Showing 126001 words to 129000 words out of 189325 words

Chapter 43 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

247

da Baba Amina, haka ya yi ta yiwa Humaira nasiha. Hakan ya sanya tsantsar so da kaunarsa wadanda ba ta san mafarinsu ba suka shiga ratsa ta sosai. Ya karashe zancen da fadin.

"Yauwa, kuma bana son kina yin asarar hawayenki musamman da yake bana kusa."

Ta Wan russunar da idanun kamar yana kallonta saboda jin nauyin maganarsa.

"Bari na kyaleki ma yi magana anjima in sha Allah."

"Toh, na gode a gaida mutan gidan."

"Zasu ji, nace ba?"

"Naam?" Ta amsa gami da tattara nutsuwarta don a sautinsa ya nuna ko ma mene zai fadi nada matukar muhimmanci.

"Ina matu?ar kaunarki."

Sai ta sauke ajiyar zuciya har tana jin tsikar jikinta na mi?ewa, tana son furta masa ita din ma hakan ce a wajenta amma wani kunya ya hanata aikatawa. Sai kawai ta ji Wif ya yanke kiran. Ta numfasa kafin ta ja ?afafunta zuwa ciki duniyar na mata wani irin dadi ga kaunar Fadeel dake ?ara tsuma ta.

***
A Sangaren Fadeel kuwa, ajiye wayar ya yi jikinsa duk a mace saboda shauki da kewar Humaira da ya mamaye shi lokaci guda, har yanzun yana shakkar kada wani abu ya sauya zuciyarta daga gareshi, sati ukun da kwanakin da suka yi saura jinsu yake tamkar shekaru duk kuwa da cewar a zahiri ga Ibb na ta faman tashi faWi wurin ganin an haWa dukkan abin da ya dace dangane da lefe da ma kuma list na wadanda zasu gayyata. Fadeel din shima sosai ya maida hankali ga ginin gidansa wanda an kammala komai sai kayayyakin furniture da yake sanyawa don al?awari ne ya daukarwa kansa da yardar Allah sai dai Humaira kawai ta shigo gidansa amma ba ya bukatar a yi mishi hidimar da babu wanda zai mora sai shi sai kuma matarsa. Ita din yake so da kauna ba komai ba.

A wannan lokacin ma zaune yake a falon Ibb din wanda yake amsa wayar Daddy, ya yi shiru cikin tunanin Humaira yana mai murmushi idanun a rufe ruf. Ba zato ya ji an wurgo mishi filo, ba kowa ba ne sai Ibb.

"Allah ya sauwa?e maka kai kam Romeo. Ina ce shirin aurenka ake yi da yarinyar nan? Toh mene ne kuma na wannan dogon tunanin kamar ba yanzu ku ka gama waya da junanku ba?"

Fadeel wanda tun jifa da filon ya wartsake, Wan harara ya wurga masa.

"Toh sannu, kai me za a kiraka idan ka kira ni da Romeo? Mutumin da hatta da gabatar da lakca ba ta hana shi amsa wayar Madam kamar ba daga gidan ka fito ba."

Murmushi Ibb ya yi kaWan.

"Ni yanzu ba wannan ba, ya ake ciki kai da mutuniyar taka?"

Shi din ma Fadeel martanin murmushin ya maida masa gami da kwantar da kai jikin kujera.

"Alhamdulillah, akwai cigaba kwarai ba kamar baya ba. Kai ba ka ga alamu ba?"

Jinjina kai Ibb ya yi.

"Na gani tabbas. Amma ba anan gizo ke sa?ar ba, mu dai fatan Allah yasa ba Sangare guda ke so ba."

"Ina da ya?ini da tabbacin yanzu tana sona, sai dai ta kasa furtawa ne saboda dalilinta. Kai ni koda babu son daga fanninta, zan koyar da ita na tarbiyyantar da ita soyayyata. Har yanzu kana tantamar irin kaunar da nake yi mata wai?"

Ibb na ?ar dariya ya girgiza kai.

"Ko kusa, na san ai kai tuni ta shafe babin kowace mace a zuciyarka. Hakan nada kyau. Allah dai ya sanya alheri."

Fadeel ya amsa yana sannan ya sanar da shi haihuwar Ummita. Sosai Ibb ya tausaya mata.

"Ya ake ciki batun binciken can?"

?an yarfa hannu ya yi.

"I dnt know, ban yi waya da shi ba, kuma bai kirani ba. Amma a satin da ya wuce ya bani tabbacin da alamun nasara don suna bincike akan accounts din da aka bude na whatsapp da instagram har da facebook da sunan Feedy Baby. Ya kuma ce an soma samun bayanai akan ta don ba ta rufe akawun din ba na instagram ta cigaba da amfani da shi a Soye, hakanan whatsapp, yanzu dai su na monitoring kowane motsinta."

Ibb ya yi fatan nasara, haka suka yi ta tattaunawa har dai Salma ta shigo ta sanar musu abinci ya kammala wannan ya katse su suka mi?e.

***
Mami gaba daya ba a nutse take ba, Wizzy ya jaddada mata cewar sai ya dauki fansa a kanta ko kuma ya tona mata asiri matu?ar ta hana shi gudan jininsa saboda yana tambayarta ko an haihu ko aa ta yi mishi ihun ya rabi da ita babu ruwansa. Wannan ne shima ya fusata shi har ya kaifafa harshe a kanta ya yi mata munanan kalamai. A karshe dai dole haka ta bar asibitin ta kkma gida don samun damar yin tufka da warwara.

***
Ummita kuwa kwanansu Waya aka sallamo ta. Ko ta ya ya? Oho, sai ga makwafta na Sullowa ganin jariri, aka rasa wanda ya sanar da su. Jannat kuwa ko dakin su Ummitan ba ta shiga. Tasleem zuwanta daya ta koma, dalilin jego ne ya sanya Abba bai yi mata faWan rashin nuna kulawa ga ?ar uwarta ba. Ita kuwa Futuha Abba ya yi rantsuwar kada ta sake a nan kusa ya ga ?afafunta a gidansa, kuma ya tabbatar mata muddin ba ta goge dukkanin shafukanta na kan yanar gizo ba zai saSa mata. Dolenta babu yanda ta iya duk da irin tara jama'ar da ta yi a kafafen musamman Tiktok hakanan ta shafe su don Mubarak na lurar wa Abba ko ta aiwatar ko a'a.

Anti Maijidda ta zo bayan Ummita ta cika sati da haihuwa, ta Wan ji dadi ganin yanda ta kwantar da hankalinta ta ke kuma ba yaron kulawa, idan an ce mata kafin haihuwar za ta yi haka ba za ta yarda ba. A ranar Anti Maijidda ta tattara ta bar gidan domin ta rantse ba za ta kwana a gidan da Mami ke cikinsa ba.

***
Mami ce zaune a falon Abba cikin amsa kiran da ya yi mata don su yi magana mai muhimmanci.

"Ina sauraronka." Ta yi furucin ciki-ciki, tun sadda Abban ya ce ba zai taSa hana Fadeel auren Humaira ba ta ke jin haushinsa ga uwa uba takurar da ya soma yiwa yaranta. Babu dama Yassar ya kai sha biyu a waje sai ya bude masa wuta kamar ya ari baki, wai ina yake samun kudaden da har yake shigar tsadaddun kaya yake yawon fita taWi? Ga Futuha da gaba daya ya yi mata geji da gidansa, hakanan Dawud shi ma ya hana shi mu'amala da wasu abokansa Sata gari. ?assim kuwa koyaushe yana gidan makwafta wurin abokansa yaran gidan, haka zasu ja shi yawo wuraren sha?atawa iri iri na masu kudi a yi ta kashe masa kudade yana shigar kece raini, a yau din ma ganinsu da Abban ya yi da matasan gidan uku wadanda aka yiwa tambari marar kyau har ana zarginsu da shaye shaye da abubuwa barkatai, Abban har marinsa ya yi a gaban Mamin, wannan ma ya taSa zuciyarta kaca-kaca don haka take cika da batsewa ?iris ya rage ta fashe.

Ga Abba kuwa bai damu da yanayin dake saman fuskarta ba ya soma magana.

"Sanin kanki ne auren Mamana ya zo sai dai yanayin da muke ciki ya hana a yi abin da ya kamata na shirye-shirye, ita dai a satinnan za ta je Nijar ta yi musu sallamar aure, iyayen yaron da shi kansa sun jaddada min ba sa bu?atar koda tsinke daga wajenmu, za su yi mata komai na gidan aure iyaka a kai musu ita amma matsayinmu na masu mutunci ba zamu naWe hannuwa hakan ta kasance ba, ko ya ya mu yi mata wasu kayayyakin kamar daga na kicin da dai sauransu. Ku ne mata, kun fi sanin abin da ya kamata a yi. Abu na gaba kuma ?arshen satin nan mai kamawa za su kawo lefe."

Zantukan suka shiga tafarfasa zuciyar Mami, ji take yi tamkar ta yi fiffike ta dira a jikin Abba ta sha?e wuyansa har lahira. Daukaka dai Waukaka wanda ta sani shi ne abin da ya iso rayuwar Humaira? Toh wai tana mene ne haka? Kai jama'a.

"Da sake!"

Ta furta a fili tana wani irin tsuma kamar na zakanyar da ta wuni ta kwana ba ta ci ba. Abba cikin rashin fahimta da yi mata uzurin Sacin ran da take tattare da shi a yinin ranar ya sanya shi kai zuciya nesa ya jefamata tambaya.

"Ban fahimceki ba."

Ta dube shi tsakar ido, fuskarta muraran ta bayyana abin da ke cin zuciyarta murya a sama ta ce.

"Eh nace da sake! Ba za ta saSu ba wallahi! Muddin ina raye ba zan bari Humaira ta auri dan iskan yaron nan ba mazinaci!"

Kalmar mazinaci ta yi matukar girgiza Abba har sai da ya ji wata iriyar faWuwar gaba. Salati ya yi da karfi yana nuna Mami da yatsa dake kakkarwa.

"Maryama ki tsoraci Allah, kar tsanar yaron nan ya kai ki da daukar hakkinsa? A ina kika gani da idanunki yana aikata zina? Wai Maryama meke damunki? Wannan sauyin da kike nunawa na menene?"

Ta Wan yi jim tana girgiza ?afafa kamar ta karya ta, so take ta ce masa sauyin na ubanka da uwarka ne amma kuma tana tan?wasar kanta gudun lalacewar aikin shekara da shekaru, don haka sai ta rasa mafita, bakinta kuma ya Winke, kawai sai ta fashe masa da kuma.

Humaira dake tsaye a ?ofa ri?e da jug wanda ta yiwa Abba lemun cittar da ya sanya ta, tun sadda Mami ta soma ambaton kalmar Da Sake! Take tsaye kamar an Waure mata ?afafunta ta kasa motsawa. Komai ya shiga kunnuwanta hatta da kiran Fadeel mazinaci da Mami ta yi. A yau Waya kuma karo na farko da ta ji a ranta Mami ta ba ta haushi dagasken gaske.

'Mami lokacin da aka nunawa abu tsana, lokacin zuciyata take tafarfasa saboda kaunarsa. Kiyi hakuri, Fadeel koda mazinaci ne zan jure tarayya da shi, ballantana kuma zuciya da ruhina su na karyata kalamanki gareshi.'

Wannan duk zantukan zuci ne da Humaira ke yi lokacin da ta juya ta soma tafiya da nufin maida haWin firij har zuwa sadda za su kammala tattaunawa. Haka ta koma Wakinsu zuciyarta a Sace, Raihana da Ummita da kuma Sa'ade bazawarar Wiyar Baba Amina dake kula da Ummita suka zubamata idanu.

"Lafiya Humaira?" Har su na haWa baki wajen tambayar, sai kawa ta girgiza musu kai da murmushin ya?e bayan ta yi dabarar dauke ruwan hawayen da ke kokarin zubomata.

"Ba komai."

"Haba Amarsu, tun ma ba'a yi komai ba?"

Fadin Raihana cikin son kawar mata da damuwa da bagarar da zancen. Su Ummita suka Wan dara. Ita dai ban da murmushin dole babu abin da ke saman fuskarta.

***
Mami kuwa sosai suka fafata da Abba don ta rantse ita dai ba zaa yi auren ba, wannan ya sa Abba ransa Saci suka samu mummunan saSanin da har sai da ya kira Baba Amina a waya da zummar ta zo ya sanya ta hidimar auren Humaira. A cewarsa shima yana da ?ar uwa.

Mami ta wuce dakinta a fusace ta rufe ruf, kanta take duba ta madubi ta yi kwafa.

"Lokacin da za ka mutu yarana su mallaki arzikinka ya yi Yusuf. Idan har tsafi gaskiya ne sai na kashe ka."
Ta furta a kaifafe.
***
Mami ta ga abin na Abba dagaske ne, a gefe ga Humaira dake shirye-shiryen tafiya Nijar sai Woki take yi saboda tsabar jimawar da ta yi ba ta je ba. Abba kuwa kamar yanda ya ce ne, Baba Amina ya kira suka yi magana ya ba ta ragamar siyayyar kayan kicin wanda a farko ta nuna sam ita ba za'a yi haka ba idan an yi ba'a yiwa Mami adalci ba. Sai da Abban ya Sata rai ya zayyane mata yanda suka yi, da kanta ta samu Mamin da zancen amma Mami ta buWe mata wuta da zummar babu abin da ya shafe ta da auren Humaira da Fadeel. Jiki a mace da kuma Wumbin mamaki Baba Amina ta dawo a dole ta karSi wannan ragamar ta kuma taushi Abban akan ya yi mata uzuri tunda hakan ba ta taSa faruwa tsakaninta da yaran ri?onnata ba.

Humaira kuwa sosai Mami ta dauke mata wuta, gaisuwarta ciki ciki take amsawa, hakanan ko tsinke ta bar sa Humaira dauke mata balle ta sanya ta aiki. Raihana da Ummita lamarin duka ya dame su. Humaira ma tana jin zafin hakan, duk ta bi ta rame amma ba ta jin za ta iya yiwa Mami alfarmar rabuwa da Fadeel alhalin ba ta da kwakkwarar dalili ba. Idan har a yau ta yi yanda Mamin ke so tana da tabbacin alhakin Fadeel sai ya kama ta. Ba kuma za ta taSa samun rayuwar jin dadi da walwala ba a duniyarta.

A? yau ma tana zaune tana gyara kayanta cikin jaka tana yi tana sauraron Raihana da Ummita dake faman zantawa akan lefen da za'a kawo washegari wanda ita kuwa ana kawowa da kwana Waya za ta wuce Nijar. Ba ta ce musu uffan ba, sai bayan fitar Raihana ne Ummita ta dube ta.

"Ya kamata ki je ki sami Mami kuyi magana Humaira. Haka za ki tafi tana fushi da ke?"

Ta ajiye set din kayan da take shirin sakawa a akwati a saman cinyarta bayan ta zauna gefen gadon jiki a sanyaye.

"Toh ya zan yi Ummita? Kina gani fa Mami ko gaisuwata ba ta amsawa."

Ummita ta girgiza kai.

"Hakanan za ki mayar da komai ba komai ba ki je ki kara ba ta hakuri ki lallaSa ta. Mun yi mata uzuri saboda sanin da muka yi cewar kowane DAN ADAM ajizi ne. Mu kara yi mata mu gani."

Sauke nannauyan ajiyar zuciya ta yi.

*"Shikenan, bari na je na gani ko za ta saurare ni."

?an murmushi Ummita ta sakar mata na karfafa gwuiwa. Wannan ya sanya ta mikewa ta nufi dakin Mami. Ta shiga da sallama a bakinta amma babu amsa, don ta tabbatar ko ba ta dakin ne ya sanya ta Waga labule ta shiga. Mamin hankali kwance tana zaune gefen gado sai faman danna wayar hannunta take. Abin bai ba Humaira mamaki ba, ko ba komai zuwa yanzu dama ya ci ace ta saba da hakan. Don haka ta daure ta karasa ta durkusa a gefe, Mami kuwa tun shigowarta ba ta ko kalleta ba sai ma fuskarta da ta tamke tamkar hadari ya haWo.

"Mami ina sane da cewa har yanzu kina fushi da ni, na zo ne domin na ?ara ba ki ha?uri akand laifin da ban san na aikata ba."

Wani kallo ta Wago ta watsa mata wanda ya sa Humaira sunkuyar da kai gami da yin shiru.

"Kin zo ne don ki nunamin ke din ba ki da mutunci kuma butulu ce?"

Jin haka sai abin ya daure mata kai.

"Mami har ga Allah ban san ta?amaiman laifin da nayi ba."

"Dakyau! Ai idan ba ki yimin wannan butulcin ba, ba ki cika Wiyar Fatima ba."

Maganar ta daki zuciyar Humaira da har sai da ta ?ara buWe idanunta wurin kallonta sosai. Mami me yawan yabon halayen Mahaifiyarta, yau kuma ita ce saboda son zuciya irin nata ta ke kushe ta?

"Kiyi hakuri Mami, kiyi hakuri idan har da abin da na maki mai zafi amma domin Allah kada laifina ya ture kyawawan yabon da Mahaifiyata ta samu a wurinki. Babu abin da take bu?ata a wurinmu face fatan alheri."

Muguwar harara ta watsa mata, kamar ta ce fatan alherin uwarki sai kuma ta danne zuciyarta dakyar.

"_Kar ki yi saurin rushe komai don ba alheri ne gareki ba._ _Nace maki mu bi komai sannu har mu cimma gaci._ _Aure dai ki kwantar da hankalinki ba zai faru ba kamar yadda Babandi ya tabbatar mana._"

Maganganun Hajiya Lubna ke yawo a ?o?on ranta, don haka sai ta yiwa Humaira nuni da ?ofa.

"Ficemin a Waki tun ban kwaWa maki mari ba. Ke har kin kai ki faWamin abin da ya dace da ma wanda bai kamata ba? Ko kin ga ni Maryam na shiga shirgin aurenki da wancan lalataccen? Toh kamar yanda ban shiga ba ki je can ku ?arata ke da shi, ai kowa ya san abin da za ku aura daga ke har shi."

?an shiru Humaira ta yi tana nanata kalaman ?arshe na Mamin a zuciyarta idanunta kuwa ?urr a kanta, to me take nufi? Gaba daya ta kasa fahimtar manufarta da kuma inda ta dosa. Sai da Mamin ta yi mata wata tsawa kan ta fice mata a Waki sannan ta mi?e gwuiwa a matukar sanyaye ta fita tana fidda hawayen bakin ciki. Tunanin ba Ummita kadai ce a Wakin ba saboda lokacin yi mata wanka ya yi sai kawai ta shige kicin ta zauna tana kuka sosai. Tana kara gas?ata cewa dai wasu sabbin halayyar Mamin da ba ta sani bane suke bayyana a muraran. Lallai ta fara sha?ar ?amshin gaskiya a kalaman Anti Maijidda, za kuma ta so tasan ko menene ta sani akan Mamin har ta kasa aminta da zuciya Waya take zaune da Ummita da ma ita kanta. Sai da ta kammala kukanta ta share hawaye ta koma sashinsa bayan ta wanke fuska amma ina, duk da haka Ummita da Raihana dake zaune ri?e da Ahmad a hannu wanda ya sha wanka suka fahimci akwai ta yi kuka sakamakon sauyin da fuskarta ta yi.

"Lafiya Humaira? Me aka yi? Kin bar waya tun Wazu angonnaki ke faman kira."

Ta yi murmushin ya?e kafin ta amsawa Raihana.

"Babu komai, ina wayar?"

Ta mi?a mata tana mai ?ara jefamata tambaya don ita sam ba ta yarda ba, a ?arshe ta ce.

"Mami ce ko? Don nasan ba kya shiga sashin Anna balle nayi tunanin ko..af ko kin haWu da Anti Jannat ne? Ba ta jima da fita a dakinnan ba ko kun haWu?"

"Ke dai Raihana ko ma wacece kuma ko mene ne tunda dai ya faru ba shikenan ba?"

Ta Wan yatsine fuska.

"Allah ya kyauta dai." Ummita ta amsa da amin. Sai da Raihana ta bar wurin ne ta kwashe duka yadda suka yi da Mamin ta sanar mata. Ummita yarinya mai kaifin basira da kwakwalwa tsaf ta fahimci manufar zantukan Mami amma sai ta Soye ga Humaira duk kuwa tana tunanin watakila itama ta fahimta kawai dai ba ta son fassara zancen yanda zai yi mata ?una a zuciya ne.

***
Washegari kuwa ya kama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login