Showing 30001 words to 33000 words out of 189325 words

Chapter 11 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

229

jama'a sakamakon daurin auren Fu'ad da aka yi a ranar, haka ya dinga kutsawa ransa duk a Sace har ya shige bangarensu, kai tsaye dakinsa ya nufa, tun daga falo ya cire hularsa ya yi jifa da ita, hakanan babbar rigarsa blue itama ya ajiye saman kujera kafin ya zauna ya shiga kokarin cire covershoe din da ke a ?afarsa da kuma safa. A duniya Fadeel ya tsani hayaniyar jama'a, wannan ta sa kansa har wani sarawa yake yi. Ya ja guntun tsaki gami da kwantar da kai jikin kujerar ya lumshe idanu. Zafi biyu ya haWe mishi, ga na rashin samun haWin kan yarinyar da yake jin ta a ?o?on rai, ga kuma wata irin yunwa da yake ji domin ko karin kumallo bai yi ba suka fice masallaci wurin daurin aure. Kowa kuma a dangin sai ya yo kansa da tsokana a wajen, su na fadin saura kai babban yaya. Wadanda ba su da labarin dawowarsa kuwa, sai a ranar suka gan shi. A hankali ya bude lumsassun idanunsa ya murza yatsunsa suka yi ?ara, har wani zogi suke yi mishi saboda gaisuwar da ya dinga yi da jama'a. Lokaci guda kuma ya mi?e ya nufi bandaki, hannun ya wanke tas da hand sanitizer sannan ya fito rike da karamin tawul yana gogewa. Ya yi daidai da shigowar Ibb tare da wani dan uwansu Imran.

Sallamarsu ya amsa ya koma mazauninsa har da kwanciya wannan karon. Kafin Ibb ya yi magana ya riga shi.

"Wai so ku ke na mutu? Yunwa fa nake ji."

Harararsa ya yi.

"Kai dai an yi Wan iska, muna can Alhaji ya sa mu nemoka ku gaisa da abokansa ashe kai nan ka yo? To sai ka tashi ka shirya muje idan ya so kafin mu dawo na yiwa Anti Amarya magana a kawo mana abinci."

Fadeel ya lumshe idanu.

"Kasan Allah ba zan iya fita ko'ina ba, ni fa ji nake idan ma na kara sa ?afa na fita cikin wannan ranar hanjin cikina za su fito waje."

Imran ya kwashe da dariya, shi kuwa Ibb kamar ya sha?o amininnasa haka yake ji. Yana niyyar magana kuma sai ga kiran Alhaji karo na uku. Ya Waga ya mishi bayani, dama bai tsammaci faWan Alhajin ba, cewa ya yi babu komai maza ya yi waya a kawomusu abinci. Da wannan suka yi sallama shi kuma a nan take ya yi kiran Anti Amarya ya sanar da ita.

A bangaren Anti Amarya wacce ta ci ado cikin arnen leshi ruwan toka da ya sha adon stones, ga ?unshi ta yi sai baza ?amshi take, jin wayar Ibb ya sa? da rawar jiki ta amsa ta ba Waya daga cikin hadiman gidan Larai umarnin haWawa Fadeel da abokansa abinci za ta turo a kai musu. Ta shiga falonta inda yan uwanta hudu ke zaune su na shan hira. Uku a cikinsu matan aure ne, Waya yayarta sai sauran gaba daya ?annenta. ?anwarta Murja dake kwance tana danna waya ta kai wa duka a ?afa.? Ba shiri ta mike zaune.

"Ke tashi maza ga dama ta samu, jeki wurin Larai na sa ta haWa abincin su Fadeel ki kai musu, kika sani ko Allah zai sa a dace ko cikin abokansa wani ma ya ce yana so?"

Jin haka babbar yayarta Saddika ta amshe.

"Ke wallahi hakane kam, tashi Murja, Allah ya Wora ki akan su."

Murja ta haWe girar sama da ?asa.

"Nikam wallahi Fadeel nake so. Shi dai za ku taya ni addu'a ya ce yana sona."

"Kin ji wawiya, ke kanki kinsan kaf abokansa ma babu na yar wa musamman Ibb. Ai dai kinga irin jama'arsa da suka kawo masa ziyara muna nan dake a gidannan tun zuwansa ko?"

Murja wacce ta zo hutun makaranta gidan ?ar uwarta ta, ta mike tana gyara zaman Waurin dankwalinta.

"Nidai kam shi nake so, ai duk kyawunsu ba su kai shi ba. Malam ga aji na musamman. Kiga fa ko sadda su Sholy suka zo gidannan ko kallo basu ishe shi balle su ga ha?oransa. Nima din ba.."

"Ki yi zaman hira har sai ya gaji ya turo wani ya karSar musu abincin. Shashasha marar wayo kawai. Ana kai ki kina ?in zuwa. Ke kika sani. Zauna har ki yi biyu babu."

Jin haka da sauri ta fice daga falon tana dariyar maganar Zuwaira, mai bi wa Anti Amarya.

A kwando ta ga Larai ta haWa komai har da cokula da farantai, ta kinkima ta yi gaba inda ta tsallake yan uwan Alhaji da suka zo daga ?auye ko kallo ba su ishe ta ba ballantana ta yi tunanin gaishe su. Su kam suna hau gulmarta da harshen fulatanci. A ?asan ranta ta ja Allah ya isa.

Tana zuwa ?ofar ta kwankwasa, Ibb ya ba da umarnin a shigo. Lokacin dukkansu har Imran sun cire babbar riga ana shan iskar fanka ana hira, sun zama su biyar a Wakin sakamakon shigowar abokan Ibb biyu, Saifullahi da Idris. Da sallama a bakinta ta shiga, kasancewar Fadeel ne a saitin ?ofa ya bi ta da kallo Waya ya kauda kai ya maida saman kwandon dake hannunta. Dama abin da yake jira kenan, ita kuwa kusan zaucewa ta kusa yi sakamakon kwayar idanun Fadeel da suka haWu da nata, gaba daya ta ji ta ?ara narkewa a tekun sonsa. A ranta tana ayyana ba gudu ba ja baya shi din dai ranta ke so. Babu wani abokinsa da ta ga ya burge ta, gwara ma Ibb don a baya tana mishi kallon hadadden saurayi duk sadda suka hadu ya zo gaida Alhaji, ita kuma ta zo gidan, yanzu kuwa ta fahimci Fadeel ya kere shi.

"Ba sai kin zuba ba, bar shi za mu yi serving da juna." Fadin Ibb fuska a sake ganin ta sauke kwandon ta hau fito da kayayyakin tana shirin buWe warmer.

Ta kalle shi kadan tana dan murmushi.

"Lah ba komai, bari na zubamaku, wannan ai aikinmu ne mata."

Bai kara magana ba sai mayar da hankali ya yi ga Imran dake nuna mishi wani hoto a waya. Shi kansa Ibb ba mai yawan zance ba ne sai ta kama, don haka bai hanata ba. Shi kuwa gogan kallonta bai kara ba, sai Idris da ya zuba mata ido kamar ya haWiye ta. Shi dai kam lokaci guda ya ji ta kwanta masa a ?o?on rai. Don haka bai yi ?asa a gwuiwa ba ya dubi Fadeel.

"Wannan ?anwarmu ce?"

Tsaf Fadeel ya karance shi, don haka ya gyada kai kawai fuska Waure. Ita kuwa da rawar jiki ta mi?a kwanon abinci ga Fadeel. Madadin ya karSa sai ya dube ta. Ta ji kallon tun daga tsakar kanta har tafukan sawayenta.

"No, ki fara ba su tukunna."

"Kai Malam, idan za ka karSa ka soma ci ka karSa. Tun Wazu ka ke mana raki da kukan yunwa kamar wanda ya shekara bai ci ba. Wannan ta ya ya kake azumtar watan Ramadan?"

Jin haka ya ja filo ya jefawa Imran a fuska, gaba daya aka sa dariya shi kuwa ya shafi sumar kansa yana mai lumshe idanu lokaci daya ya bude su akan Murja, wannan karon sai da ta ji miyan bakinta ya sar?e ta sai ga shi ta soma tari ba ?ak?autawa. Idris da sauri ya mi?a mata ruwan roba dake gefensa saman kafet. Ta karba ta sha tana satar kallon Fadeel da bai ?ara dubanta ba sai waya da ya ke faman dannawa. A haka da rawar jiki ta zuba kowa ta mi?a mishi. Friedrice ne da hadin coslow sai chicken pepper. Ta bude firij ta ciro musu lemuka ta ajiye. Daga haka ta sa kai ta fita. Tana fita Idris ya gyara zama ya shiga rantse musu akan ya ga matar aure shi dai yana sonta idan za'a ba shi. Fadeel ba ya fahimtar komai ban da ta cikinsa da ya ke yi, ganin duk da ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fankar da ke busawa yana gumi kawai sai ya mike ya cire rigarsa daga shi sai dogon wandon shadda da vest ya koma ya zauna. Sai da ya tashi da abincin tas kafin ya Wauki ruwa ya kora ya dubesu. Kowannensu bai kai ga kammala ci ba, suka kwashe masa da dariya, shi kansa murmushi da tsaki ya yi lokaci guda kuma yana sa hankicif ya goge fuska.

"Ku na da matsala wallahi, ba za ku gane illar da yunwa ke min ba. Yanzu sai ta tayarmin da ulcer."

"Ai mun gane komai ranka ya daWe. Ko za ka ?ara?"

Saifullah ya faWi da zolaya. Fadeel ya Wan harareshi.

"Saboda na zama rumbu ko?"

Haka suka yi ta zolayarsa shi kuwa tuni ya maida kai kan wayarsa yana kiran abu na biyu da ya tsaya mishi a ?o?on rai amma har ta kammala ringing ba a Waga ba. Haka ya kira har sau uku, sai a na huWun, aka Waga. Kafin ya kai ga cewa komai ta soma faWa.

"Wai Malam kai din maye ne?! Na ce ka bar kirana ka ?i! Dole ne zuwanka gidan namu? Haba, wannan jaraba da naci har ina wai? Mtsw."

Daga haka kit, aka kashe kiran, nan da nan kansa ya yi wata irin sarawa, dama ga ciwon kan da tun Wazun yake ji. Gumi ya karyo masa saboda tsananin Sacin rai, idanunsa tuni suka kaWa. Sauyawar yanayinsa ya sa Ibb ?uramasa idanu. Sai dai bai ce komai ba ganin ba su kaWai ne a falon ba. Sai bayan da gaba daya suka fice don gaisawa da Alhaji sannan Ibb ya dube shi, lokacin ya mayar da kai jikin kujera ya lumshe idanu don har su Imran suka fita sun yi zaton bacci ne ya kwashe shi su na mishi tsiya. Shi kuwa duk yana jin su ba shi dai da karfin biyewa shirmensu.

"Fadeel, wai meke faruwa haka?"

Jin muryar Ibb yasa shi bude idanun, ya mike zaune sosai.

"Yarinyarnan nema take ta kashe ni, daga ranar da na gan ta har zuwa yau ban huta ba."

Cikin rashin fahimta Ibb ya dan wurga hannu.

"Wace yarinya ce haka? A rayuwarka har ta hanaka sakat? Wace ce?" Tsakaninsa da Allah ya yi furucin don shi gaba Waya ma ya manta da wata Humaira.

"Wacce muka haWu da su tare da wannan Wan iskan yaron."

Shiru Ibb ya yi cikin nazari sannan ya dube shi a hanzarce.

"Are you serious? Kana nufin ka kira ta?"

Cikin ido Fadeel ya dube shi.

"Yes, mun yi waya, amma duka ba masu dadi ba ne."

Ya kora mishi bayanin duk abin da ya faru, Ibb ransa ya Saci.

"Unbelievable! Yanzu akan mace ne ka shiga wannan yanayin? Fadeel kai ne dagaske dai wanda na sani? Mutumin da gaisuwar kirki abu ne mai wuya a ganka kana yi da wacce ba muharramarka ba, kai ne yau da bakinka ka ke faWin cin kashin da wata shashasha can take maka? Kuma har ka ke tolerating in the name of love? Is this love or madness?"

A fusace Fadeel ya soma magana, tun da Ibb ya jefi Humaira da kalmar shashasha ya ji ransa ya yi masifar zafi.

"Oho! Idan ma haukan ne naji ni na jefa kaina ai ba da sa hannunka ba ko? Ban damu da duk wani tunani da za ka yi ba. Ina sonta, ka zo gabana kana kiranta da shashasha ba zan iya jura ba Ibb! Ina haWa ka da Allah, idan har ba goyamin baya za ka yi ba toh kada ka kara kuskuren zaginta a gabana. Kawai dai ina ji a jikina wataran za ta gane ni din masoyinta ne na gaskiya."

Yana kaiwa nan ya mike ya nufi hanyar Waki, Ibb kuwa baki a wangale yake binsa da kallo har ya Sace masa. Meke damun Fadeel? Ya jefawa zuciyarsa tambaya, a take kuwa amsar ta zo masa, Soyayya ce. A fili ya ce.

"Idan kuwa har wannan ita ake kira da soyayya, ina nemawa kaina tsari da ita. Kai kuma Fadeel ina ro?on Allah ya yayemaka wannan haukan son."

Daga haka ya mike ya fita a dakin domin shi har ga Allah ba ya fatan wannan rashin hankalin da mace za ta zage shi ya kasa daukar mataki a kanta. Ko ?ar uban wace ce ba zai ?ara yi mata kallon wata abar so ba, ballantana har ta ci galabar yi mishi son ranta.

***
Humaira na? kwance a yammacin ranar juma'a ta ji ihun ?an matan gidan ya karaWe falo, ta mike zaune tana mutsistsi?a idanu. Hayaniyar ta mene ne? Kafin bacci ya gama wartsake mata sai ga Ummita ta shiga fuska ba yabo ba fallasa.

"Wai hayaniyar me ake yi?" Fadin Humaira. Tsaki Ummita ta ja haWi da taSe baki.

"Aunty Jannat ce ta zo, kanwar Mami."

Humaira ta zaro ido, ba ta taba zama da ita ba amma ta sha jin labarinta a bakin Ummita na irin u?ubar da ta sha a wajenta sadda tana rayuwa a gidan.
"Dagaske? Ki ce mun shiga uku."
Ganin ruWewae Humairar har ya so ya fi nata ne yasa ta dariyar dole wanda ba ta shirya masa ba.
"Ke da ba ki taSa zama wuri guda da ita ba? Ba lallai ki fuskanci matsalar da na fuskanta ba ai."
Ita dai Humaira ta ji ne kawai ba don ya zauna a kwakwalwarta ba.
Suna nan zaune Humaira na cewa? ita kam za ta so ganin ya wannan Jannat din take mai shegen son mulki sai ga Muhsin da Waleed sun faWo Wakin a? guje. Kira ne daga Mami akan su fito a gaisa da Jannat. Ummita ta dafe kirji, yayinda Humaira mikewa ta dube ta.
"Wai ya haka, kinsan fa yarannan akwai daukar zance yanzun sai su fasalta musu yanayinki."
Ummita sai ta maze ta mike. Suka kama hanyar falon, tun kafin ma su kai ga ?arasa shiga ta hange ta. Kamanninta sak da Mahaifiyarsu wato Anna. Kusan har ta so ta fi Mamin hasken fata, siririya ce ba ta da tsawo duk kuwa da cewar tana daga zaune ne. Yaranta ?an biyu tamkar an tsaga kara an karya, ba su wuce sa'o'in Muhsin ba. Wato shekaru goma a duniya. Riga da wando ne a jikinta sai abaya dake ajiye a hannun kujera wanda ga dukkan alamu cire ta ta yi. Gashinta ya sha kananun kalba an tufke a tsakiyar kan ya yi kamar ta sa ribos din acuci. Gaba daya iyalan Mami na falon ciki kuwa har da Anna wacce ba kasafai ta fiye fitowa ba. Humaira ita kanta sai da ta sha jinin jikinta ganin Anna a falon, sai da itama ta ji kamar ta ja hannun Ummitan su juya. Aikuwa su na ganinsu Anna ta tamke fuska gami da juya harshe zuwa buzanci. Ko me ta fadi oho, gaba daya suka kalli su Humaira, matasan suka gimtse dariyarsu sakamakon Mubarak dake zaune, sun tabbata muddin suka ce fiddo shi waje to fa kashinsu ya bushe wurinsa.? Hatta da Raihana ba ta ji dadin zancen Anna ba domin har ga Allah yanzu ba ta da matsala da su, ta ri?e su ?an uwan na gaske kuwa.

Ita kuwa Jannat kallon Humaira ta ke yi kamar wacce ta ga kashi. A yatsine ta amsa gaisuwarta, Ummita kuwa gaisuwar ma ba ta samu ba sai harara da ta watsa mata ta ja tsaki.

"Wai Anti Jannat har yanzu wato kina nan yadda na sanki."

Mubarak ya fadi ransa duk ba dadi, tun daga kalmar agolar da Anna ta kira Humaira da shi har zuwa yanda Jannat ta karSi gaisuwarsu.? Rai a Sace ta amsa.

"Toh ko za ka sa hannu ka buge ni ne? Dama ai kai na faWa can dai dangin uba ka biyo ba mu ba."

Zai yi magana da sauri Mami ta Waga mishi hannu, aikuwa abin da take gudu shi ya afku domin Anna faWa ta hau yi kamar ta ari baki wai laifin na uwarsa ce da ta fifita bare a kan nata. Ganin dai abu ya ?i ?arewa Humaira ta mi?e tana mai jan hannun Ummita, itama ba shiri ta mi?e sun kama hanya tana ji Jannat ta kwalawa Ummita kira tana ba ta umarnin ta ja Hassan da Hussein Wakin su Muhsin ta musu wanka. Ita dai Humaira a fusace ma ta karasa Wakin don ta matsu ta daina jin muryar tsohuwarnan da ma Jannat din wacce ta ji tsanarta lokaci guda ya rufe ta. Me ake da wanda bai san daraja ta DAN ADAM ba?

Ita kadai a dakin ta yi ta mita tana tsaki. Ji take kamar ta je ta sha?e wuyansu baki Waya. Sai kuma ta yi kwafa tana cije lebbanta, ita kadai ta san damuwar da take dannewa a ranta, amma a kwanakin nan abin yana neman fin karfin zuciyarta. Damuwar bai wuce Abba ba, mutumin da ya kasance bango majinginarta a gidan, wanda shi take yiwa kallon uwa kuma da uba. Wannan kauna da soyayyar da ya nuna mata a farkon zuwanta gidan yanzu ta rasa laifin da ta yi mishi ya sauya. Hira ma ya ?i ba da fuskar ta ja shi da shi, idan har ita Waya ce a falonsa, nan da nan zai hau wasu ?an aikace-aikacensa kamar gyara takardu ko kuma kiran abokan cinikayya, shaida dai ta cewar ba ya son ta ja wani dogon zancen. Ba dai za ta ce ba ya mata fara'a ba ne, sam a'a, sai dai babu ja a jiki balle har su sha?u tamkar yanda ya nuna a farkon zuwanta. Toh wanda ma ka ke ta?ama da shi bai wani damu da sha'aninka sosai ba ina kuma ga wasu can da har gobe sun ?i karSarta matsayin ?ar uwa ta jini? Kewa, kewar Dada da Kawunta duka suka mamaye ta, ba ta san cewar ta soma zubar da hawaye ba sai bayan ta sa hannu saman fuskar ta ji danshin lema. A hankali ta share su, ya kuma yi daidai da shigowar Raihana Wakin. Ganin hawaye a fuskarta gaba daya sai ta ji ba dadi, ko ita ce ake yaren da ba ta ji tsarguwa yake sanya ta ballantana kuma wannan da dama din sun san ba da kowa ake ba sai su.

"Humaira kuka? Don Allah ki yi hakuri."

Ta fadi a sanyaye gami da zama a gefenta. Jin haka ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo lokaci guda tana gwale idanun da hannu tana share su.

"Ke ba fa komai, ba kuka nake ba. To me aka yi da zan yi kukan?"

Raihana itama murmusawar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login