Showing 174001 words to 177000 words out of 189325 words

Chapter 59 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

251

kuwa me?!!"

"Maryam!"

Suka juya gaba daya ga Abba dake tsaye ya shigo, dama tunda ya ga ba ta amsa wayarsa ya san wata taSargazar za ta yi.

Ta juya ta watsa masa wani kallo kamar idanunta za su faWo, fuskarnan ta da a Waure, ba ya so su raba halin a gaban ba?i don haka ya yi mata nuni fa hanyar waje.

"Muje falona, ko me ake ciki zan sanar da ke."

Ta yi Wan jim kawai har lokacin ba ta Wauke idanu a kansa ba. Sai da ya ?ara maimaitawa kafin ta kauda kai ta bi falon da kallon tsaf sannan ta kalli Baba Amina dakyau kallon zan dawo kanki kafin ta wurgawa sauran matan harara ta yi gaba.

***
"Kin je za ki tayar da hankalin gida kin manta da yaranki, kefa ba yarinya ba ce."

Abba ya fadi yana cin magani bayan shigarsu Wakin, ita kuwa Mami tsaye ta yi masa a kai, hannunta a saman ?ugu ta Wan juya kai idanunta a rufe sannan ta bude su.

"Kaga Yusuf, idan ma tarwatsa hankali zan yi wannan bai shafeni ba, ka fito a mutum sak! Ka fadamin dalilin wannan gyara na munafunci, wanda ba a tashi yinsa ba sai bayan ba na nan, kuma ka sanar da ni zaman da waccan annobar ke yi a cikin gidana!"

Abba ya ji zafin maganganunta, kai tsaye yana kallonta ya amsa.

"Zaman aure take yi kamar ke. Auro ta nayi, matata ce!"

Ai da jin haka sai ga Mami ta daka wani wawan tsalle ta sha?e wuyan rigar Abba gami da sakin wani irin kururuwa tana kiran wayyo!!!

"Ba ka isa ba! Wallahi ba ka isa ba ka yi kaWan! Ni za ka wula?anta? Ni za ka ci ma mutunci? ?an iska Wan tasha! Yusuf na fika iya tashanci! Daga kai har Maijidda kashe ku zan yi! Munafukan banza mu...!"

Wani wawan mari Abba ya Wauketa da shi kafin ya SanSareta daga wuyansa ya hankaWa ta. Ta kuma yun?urowa daidai da shigowar Baba Amina a rude da ma su Yassar wadanda ke zaman jiran wannan lokaci da Maminsu za ta san da batun auren Abbansu, sun sani dama abin ba zai kyau ba.

Wannan karon ba ta yi gigin ri?e wuya rigarsa ba sai ihu da magana cikin ?arfi da ta cigaba da yi.

"Na fada na kara, kai da Maijidda munafukai ne! Ni za ka yaudara? Dama ai tunda naga take-taken wannan ?aramar yar barikin na san cewa sai ta yi yanda ta yi ta shigomin gida! Ta zo ga ka nan ta ga idan wata uwar kake tsinanamin a gado da ma tukunyar girkina! Wayyo ni Maryam na shiga uku na lalace! Maijidda? Maijidda ba?ar karuwa?!"

Sai ta tafi a guje ta rarumi tv dake saman tv stand za ta kai shi kasa da sauri Yassar da Dawud suka ri?e ta kuwa haWa da su da shi din ta hankaWa suka kife. Wani mugun ?arfi ne ya zo wa Mamin na kishin fita hayyaci da hauka.

Abba gaba daya idanunsa sun kaWa tsabar ba?in ciki da wannan abin tirr da Mamin ke yi a gaban yaranta. Bai dauka haukarta ya kai nan ba. Ga zaninta kuwa ya kunce yana terere a tsakiyar falon don ma Allah ya taimaka tana sa dogon wando a ?asan kayanta.

Zagi ta uwa ta uba haka ta dinga kwaranyowa Abba da Maijida har ma da Baba Amina dake tsaye. An kira ta da munafukar da ta ?ulla komai, har da gorin suturu da ma tallafin abinci da tayi mata a baya kafin mijinta ya samu arzi?in kansa.

Dakyar Yassar da Dawud suka fitar da Mami suka sada ta da dakinta, ta tsine musu ya fi cikin kwando akan idan ba su rabu da ita ba za ta Waga musu nono. Sai da suka rufe ta sannan suka hau maida numfashi, Dawud goshinsa har ya kumbure saboda wani duka da ta kai mishi da gwangwanin maganin feshi na sauro dake ajiye saman wani ?aramin katako dake jikin bango hanyar dakin Abban.

Daidai lokacin Tasleem ta shigo gidan goye da Wiyarta Anisa dake bacci. Lokacin ana kiraye-kirayen sallar Magriba. Muhsin da Waleed kuwa sun tsaya cirko-cirko a tsorace sai kuka suke yi ganin Maminsu tana wasu abubuwan da ba zasu ce gashinan ba. Abin dai bai kai hankulansu su dauka ba.

Kirjin Tasleem na bugu da sauri-sauri ta ke duban su Yassar da kuma Mami dake bugun ?ofa tana tsinuwa garesu akan su buWe mata yau sai ta kashe Abba da Maijidda.

"Yaya Yassar meke faruwa? Anyi wani abu?"

"Aure Abba ya yi, ya auro Aunt dinnan ta Ummita shi ne fa."

Zaro idanu Tasleem ta yi waje.

"Anti Maijidda? Kut! Abba wannan ai cin amanar Mami ya yi? Duk irin yanda suke takun sa?a? Ya mance da wannan?!"

"Tasleem buWemin kofa wallahi ko na haWa har ke na tsinewa na kwashemuku albarka!"

Suka tsinci muryar Mami wannan karon ma har da kuka ta kara da fadin.

"Ku ka bari waccan karuwar ta shiga dakin Abbanku sai na tsinemuku. Shegu wadanda ba su kishin uwarsu! Ku budemin ?ofa na je na kashe su kamar yanda na kashe Sani da Jamila!"

A mugun firgice suka dubi juna, Tasleem wacce ta jima da sanin wannan Wanyen aikin da uwarta ta yi sai ta yi saurin duba hanya ko akwai wani bayan su da ya ji. Yassar da Dawud kuwa suka yi saurin buWe ?ofar.

"Mami, kika ce me? Su wa kika ce kin kashe?"

Ta banka masa harara.

"Uwarka da ubanka na kashe! Matsa ku bani hanya!"

Ta hankaWe su za ta fice, Tasleem ta tari hanya.

"Mami ki yiwa girman Allah kar ki je yanzu. Ki bari sai dare ya ratsa sai muke mu kashe su. Yanzu idan kika je za'a kama ki!"

Mamin ta yi shiru jikinta sai mazari yake tana tsuma, ita fa ba ta gane komai, Maijidda da Yusuf kawai take so ta ga sun bar mata sararin duniyar. Tasleem ganin kamar ta dan nutsu tana sauraronta dai ta cigaba da yi mata kulla kulla na ?arya duka dai don ta samu ta nutsu, kawai Mamin sai ta dora hannu a kanta. Ita ba za ta ce me take ji ba, ashe dai a can baya kishin banza ta yi wannan na yanzun shi ne ainahin kishi?

Sai kuma ta juya ta shige Wakinta tana kururuwar kuka mai sauti. Yassar da Dawud dai sun yi jigum don sun ji abin da ya girmi kunnuwansu sai kowannensu ya kasa cewa komai suka soma taku domin zuwa gabatar da sallar Magriba wanda tuni har wasu masallatan sun idar. Tasleem da sauri ta dakatar da Dawud. Takarda ta yaga a littafin da Muhsin ya barbaza yana aikin makaranta sai biro da ta gani a saman tv, sunan allura ta rubutawa Dawud din ta ba sa.

"Ka taho da shi don Allah, a chemist din Tj, zai ba ka idan kace inji ni, na Mami ne."

Ya karSa ba musu ya tura cikin aljihu ya fice, ita kuwa tana hawaye ta ja su Muhsin dake faman kuka zuwa dakinta. Yau dai idan har ba allurar baccin aka yiwa Mami ba akwai babbar matsala a gidan.
***
Kallonta kawai yake yi tun daga sama har ?asa cikin shigarta na ?aramar riga da wando iya ?auri yana buga murmushi lokaci guda yana jefa gurgurun dake ajiye saman centertable a baki. Ita kuwa Humaira ta haWe girar sama da ta ?asa ta cika ta yi fum yayinda kumatunta suka kumburo. Sanadin wannan fushin bai wuce na amsa wayar abokiyar aikinsa da ya yi ba har yana dariya. Shi kuwa wannan kishi na Humaira masifar burgeshi yake, ba da son ransa yake motsa mata shi ba, kawai dai yana ?ara tabbatarwa kansa da irin son da take masa yanzu ya shallake tunaninsa.

? Ita kuwa Humaira ganin da ta yi ya maida ta kamar ma wata cartoon bai dauki lamarin da muhimmanci ba don haka sai ta mi?e fuu za ta wuce zuwa Waki, ya sa hannu ya ri?o nata hannun, ta juyo ta dube shi, shima ya narkar da nasa kwayoyin idanun cikin nata kafin ya fisgota ta faWo saman kafafunsa.

"Allah ya huci zuciyarki, kinji?"

Ta kauda kai tana huci ba ta ce uffan ba. Fadeel ya sanya hannunsa saman haSarta ya juyo da fuskarta suna kallon juna. Ta runtse idanu gami da tsuke baki ita a dole ya mata laifi. Murmushi ya yi ya dubi leSSan kafin ya sa yatsa ya bi samansu.

"Please bana son fushinki. Ki yi hakuri kaina a ?asa. Yanzu ke a tunaninki wannan kirjinnawa akwai gurbin wata bayan ke?"

Ta Wan ji sanyin kalamansa, ta buWe idanun tana duban hannunta da ya Wora saman kirjinsa sai kuma ta dubeshi tana Wan harararsa.

"Toh naji amma ni meyasa ka?ke yi mata dariya haka? Har fa nan sai da ya lotsa."

Ta faWi tana kai yatsa saitin kumatunsa gami da dannawa da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~??arfi. Ya Wan saki ?ara yana ri?e yatsun gami da sumbata.

"Boddo wannan da biyu fa."

Ta yi murmushi. Ya ri?ota sosai.

"Idan na rantse za ki yarda?"

Ta girgiza kai.

"Bana bu?atar sai ka rantse, ban taSa kama ka da laifin ?arya ba, na kuma sani ba da gangan ka yi ba. Amma ai ni kadai ya fi cancanta a yiwa ko? Ba wata Jennifer ba."

Ta ?arashe da turo baki. Ya sumbaci kuncinta.

"Naji na karSi laifina, a yimin gafara." Ya ?arashe yana mai kai hannayensa dukkan inda kwakwalwarsa ta ayyana masa. Lamarin da ya fi karfin daukar kwakwalwa da zuciyar Humaira har sai da ta shiga mayar da martani kafin ta tureshi ta mi?e tsaye tana dariya dalilin wayarsa da ta yi ?ara. Ya shafi sumarsa gami da bin ta da kallo wanda babu wani mahalu?i da ke ganinsa a wannan yanayin idan ba ita ba. Wayar ta mi?a masa ganin sunan Alhajinsa a jiki. Babu shiri ya yi kokari wurin saita kansa gani da daukar gorar ruwa ya kwankwaWa sannan ya bi kiran Alhaji don tuni har ya katse. Ita kuwa ta dauki gurgurun da yake ci ta zauna can gefe tana ci hankalinta kwance. Ba ta yi aune ba sai ji ta yi ya sunkuce ta har gurgurun na zubewa tayi dariya bai tsaya a ko'ina ba sai Wakinsu.

Rayuwar tasu gwanin sha'awa, kusan basu da wata matsala ko damuwa. Sai da ya nutsa yake sanar da ita haihuwar da Hannatu ta yi, an samu Wa namiji. Ta kuwa har murna za ta je Yola kafin bikin su Raihana ta dawo. Ya ji ta amma bai yi na'am ba, shi dai ya sani ba zai iya jure ta yi masa nisa koda kuwa na kwana Waya ba ne balle wasu kwanaki.

***
Firgigit ta tashi daga baccin dolen da Tasleem ta sanya ta. Ta hau murza idanu gami da duban gari, garin ya waye tarr, ta mike a razane ta buWe window. Rana ce sosai, ta dubi lokacin ta ha ?arfe tara da rabi na safe. Abba da Maijidda ta tuna ba ta ko yi tunanin wata aba wai sallah ba, ta yi wuf ta fice ba ta bi koda ta kan wayarta dake faman ruri ba.

A falon ta iske Tasleem da su Yassar a zaune suna tattaunawa, Futuha itama tana nan ta zo dalilin labarin bazata na auren Abba da ya same ta daga bakin Tasleem a waya. Suna ganin Mamin gaba daya suka mi?e tsaye.

Ta banka musu uwar harara. Ta dubi Tasleem.

"Don ubanki ni za ki yaudara ki yimin allurar bacci? Ni da na haifeki da ke za'a haWa baki wajen cutar da ni? Kuna ji kuna ganin abin da ubanku ya yimin ko?! Ya auri wata banzar karuwa yau har ya tare a Wakinta amma ku kasa Waukarmin mataki? Kai yau nidai Maryam na haifi ?an iskan yara tsinannu!"

"Haba Mami! Haba don Allah, ki bar tsine mana hakanan. Idan fa muka lalace ke ce za ki soma kuka kafin wani ya yi. Aure ai ?addarar Ubangiji ne, ya muka iya tunda mai afkuwa ta afku?"

Yassar ke wannan zantukan don shi ya gama kai wa bango, ya gaji da wannan tsine-tsinen da Mamin ke musu, ba kuma ya so ta je gaban su Abba ta yi Saran Saramar da za ta tona asirin kanta ta jaza musu wani sabon bala'i don sun riga da sun gama jin labarin duk abin da ta aikata a bakin Tasleem da suka ga alamar ta san wani abun.

"Yimin shiru! Shashashan wofi kawai da ba ya kishin uwarsa mahaifiya! Wallahi da ace ba a gida na haifeka ba Yassar da yau zan ce kai din shege ne ba jinina ba!"

"Ya isheki Maryam!"

Suka dubi mai magana, Abba ne wanda ya shigo tare da Anti Maijidda don ta nace akan lallai ya kamata Abban ya hada su ya kuma ba Mami hakurin rashin sanar da ita, duk ta fadi ne don a samu maslaha a zauna lafiya wanda ba ta da tabbas a kai. Ta ci ado cikin atamfarta Holland mai golden da Wan ratsin ja, ta yafa mayafi ja a kafada sai baza ?amshi take hakanan shima Abban da ya yi shirin fita aiki. Ina wuta Mami ta tsoma wadannan bayin Allahn biyu? Haka ta ji a zuciyarta, sai ga wasu zafafan hawayen ba?in ciki wanda ba ta shirya musu ba sun zubo saman kuncinta. Kai Yusuf an yi dattijon banza, wannan cin amana da ya yi mata ba ta jin an taSa yi nata irinta ko zamanin budurcinta.

Shi kuwa Abba ?arasowa ciki suka yi, ya dubi su Yassar fuskarsa a Waure. Su kuwa gaba daya suka nutsu, Futuha dai kallon da take yiwa kowane maza na marasa al?awari da amana irin mijinta, a yau da ta ga Abban da Anti Maijidda a tare, irin kallon da ta yi musu kenan. Ta ji mugun tsanar Anti Maijidda a ruhinta, ta kasa ma kallon Abban tsabar taya Mami kishi. Wannan ai yaudara ce, a cewarta.

"Me ya hanaku shirin fita kasuwa?"

Yassar ya Wan sosa ?eya.

"Yanzu zamu yi Abba. Dama saboda Mami.."

"Babu ruwanku a cikin wannan lamarin, ku fice ku shirya. Shi kuma ?assim yana ina?"

Suka rasa ta yanda za su ce da Abban akan ?assim, ko kadan bai kwana a gidan ba.

"Yassar an tashi lafiya?"

FaWin Anti Maijidda tana dubansu dakyau. Mami ta watsa mata banzan kallo. Shi kuwa Abba ya kara dubansu.

"Don ubanku ba ku iya ku gaishe da ita ba?"

Ba musu suka gaida ta ta amsa da murmushi, Futuha kuwa ta ?i ko magana sai Tasleem ce da gaisuwar don ita yanzu ta fi damuwa da matsalar kanta akan ta wasu. Nata ma ya ishe ta.

Su Yassar suka fice har sannan Mami ta kasa koda tari, ta ma rasa me za ta ce ga Abban na wannan rainin hankalin da yake yi a gabanta.

"Kai ku bar nan zan yi magana da mahaifiyarku."

Ba musu Tasleem ta dauki Anisa dake kwance saman kujera ita ko Futuha ta rarumi jakar hannunta suka wuce daki.

"Maryam zauna ina son magana da ke."

Mami sai a lokacin ta saki wata dariya gami da tafa hannuwa. Gashinta kamar na sabuwar mahaukaciya kasancewar babu kitso duk ya mi?e tsaye, daga ita sai kayan jiya wanda har a sannan ba ta cire ba.

"Ni dai Yusuf? Ni Maryam ka ke son magana da ita? Ai babu sauran abin da za ka cemin, azzalumi maci amana."

Ya maida duba ga Maijidda dake tsaye tana kallon ikon Allah.

"Kin gani ko? Ai na faWamaki ba za ta saurare ni ba. Muje kawai."

Cikin salon kissa Anti Maijidda ta ce.

"Ranka ya daWe, daga ni har Maryam karkashin ikonka muke. Idan ka zartar dole mu bi umarninka. Don Allah kada wannan shirmen da take yi ya sanya ka fasa abin da ka zo da niyyarsa. Ke kuma Hajiya Maryam ina ke ina faWa da abin da Allah ya riga ya zartar? Ki samarwa zuciyarki nutsuwa mu zama ?oramu masu sanyi wajen hutawar mijinmu, mu samar da farin ciki a rayuwarsa da na iyalinsa."

"Uban uwar farin ciki! Nace maki uban uwar farin ciki Maijidda! Makirar banza makirar wofi! Kedai wallahi ban taSa sanin ba?ar mayya ba ce sai yanzu. Dama ni nasan tun kafin ki kashe tsohon mijinki Babayo kike bibiyar mijina. Ai da biyu kike zuwa gidan Jamila! Tsohuwar kwartuwa, ina maki albishir da kin sanyo ?afarki a gidan masifa da bala'i. Na rantse sai kin gwammace zaman cikin kabarinki akan wannan gidan nawa da kike ciki. Mu zuba daga ke har shi daidai nake da ku!"


Daga haka buguzum-buguzum ta nufi hanyar daki sai kuma ta dawo a guje ta daka tsalle ta sanya hannu a bakinta kira take.

"Hooo kun ji kunya! Hoo kun ji kunya wallahi! Kwartayen banza! Tirrr!"

Daga haka ta yi dakinta ta rufe ?ofa ta bar Maijidda da buWe baki shi kuma Abba na aikin girgiza kai kawai.

"YallaSai, anya ?alau take? Gaskiya ya kamata a kira likita ya duba ta. Kada fa wannan abu ya zautar da ita."

Abba ya dan yi murmushi mai ciwo.

"Kar ki damu Jidda, Maryam ce, za ta aikata fin haka. ?an kiramin yarannaki ina son magana da su."

Ta amsa da toh sannan ta nufi dakin su Tasleem kanta tsaye. Kunnuwanta ya yi mata kyakkyawan ji inda Tasleem ke ikrarin ba don cikin dake jikinta ba tsaf za ta haWa kaya ta shiga duniya. Wannan kalma ta ciki ya sanya Maijidda cikin fargaba, ta kuwa shiga kai tsaye.

"Ciki Tasleem? Ciki kike da shi?"

A firgice Tasleem ta dube ta, ta kasa magana. Matar tun can taba da mugun kwarjini da ba'a iya yi nata fitsara komai ?an?antarta balle kuma yanzun da take matsayin amaryar babanta ta jiya jiya.

"Ba maganarki muke yi ba."

Futuha ta bata amsa a fusace don ji take inama ta yi mata dukan tsiya. Daga dai wannan ba ta jin akwai wata tsiwar da za ta iya yi. Anti Maijidda ta sauke ajiyar zuciya, tabbas ciki ne da Tasleem, sai yanzun da ta tsura mata idanu ta hankalta. Ta bar zancen tunda yanzu ba hurumin yinsa bane.

"Ku fito mahaifinku na son ganinku."

"Toh." Tasleem ta amsa da sauri, ita yanzu gaba daya jikinta ya yi sanyi, tsoronta kar ta sanar da Abba batun wannan ciki, ta mayar da zumSulelan hijabin da ya zama na yawonta na dole, sai ta ji dama ace da ta shigo dakin ba ta cire

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login