Showing 159001 words to 162000 words out of 189325 words

Chapter 54 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

237

ta samu, ya kuma ji kwarin gwuiwar ganin wata ?ar albarkar ta rage masa aiki ta hanyar karSar Ahmed da kuma nufar hanyar ?ofa da shi inda ?awayenta yara suke tsaye ana wasa.

Ya fa?aici idanun jama'ar dake wurin ya yi saurin yin baya. A wannan fakar idanun Ummita idanunta suka kai kansa, har abada ba za ta taSa mance wannan mummunan fuskar ba duk kuwa da irin shigar manyan kaya na kamala da ya yi ba a can da yake shigar ?ananan kaya, kayan ma na ?an duniya irinsa. Kirjinta ya hau bugu, ta ga ya juya zai fita, ta kasa sukuni ta bi bayansa, ta kasa magana saboda ta fi bu?atar tantance komai da idanunta kan ta yanke hukuncin ihu za ta yi ko kuwa gudu za ta yi. A yayinda hankalinta ke kan Wizzy, shi ko Ridwan nashi hankalin ya koma kanta ganin ta zo ta tsakiyarsu inda za'a yi hoto ta wuce ba a hayyaci ba. Ya juya da sauri ya bi bayanta daidai sadda Wizzy ya sa hannu ya karSi Ahmed da yaudararriyar murmushi da ya sakarwa yarinyar gami da fadin ta ba da shi ya ga wannan fine boy din. Daga haka ta ga ya nufi wajen falon da shi yana Wan yi mishi wasa. Ihun da ke ma?ale a fatar bakinta shi ta saki gaba Waya iyaka ?arfinta. Wannan ya ankarar da Wizzy, da wani irin sauri ya zura Ahmed cikin babbar riga ya soma? gudu zai fice. Ai cikin wani irin zafin nama Ridwan ya bi shi da sauran mazan dake a wurin. WaWanda ke waje kuwa suka yi nasarar cafke shi, Ummita kam tuni ta fita hayyacinta kira take "Shi ne! Wallahi shi ne! Ya zo ya Waukemin Wa!"

Humaira da Fadeel da sauran jama'a hankalinsu ya tashi, Fadeel ya ri?e Humaira gam ganin yanda jikinta ya hau wani irin mazara, aka fita gaba daya zuwa farfajiyar gidan inda Ridwan ke ri?e da Wizzy gam! Ahmed ko yana hannun Dawud. Ummita na zuwa ta karSi Ahmed ta rungume tana ja baya sosai daga Wizzy, kallonsa take yi a mugun tsorace jikinta na Sari, Anti Maijidda da Hajjo suka ri?e ta sosai. Wizzy kuwa idanunsa sun raina fata, Humaira ta bishi da kallon tsaf. Tabbas shi ne. Ta hau nuna shi da yatsa itama.

"Fadeel wallahi shi ne ya ketawa ?ar uwata haddi! Shi ne ba?in azzalumin da ya cuci rayuwarmu!"

Sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, Fadeel ya rungumeta sosai cikin alamun rarrashi. Nan dai Ridwan ya yi waya ga abokan aikinsa akan su iso da gaggawa.?

Abba da jama'arsa dake zaune a falonsa na saukar ba?i jin wannan labari suka fito, ya nufi Wizzy ya bishi da maruka hagu da dama.

"Yanda ka shigo hannu da yardar Allah ?arshenka ya zo. Muje ni da kai shari'a yanzu aka fara. Azzalumi!"

Wizzy dake cika da batsewa yana hura hanci kamar tsohon salansa sanadiyyar marin da ya sha na Abba ya tari Abban da sauri.

"Ka dinga yin jam'u ai YallaSai! Azzaluman ai biyu ne ba Waya ba! Akwai azzaluma irin matar mai wannan gidan?! Ita ce ta sanya muka aikata wannan mummunan aikin don ta samu ta mallaki dukiyarka!"

Ana ga wata ga wata! Nan fa kallo ya koma sama! Jama'a suka yi caa ana maganganu, kowanne da abin da yake faWi. Abba kuwa ai sai da ya ji duniyar na juyamasa, yana ji abokan Fadeel suka yi caa a kansa akan ya ?ara shirga wata ?aryar sai sun fasa bakinsa. Shi kuwa Wizzy ya dinga rantse-rantsensa cewar har da hannun matar Abba. Daidai lokacin motar ta iso aka titsa ?eyarsa aka tafi. Su Fadeel ma babu jinkiri suka tafi, shi kam a son ransa ya so a ba shi matarsa kawai su fice tare don ya tabbatar wannan lamarin sai ta dinga kuka a kansa. Ibb ne ya nunamasa ba a haka tunda dai su na cikin rashin nutsuwa ya ?yale su samu hankula su kwanta.

Magana dai har yamma ana ta yi, kallo sai ya koma sama. Madadin hirar da ta shafi biki da kuma sabga ta mata sai gulmar Mami. Da yawa sun cika da al'ajabi sun kuma yi rantsuwa kan cewar za ta aikata. Wasu kuwa sun ce sam! Mami ta ri?i yaran da zuciya daya, kawai dai akan auren Humaira ne aka yi ya?i da ita don a fili ta nuna ba ta ra'ayin Fadeel, zai kuma iya zamtowa akwai dalilinta. Anti Maijidda kuwa kuka sosai ta shiga yi tana hamdala da Allah ya nunamata ranar da kusan kowa ya gane wace ce Mami.

***
Wai ina Mamin?

Tun shigowar su Fadeel tana Waki, ta yi wanka sai dai ta kasa fiddo kaya balle ta sanya. Ba?in cikin wannan gidan arzikin da Humaira za ta shiga shi ya tsaya a ?o?on ranta, ?arshe ma kuka ta shiga yi. Abin mamaki, kuka na ba?in ciki da jin inama ta mutu kafin wannan rana. Wai Wiyar Fatima ce kishiyarta, ita ce dai ta samu wannan Waukaka ta ko'ina. Ita kuwa nata yaran daga bazawara mai ?ananun shekaru sai ko wata can da aurenta ke gantali, su kansu mazan sun ?are karatunsu babu aiki. Kasuwar ma Abba ya dakatar da su daga zuwa saboda irin Sarnar da ya ce suna yi masa. Yassar da Abban yace zai samar masa koyarwa ya rantse ba zai yi ba, shi kam Allah ya kiyaye a ganshi yana koyarwa. Wannan ya hasala Abban har ya fita hanyarsa ya ce ya yi duk yanda ya so.

Tana nan kwance ta ji ihun Ummita da ya karaWe gidan. Ta mike har zaninta na faWuwa tana ja tana Worawa. Jiki na rawa ta Wauki dogon hijabi ta zura. SaWaf saWaf ta bude ?ofar ta fita lokacin hankulan jama'a duka ya yi waje an fita an bi Wizzy. Ba ta fahimci wa Ridwan ya ri?e ba sai da kunnuwanta suka ji muryar Humaira na sanar da Fadeel? wai shi ne mutumin da ya keta haddin yar uwarta. Ai cikin Mami sai da ya yi wani irin kaWawa. Jiki na rawa ta nemi hanya ta koma Wakinta ta datse gam! Gumi fa ko ta ina ya shiga tsastsafo mata. Tana nan ta dauki waya amma rawar da hannunta ke yi ya sanya ta kasa koda bude wayar balle kuma ta kira. Ta yi wurgi da wayar sakamakon cikinta da ya shiga murWawa ai sai ta nufi bandaki ta hau gudawa. Can ta ?ara fitowa ta yi jim a jikin ?ofar Wakinta don jin me ke gudana, wani sabon al'amari ta ji, Anti Maijidda ke kuka da hamdala wai Allah ya toni asirinta. Yau gashinan Wizzy ya ce tare da ita ce suka haWa baki suka yi garkuwa da su Ummita.

Ai Mami sai ta sulale a wurin ta zauna daSas! Wannan tashin hankalin da me ya yi kama? Duk da ta sani babu wata hujja da Wizzy zai nuna ya ce har da ita ciki amma wannan furucin nasa babban barazana ce a gareta. Haka ta wuni ta ?i fitowa a Wakin, duk irin bugun duniya da kiran wayarta da aka dinga yi amma ta yi biris ko kallon wayar ta kasa balle ta ga mai kiran. Tana ji wasu na rantsuwar tana ciki wasu kuwa cewa suke yi ga dukkan alamu dai ta fice a gidan tunda akwai wadanda suka ce sun ga fitowarta sanye da hijabi.

Raihana kuwa a ranar asibiti ta kwana saboda tsananin ciwon kai da zazzaSin da ya yi mata dirar mikiya.

Hakanan a wannan daren Abba yace babu abin da zai sa a jinkirta kai Humaira Wakin mijintaz da wannan tashin hankalin suna kuka suka rungume juna ita da Ummita tamkar kar su rabu. Ga ?ar uwarsu can a asibiti kwance, haka aka tsitsa ?eyar Humaira bayan sun yi sallama da Abba ya yi mata nasiha zuwa gidanta na aure.

***
Washegari kuwa tun asuba Mami ta shiga wurin Abba, yana dawowa daga masallaci sai ganin mace ya yi a zaune tana faman kuka. Ya kalle ta bai ce uffan ba ya kama hanyar shiga Wakinsa. Ta tare shi da sauri ta rike kafafunsa tana kuka kamar ranta zai fita.

"Abban yara, kada dai ace ka yarda da wannan ba?in ?azafin da aka shiryamin? Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Wallahi Abban yara muddin aka ce kai ma ka mara wa masu zargina baya nikam ban ga wanda zan kama ba. Ni Maryam me marayun Allah suka yimin da zan cutar da rayuwarsu?"

Abba kallonta kawai ya ke yi da idanunsa da suka tasa ga dukkan alamu bai samu wani baccin kirki ba. Murmushin ya?e ya bita da shi.

"Ni kin ji na ce maki ina zarginki ne Maryama? Kin ji wani abu daga bakina?"

Sai ta mike tsaye suna duban juna.

"Ba ka faWi ba, amma shirunka ya nuna ka aminta da zargin masu zargi."

Ya kauda kai don wallahi ji yake yi a duniya a yanzu babu abin da ke mishi muni ya kall sama da fuskarta.

"Maryama, abar zancen. Tunda shi wannan ba?in azzalumin ya shiga hannu, gaskiya za ta yi halinta ai yanzu. Ki kwantar da hankalinki masu zarginki za su bari muddin komai ya bayyana."

Yanayin da ya yi zancen sai ba ta gamsu babu komai a zuciyarsa ba dangane da ita. Ta dai matsa mishi kamar yanda ya bu?ata ya faWa Wakinsa.

***
Ina labarin Humaira da Fadeel?
Kukan Humaira ya ?i ci ya ?i cinyewa. Abubuwa da dama ne ke ?ara mata ?arfin kukan. Wannan tashin hankalin na jin wai da sanya hannun Mami a garkuwa da su ya tsaya a ranta. Ta dinga tunano kalar rayuwar da suka yi da ita a gidan tsawon shekarun da ba su da yawan da za a kasa ?irgawa, irin kulawa da nuna kaunar da ta dinga yi mata. Ita kuwa komai da Mamin ta ke mata ta Wauke shi da zuciya Waya, ba ta taSa kawo wani abu na mugun zato a kanta ba idan aka cire sanin da ta yi Mami ba ta farin ciki da aurenta da Fadeel. Sai yanzun abubuwa da dama suke mata yawo a kwakwalwa, wai dama ya za'a yi macen da ta haifi yara da kanta ace ta fi kaunarsu akan abin da ta haifa? Kenan ta tabbata batun Hajjo da ta ce da biyu Mamin ta dakile ta daga karatun boko? Toh idan ita din ta kasance Wiya ga tsohuwar kishiyarta da ta rasu, me Ummita ta tare mata? Me ta yi mata a rayuwa da har sa ta nakasta rayuwarta har haka? Ta maida ita ?aramar budurwa kuma bazawara? Tayi sanadin da aka keta alfarmarta har wannan masifa ke bibiyarta wato Wizzy. Ta yi sanadin da aka fasa aurenta da masoyinta Sahabi. Mene ne ribar Mami da ta shuka dukkan waWannan munanan ayyukan. Shin kodai Raihana ta sani ne? Tambayar da ya shiga kwakwalwar Humaira kenan. Ta Wan muskuta ta share fuskata. Anya Raihana ba ta da wani labarin dangane da Mami? Yarinyar a yan kwanakin nan ta sauya gaba daya ba ta rabo da kuma da damuwa? Sai an matsa da tambaya sannan ta ke saita kanta ta shiga harkokinta? Kai gaskiya tana da tabbacin akwai abin da Raihanar ke Soyewa. Sai tausayin ?anwarta ta ya mamaye zuciyarta, ita Win ba ta da wani aibu a yanzu, ta tsarkake zuciyarta daga dattin ?iyayya da hassada irin wanda yan uwanta Tasleem da Futuha suka Worawa kansu. Tana kaunarsu tana kuma zaune da su da zuciya Waya babu wani abu bayan hakan.

Turo ?ofar da aka yi gami da sallama cikin tausassan murya ya katse tunanin Humaira, ta ?ara sunkuyar da kanta tana Wan sakin numfashi irin na wacce ta ci kuka kuma take kan yinsa. A can ?asan zuciyarta ta amsa sallamartasa.

Ya ?araso cikin dakin sosai, ya yi wanka ya sauya sutura zuwa jallabiya fara ?al wacce ba ta Soye kyakkyawan tsarin halittar da Allah ya yi mishi ba. Sai baza ?amshi yake yi ta ko'ina. Ya Wan bi Wakin da kallo kaWan yana murmushi da alfahari da zaSin da ya yiwa Humairar na kalar da ta fiso wato kore. Sai adon Wakin ya kasance farin da kore. Zama ya yi a gefenta har kafaWunsa na gugar nata. Fadeel kenan, shigowarsa babu aboki ballantana Wan rakiya.

Hannu ya sa ya yaye rufin fuskarta. Ganin hawaye kwance ya sanya shi saurin ri?o haSarta da Wago kan suka dubi juna, ai yanda ya ga idanunta sun kumbure sun yi ja sai ya ji wani sabon tashin hankalin na daban.

"Boddo, kukan kike ta yi? Ya Salam, sai ki janyowa kanki wani ciwon?"

Ya shiga taSa goshinta da gefen wuyanta don ya ji ko jikinta da zafi, ita kuwa sai no?ewa take shi ko zuciyarsa daya yake yi. Gaba daya ganinta cikin wannan halin bai masa dadi ba ko kaWan.

"Please ya isa hakanan. Kinga yanzu babu zafi jikinki. Kiyi hakuri tunda komai yanzu yana hannun hukuma. Idan kuma don kin ji ya ambaci Maminki ne kar ki bari wannan ya yi tasiri a zuciyarki. Tunda har ya gan shi a hannun hukuma to zai iya ?ir?irar kowane sharri ya faWi. Ki kwantar da hankalinki koma mene ne bincike zai bayyana."

Ta gyaWa kai, ya lalubo tafukan hannunta ya sanya cikinnasa. Rashin sabo da hakan daga shi din har ita sai da suka ji wani yarr.

"Kina da alwala?"

Shi ne tambayar da ya yi mata, nan din ma kan ta gyaWa ta a kokarin zare hannunta. A hankali ya saki sannan ya faWa banWakinta. Can kuma ya fito ya yi mata umarnin zuwa su yi nafila. Ba musu ta mi?e ta gyara zaman laffayarta. Bayan sun idar ya dafa kanta ya yi mata addu'o'i. Daga nan ya kama hannunta ya mi?ar suka fita suwa falo. Ta Waga kanta a hankali tana kallon falon, hamdala ta shiga ui a zuciyarta, yau ita dai Humaira ita ce ta mallaki wannan irin falon da sai dai ta gani a soshal midiya su na yawo don ko gidan Futuha da ake ta santinsa bai kai rabin nata tsaruwa da kyau ba. Komai a falon adon skyblue ne da fari, iyakar kyau da tsari ya yi.

Jan hannunta da Fadeel ya ?ara yi ne ya maido ta hayyacinta, ta Wan yi saurin janyewa tana Wan tura baki. Da alama ita ba ta son wannan ba?on halin nasa na ri?e mata hannu. Ya yi murmushi ya matso dab da ita gami da sa hannunsa saman ?ugunta ya matse ta gam har fuskokinsu na haWuwa wuri guda.
Idanunsu a lumshe ba ka jin komai sai bugun da kirjin kowannensu ke yi. DaddaWan kamshi babu ko digon wari shi ke fita daga bakunansu.

"Kin zamo mallakina Humaira, babu sauran wata ?ofa da ke buWe tsakaninmu. Babu kuma sauran sharaWin da ya yi saura. Ki taimake ni ki bar kokarin yimin iyaka da dukkan inda hannuna ya sauka a jikinki."

Ya yi maganar da muryar da ta rasa na Fadeel ne ko kuwa, har sai da ta buWe idanunta, aka yi sa'a shi Winma kallonta yake yi a lokacin, sai dai ga mamakinta, hawaye ne kwance saman kumatunsa. Ta yi kokarin ja baya a Wan ruWe, ya yi saurin ?ara ri?e ta sosai.

"No Humaira, bar ni na ji Wuminki, na ?ara samun tabbacin Fadeel ba mafarkin da zai iya farkawa yake yi ba. Alhamdulillah Ya Rahman."

Ya furta zuciyarsa da wani irin nauyi ga farin cikin da yake lulluSe shi. Sabuwar soyayyar Humaira na ?ara huda dukkan wata ?ofa ta jikinsa tana shiga tana mamayarsa. A Sangaren Humaira kuwa ba ta san sadda yatsunta suka sauka a kuncinsa ba, dauke masa hawayen ta yi yayinda itama nata su ke zuba. Ita ya kamata ta koka ba shi ba, ta wahalar da shi iyaka, ta kuma yi mishi cin fuska kala-kala, sai dai dukkan wadannan bai sa ya juya baya ya ha?ura da ita ba. Sanadinsa za ta iya cewa ta samu warakar zuci da gangar jiki daga cutar da ake tunanin iskokai ne masu sanya ta tsanar dukkan wani Wa namiji a rayuwa. Ya ri?e yatsunta idanunsa a cikin nata gami da kai su baki ya sumbata. Ta runtse idanun tana jin kamar ta kwace yatsunta amma kuma ro?on da ya gama yi mata na kar ta yi mishi kowane iyaka ne ya sanya ta daurewa. Tana jinsa ya dinga yin yanda ya so har sai da suka nemi faWuwa sannan ya bar ta. Ta yi saurin zama a kujera mafi kusa da ita. Shi kuwa dur?uso ya yi a gabanta gami da ri?o dukkan yatsun hannayenta yana dubanta kai ka ce ranar ya soma ganinta a rayuwa. Murmushi sosai yake yi yana kallonta yayinda ita kuma ta kauda kai zuwa gefe guda, kallonsa na haifar mata da yanayi mai kashe kuzarin jiki.

"Nagode, nagode da kika aminta da aurena. Ina mai miki albishir da cewa kin dace in sha Allahu, kamar yanda dama ni tun tuni na sa a raina samunki a rayuwa shi ne dacewar da zan yi. Alhamdulillah. Yau ga Fadeel ga Humaira. Kin ga ranar ha?uri ko?"

Ta Wan yi murmushi. Ya kai hannu ya shafi leSSanta.

"Soyayyata kaWai ta isa mu rayu cikin farin ciki da aminci. Nidai na san koda ace har yau ba a wani sona, toh ana ji da ni."

Ta yi ?asa da kanta, shiru ya biyo baya, shi bai bar wasa da yatsunta da kuma bin ta da kallo ba, ita kuma ta kasa furta abin da ke yawo a zuciya da saman leSSanta. So ta ke ta ba shi tabbacin cewa itama fa tana so da kaunarsa wanda ta san ya sani kawai so yake yi ya ji daga bakinta.

Mi?ewa ya yi ta bishi da idanu har ya je fa ledojin da ya shigo da su yana fadin shi yunwa yake ji saboda tun safe bai ci komai ba murnar an Waura aurensu.

Suka ci har ta mi?e ta bar shi, yana jinta tana masa sai da safe ya gyaWa kai kawai yana bin ta da murmushin da shi kaWai ya san ma'anarsa. ?akinta ta shiga ta Wan tura ?ofar, laffayar jikinta ta warware ta ninke ta buWe sif? dake manne jikin bango ta sanya. Rigar da ta ji Hajjo ta ce mata ta sanya shi ta fiddo, warware

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login