yi ca a kanta musamman ma 拼a拼anta da babu wanda ya damu dan kasan kai dai ba ka yi komai ba, ko Izzatu ma da take da wasu daga cikin halayarta bata san komai akan abinda take shiryawa ba. Da azama aka 蓷auketa zuwa asibitin dake jere da gidan sarki duk da aqibitin maqarautar ce amma ta fi kar蓳an ba茩i daga waje fiye da daga masarautar.
A lokacin da suke likita cirko cirko galadima da waziri suka samu rufaffiyar wasi茩arsu daga mai martaba cewa an ciresu daga mu茩amensu washe gari kuma za'a yi sabon na蓷in wasu, hakan ya 茩ara dagula musu lissafi da tunanin ina zasu kai wannan abun kunya, su basu samu babban matsayin ba kuma an tun蓳ukesu daga wanda suke da. Dan haka ma basu kula da kururuwar da 拼a拼an gimbiya Kubra suke yi ba sanda aka fa蓷a musu ta samu shanyewar 蓳aren jiki, sai dai akwai yiwuwar a kaita babbar asibiti.
*Kwana biyu* kenan gimbiya Kubra na babbar asibiti tana kar蓳ar kulawar likitoci, gashi asibitin dama tsari biyu gareta, in ma ka bar kulawar marar lafiya a hannun likitocin, ko kuma dai mai kulawar ya zama guda ce dan ba'a son tarwatu, gimbiya Kubra kuma duka 拼a拼an nata guda biyar mata uku ne dama biyu manyan sune masu aure, sai maza biyu duk suna karatu sai Izza, hakan yasa ita ka蓷ai ba za ta iya kula da ita ba dole aka barta hannun likitocin. Gashi yanzu tana kwance asibiti ba ma a masarautar ba bare ta ga me ke faruwa, kuma kusan hakan shi ya fi mata alkairi, dan kuwa a gidan soyayya da kulawa ce ta musamman ake ba wa Saleema da kowa ke ta fatan saukarta lafiya, ba ga hadiman ba baga uban gidan ba da Ummi.
Yanzun ma ayabar da ya bu蓷e ya saje mi茩o mata yace "Daure ki ci wannan to shikenan, kinga fa ce min akayi mai ciki ta dinga ci sosai tana koshi."
Juyar da kanta tayi kamar za ta fashe da kuka tace "Ni wallahi na gaji yalla蓳ai, ta isheni hakan."
Iska ya huro daga bakinshi ya aje ayabar ya sake matsawa kusanta yace "To yanzu me kike so.?"
Girgiza kai tayi tace "Ba komai, ni bana son komai yanzu."
Murmushi yayi ya jawo kanta ya 蓷ora a 茩irjinshi yana shafa mararta yace "Kinsan me? Yanzu fa蓷a min burinki a kan 蓷inkin da kika koya?"
Numfashi ta sauke sannan ta kamo