Showing 24001 words to 27000 words out of 189325 words

Chapter 9 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

198

ta dake ba ta ko kalle ta ba ta ?arasa ciki, dama mayafin abayarta za ta Wauka zasu je Shoprite ita da Ummita, Mami ta aike su.

Raihana kuwa ganin Humaira ya sa ta shan jinin jikinta. Ta kasa magana kwakkwara sai um da humm ina jinka. Guntun tsaki Humairar ta ja ta fice, ta sha alwashin ko ina ne a goben sai ta bi bayanta ta kuma kama Wan iskan dumu-dumu ta ci uwashi.

? A falon ta haWu da Ummita, har suka soma tafiya ta ga dai hira suke amma ita ke kiWa da rawarta hakan yasa ta dube ta.

"Wai ke lafiyarki kin wani haWe rai kamar wacce aka aikowa sa?on mutuwa? Koda dai Sata bakina nake dama ai halinki ne. Amma naga ai yanzun ba kiciSus kika yi da ma?iyinki naki ba ko?"
Tana nufin saurayi, Humaira ta ja tsaki ta girgiza kai.

"Ba komai fa."

TaSe baki Ummita ta yi ba ta ?ara magana ba sanin hali. Sai kuma can don kanta ta saki fuska suka hau hira. Kayan ma?ulashe irin su Jam, Ketchup, Mayonnaise da sauransu, shi Mami ta bada su siyo na Yaya Mubarak. Sun kammala suna dab da ficewa suka tsinkayi sallama a gefensu. Lokaci guda suka juya ga mai shi, wani matashin saurayi ne gajere mai ?iba. Irin ?ibar da ba ta da muni. Daga yanayin yadda ya saki fuska za ka fahimci mutum ne mai fara'a. Humaira wacce kallo Waya ta mishi ta dauke kai gami da ci gaba da tafiya, ganin haka itama Ummita ta mara mata baya, ya kuma bin bayansu da sauri ya sha gaban Humaira.

"Ranki ya dade, kiyi hakuri na tsayar da ke. Nima kuma na san darajarki da ?ima ta zarce a tsayar da ke a hanya a..."

"Kai Malam saurara don Allah! Ni nan da ka ke gani da mijina a hannu don haka kama kanka. Muje."

Ta fisgi hannun Ummita ta bi gefe suka fice a nan. Hakan da ta yi ba karamin Satawa Ummita rai ya yi ba, ba yau farau ba, idan da sabo ya ci ace ta saba da ganin irin cin kashin da yar uwarta ke yiwa samari. Ita har mamaki take yadda gaba daya Humairar ke sauyawa kamar ba ta taSa zama haWa hanya? da wani abu wai shi mutunci ba. Ta fara gas?ata zancen Raihana da ta ce jinnu ne da ita. Kamar kuma ba ita ba, sai ga shi a hanya ta saki rai sun ci gaba da hirarsu lafiya lau.

***
? Washegari tun safe take dakon Raihana tana jira ta ga sadda za ta fita ta mara mata baya. Aikuwa wuraren karfe biyu tana zaune a falon da littafi a hannunta na koyon rubutun hausa tana Wan duba inda muhsin ya biyamata, Mami kuwa na gefe tana yankewa Muhsin farce sai ga Raihanar,? ta tambayi Mamin zuwa gidan ?awarta Munirat. Farko Mamin ta hana sai can kuma da ta dage da naci ta samu Mamin ta aminta. Humaira ba ta ko Waga kai ba balle ta yi yunkurin mi?ewa, har sai da Mami ta soma barin falon, tana nan zaune ba ta ko motsa ba har Raihana ta fito cikin shigar fita, ta ci wani arnen kwalliya ta sanya riga da siket da ya yi matu?ar kama ta sai ta dora afterdress a sama wanda da shi da babu duk Waya. Tana fita Humaira ta yi wuf ta mi?e ta zari hijabinta dake hannun kujera. Tuni ta yi shirinta dama ta sa kuWi a bayan gidan wayarta. Bayan Raihana ta bi, sai da ta kai ?arshen layin ta nemi can jikin wata? bishiya ta Soye fuskarta cikin facemask. Haka ta shiga Wan sahu ta bi bayanta har gidan su Munirat. Kamar yanda ta zata kuwa hakan ne, wani saurayi matashi ne tsaye jikin wata mota suna hira da wata budurwa. Raihana na karasawa ta cafke da budurwar da bayan ta matso ta gane Munirat ce saboda ta taSa zuwa can gidannasu ba sau Waya ba ba biyu ba.
? ? Can kuma sai Munirat ta shige gida ita kuwa? saurayin ya buWe mata gidan gaba ta shiga ya maida ?ofa ya rufe. Ba?ar mercedez ce mai ba?in tinted wanda duk iyaka hangen mutum bai isa ya ga na ciki ba.

Humaira ta ji ?irjinta na dukan tara-tara da wani irin sauri ta soma takawa ta nufi wajen kai ka ce kafin ta karasa abin da take tsoron afkuwarsa ya afku.

Da tsayuwarsu a wajen, da shigar budurwar motar, duka ya faru ne akan idanun Ibb da Fadeel wadanda ke tsaye a ?ofar gidan su Fadeel Win su na taSa hira. Ya rako Ibb ne zai wuce gida suka tsaya. Ganin shigar budurwar ya sa Ibb jan tsaki.

"Wallahi ina mamakin rayuwar ?an matan yanzu da ba su da kunya kuma ba su san mutuncin kansu ba. Yau da ?anwata ce daga ita har shi sai sun raina kansu."

Ya faWi ransa na wani irin ?una, Fadeel kuwa da zuciya ta kai mai wuya bai san sadda ya soma takawa ba da sassarfa hakan da ya yi ya sa Ibb bin bayansa da sauri ya dakatar da shi sanin hali.

"Aa Fadeel, please don't, ba ka san waye ba a.."

"Sai nasan waye? Idan ?anwartaka ce za ka zuba ido kana kallo rayuwarta ta Saci!"

Yana kai wa nan ya fisge hannunsa, sai dai kafin ya kai ga tafiya suka hangi Humaira wacce gadan gadan ta nufo motar a fusace. Zuciyar Humaira har wani tafarfasa ta ke yi, tana isa ta sa hannu ta ja murfin motar cikin sa'a kuwa ?ofar ta buWe. Raihana wacce yatsunta ke sar?e da na Musaddam gaba Waya ta kasa sukuni amma ?arfin soyayyarsa a ruhinta ya sa ta daurewa ranta, daidai sadda ya kai bakinsa ne da nufin sumbatar hannun aka wangale ?ofar hakan ya sa a firgice gaba Waya suka juya. Humaira ta fisgo Raihana, ba shiri ta fito har tana tuntsirawa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?. Ba ta yi wata wata ba ta Wauke ta da mari hagu da dama ga wasu zafafan hawaye da suka zubo saman fuskarta lokaci guda. Musaddam tuni ya fito ya zagayo wurinta, hannu ya Waga shi ga marar kunya zai ramawa Raihana marin, amma tuni Humaira ta ri?e hannunsa ta ba shi nasa rabon. Hannunta har rawa yake ta sa hannu ta fisge facemask din da ke rufe a hanci da bakinta.

Fadeel ya yi mata ?uri da idanu babu ko kyaftawa yana jin tamkar gangar jikinsa ne kawai tsaye a wurin, hannu ya sar?e a kirji yana so ya ga matakin da za ta Wauka. Humaira da ba ta san wainar da ake toyawa ba, gaba Waya ba ta tattare da nutsuwa hankalinta kacokam a tashe yake, yana kan Musaddam da take jin kamar ta sha?e shi. ?an firit da shi sai sirantaka, fari ne yayinda lebbansa suke ba?ake wuluk shaidar yana shan sigari. Hannunsa dafe da ?unci yake duban Humaira rai Sace ya ce.

"Ke! Ni kika mara?"

Bai yi aune ba ta kara wanke shi da mari.

"Yanzun ka daina tantama? Eh marinka nayi! Da kuma ace ni wata mai ikon ce, abin da ya fi mari shi zan maka. ?an iska marar tarbiyya! Ka yi amfani da son da ka ga yarinya na maka za ka cutar da ita saboda a gidanku ba a baka isassan tarbiyyar islama ba sai na bokon da bai amfaneka da komai ba. Idan har ba ka raba kanka da kanwata ba ina maka rantsuwa da Allah sai na yi maganinka ta yadda rayuwarka za ta ?are a kurkuku. Ke kuma..."

Ta juya gaba Waya ga Raihana wacce ke kuka ga dukkan ilahirin jikinta na rawa. Ba ta jin an taSa tozarta ta irin yau, a gaban saurayin da take yiwa son duniya? Lallai Humaira ba ta da kirki ko kaWan. Aljanun nata ma ?an iska ne na ?arshe da alama.

"Kin Wauka ba shi jikinki shi ne zai sa ya ga mutuncinki ya gane irin son da kike mishi har ta aureki? Toh kin yi kuskure, wallahi wallahi duk sadda kila bari wannan Wan akuyan ya kusanceki kin cuci rayuwarki har abada Raihana, za kuma ki yi kukan nadamar da babu mai share maki hawaye. A haka kuke kirana da ?ar kauye, wannan ita ce wayewar? Toh wannan birnin naku na jahilai ku ke ciki, idan za ki farka tun wuri ki farka idan kuwa ba haka ba wallahi muddin irin haka ta ?ara faruwa a kunnen Abba. Wuce kuma mu tafi tun ban kakkaryaki ba."

Raihana ta dubi Musaddam da ya haWe girar sama da ta kasa yana kallonta, ta maida duba ga Humaira wacce ke cika da batsewa kiris take jira ta fashe ga hawaye kace-kace a fuskarta. Ta lura ma jikin Humairar har rawa yake.

"Muddin kika bi umarninta ki sani daga yau babu ni babu ke Raihana, ala?armu ya zo karshe. Sannan ke kuma ba ki san waye ubana a ?asar nan ba ko? Zan nunamaki daga kaina ba za ki ?ara gangancin marin wani namijin ba."

"Musaddam Wan gidan Alhaji Jafar Nababa, right?"

Gaba daya har Humaira suka juya a inda suka tsinci muryar, Raihana ta yi mutuwar tsaye ganin Ibb Gusau mutumin da yar uwarta Futuha ke mahaukacin so tare da wani haWaWWen guy wanda ko fuskarsa da take a haWe ka kalla, sai ya burgeka. Kunyar da ta ji ne ya sa ta saurin amfani da gefen mayafinta ta rufe baki da hancinta gudun kar su gane ta. Humaira kuwa kallo Waya ta musu ta maida duba ga Musaddam Win fuskarta har lokacin a mugun Waure tana jiran ta ji amsar da zai ba da.

Musaddam ya kai duba ga me maganar, nan da nan ya ji gumi ya karyo masa, Malaminsa ne a jami'a da ya taSa yiwa gadara da matsayin Ubansa, shi kuwa ya nuna masa nashi Uban da matsayi sun kere na babansa. A sanadin wani rikicinsu sai da Musaddam din ya yi kwanaki uku a ofishin ?an sanda kafin a fiddo shi. Ya kasa cewa komai sai shafar ?eya, Ibb Gusau ya nuna shi da yatsa.

"Kai ba za ka taSa nutsuwa ba kenan a rayuwa ko? Ina mai gargadinka, wannan ya zama na ?arshe, ke kuma zan ba ki lambata duk sadda kika ?ara ganinsa da ?anwarki ki kirani kai tsaye nasan maganinsa. Ke kuma ki yiwa kanki faWa ?anmata, kar ki bari shaiWan ya kaWa maki ganga, irin su Musaddam ba su dace da ke ba. Daga ganin yanayin ?ar uwarki an san daga gidan mutunci ki ka fito saboda haka please be careful."

Raihana da ta yi mutuwar tsaye da mamakin mutumin da Futuha ta ce ba ya magana mai tsawo yana zuba zance ta gyada kai. Ga kuma wani iri da ta ji cewa wai zai ba Humaira lambarsa. Aikuwa Humaira ta mi?a mishi wayarta ya sanya mata lambar ya danna kira ta fito kan wayarsa sannan ya mi?a mata. Musaddam dai na tsaye kamar an kafe shi a wurin ya kasa motsi sai wani Waci da ya ke ji a ma?oshi ganin an dake shi an kuma hana shi kuka. Ya yi biyu babu kenan.

"Ko za su bi ka ka sauke su a gida?" Ya yi furucin da sassanyar murya. Sai a sannan ma hankalin Humairar ya kai gareshi karo na biyu don ta mance ma? da wanzuwarsa, ranta ya yi fari sol da taimakon da Ibb ya yi mata, ko ba komai ta ga tsoro fal a saman fuskar Musaddam wanda hakan ya fi komai faranta mata. Ganin irin kallon da Fadeel ke jifanta da shi ya sa ta kauda kai.

"Aa mun gode, zamu hau Wan sahu."

Fadeel kamar ya tanka sai kuma kawai ya basar bai ce uffan ba. Humaira ta kalle su, kalmar godiya ce kadai ta fito a bakinta kafin ta juya ta dubi Raihana.

"Muje." Ba musu kuwa Raihana ta bi umarninta, zuwa yanzu jikinta a mugun sanyaye yake. Ta dai tabbata Humaira ta fi ?arfinta. Ba kuma ta son tada wani borin su Ibb su ?ara ganin rashin kunyarta ?arara.

Bayan tafiyarsu, Ibb ya shiga yiwa Musaddam faWa mai haWeda nasiha, a karshe? ya ba shi damar tafiya. Sai da ya bar wurin sannan ya dafa kafaWar Fadeel yana murmushi.

"Toh ya aka yi?"

Fadeel ya zura hannuwansa cikin aljihu ya fiddo hannunsa na dama ri?e da waya ya mi?awa Ibb gami da Wan Wara? gira kaWan. Dariya Ibb ya yi ya girgiza kai.

"No, haba Malam, da wuri haka?"

Ya narkar da wuya.

"Please, ina rantsuwa da Allah ban taSa jin abin da na ji a kan wata ba sai ita."

Murmushi Ibb ya faWaWa.

"Alhaji da sannu dai Allah zai cika masa burikansa."

Guntun murmushi Fadeel ya yi.

"Ko? Kai kuma kana neman ka dakile faruwar hakan."

"Ah wane ni? Ba ni na sanya maka."

Ya karSi wayar Fadeel da tuni ya buWe, lambar Humaira ya sa a ciki sai kuma anan ya dafe goshi.

"Oh no, ka ga ko sunanta ba mu sani ba. Da me zan maka saving?"

Jin haka ya lumshe idanunsa yana hasko kyakkyawar fuskar Humaira wacce kumatunta har wani she?i suke saboda fushi, ya kuma lura ko ya ya ta buWe bakinta sai wushiyarta ta bayyana. A hankali ya ce.

"Mrs Fadeel."

"What?" Ibb da kunnuwansa kamar ba su ji ba ya tambaya. BuWe idanunsa ya yi ya dube shi dakyau.

"Yes, haka za ka yi saving lambar."

"Aa, ri?e ka yi da hannunka. Ka gani koda wani abun ya je ya zo, ba za ka kalle ni da shi ba."

"Babu abin da zai je ya zo face alheri. Da yardar Allah ba ta da miji sai Fadeel."

Ya ba wa Ibb amsa sa'ilin da ya sa hannu ya karSi wayar. Aikuwa da hakan ya yi saving sunan. Ibb dai mamaki ma yake, to kodai Wan lokacin da ya kwashe ba ya tattare da su ya sauya ne daga yadda ya san shi? Mutum da zancen aure ma ba ya so a yi mishi, daidai da hira idan ta budurwa ce aka Wauko cikin abokai yanzun gayyar za ta watse a wurinsa don tsam yake tashi ya bar musu wurin yana mitar ba shi da lokacin shirme.

"Sai goben?"

Maganar Fadeel ta katse mishi tunanin, ya sauke ajiyar zuciya.

"Allah ya kaimu. Amma ina mai ba ka shawarar kada ka zurfafa, duk abin da aka zurfafa ana shan wuya a cikinsa. Balle kuma irin wannan faWawar da ka yi lokaci guda."

Madadin ya amsa sai ya yi murmushi ya soma tafiya kawai, sanin da Ibb ya yi shikenan sallamar tasu ya sa shima ya nufi motarsa cike da fatan shi din ma Allah ya kawo mishi mace ta gari ya huta da gorin ?annensa sun yi aure sun bar shi da Mahaifiyarsa ke yawon mishi.

***
? A can gida kuwa, Mami tun da ta ji wai Humaira ta fita ba da saninta ba gaba daya ta ji ta kasa sukuni. Har ta kasa Soye Sacin ranta ta hau faWa a falon.

"Wannan wani sabon salo ne da har Humaira za ta sa ?afa ta fice a gidannan ba tare da neman iznina ba? Me take so na faWawa Abbanku idan ya tambaye ta?"

Tasleem da Futuha suka kalli juna suka taSe baki, yayinda Ummita da aka kira tuhumar ko ta san inda take, ta ke gefen kujera a zaune.

"Toh wai Mami, ba Humairar na da waya ba? A kira mana." FaWin Mubarak wanda ke shigowa falon daga masallaci, tun kafin fitarsa Mamin ke faWan fitar har dai ya dawo ba ta chanja zani ba. Ganinsa ne ya sanya su Tasleem nutsuwa. Mamin kuwa dubansa ta yi kafin ta kauda kai ta ja guntun tsaki na takaici.

"Kira na nawa kuma? Wayarta idan ba a kashe take ba to na fi tunanin babu network."

Ya kai duba ga Ummita.

"Ke ba ta faWamaki komai ba?"

Kafin Ummita ta amsa, Futuha ta yi caraf.

"Nima dai ita nake zargi don babu ta yadda za ta fita ace ba ta sanar mata ba. Bakinsu daya wallahi Yaya."

Kallon da ya watsa mata ya sa ba ta ?ara cewa uffan ba, Mami ta ja tsaki karo na ba adadi ta nufi Wakinta. Ganin haka Ummita ta mi?e ta yi nasu dakin da zummar gabatar da sallar La'asar, ita kanta tunanin da take yi bai wuce na inda Humaira ta je ba tare da neman iznin Mamin ba kamar koyaushe. Tsoronta kar Abba ya dawo ya tambaye ta ace ta fita alhalin ba ta da makaranta yau.

Aikuwa dai sai wuraren biyar da mintoci suka shigo gidan, ko ci kanki ba wanda ya cewa wani a cikinsu. Su Yassar dake zaune cikin abokansu a kofar gidan su ka bi su da kallo.

"Ga uwar girman kan gidannan ta dawo." FaWin wani abokin Yassar yana nuni da Humaira. Tun ranar da ya yi gangancin kulata da sunan so ta ci mishi mutunci yake jin tsanarta. Yassar tsaki ya ja.

"Kai ka so ai dama ka ga kalar nata girman kan, amma ga mata a gari kamar ?asa ka rasa ta kulawa sai wannan ?ar ?auyen nijar din?"

Sauran suka yi dariya. Shi kuwa Yassar mi?ewa ya yi ya bi bayansu ganin kamar Raihana na sharce hawaye, jikinsa har mazari yake don muddin ya kasance Humaira ce sila to ya rantse sai ya rama mata koda kuwa gaban Abba ne ba Mubarak ba.

***
A falon gidan suka iske su Futuha zaune, sallamar Humaira ta dakatar da Ummita daga shiga kicin, ta dawo cikin falon da sauri don ta ganewa idonta ko ita Win ce. Futuha da Yasmeen kuwa ido suka bi Raihama da shi ganin yadda fuskarta ta yi ja ga shatin yatsu kwance saman fuskarta.

"Ke, Raihat, me nake gani haka? Uban waye ya mareki?!" Tasleem ta faWi da buWaWWiyar murya tana kallon Humaira. Humaira da ita dinma kiris take jira ta dube ta dakyau.

"Ni ce nan, ko za ki rama mata ne?"

Aikuwa jin haka gaba daya Tasleem da Futuha suka yo kanta, ta kuwa shiga tarewa, duk wacce ta bugeta sai ta sa hannu ta rama da iyakar ?arfinta, duk da cewar su biyu ne a kanta, ta yi iyakar kokarinta amma itama ta ji jiki. Ummita ta hau kwala ihun kiran Mami, ga Yassar a gefe da ya ?i ya tsawatar don dama ya jima da haushin Humaira a ?o?on ransa. Raihana na ihun su kyaleta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login