Showing 180001 words to 183000 words out of 189325 words

Chapter 61 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

228

lokacin da mai labaran ya soma magana akan Hajiya Maryam, matar da shekaru bakwai a baya aka fasa yanke nata hukunci sanadin hauka.

"Cikin iko na Ubangiji, ta samu lafiya ta warke ras bisa tabbacin da aka samu daga wurin kwararren likitan kwakwalwa Dakta Yusha'u Rano. Sai dai kuma ba anan gizo ke sa?ar ba..."

Abba ya katse yana mai jin wani irin Waci a ransa. Anti Maijidda ta dube shi gami da Wan dafe hannunsa.

"Naga alama ba ka kaunar wannan labarin, tun jiya da aka yi zaman shari'arnan ka ke matsawa kanka da tunani."

Abba ya yi murmushin ya?e.

"Haba Jidda, kin san dole na ji zafin wannan al'amari, na sani al?alan gwamnati sun yi iyaka kokarinsa na ganin an samu kwakkwarar shaidar da za'a yankewa matar sn hukunci da shi a gaban al?ali amma kuma babu koda Wigo, sai dai ta ina kike tsammanin hukuncin zai min daWi bayan ta yanke kauna tsakanina da Wan uwana? Kai bana jin a duniyarnan zan iya yafewa Maryam. Ta cutar da ni ?arshe."

Ajiyar zuciya ta saki ta jinjina kai.

"Tabbas hakane, ba kai kaWai ba, ta yiwa kowannenmu tabon da har abada ba zamu mance da shi ba. Amma babu yanda muka iya tunda mai afkuwa ya riga fa ya afku. Don Allah ka cire komai a ranka, ina mai tabbatar maka cewa duk inda Maryam za ta shiga a duniyarnan alhaki ba zai bari ta runtsa ba. Ai ha??okin da ta ci yawa ne da su. Wallahi tun ba ta mutu ba za ta soma girbar abin da ta shuka."

"Allahu ya sa hakan."

Sallamar ?assim ce ta katse Anti Maijidda, gaba daya ya tsome ya yi wata iriyar rama saboda masifar shaye-shaye da ya yi a baya wanda a yanzun ya haWu da ciwon hanta da ya yi sanadiyyar ba shi tsoro har ya yiwa kansa faWa da kuma taimakon addu'a da nasihohi daga Abba da ma Anti Maijidda da ta ja shi a jiki, aka samu ya rabu da sha.

Dur?usawa ya yi ya gaishe su. Suka amsa da kulawa.

"Abba, dama Mami ce ta zo gidannan, tana falon ?asa."

Har ga Allah shi bai ma kawo wace Mamin ba.

"Wacece Mami?"

Ya tambaya da zuciya daya, Anti Maijidda kuwa tuni ta je gano. Wato dai Hajiya Maryam ba ta da kunya, kenan tana nufin ta biyo igiyar aurenta tunda har yanzu da aure tsakaninta da Abba? Bai tsinka igiyar ba. Sai ta yi shiru kawai tana jin ?assim na yi mishi bayanin wace Mamin. A ?arshe ta ga ya fusata ya a faWan me ya kawo ta gidansa? Kafin ma su kai ga wani yunkurin sai ga sallamarta a falon. Gaba Waya suka dube ta. Hajiya Maryam sarkin gayu da ?amshi, ita ce cikin wani tsohon atamfar shekara fa shekaru sai ko hijabi koWaWWen dake jikinta. Ta rame kwarai kuma ta yi duhu hakan ya ?ara bayyana gajartarta. Ta karaso tana ?arewa falon kallo, ko ba a faWa ba an narka uban dukiya. Ganin Maijidda ya sa wani abu ya soki zuciyarta, ta kauda idanu daga kanta ta maida saman na Abba. Kan ta kai ga magana ya riga ta bayan fitar ?assim.

"Me ya kawo ki gidana?"

Da Wumbin mamaki ta dube shi.

"Yusuf, ni kake tambaya me ya kawo ni gidanka? Kai fa mijina ne, uban ?a?ana ai duk lalacewata bai kamata ka wulakanta ni ba."

Ya Wan Wagamata hannu.

"Dakata, ke Maryam ai ba ki da darajar da za'a wulakantaki dominsa, dama can kura ce da fatar akuya. Ni dai babu wani ja in ja da zan tsaya yi da ke, aure kuma da kike maganarsa ki je babu shi tsakaninmu, na sake ki. Har abada ba na jin zan ?ara rayuwa dake Maryam. Abinda kika aikatamin da zuri'ata ke da Allah wannan, ga ki ga duniyar, ta isheki. Ki tattara ki ficemin daga gida wallahi daidai da dakika ba kaunar ganinki nake ba."

Mami ta ji wata kaWuwa sosai, a tarihin rayuwarta ai ba ta taSa kawo saki tsakaninta da shi ba. Yau kuma ya sake ta a gaban ma?iyiyarta. Ta yi kwafa.

"Dama nasan a rina tunda ka auri Maijidda! Ke kuma sai ki zuba ruwa a ?asa ki sha. Yusuf kai kuma wallahi sai ka san ka yi da ?ar halak. Allah ya isa tsakanina da ku."

Tana kaiwa nan ta juya fuu ta bar falon tana kuka. Shikenan ita kam ta shiga uku, abubuwa goma da ashirin sun bi sun haWe mata.
***
Maigadin ya bita da kallon tsaf yana mai nazartar yanayin halittarta. Ya kai ta ma?ura don haka a tunzure ta ce.

"Wai Bello ba ka shaida ni ba? Hajiya Maryam ce aminiyar Hajiya Lubna uwargidan Honarabul."

Sai a sannan ya dauki murya da ma kamanni amma abin dai da Waure kai yanda duk ta lalace ta yi muguwar rama. Kamar ba ita ce wannan Hajiyar mai ta?ama ba da take zuwa tana amsa gaisuwarsu dakyar. Dama can ya tsane ta ballantana da wannan Wanyen aikin da ta yi na rashin imani ya cika ko'ina duk da a yanzu ya zama cikin tsoffin labarai amma jin ta fito ya ?ara tada cece-kucen jama'a a kai.

"Ina magana Bello ka yi min banza kuma ka tare hanya?"

Ya Waure fuska tamau yana zabga mata harara.

"Wacce kika zo wajenta ai tuni ta jima da barin wannan gidan. Can garin bin yawon bokayenta ta kama hanyar Chadi a mota tayi mummunan hatsarin aka yanke mata ?afa guda. Yanzu dai ta koma garinsu can ?auyen Auyo cikin Jigawa, domin Alhaji tuni ya sallama mata, maganar nan da nake maki shekaru biyar kenan da afkuwarsa. Sai ki bita can."

Ya ?arashe yana juyamata ?eya. Mami sai ta ji wani irin yaam tsikar jikinta ya tashi, an yankewa Hajiya Lubna ?afa kuma ta koma ?auye? Ita kuwa ta shiga uku, da Hajiya Lubna ta dogara, wurinta take tunanin za ta ji samu kuWaWenta da ta biyo bashi wanda ta aikamata ta akawun don ta tura ga Babandi, ba ta kai ga tura masa ba ne alikacin suka samu labarin mutuwarsa ta hanyar yaronsa na ?ut-?ut. Ga babu komai a akawun din nata kaf ta haWa don ayi nata aiki mai kyau akan Abba da Maijidda da kuma Humaira.

Kuka sosai ta fashe da shi, gefe guda ta tausayawa aminiyarta, a wani gefen kuma na takaici da tunanin inda za ta nufa. ?assim ya ce nata Mubarak ya yi aure kuma yana zaune ne a can kudu da matarsa kuma bayarabiya ya aura musulma. Ta dai karSi lambarsa da zummar za ta kirashi. Hakanan ta juya saboda mitar da Bello ke yi akan ta bar ?ofar gidan kar ta yi masa sanadin aikinsa.

Kai tsaye gidan Futuha wanda dama tun farko ita ce ta je ta taho da ita, amma firr Mamin ta ?i zaman koda mintuna biyar ne tace ita dai sai ta je ga Abba ta koma Wakin aurenta. Duk yanda Futuha ta so nuna mata hakan ba mai yiwuwa bane ta yi kunnen uwar shegu da ita.

Ta iske Futuhar zaune tana cin fara da mai sai ko salad da ta yanka a kai, tana ganinta ta yi saurin mi?ewa tsaye.

"Mami kin je? Ya ku ka yi da Abban?"

Sai ta zauna ta fashe da kuka, cikin kukan ta ba Futuha labarin komai hsr na zuwanta gidan Hajiya Lubna. Futuha ta koma ta zauna jikinta a mace tana sharce nata hawayen.

"Mami kin gani ko? Ni nasan Abba har abada ba zai mayar da ke Wakinki ba. Kin ma yi kuskuren tunkararsu. Mami komai fa dake faruwa ke ce silarsa. Kin jefa rayukanmu cikin masifu iri-iri tsabar don zuciya irin naki. Ni yanzu ki dube ni Mami da abin da nake ?arewa koyaushe, cimar da nake ci kawai lokutan da nake kwadayinsa shi ya zame min cin safe da dare. Arzi?in da Yakubu ke ta?ama da shi babu, ya saki ?ar snow ni kuma da uwar gidansa ya rantse ko za'a kashe shi ba zai sake mu ba. Koda dai ni ke son sakin saboda cin mutunci da wulakanci da gorin da yake yimin tun faruwar lamarinki. Abba ya mara masa baya akan idan har na kashe aurena to ba dai gidansa ba. Shi kuwa ya hau ya zauna, Wan abin da zan samu na kudi daga yayyuna, haka zai zo ya amshe su ta hanyar yimin dadin baki, wataran har da duka. Mami kina kallo dai ya ganki a gidannan amma kasancewar girma ya fadi bai ko kalle ki ba ballantana akai ga gaisuwa. Kiyi hakuri Mami, amma bayan fitarki ya cemin bai yarda ba kuma bai amince da zamanki a gidansa ba. Akan haka har faWa muka yi ya kira Abba ya sanar da shi, shima kuma Abba ya ce koda wasa kika zauna sai ya Wauki mataki a kaina. Ni dai na shiga uku wallahi, rayuwar duka babu dadi a tsawon shekarun aurena da Yakubu, ga haihuwa da nake so amma an tabbatarmin ba zan haihu ba saboda mahaifar ta samu matsala. Mami ke ce silar gurSacewar tarbiyyarmu. Ke kika ja mana."

Sai ta fashe da kuka sosai fiye da na baya, Mamin itama kukan ta soma iyakar ?arfinta, tausayin kanta da na Wiyarta na ?ara mamayarta.

"Aa Futuha, ni ban cutar da ku ba asalima na fi kaunar na ga rayuwarku ta inganta. Akwai uwar da ke son ganin ta gurSatar da rayuwar ?a?anta? Nayi komai don na samar da dauwamammen farin ciki a duniyarku sai dai abin ya juye. Kuyi hakuri zan gyara komai."

Futuha ta dago rinannun idanunta da suka ci kuka, fuskarnan har ta yi jazur.

"Me za ki yi ki gyara Mami? Wani mummunar za ki ?ara aikatawa da sunan gyara?"

Ajiyar zuciya Mamin ta sauke tana jan hanci.

"Babu wanda zan ?ara kashewa, amma ai ina da ha??i akan Wana Mubarak? Zan kirashi, shi zai nema min muhallin zama ba zan kashe maki aure ba. Ita kuwa Tasleem duk r??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????adda ta ?ara kiranki da wata Soyayyar lambar ki yi mata albishir da fitowata. Ki kuma ro?e ta akan ta dawo gida ta bar duk inda take ta zo Maminta ta tuba."

Futuha ta ?ara fashewa da kuka tunowa da ta yi da Tasleem, tun bayan kamun da aka yiwa Mami, cikinta ya bayyana aka soma maganganu wanda ya yi silar shigarta duniya bayan ta ajiyewa wasi?ar neman gafarar Abbansu.

Haka Mami ta tashi babu kuzari da tunanin inda za ta je kwana, Futuha ta tsaida ta ta kira layin Yassar, nan ta ro?i ya aiko kudi a ba Mamin tasu, Yassar da Dawud wadanda ke aiki a kamfanin Alhajin Fadeel wanda yau shekaru hudu kenan da buWe shi a garin Abuja, a can suke zaune tare da matansu, babu musu ya ce ta turo akawun lambarta. Amma koda ta zo masa da batun Mamin ta zo gidana ya nuna shi sam bai aminta da hakan ba. Gwara dai a san yanda za'a yi kawai, amma ba zai amince ta Sata rayuwar gidansa ba. Hakanan Dawud shima da aka kira, yace dai zai taimaka amma babu batun masaukinta a gidansa. A cewarsa Matarsa ba za ta ji dadi ba. Duka a loudspeaker na wayar Futuha da ta bude, komai yana shiga kunnuwan Mamin. Na karshe kuwa da aka kira Mubarak ne, ya Waga bayan sun gaisa Futuha ke ba shi labarin Mami da halin da take ciki na neman taimako.

"Zan aiko da abin da ya samu, kin san Hafsatu ta kusa haihuwa akwai hidima a gabana. Daga baya za ga abin da zan iya yi. Ki turo account number."

"Toh, ga Mamin za ku gaisa."

"No please, meeting zan shiga sauri nake. Later."

Daga haka ya katse wayar.

Mami ta ?ara sautin kukanta sosai, Futuha dai sai kallonta take tana Wan matsar kwalla.

"Yau ni dai Maryam ni ke ganin wannan ranar? Na ci kashin yarannan na ci fitsarinsu amma ni suke yiwa wannan tofin Allah tsinen? Ni ni Maryam yau ni ce yarana ke gudun raSa?"

Futuha dai lallashinta ta cigaba da yi da ban baki, ba jimawa sai ga alert ya shigo daga Yassar, dubu goma ce kacal ya turo sai ko can Dawud ya turo dubu biyar. Futuha ta zari hijabi suka fita tare da Mamin, P.O.S suka karasa ta zaro mata kudaden ta ba ta sannan ta fidda layin da ba ta amfani da shi sosai ta ba Mamin akan ta nemi ko ?aramar waya ta sanya sai ta yi kiranta. Mami ta dube ta da hawaye.

"Yanzu shikenan kema rabuwa zan yi da ke Futuha?"

Futuha ta girgiza kai wannan karon ta ma kasa tsaida ruwan hawayenta sai kwaranya kawai suke.

"Aa Mami, ai muna tare. Kiyi hakuri, yanzu bani da wani abu da ya fiyemin face na cigaba da rayuwata a Wakin mijina, idan ma na fito ba wani dadi zan ji a gidan Abba ba duk da Anti Maijidda tana kawomin ziyara wasu lokutan har ta yimin alkhairai bani da matsala da ita, amma Abba ba zai lamunta da kashe aurena ba. Har jari fa ya bani amma Yakubu ya karSe ya cinye. Duk sana'ar da zan gwada a aljihunsa yake tafiya. Kiyi hakuri duk inda kike zan dinga zuwa, ni da ace za ki bi shawarara da kin yi kudin mota kin tafi wajen su Anna."

Ta girgiza kai da sauri.

"Allah ya sauwake, idan na koma kauyenmu a haka abin kunya ne garemu baki daya. Ni kuma na fi karfin wani Wan kauye ya wulakanta ni. Kar ki damu zan yi kudi kwanan nan. Komai zai warware. Ba zan iya rayuwar kauye ba. Ni nasan me na baro don haka ba zai yiwu na koma cikinsa ba."

Futuha ta kasa magana kawai sai kallon Mamin, ita wato duk wannan abu bai sa ta shiga taitayinta ba? Hakanan suka yi sallama Mamin ta kaWa.

Futuha ta kasa hakuri sai da ta kira Abba ta sanar da shi duk abinda su Mubarak suka yi tana kuka. Abin bai masa dadi ba, ai duk yanda ya kai ga son kada su raSi mahaifiyarsu biyayya gareta wajibi ne a kansu musamman ma su maza. Sai da ya kira su a waya daya bayan daya ya bude musu wuta sosai karshe ya rufe da nasiha. Wannan ta sa suka ba shi hakuri suka kuma ci alwashin kiran Futuha don ta kara hada su da Mamin amma fushi da zafin zuciya ya hana ta Wagawa.

***
Idanunta bai raina fata ba sai da ta kasa samun gidan da take bu?ata, a iyaka lissafinta ta fi kaunar gida mai Wakuna koda falle biyu ne sai falo da kuma kicin. Ta fi kaunar kuma ya kasance muhalli ne mai kyau mai tayil ba wai suminti ba. Sai dai ta kasa samun koda mai simintin ne da kudaden hannunta balle ta shiga, ga yamma ta yi. Hankalinta ya yi mugun tashi, duk inda ta san za ta samu alfarma wurin ?awayenta ?an ?arya da fafa duk ba ta samu ba. Gidaje har uku ta je amma guda daya kawai ta samu ganawa da matar gidan kuma surukar Hajiya Lubna, itama a wulakance ta tarbe ta. Ko gama sauraronta ba ta yi ba ta ce ta tashi ita kam sisinta ba zai shiga tsakaninta da ita ba. Da ace dai za ta aminta da yi musu aikace-aikacen gida ne sai a dinga biyanta albashi. Wannan cin zarafin da Hajiya Zulaihat ta yi mata ya mugun ?ona ranta, ita dai Maryam ita ake nufi ta yi wanke-wanke? Ai ko giwa ta mutu, gawarta ta fi karfin kiyashi ya ja.

Da wannan ba?in cikin ta fito fuuu ta yi titi ba a hayyaci ba. Ta rasa ina za ta shiga, sai kawai ta dora hannu a kai ta kurma ihun kuka ta durkushe tana yi ba ?a??autawa har mutanen da suka shiga sallar Magriba suka fito aka taru ana bin ta da kallon mahaukaciya. ?arshe ta yanke komawa gidan Futuha don ba za ta yarda ta kwana a titi ba.

***
Zaune take da tulelan cikinta haihuwa yau ko gobe tana kallon Age Is Just A Number a tashar ZeeWorld, hankalinta kwance take cin tuffa daidai sadda ta ji hayaniyar yaran a kunnenta. Ta dube su, girgiza kai ta yi, wato Fadeel ba ya jin nauyin kowa a kan yaransa, akan ya bar su su cika sati gidan Abba ya gwammace ya tattaro su ya maido mata su ko kwanaki uku ba su kai ga cikawa ba. Bakinta ta kama kawai gami da hangamewa, sai ta ji ita ke kunyar su Abban ma ba shi ba. Suka taho a guje suka rungume ta su na kiranta da Ummee. Gogan ya shigo janye da akwatin kayansu. Wayarta ta yi ?ara daidai lokacin, Anti Maijidda ce. Ta san zancen bai wuce na su Twins ba don haka ta daga ba ta ko jira sun gaisa ba ta hau yi mata kashedi akan kar ta ?ara aiko mata twins hutu tunda su kam babansu bai bari. Gwara ta ji da su Afnan. Hakuri ta dinga ba ta ita kuwa jin muryar yaran yasa ta katse wai ashe babansu ya shigo. Humaira ta ajiye wayar gami da kallon Fadeel da ke faman bude musu robar ice cream.

"Habeebee, haka muka yi da kai? Fisabilillah ka kyauta da ka kawomin su? Kai ko tausayina ma ba ka ji a yanayin nan?"

TaSe baki ya yi.

"Ni gaida Abba na shiga yi yara suka ma?ale za su biyo ni, toh meye nawa a ciki? Kuma su da ga Nannynsu a gida kuma ga ni nan me zai dameki? Kedai Allah ya sauke ki lafiya."

Ta sauke ajiyar zuciya kawai da firta ai shikenan daga haka ba ta ce komai ba ta kwashi akwatinan yaran ta nufi dakinsu da shi. Sai da suka ci abinci da Daddynnasu sannan ta titsa ?eyarsu wajen Yadikko, dattijuwar da ke kula da su, ita ta yi musu wanka suka sauya kaya suka bi lafiyar gado.

Ita ko Sangaren mijinta ta shiga ta taimaka masa wajen rage suturar dake jikinsa domin shiga wanka. Ya tallafo ta gaba Waya har cikin dake jikinta yana shinshina ?amshin turarukan da ba ta rabo da su har sun zame mata ma jiki.

"Ke kam bakya tsufa, kullum wata ?ar budurwa kike koma min."

Ta Wan ja karan hancinsa da ?arfi har ya Wan yi ?aramin ?ara.

"Ko? Ka ?ara kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login