Showing 42001 words to 45000 words out of 189325 words

Chapter 15 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

230

ya Wuri ruwa, yanzu wa za ta faWawa wannan abu? Muddin Mami ta ji ranta zai Saci don dama ba da son ranta Futuhar ke Wora bidiyo a Tiktok ba. Anna kuwa, ba lallai shawararta ya yi wani tasiri ba. Don haka kawai sai ta yi Wakin samarin yayyunta. Kwankwasawa take iya karfinta, babu kowa sai Dawud dake baccin rana. Ya taso a firgice, har zai soma masifa amman ganin yanayinta sai ya fasa.

"Meyafaru?" Ya tambaya a ruWe. Ta bude wayar da tuni ta shige lock, mi?amasa ta yi. Ya kalla tun farko har karshe, ya dafe kai yana mai runtse idanu.

"Kinga irinta ko! Kin ga abinda nake faWamaki. Na faWamaki matan nan na Tiktok muddin suka ga kina musu shiga hanci da kudundune zasu sanyoki a gaba. Ballantana ma ganin kin kama hanyar shahara. Sa'a ?ar snow! Yarinyar ba ta da mutunci ko kadan, matar da ke ikrari a fili ita karuwa ce kuma ba ta ga ranar da za ta rabu da karuwanci ba sannan ta shirya tone-tonen yan barikin tiktok."

Futuha ta jinjina kai har sannan tana sheshsheka, ta san da wannan, haka Win ne ma ya sanya ta shiga ruWu da tashin hankali, waWanda za su yarda da zancen sun fi waWanda ba za su Wauka ba yawa. Ko ba komai jita-jita ya fi saurin yaWuwa koda kuwa akan ?arya ne.

"Ya zan yi Dawud? Na shiga ruWani, me zan ce jama'a su yarda sharri ne aka yimin?"

Dawud ya yi shiru, shima dai kansa ya yi masifar ?ullewa. Ya rasa me zai ce, daga? kuma irin yanda ake zuba ruwan comment na zagi da ma? masu rubuta ai za ta aikata lamarin ya samu karSuwa kenan.

Kafin su ce komai sai ga wayar Aina'u ya shigo, Dawud ya Waga.

"Ke Futuha! Kinga wani? Wan iskan bidiyo da Snow ta yi a kanki? Wallahi na shiga rudani, mene gaskiyar abin da ta ce game da ke?"

Hankalinta ya kara tashi.

"Aina'u ke ce mafi kusa da ni a ?awayena, yanzu kin yarda da abin da aka ce a kaina? Idan kika yarda waye ba zai ?i yarda ba? Wallahi Allah karya take yimin, ni Futuha ban taSa zina ba a rayuwata. Ke kanki kin sani."

"To ai kuwa wallahi kinji na rantse sai kin yi dagaske za ki wanke kanki a idanun duniya musamman ?an Tiktok, yanzu na faWamaki a whatsapp na ci karo da bidiyon an turo group dinmu na makaranta."

Zaro ido Futuha ta yi, ji take komai tamkar a mafarki, ta kasa amsawa. Ga Aina'u a layi tana faman hello hello, ga kuma sunan Babban Yaya (Wato Mubarak) yana yawo a saman screen din, shaidar kiransa ya shigo. Dawud zai katse na Aina'u ya Waga? cikin sauri Futuha ta warce wayar ta kasheta gaba Waya. Cikinta ya murWa ba ta tsaya ba shi amsa ba ta ruga Wakinsu. Ta tsallake Mami wacce fitowarta kenan daga bangaren Anna su na tattaunawa akan auren Tasleem da wadanda ya dace su gayyata cikin yan uwansu na Agadez. Mami ta bi ta da kallon mamaki da tunanin ko lafiya, wayarta ta yi ?ara, ganin Mubarak yasa ta Waga.

"Mami, kina sane da abin da yarinyar can ta aikata ko?"

Cikin rashin fahimta da tsananin ruWewa ta ce.

"Wa kake nufi? Meyafaru wai?"

Nan ya ba ta labarin ire-iren raye-raye da Futuha ke Worawa a Tiktok, ya kuma cewa Mamin ta duba whatsapp zai aikomata da wani bidiyo ta gani. Hannayen Mami har rawa suke yi, ta hau online bayan ta kunna data, sa?onni suka shiga faWowa har na Hajiya Lubna wacce itama bidiyo ta aikomata. Sam hankalinta ya yi gaba akan sa?on Mubarak, ta buWe ta soma kallon irin ruwan rashin mutuncin da wata wai Sa'a ?ar Snow ta saukewa Futuha, ga hoton Futuhar nan daga ?asa. Mami tuni hawaye sun wanke fuskarta, ban da innalillahi ba abinda take furtawa, ya yi daidai da shigowar Dawud falon, ganin yanayin Mamin sai ya tabbatar abin da yake gudu ya afku, wato dai Mubarak ya sanar da Mamin komai. Ya kuma san halinsa, maganar ba iyakar Mami za ta tsaya ba, sai ya dangana da Abbansu.

Ganin tsayuwa na neman gagarar Mamin sai ta zauna a hannun kujera mafi kusa da inda take tsaye. Dawud ya karasa da sauri.

"Mami, yi a hankali."

Ta girgiza kai, ina batun hankali anan bayan Wiyarta ta jawomusu abin kunya abin kuma magana. Kamar kuma wacce aka tsikara ta mike da sauri ta nufi hanyar dakin su Futuha sam hankalinta ba ya tare da ita. Ganin haka Dawud ya mara mata baya, fadi yake "Mami wallahi sharrin ?an Tiktok ta hadu da shi, ke kin sani diyarki ba za ta aikata maki abin kunya ba. Don Allah Mami ki saurare ni, nasan wace wannan Sa'ar, ba ta da mutunci na ?arshe."

Inaa! Ba ta san ma yana yi ba, shigarta Wakin ya yi daidai da fitowar Futuha daga banWaki, har a lokacin sheshshe?a kawai ta ke yi. Humaira tuni ta tashi tana zaune gefen gado ta yi shiru, ita dai ta san babu lafiya. Ba ta taSa ganin Futuha na irin wannan kukan ba kamar na wacce aka yiwa mutuwa. Shigowar Mamin ya sa ta maida hankali gareta, ba ta yi wata-wata ba ta hau dukan Futuha tana kuka tana fadin.

"Shegiya marar tarbiyya! Wato ke ga yar iska ashe raye-rayen da na nunamaki bana so shi ne kika cigaba da yi har ya jawomaki kalmar karuwa?!"

Mami bugu take ita kuwa Futuha tana ihun kuka. Humaira da Dawud hakuri kawai suke ba Mami, su kansu hankalinsu ba a nutse ba. Babu kamar ita Humairar da ba ta san hawa da sauka ba. Mami don kanta ta ture Futuha ta juya, har za ta fice ta dawo ta nuna ta da yatsa.

"Na ba ki mintuna uku ki gaggauta goge account dinki kaf na social media da kike raye-rayen banza, wallahi kika bar ko guda daya ban yafemaki ba. Shashasha kawai!"

Tana kai wa nan ta fice daga dakin har tana bangazar Dawud. Jikin Humaira a sanyaye ta kalli Dawud, kamar jira yake kuwa ya watsa mata banzan kallo.

"Algunguma, ficemin daga daki za mu yi magana da yar uwata."

Kamar ta ce mishi ai Abba ya hana su shigowa dakin sai dai ta hadiye ta fice sum-sum zuwa falon da babu kowa ta zauna jugum. Yau ba ta je gidan Anti Laila ba sakamakon rasuwar da aka yiwa Anti Lailar a can dangin mijinta. Tana nan zaune ta ji muryar Abba a bangarensa yana tashi har zuwa cikin falon, faWa yake kamar zai ari baki. Mamaki ya kama ta, Abban bai fita kasuwa ba ko kuwa dawowa ya yi? Yanzun tare suke tafiya da su Yassar har Dawud wanda shi yau din bai jw ba sanadin ciwon kai da ya addabe shi Abban ya ce ya zauna, ya ce musu sam ba ya son zaman banza.

Humaira ta mike tsaye kirjinta na bugawa da sauri. Ta dai tsinkayi Abban na cewa "Cire ta zan yi daga makarantar! Itama ta fiddo miji na aura mata ko kuma na aurar da ita ga koma wane ne don wallahi ni dai Isuhu ba za ta yi sanadin zubewar mutuncina ba a garinnan!'

Gaba daya jikin Humaira ya hau rawa, ko ba a faWa ba ta sani akan Futuha ake tashin hankalin nan. To me ta aikata mai muni har haka da maganar ta yi zafi? Tana nan tsaye Yassar ya shigo falon bai ko kalle ta ba ya yi hanyar dakinsu, shi ma Dawud na ciki. Ba ta motsa ba kuma sai ga yan makaranta sun dawo. Hankalinta ya dan kwanta ganin Raihana da Ummita. Ta karasa da sauri.

"Ku gidannan fa ba lafiya. Kin sani ne?"

Ta jefawa Raihana tambaya ganin yanda hawaye suka wanke fuskarta. Jikinta ya kara yin la'asar. Raihanar ce ta ba ta labarin abin da aka yiwa Futuhar, dafe kai Humaira ta yi gami da ambaton sunan Allah.

"Tir?ashi!" Abin da kawai ta ce a baki kenan. Dama tun sadda Futuha ta soma yayin Wora bidiyo Tiktok ta so ace ta mata magana amma ta sani ba za ta ji komai ba. Watakila ma ta kira ta da mai hassada kamar yanda ta kira Tasleem sadda ta yi yun?urin hana ta Worawa. To na kusa ma an mishi wannan ikrarin ina kuma ga ita da suke mata kallon bare a cikinsu?

Yinin ranar dai gidan ya kasance babu dadi, Abba ya yiwa Futuha kaca-kaca ya kuma rantse ya dakatar da karatunta har sai idan ta samu miji ta yi aure. Ya ba ta lokaci kankani akan ta fitar da daya cikin masoyanta a haWa bikin da na yar uwarta. Idan kuwa ta ?i shi da kansa zai nema mata abokin rayuwa.

Tasleem haka ita ma ta dawo daga asibiti ta iske wannan abin wanda tuni tana da labarin komai. Futuha ranar kamar an aikomata sa?on mutuwa haka ta wuni babu ci babu sha, Mami ta ce a kyale ta. Ganin ba ta da mafita ya sanya ta komawa Sangaren Anna inda anan ne ta samu sassauci domin Anna goyamata baya ta yi, ta ce Mamin su yi mata uzurin kuruciya. Ta dai lallaSa ta kwantar mata da hankali.

***
A sati biyun da Abba ya Wibarwa Futuha don ta fiddo mijin aure, a wannan satin kafin su cika gaba daya ta rame ta zama mai wani irin sanyi, yan uwan Abba babu wanda ya goyi bayanta balle ya lallaSa mata shi. Ganin haka Mami ta tashi takanas ta je ga aminiyarta Hajiya Lubna ko za ta amince Khalil Wanta ya auri Futuha
su rufawa junansu asiri. Amma ina, Hajiya Lubna ta nunamata ita gogaggiyar yar boko ce ta biyo mata ta kissa ta nunamata ta amince, amma bayan kwana biyu ta kira ta tace Baban Khalil ya ce shi kam ya riga ya gama magana da abokinsa akan ?arsa da yake son Khalil din ya aura. Ta kwantar da Mamin hankali akan Futuha fa kyakkyawa ce son kowa ?in wanda ya rasa, ta kwantar da hankalinta komai zai tafi daidai.

Aikuwa cikin ikon Allah dai ga wani matashin Wan chanji Alhaji Yakubu ya zo takanas ya samu Abba akan yana son aurenta. Mutumin ya jima yana ganin fuskar Futuha a Tiktok, kasancewarsa Wan duniya, yana son mace mai irin wayewarta ya kuma jima yana bibiyarta akan ta amince ya aure ta, tana wula?atanshi. Tashi guda da ya ga abin da Sa'a ta yi mata ya ga dama ta samu da zai yi wuf da ita. Yana da mata Waya da yara uku, ya kuma tabbatarwa Abba koda Futuha ba ta son zama da matansa shi Win zai nema mata wani muhallin daban cikin waWanda ya mallaka. Abba ya yaba da salon nutsuwa da ladabin da ya zo mishi da ita don haka ya ce ya je nan da kwanaki uku ya turo iyayensa. Wannan lamarin ya yiwa Yakubu daWi sosai. Ya yi ta godiya.

Bayan tafiyarsa Abba ya yiwa Mami zancen, ta yi murna da hakan a fili musamman ganin yana da rufin asiri. Abba ya san shi don Alhaji Yakubu ba Soyayye ba ne, yaro ne abokin tafiyar manya. Yana da kuWi sosai sannan akwai shi da kyauta. Ko kusa abin hannunsa bai rufe mishi idanu ba. Ya samu kyakkyawar shaida wajen jama'a da suka san shi a waje, a halayyarsa kuwa na baWini wannan daga shi sai Mahaliccinsa sai kuwa wadanda ya buWamusu suka san??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i.

Futuha fashewa ta yi da kuka sadda Abba ya yi mata zancen.

"Wallahi Abba bana sonsa, mutumin yana da son mata kuma..."

Wurgin da Abba ya kai mata da carbin dake gefensa ya sanya ta saurin yin gum da bakinta.

"Rufemin baki nace! Ke har kina da fuskar da za'a gani a aureki da ita, ban da ma shi so ba ruwansa, mutum mai mutunci da ?ima irin Yakubu mai zai yi da ?ar rawa? Macen da ba ta killace jikinta ba ta sake shi ko'ina yana yawo ana kallonta? Toh bari ki ji, muddin ni dai mahaifinki ina raye, ba ki da miji sai Yakubu. Na kuma ba shi damar turo magabatansa nan da kwanaki uku, karatu idan ya amince maki ki cigaba wannan shi ya ga zai iya, nidai ubanki ba da yawuna ba saboda ni yanzu tsoro kike ba ni, nema kike ki fi karfinmu. Wannan wayewar ta banza kuma da kika Waukarwa kanki, ki je can ki ?arata da ita, Allah ya shiryeki idan ke mai ganewa ce. Tashi ki fice ki ban wuri, saura ki je ki kai ?arata tun da ban isa da ke ba."


Yana nufin kai ?ara wurin surukarsa Anna kamar yanda ta yi a farko da ya yi batun auren har sai da Annar ta tako sashinsa da zummar lallaSashi ya janye. Cike kuma da ba ta girma ya ce ta yi hakuri amma ba zai zuba idanu tarbiyyar yaransa su lalace ba. Ganin ba ta taSa neman alfarma a wurinsa bai yi ba sai wannan ne ya sanya ta kama mutuncinta ta yi shiru da baki.

***
Su Humaira na Waki sai ganinta suka yi ta shigo tana aikin da ta saba kullum, wato aikin kuka. Humaira kukan yanzu kam ko a jikinta, ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, ta lura hatta Tasleem itama abin ya bar sosa ranta, kowa ya fice a harkarta ya gaji da rarrashi. Tasleem dai waya take amsawa da Hamza, ganin ihun kukan Futuha ya cika dakin kawai sai ta ja guntun tsaki ta fice. Su din ma hirarsu ta tsaya, kowa ya shiga danna waya, su kansu Abba ya ja musu kunne sosai ya kuma rantse duk wacce a cikinsu ta yi irin gangancin Futuha ba zai duba komai ba zai aurar da su. Wannan ya sa bakinsu ya mutu murus.

Humaira ta bude sa?on da ya faWo wayarta a lokacin. Ta sani, shi kadai ne zai yi mata sa?o don haka ta buWe.

_"Ko kinsan mai hakuri ba ya taSa karo da rashin nasara a rayuwarsa? Ki sani ni Win masoyi ne a gareki, ba kuma hakan zai sauya komai ba. Ma'ana, koda ace zamu shekara kina wahalar da zuciyata, Humaira ki sani, Fadeel bai fara sonki domin ya daina ba. Muddin rai ba zan fasa neman soyayyarki ba."_

Ta karanta kusan sau uku, ta rasa dalilin da yasa ba zai taSa turo kata sa?o ta karanta sau Waya ba, kuma ko kadan ba ta iya goge sa?onninsa. Abin da yake ba ta mamaki shi ne, ta ga yana hawa whatapp amma ko sau daya bai taSa yunkurin yi mata magana ta can ba. Kira ma da ya ga ba ta Wagawa ya bari. Sai dai akwai lambar da take zargin ko shi ke kiranta da shi. Za a kira ta Waga amma ba za a ce komai ba sai dai ta yi ta sallama tana sababin an?i magana ?arshe kuma ta ji Wif an katse kiran. Wannan abu na ba ta mamaki, tana kuma zargin Fadeel ne. Ta yi shiru tana so ta hasaso dalilin wannan ?iyayya da ta ke yiwa Fadeel amma duk iyakar tunaninta ta kasa, karshe ta ja guntun tsaki. Ta bar shi akan kawai ita ba ta kaunar soyayya, ba ta kaunar kowace mu'amala da za ta haWata da namiji. Da wannan ta watsar da tunaninta.

***
BAYAN SATI UKU...

Garin aka tashi da shirye-shiryen shiga wata mai alfarma wato Ramadan, wanda ake kyautata zaton ganin wata a ranar ko washegari hakan yasa Mami suka yi dogon list na cefane ita da Humaira. Mamin ta dube ta bayan sun kammala tana murmushi.

"Wannan azumin a daWinmu, girkinki zamu ci. Kin ga kina yi idan kin shirya komai sai ki yi hoto, Raihana ta buWemaki account a instagram kina Worawa da sunan tallah, idan Allah ya taimaka zuwa sallah sai mu samu odar girkin sallah ko su samosa da sauransu. Da kaWan-kaWan kuma ki ji an soma neman ki yi na biki. Ina mai tabbatar maki da wannan iya girkin naki za ki samu alheri mai yawa da zai yi maki amfani har na kusa da ke."

Humaira cike da jin dadi ta hau murmushinta mai bayyana wushiryarta ya kara fiddo da usulin kyanta. Ta ma kasa magana don murna. Mami ta yi dariya.

"Allah ya kyauta, wannan dariyar duk ta murna ce? Tashi dai maza ki je kar yamma ta kawo kai. Kinga siyayyar da yawa."

"Toh Mami." Ta mike ta gyara zaman mayafin doguwar abayar dake jikinta ruwan madara mai dark brown din mayafi. ?afarta sanye da safe ba ka ganin komai sai tafin hannunta sai kuwa fuskarta da ta shafa hoda ta zizira kwalli. Ta yi kyau tsaf duk kuwa da cewa ba kwalliya ta yi ba. Irin matan nan ne wadanda ko ba kwalliya su na kyau. Har ta fice a Wakin Mamin na bin ta da kallo tana murmushin da ta ba kanta sanin ma'anarsa.

Ta yi tafiya daga gidan zuwa titi na Wan mintuna sannan ta fito babban titi. Garin akwai rana sosai duk kuwa da cewar an yi sallar azahar amma hakan bai sa ya Wan yi sanyi ba. Dakyar ta samu abin hawa ta shiga. Sun yi tafiya mai Wan tazara sun tsaya a daidai junction din sabon titi wayarta ta Wau ?ara. Ta ji gabanta ya fadi don tsoro, Ummita ta ce mata ana satar waya a Wan sahu wannan yasa kodayaushe idan za ta fita ta ke sanya ta a vibration amma yau sauri ya mantar da ita. Ta Wan kalli mata biyun da ke gefenta sai ta ga ba su yi mata kama da Sarayi ba don haka ta ciro ta da sauri, ganin sabuwar lamba ya sa ta Wagawa da sallama. Madadin ta ji shiru an yi kamar yanda aka saba yi mata, sai ta ji wannan karon an amsa. Duk da ta Wau muryar hakan bai sa ta tambayar "Wa ke magana." ba.

"Wallahi ina sonki."
Ya furta cike da kasala, abinda bai taSa faruwa ne ba gareta ta afku a sannan. Ji ta yi tsikar jikinta ya tashi, ta ji lebbanta sun mata nauyi ta kasa buWe baki balle ta rufe shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login