Showing 114001 words to 117000 words out of 189325 words

Chapter 39 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

250

amanarsa, amma kuma wannan ta tsani ma a yi mata batun abin da za ta haifi duk kuwa da rayuwar da take gudanarwa ma?ale da shi a jikinta.

Ummita dake tsane jikinta tana kallon Humaira ta madubi wacce ta zubamata idanu ta yi Wan murmushin ya?e.

"Kallona kike kamar irin kina bankwana da ni zan mutu wajen haihuwa ko?"

Maganarta ta girgiza zuciyar Humaira sosai, ta ji nan da nan hawaye sun cicciko mata ta kauda kai daga dubanta.

"Allah ya kiyaye, hakan ma ba zai faru ba da yardar Allah. Don Allah ki daina yawan irin waWannan kalaman basu da dadi. Ke dai ki yi addu'ar rabuwa lafiya da abin da ke cikinki."

Murmushi kawai Ummitan ta yi wanda hausawa ke kiransa da ya?e daga nan ba ta ce uffan ba, itama Humaira ba ta son zancen don haka ta mi?e ta dauki zani da brush ta yi banWaki.

***
Yarinyar Tasleem sak mahaifinta har duhun fatar, haka dangin mijinta suka dinga zarya a gidanta don tuni aka sallameta a yammacin ranar da ta haihu wato Asabar domin lafiya lau ta haifi Wiyarta. Ta so kwarai ta je gida wanka amma Mami tana sanar da Abba ya ce sam aa, babban dalilinsa kuma kada a je a yi ta zuwa ana ganin Ummita ana ?ara mata wata damuwar ta daban. Wannan ya sanya hakanan ba don ta so ba ta zauna sai Ladidi ce ta je mata zaman wanka don dama bazawara ce mijinta ya rasu sai ko marayun yaranta da ta bari wajen tsohuwarta.

Humaira ba ta le?a ta ba sai da aka yi kwanaki uku, kullum dai ita ke girki ana kai wa. Sai da Mami ta yi magana sannan ta shirya ta je. Raihana na makaranta su na rubuta jarrabawar mock daga nan kuma ba jimawa za ta soma WAEC.

Fuska a yatsine Tasleem ta amsa gaisuwar Humaira gami da fadin.

"Sai yau kika ga damar zuwa kenan? Ai da ma kin bar shi gaba daya."

Ta kuwa ji zafin maganar ta ji dama sam ba ta zo ba. Wato ba ta ga bautar girkin da take yo mata ba ana kawo wa ba sai kawai ?orafin ba ta zo ba. Don haka ta ?i tankawa ta mi?awa Ladidi jaririyar don a yi mata wanka. Ba ta wani jima ba ta fice abin ta. Tare suka wuce da ?asim a mashin Winsa don yanzu sam Abba ba ya kaunar shigarsu ?an sahu. Adalilin haka ne ma yake ?o?arin siyar ?aramar motar fita unguwa bayan tasa ta amfaninsa dake gidan.

Wannan haihuwa ta Tasleem ita ce ta yi sanadiyyar zuwan Jannat garin Kano da kyakkyawan albishir na dawowar da zasu yi Kano ita da mijinta da ma yaransu a dalilin sauyin aiki da ya samu ta zo wa Tasleem. Ta kuwa ji dadi don har tsalle ta yi ta rungumeta har sai da ta yi mata tsawa akan ta bi a hankali.? Futuha ma ranar da Jannat ta zo itama ranar ta ?ara zuwa na biyu, nan take ba su labarin gidan da Yakubu ya gina mata a sama kaWan da su Tasleem. Ko kusa Tasleem ba ta yi wani murna ba sai murmushin ya?e saboda ba?in cikin cigaban da Futuhar ke ta samu a rayuwa, ita kuwa Anti Jannat sosai ta ji dadi ta taya ta murna.

***
Fadeel ya ?urawa matashin da ya ci suna Joshua idanu, siriri kuma dogo ba?i wuluk. Kallo Waya za ka yi mishi ka san ya ?are saboda tsabar shan sigari da kuma kayan maye. Sar?a mai tambarin cross ce a wuyansa. Ya dubi Ridwan ya ce.

"Wannan dai shi ne wanda ya yaWa rumours akan su Humaira?"

Ridwan ciki da tabbaci ya gyaWa kai.

"Shakka babu shi ne, komai na shaidun da muka samu daga abokansa ya nuna hakan kuma shi da? bakinsa ya gas?ata ya kuma ce sanya shi aka yi amma a yi hakuri."

Mamaki ya ?ara kama Fadeel.

"Amma kuma YallaSai alamunsa sun nuna tamkar bai ma jin Hausa gaba daya."

?ar dariya Ridwan ya yi.

"Haka kowa zai yi zato, amma shegen ko wani Bahaushen ba zai nuna masa Hausa ba. Hatta karatunsa a kwalejin ilimi na Kano abinda ya karanta kenan Hausa da English. Ko ba haka ba?"

Ya watsa tambayar ga Joshua da ya yi tsuru da idanu yana jinsu. Jiki a sanyaye ya amsa.

"Hakane Sir."

Fadeel ya daure fuska. Ya ji tamksr ya sha?e wuyan Joshua ya huta, ba iyaka haushinsa kawai yake ji ba akan abin da ya aikata aa, har ma da Satancin sunan da ya kusan haddasawa ya rasa Humaira gaba Waya a wurin Alhajinsa domin ya tabbatar masa idan zargin da ake yi ya tabbata to fa sai dai ya ha?ura da Humaira. Ba shi kuma ya samu nutsuwa ba sai da shaidun da suka tabbatar da satar suka rinjayi masu ?aryatawa. Wannan dalili kuma ya sanya Alhaji ya sauko akan? bakansa ya kuma ce nan da wata Waya za a yi aurensa da Humairar muddin dagaske iyayenta suke za su ba shi ita. Shima ya aminta da hakan, hakanan Abba ya san da zancen amma ko kadan bai sanar da wani a gidan ba.

"Yanzun ka shirya faWa mana wacce ta sanyaka aikata hakan?"

Tambayar da Ridwan ya watsa masa kenan. Ya sunkuyar da kai kirjinsa na dukan tara tara amma gwara ya tona asirin ya huta don bai ga hanyar tsira a hannunsa ba. Miyau ya haWiye ma?wat sannan ya ce.

"Wata ce ta haWa ni da wata mata mazauniyar ?asan Egypt ta ce tana da wani zazzafan aiki wanda idan har nayi mata komai ya tafi yanda take so za ta yimin kyautar dubu dari biyu."

Ridwan da Fadeel suka dubi juna sannan suka maida hankula gareshi.

"Ya sunanta? Ka ba mu labari tiryan-tiryan don mu san abin da ya faru."

Joshua ya kasa cewa komai sai zufa.

"Look Joshua, ba wani abu muka ce zamu yi maka ba, muna son mu je root din matsalar ne don mu magance ta. Ka fito ka faWamana su waye ke da hannu a ciki."

Ya jinjina kai cikin aminta da zancen Ridwan ya soma magana.

"Nidai ina tare da Babana ne a nan Kano, Mamana asalinta ?ar ?asar Ghana ce. Toh tana aiki a Misra ne gidan wasu larabawa ne kamar ban dai sani ba. Toh matar ce ta ba wa Mamana aiki kan ta nemo mata wanda ta san zai iya yaWa labarin ?arya akan case din Ummita da Humaira kuma itama ba aikinta bane sanya ta aka yi ta nemo wanda zai yi a biyashi. Wannan dalili ne ya sa Mamana kirana ta yimin bayanin komai, nan da nan batare da dogon tunani ba na aminta zan karSi aikin nan. Tun daga nan magana ta koma tsakanina da ainihin matar da zan yiwa aikin ba Madam din da Mama ke aiki a gidanta ba, ta instagram oage dinta muka soma magana na lura sabon buWewa ne shafin nata, anan ne ta ke yimin bayani sosai na aikin har ma da ?ara jaddadamin wadannan kudaden da za ta bani. Toh shi ne na shirya labarin na aikamata ta lambar da ta turon na can Egypt ta ce da zarar na kammala na aikamata ta whatsapp, hakan kuwa aka yi nantura mata, sai da ta tabbatar komai ya yi kafin ta yimin umarnin samun lambar da ba a san ni da ita ba na yaWa. Ta sanya na buWe shafukan media sababbi da ba a sanni da su ba, har sai da labarin ya yaWa yanda take so sannan ta bani umarnin rufe dukkan akawun din. Kuskuren da nayi sai na sanar da abokaina su huWun nan da ku ke gani, suka goyamin baya amma suka ce sai na ba su kasonsu a kuWin da za'a ban, akan kuWin mun samu matsala da su. Sai kuma da aka sa kuWin da ya ninka na aikin da aka bani cewar ana neman wanda ya aikata laifin shi ne suka ci amanata suka fallasa. Kun ji yanda abin ya kasance. Ita kuma matar tun bayan lamarin ta yi blocking dina bayan ta sallame ni. Mamana ta ce kada na ?ara tayar da zancen bisa umarnin Madam dinta, kuma kada na bari Babana ya sani. Sannan ni ko sunan wacce ta sanya ni bansani ba, Maman ba ta taSa ambatonta da sunanta ba. Wannan shi ne abin da ya faru YallaSai. Ku gafarceni."

Fadeel ya dun?ule hannunsa bai ce komai ba, Ridwan ya yi umarni aka mayar da Joshua ma'ajiyarsa sannan ya dubi Fadeel.

"Ita kuwa wannan mene ne dalilinta ko ribarta na aikata hakan? Abu Waya dai da na fahimta, ko wace ce tana da relation da su biyun nan. Hakanan kawai ba za ta sanya a yaWa rumours akan su ba."

Fadeel ya jinjina kai, tabbas hakane amma kuma shi a iya tunaninsa kamar dai ba su da wani dangi a ?etare.

"Hakane YallaSai. Yanzu mene ne abin yi?"

"Abin yi Waya zuwa biyu, zamu karSi lambar ita Matar da ma Mamansa idan ta kama. Idan binciken zai kaimu har can gidan su Humairar toh sai a je."

"Shikenan hakan yayi. Zan yi waya da Abbansu na sanar da shi komai."

"Ok ba damuwa. Nima nan zamu yi kokarinmu."

Daga haka suka yi sallama Fadeel ya bar ofishin.

***
Ranar sunan Wiyar Tasleem yarinya ta ci sunan mahaifiyar Hamza wato Asma'u suke kiranta da Husna. Sunan da kusan rigima aka yi tsakanin Tasleem da Hamza don ta rantse sai dai ya sanya sunan nata uwar shi kuwa ya rantse ba zai fasa sanya Husna ba. Hakanan aka ci suna idanun Mai jego duk a kumbure saboda kukan ba?in cikin da ta yi, uwa uba sai ga tsohuwar budurwar Hamzan kuma yar uwarsa ta kawo mata kayan barka. Ta ci uban kyau da rantsetsan leshinta ruwan ?wai an mata adon stones. Black beauty da ita fuskarnan ta sha make up sai ?amshi take yi. Bisa shawarar Jannat ne Tasleem ta danne Sacin ranta sai ya?e. Tana ji dangin Hamzan na tsokanar budurwa da sunan Amarya amarya amma sam ba su kawo komai ba. Jannat na dariya ta ce.

"Toh kin gani ma ashe ta kusa aure kike wani tada hankalinki."

Sai a lokacin itama Tasleeem din ta Wan saki ranta. Gwara ta tattara ta yi auren ko ta huta da jarabar bibiyar mijinta da take yi. Futuha kuwa a tsaisaye ta le?a sunan ta kuma wuce da Humaira da Raihana don su taimaka mata da tattara kaya saboda kaurar da zata yi sai wani rawar kai da ?afa take yi.

Hakanan suka tattara sannan ta ce su yi gaba a mota a kai kayan tare da su don tuni an kai dukkan kayan katakonta an kuma jera, sai na sanyawarta a jiki suka rage. Wannan duk budurin da ake yi ba ta ga gida ba. Humaira da Raihana suka bi umarninta zuwa gidan, yayinda ita kuwa ta wuce gyaran gashi don ta ce gwara mutan unguwar su ganta tsaf ba raini don Yakubu ya ce mata unguwar ?an gayu ne.

***
Ummita zaune ita Waya a falo tana biyawa su Muhsin karatun hadda da aka yi musu a islamiyya, haka Mubarak ya shigo ya ris?eta. Kallo Waya kawai ta yi mishi ta maida kanta ?asa tana gaida shi don a yanzun kwata kwata ba ta kaunar ganinsa ba don komai ba sai irin kallon da yake bin ta da shi da kuma manufarsa na soyayyar da yake nuna mata, koda bai furta ba alamominsa sun nuna. Madadin ya wuce sashin Anna wurin Mami kamar yanda Waleed ya sanar mishi cewa tana can, kawai sai ya Sige da zama a falon yana duban Ummita cike da wani irin kauna mai tsafta ga kuma tausayi.

"Beauty."

Ko kusa ba ta gane da ita yake ba sai bayan ya ?ara maimaitawa. Ta Wago idanunta fuska ba walwala ta dube shi. Ya yi mata sanyayyar murmushinsa, kamanninsa da Abbansa ya ?ara fitowa.

"Gobe fa zan tafi Camp, baki da labari?"

Ta girgiza kai tana maida hankalinta kan littafi mai tsarki.

"Ban sani ba. Allah ya kaika lafiya ya sa a kammala lafiya."

Ya lumshe idanunsa ya bude da murmushi saman fuskarsa.

"Amin beauty, nagode. Sai dai zan yi kewarki."

Fadin hakan da ya yi hatta Waleed sai da ya dube shi, nan da nan ya daure fuska ya ce su je su cewa Mami ya zo. Suka kuwa mike har su na rige-rige suka bar falon. Ita kuwa Ummita ta kasa cewa komai sai faduwar gaba fat fat.

"Sun watse sun barki ke Waya ko?"

GyaWa kai ta yi.

"Beauty ba magana?"

Ta dago ta dube shi da idanunta wadanda suka cicciko da hawaye. Ba ta son har abada abin da zai tuna nata da Sahabi wanda tuni aka Waura aurensa da yar uwarsa.

"Yaya Mubarak, don Allah ka kirani da Ummita. Bana jin dadin sunan da ka sauyamin."

Ya taso ya Wan yi dur?uso a gabanta.

"Ba zan iya dainawa ba Beauty. Sai dai zan yi kokarin danne abin da ke zuciyata har Allah ya rabaki da cikin jikinki lafiya. Bana son na furta yanzu amma yana nema ya rinjaye ni. Kiyi hakuri da ni zan ?ara danne zuciyata har zuwa lokacin da ya kamata komai ya bayyana a zahiri. I am so sorry."

Wannan karon da hawaye saman fuskarta take dubansa cike da tausayinsa. Bai san masifar da yake shirin jefa rayuwarsa ciki ba. Ban da abin Mubarak me zai yi da ita, Ummitan da sunanta ya gama Saci a idanun jama'a?

"Mubarak!"

Tsawar da Mami ta dakamasa ya sanya gaba daya suka dube ta, ranta a tsananin Sace take dubansu. Ta Wan jima kaWan da shigowa falon amma sam ba su lura ba. Kaf kalaman Mubarak din na karshe a kan kunnuwanta ya yi su. Ummita ta sha jinin jikinta da irin duban da Mamin ke watsa musu.
*LITTAFIN NAN NA KU?I NE. SIYA AKAN NAIRA ? 400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645


Duk iyaka kokarin Mami ta kasa danne zuciyarta saboda abu Wayannan ba za ta iya Waukarsa ba, haWa zuri'a da Wiyar Jamila wato Ummita. Mubarak ya mi?e yana dubanta hakanan Ummita tun duban farko sai ta yi ?asa da kanta kirjinta na dukan uku uku don gani tayi ma kamar Mamin cetonta ta yi daga kalaman Mubarak wadanda suke shiga kai tsaye cikin zuciyarta tamkar mashi. Ko kusa ba ta kawo komai ba face kyakkyawan zato ga Mamin.

"Mene ne haka ne? Kar ka kara yimin wannan sakarcin. Ka ri?e abin da ke ranka kuma ka kauda shi don ba zai taSa yuwuwa ba."

Mamaki ya cika Mubarak, itama Ummita ta Wan ji maganar a ranta amma kuma ta basar. To me zai dame ta ma tunda dama ita ba soyayya ce gabanta ba? Ita ta fi kaunar ma ta mutu yayin haihuwa ko ta samu shahada ta huta da ba??an cikin duniyarta. Mubarak har ya buWe baki zai ?ara magana Mami ta dakatar da shi ta hanyar Waga mishi hannu.

"Kar ka cemin komai. Fice harkar gabanka, kai da kake da tafiya a gaba mene ne za ka tsaya kana Satawa kanka lokaci kana Satawa yarinya itama?"

"Ma.."

"Nace maka bana son jin uffan daga gareka ko? Don haka ficemin a nan."

Ya jinjina kai kawai bayan ya kara duban Ummita da aka yi sa'a itama ta Wago kai suka haWa idanu ta mayar, sannan ya fice yana ?ara ?udurtawa a ?asan ransa in sha Allahu mallakinsa ce muddin dai ta amince da aurensa.

Bayan fitarsa Mamin ta karaso ta zauna sosai a saman kujera har lokacin fuskarta ba walwala ta soma magana.

"Ke yanzu idan ma wani yace maki ki yi soyayya sai ki dube shi? Yanzu ai babu abin da ya fi maki alheri face ki kula da kanki da abin da ke jikinki har Allah ya rabaki da shi lafiya. Ummita na fi kaunar farin cikinki sama da na Mubarak, yau kika biyewa yaron nan sai ya kaiki ya baro. Ni na haife shi na kuma san ra'ayinsa da ma Wabi'unsa, ba shi da ra'ayin auren bazawa.."

Sai kuma ta yi Wif jin hasalalliyar zuciyarta za ta sa ta yi katoSara. Ummita kuwa ta fahimci tsaf abin da Mamin ke ?o?arin faWi, sai ta shiga kokwanto akan anya dagaske Mamin da kanta ke wannan batun ko kuwa dai, don haka ta Wago ta dube ta ita kuma ta kauda kai karshe ma? ta mi?e ta bar falon.? Shakka babu ita Win ce da kanta, maganar ta tsayawa Ummita a rai. Bazawara fa take kokarin kiranta? Mami da kanta? Sai kawai ta ji wasu sabbin hawayen sun kwaranyo. Zuciyarta na ce mata eh ga kuma zahiri na idanunta na kara tabbatarmata da haka Win ne amma wani Sangaren na zuciyar na kokarin kare Mamin da tunanin ajizanci na kowane Wan adam, mai yiwuwa itama suSutar baki ne saboda Sacin rai ba hakan ta so faWi ba. Wannan dalilin ya sanya ta share hawayenta ta tattara kur'anan su Muhsin ta maida kowanne a jakarsa sannan ta kwashi jakunkuna zuwa Wakinsu.

***
?aramin gida ne wanda ya ji fenti daga waje ya sha kyau, ciki kuwa kana shiga, babu batun farfajiyar gidan saboda wani tsukakken wuri ne sai famfo a gefe ga bishiyu ?ananu an mishi ado da su. Daga ciki kuwa kai tsaye falo za ka faWa, ba shi da girman da zai cinye manyan kujerun Futuha sai raba su aka yi wasu aka kai safayar Waki falle guda dake? a ?ar tsakar gidan. ?aki Waya ne a ciki sai store da kicin Winta ?arami wanda hatta da freezer dinta bai shiga ba sai a zagayen baya gefen kicin aka sanya shi. Hakanan babu matsugunin kayayyaki da yawa na wuta na amfani kicin dole hakanan suka cuccusa su da taimakon ma'aikata tsohon gidan da suka kawo kaya. Gado dai ya shiga Waki amma fa ya cinye kusan rabin Wakin. Raihana da Humaira sai kallon kallo da mamaki, ita dai Humaira ba ta tanka ba sai Raihanan da ke ta jajen lamarin da hango rikicin da zai faru idan Futuha ta ga gidan da take ta yiwa rawar ?afa har Tiktok ta yi na bidiyo tana a tayata da addua za ta tare a sabon gidan da mijinta ya gina mata, har da al?awarin za ta yiwa followers dinta bidiyon gida kamar yanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login