Showing 186001 words to 189000 words out of 189325 words

Chapter 63 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

197

ta fashe da kuka, itama Lubna nan da nan ta shaida muryar.

"Maryam! Dama akwai sauran shan ruwa a gaba? Ashe zamu kara haduwa?"

Sai kuka, ganin an musu ca da idanu ya sanya Lubna jan ta zuwa wani daki dake can kusa da garken awakai. Dakin da ko Maigadin gidan Hajiya Lubna ba zai rayu cikinsa ba. Babu komai sai katifa mai kama da gado wanda ta siya tun farkon dawowarta gidan sai ko akwatunan kayanta a can gefe. Nan suka shiga maida yanda aka yi bayan sun sha koke-kokensu.

"Uhm, Maryam naga rayuwa, saura kiris na rasa raina a garin yawon bin Bokaye. Allah ya tsaga da rabon dai zan shiryu. Sanadin haka Daddyn Kabeer ya sake ni, nan shi ne muhallina a gidannan. Matan ?annena ne amma gasunan sun raina ni wulakanci iri-iri, ban isa su dafa su bani ba sai dai na yi yanda zan yi na ci abinci. Sai nayi dakyar nake samu Kabeeru ke yimin aike. Maryam mun yi kura-kurai da dama wanda sai yanzu nake ?ara nadamarsu. Mun yi imani da abin da shima din halittar Allah ne, ba zai iya yiwa kansa ba ballantana ya yi mana. Lokaci bai ?ure ba Maryam, kamar yanda na samu na nemi gafarar mijina ya yafemin duk da ya rantse ba zan kima gidansa ba, da ma danginsa wadanda na cutar, har yau kuma nake cigaba da neman gafarar Ubangijina, kema ya kamata ki nemi gafarar mutanen da kika zalunta a rayuwa. Rayuwarnan na ?ara ganewa ba komai ba ce, yanzu ji inda nake rayuwa tamkar ban taSa Wandana wata rayuwa ta daula ba."

Mami kuka take sosai, tabbas koda a baya ba ta karaya ba da al'amarin duniyarnan, yanzu ta ?ara tsorata. Ta kuma ji dagaske za ta iya dur?usawa koda a gaban Maijidda ce ta nemi yafiyarta. Haka Lubna ta dinga yi mata nasiha iri-iri akan rayuwa.

"Idan da za ki bi shawarata, ki koma gaban Anna ki zauna."

Ta numfasa, Futuha ta sanar da ita irin ba?ar wahalar da Anna da Jannat suke ciki, Jannat ta ?ara yin wani auren tuntuni, mijin ya yaudare su da ?aryar arziki ashe bai mallaki komai ba. Lefen burga da karyar da ya haWa mata ma a washegari aka zo aka kwashe su kaf. Daga karshe ake ganewa shi ya sanya, Anna da Jannat suka turje akan sai ya sake ta ya ce shi kuma yanzu ya fara aure. Shekara guda gidan da yace nasa ne ashe na haya ne, aka zo aka kawo notis, karshe dai mutumin sai ainahin gidansa ya kai ta wurin matansa biyu wadanda kansu yake a haWe ga uban ?a?a. Jannat yanzu haka yaranta uku da shi, yan biyunta kuwa ko ?eyarsu ba ta gani sun koma zaman Saudia, inda tsohon mijinta ya ?ara samun aiki. Sai dai sukan yi waya da ita da begen son ganinta wanda Babansu ya nuna ba yanzu ba. Anna kuwa girma ya ja kwarai, hakanan take rayuwar babu yabo ba fallasa.

Mami ta kwashe labarin yanda su Anna ke fama a can ta faWawa Lubna.

"To ke ba gwara kin je kin ?arasa neman ladanki ba can? Kin kula da dattijuwarnan itama ki nema mata gafarar bayin Allahn nan?"

"Hakane Lubna, wallahi rashin sanin inda Tasleem yake yanzu shi ke cimin tuwo a kwarya. Hankalina yana kanta."

Ta fadi cikin sharce hawaye.

"Babu yanda muka iya sai addu'a, muddin dai tana raye in sha Allahu sai kiga Allah ya bayyana ta."

Haka suka yi ta tattaunawa akan matsaloli, a karshe Lubna ta aika aka siyomusu alala a makwafta suka ci suka sha ruwa. Mami dai haka ta hakura suka kwana washegari bayan sun karya ta kama hanyar Kano bayan ta raba kayayyakin da Raihana ta ba ta gida biyu ta bar wa Lubna rabi. Batun kudadenta babu su, duka sun tafi a maganin Lubna kamar yanda ta ce mata, haka ta hakura da su saboda da gaske suke kaunar junansu. Haka suka rabu da kuka kamar shikenan sun yi bankwana.

***
Ba ta san hawa ba ballantana sauka, ta dai ji motarsu ta yi wata irin wulwulawa saboda bugun da aka yi mata daga baya ta bugi wani ?arfen wutar lantarki kafin ka ce me ta kama da wuta. Da?yar aka ceto rayukan wasunsu yayinda wasu suka ce ga garinku ba a tseratar da komai nasu ba sai toka. Mami gaba daya fuskarta ta babbake hakanan hannayenta sai ko kafafunta.

Tana ihu tsabar azaba da fadin.

"Na shiga uku! Wayyo Allahna! Ashe haka azabar wuta take! Wayyo ni Maryam, na shiga uku ku taimaka ku raba ni da wannan radadin!"

Ta suma ya fi a kirga har dai aka sadar da su zuwa asibitin Murtala dake birnin Kano.

***
Anti Maijidda hankalinta ya tashi da jin labarin ?onewar Mami a bakin Futuha, dakyar da suWin goshi Abba ya aminta da batunta, ya kura kaf yaran Mamin a waya ya sanar da su maza su dawo Mahaifiyarsu na asibiti rai a hannun Allah. Kafin sati dukkansu sun halarta, babu kuma wanda bai je duba ta ba, fuskarnan babu kyan gani hakanan ?afafunta da likita ya tabbatar musu zai wahala ta ?ara taka su don ba iyaka ?unar ba kawai, sun bugu da ?arfe wanda dakyar aka Sanbarota daga jiki.

Matan kuka suke yi kwarai, duk rashin imanin mutum idan ya ga Mamin sai ta ba shi tausayi yanda take ihu da fadin abubuwan da ta aikata a rayuwa tana kuma neman gafara.

"Wallahi ba zan iyaba! Ba zan iya jure azabar kabari ba ni Maryam! Wayyo Futuha baku san ya nake ji ba! Haka wuta take?! Wallahi na tuba ku yafemin, ku yiwa girma na Allah ku kiramin Humaira da Ummita na nemi gafararsu. Ina Maijidda ina Abbanku?!"

Haka ta yi ta sumbatu iri-iri, dalilin Anti Maijidda, Humaira da Ummita suka zo hakanan shima Abba da Baba Amina, babu wanda bai zubar da hawaye ba, rayuwar Mami ta ishi bawa ishara musamman masu hali irin nata. Abin duniya ba ya Suya, mutane musamman na cikin asibitin aka dinga yaWa zantuka game da abubuwan da Mamin ta ce ta aikata. Sai da aka hana shiga wajenta saboda yanda masu son kashe kwarkwatar idanunsu ke yunkurin zuwa.

***
MURFI...

Gidan cike yake da jama'a ?an suna ana taya Humaira murnar sauka lafiya inda ta haifi Wanta namiji ?osasshe mai kama da ita sak! Su Ummita gaba daya sun hadu har Futuha wacce a yanzu ko kusa ba sa ware ta a cikinsu. Sun hada kansu gwanin sha'awa. Haka suka dinga shige da fice wurin ba abinci ba?i, Humaira wacce a yanzu take da jama'a ta ko'ina, gidan sai ya kasance tamkar haihuwar fari.

Fadeel da su Ibb suna can falonsa inda aka kai musu abinci kala-kala suna ci. Kowa ka gani zuciyarsa fari ?al. Anti Majjidda da nata tawagar su ma su na gefe ana hira da raha.

Abinda zai ba ka mamaki bai wuce yanda Murja a yanzun ta yada dukkan makamanta ba suke zumunci da Humaira. Ba dai can ba amma duk sadda wata sabgar junansu ya tashi mai muhimmanci zasu taya kansu murna. Ta gama amanna cewa wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa, ta rungumi mijinta da hannu bibbiyu tana kuma yaba abinda yake mata. Bangaren Anti Amarya itama ta sanyawa zuciyarta salama, ta saduda saboda Allah Abban Fadeel da Fu'ad ke zaune da ita, wannan ne silar da itama ta yiwa kanta karatun ta nutsu tunda ba ta rasa komai daga gareshi ba ta ke zaune da su da zuciya daya ba kamar a farko ba.?

Ta shigo gidan tana raSe-raSe, yaran da ta soma cin karo da su da ma matan dake farfajiyar gidan a zaune duka babu fuskar da ta gane ciki. Ta cigaba da taku har zuwa cikin falon gidan, tana ji wata na fadin ia kuma wannan? wacece? haka sanye da nikabi?

"Ke baiwar Allah, wa kike nema ne?"

Ta juyo tana kallon mai tambayar, Futuha ce ri?e da mu?ullayen kicin bayan ta adanawa Humaira abinci na musamman na ba?in da tace za ta yi, ta ci adon ta cikin leshi pink wanda suka yi su uku, ita da Raihana da kuma Ummita. Ta dan yi ?ibarta ta kuma washe abinta. Daidai nan Ummita ta karaso tana goye da yaronta Wan watanni takwas Affan.

"Sister ina mukulli...wace wannan kuma?"

Maganarta ta yanke ganin mace da nikabi, sai kuma aka soma taruwa, a hankali ta sa hannu ta Waga nikabinta da ruwan hawaye ya yiwa kaca-kaca. Duk lalacewarta, ko a tandun kwalli za a tsoma ta a fito da ita ai ba za ta Sace musu ba.

"Tasleem!" Fadin Futuha da ?arfi, itama Ummita sai ta zaro nata idanun. Sai kawai Futuha ta rungumeta suka shiga kuka mai sosa rai. Labari ya kai ga su Maijidda da su Humaira da Raihana, nan fa aka firfito don ganewa idanu, tabbas ita ce. Humaira ta sa Futuha ta kai ta Wakin ba?i, sai da ta yi wanka ta sauya kayanta da suka ci ubansu suka koWe sannan ta dubi Raihana da Futuha sai ko Anti Maijidda da Baba Amina wadanda ke zaune sai ta kara fashewa da kuka.

"Ina kika je?" Shi ne tambayar da Anti Maijidda ta jefomata.

"Duniya na shiga, bariki na yi, na aikata zina da mazan da ban san adadinsu ba, na bi shawarar da gurSatacciyar zuciyata ta bani akan tunda har babu mai sona kuma an tsane ni na fada duniya. A daren da na bar gida na?uda ta kama ni, bayan na haifi Wan namiji sai na kai shi gaban gidan marayu na ajiye. Dama na fita da shirina na dukkan abinda zan bu?ata na haihuwa. Ina kuka haka na bar yaron bayan na bar wasi?a akan shi din maraya ne a taimaka a kulamin da shi. Daga nan na nemi wani tsohon abokina da muka hadu a fesbuk, akan ina bukatar taimakonsa. Ya cemin shi yana Kaduna sai dai ko idan zan zo. Nace naji. Ba shiri na wuce tasha na nemi motar Kaduna. Zuwan da nayi na iske shi kadai ke rayuwa a gidan da aka ba shi na ma'aikata. Na koramasa bayanin da na tabbatar zai tausayamin ya bar ni na kwana, cewa an saki mahaifiyata kuma mahaifina ya kore ni. Da wannan bai kara neman ba'asin komai ba don da alama ba shi ne a gabansa ba. Bobby shi ya soma dora ni a hanyar bariki, ya maishe ni tamkar katifarsa bayan mun yi tsarin iyali, da ya gaji da ni ya yi wata sabuwa sai ya kore ni, koda na ?i tafiya ya yimin dukan kawo wu?a, babu wanda ya zo cetona. Na kama gida na soma fita yawon club ina neman abokan banza idan sun yi amfani da ni? su ban kudi, da wannan nake cin abinci nake kuma biyan kudin haya. A karshe da nayi sabbin ?awaye suka zuga ni kan yanda nake da kyau zai fi ace Abuja nake harkokina. Da wannan na bisu zuwa Abuja. Anan ne har na samu wani inyamuri musulmi ya aure ni, amma kullum ya sha giya sai ya dake ni. Kun gani." Ta daga rigarta ta nuna musu shacin tafka iri-iri a fatarta. Ta dora da fadin.

"Sai da na shekara hudu cikin u?ubar mutumin nan, sai ya ga dama yake bani na cefane, zai shigo da mata wanda d???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?uk ya so, bani da damar da zan hana sai cibi ya zama kari, ni zan girka musu abinci idan kuma na ?i sai ya hora ni da yunwa har na tsawon kwanaki. Rana tsaka na wayi gari ya tattara kayansa ya bar gidan zuwa Lagos ya barmin wasika na amanar gidansa kan zai je wani aiki ya samu bai dawomin ba sai bayan shekara guda, ya dawo kuma da ciwo mai karya garkuwar jiki. Ban ankara yana da ita ba sai bayan ya shafamin, na yi kukan bakin ciki da danasanin shiga bariki, sai kuma a sannan naji ina son dawowa gida amma tsoron abinda zan tarar ya hana ni. Shi ne na soma kiran Futuha da lambobin mutane don naji ya kuke, kiran karshe ne take sanar da ni dawowar Mami. Nayi kuka sosai da murna, daga baya kuma labarin ?unar da ta yi da kuma na komawarta Nijar ya same ni daga bakin matar da na ari wayarta a karshe na yi kiran Futuha, ita kuma lokacin sa?o ta bayar tunda matar ta ?i aminta ta sanar da ita daga inda nake kiran. Wannan ne ya yi sanadin dawowata, sai da naje can gidan Abba ban iske kowa ba, sabon Maigadinku ya tabbatarmin kuna gidan Humaira. Shi ya yimin kwatance na zo. Kuyi hakuri don Allah ku yafemin, na cutar da rayuwata, na cutar da ku. Me zan yi na wanke kaina daga wannan zunuban?"

Ta fashe da kuka, su dinma kukan ta sanya su. Anti Maijidda da Baba Amina suka yi mata kaca-kaca da nuna mata tsantsar wautarta. A karshe dai saboda kar jama'a su ankara sai suka fita aka kyale ta daga ita sai Futuha. Nan ta ba ta labarin dukkan abinda ya faru bayan rabuwa.

"Mami yanzu kam tana Nijar, a dole ta hakura ta ce a maida ta koda mutuwar ce ta mutu a asalinta. Tasleem, zuciyoyin wadannan bayin Allahn mai kyau ne, ba su duba komai ba suka yafewa Mami. Suke kuma bada kudade ana mata aike. Humaira ita ta dauki nauyin komai na asibiti sadda Mamin ta rayu a asibitin. Ummita kuwa kullum cikin hidimar sanya direba kawo abinci take. Hakana Anti Maijidda da Baba Amina. Mami an yanke mata kafafu, ta yi nadamar komai ko kuma nace dukkanmu mun yi nadama. Rayuwar su Humaira ta inganta, namu rayukan ne bai tafi yanda muka daukake shi nuka ci buri ba. Yanzu mene amfanin badi ba rai? Ki godewa Allah da ba ki mutu ba Tasleem, Allah ya ara maki damar da za ki nemi gafarar Abba da su Humaira kema. Nikam yanzu babu komai tsakanina da su sai sam barka."

Tasleem ta hau jinjina kai cikin zubar hawaye zuciyarta cike da tsantsar nadama.

***
AGADEZ, NIJAR...

"Ta dawo? Alhamdulillah, Alhamdulillah!"

Mami ke wannan hamdalar cikin muryar kuka jin bayanin da Futuha ke mata ta whatsapp. Ta turo kekenta zuwa kusa da gadon ?arfe na Anna dake kwance sai abin da aka yi mata sakamakon shanyewar da Sarin jikinta ya yi. Cikin yare take sanar da Anna cewa Taslee ta dawo gida.? Anna har da hawaye suka shiga fita babu baki sai gwalagwalanci dakyar Mamin ta fahimci hamdala ce Annar ke yi.
Ta bude voice na biyu da Futuhar ta turo. Nan ta shiga salati da kuka sosai,? cutar kanjamau ce da Tasleem?

Sallamar da Jannat goye da yaronta karami bai sa Mami daina kukan ba. Mace mai diri da kyawu, ta koma wata siririya sai ?ashin wuya. Kirjin nan a shafe babu tudun nono duk fatar ta yamutse. Har tana tuntube ta karaso, duk karnin nono take yi. Wani kazamin goyo take da babu ko turaren jiki.

Daki ne ginin ?asa, gadon karfen Anna shi ya cinye dakin sai ko tabsrmar kabar dake malale a kasa, can gefe kuwa tsohuwar sif na kayan Jannat ne da ta ajiye sadda ta dawo gidan cikin tsoffin kayanta na gidan tsohon mijinta, gadon da madubi yana can gidanta, wannan din ma ?in shiga ya yi dakinta yasa ta bar wa Anna.

"Maryam lafiya? Ko Anna ta mutu ne?"

Ta girgiza kai ta mi?a mata wayar, ita kadai ce waya babba da suke amfani da ita don kira da samun sakonni daga can. Raihana ce ta mata kyautarta sadda za ta taho Nijar. Kuka itama Jannat ta shiga yi. Tasleem mutuniyarta ce, jininsu ya hadu, duk a yaran Mami ba ta da kamarta. K aunar da take nata na musamman ne. Haka suka hadu zuciyoyinsu cike da tsantsar nadama. Sai ga karuwancin da take kira ga bayin Allahn da ba su ji ba ba su gani ba ya fada kan wacce ta fi kauna da so cikin yaran ?ar uwarta.

***
Tasleem sai da aka kai ruwa rana kafin Abba ya yafemata, karshe sai da ya sa aka bincika duk inda ta ce ta je da kuma auren, ya samu tabbacin abin da ta fadi. Ya zubar da hawaye jin wai yarinyarsa ta ciki ta yi karuwanci. Har sai da ya kwanta rashin lafiya sanadin damuwa. Hakanan dai ya rungume ta, itama ta zauna ta yiwa kanta karatun ta nutsu. Ta soma zuwa asibiti karSar magani kuma da taimakon Allah jikinta ya soma yin kyau idan ka ganta ba kamar sadda ta zo ba. Abba da kansa ya sa aka je aka dauko yaron da ta kai gidan marayu, wani irin hatsabibin yaro ne da ba ya jin magana kuma ba ya shakkar kowa. Idan ya kai Tasleem bango ta sa hannu ta dake shi sai ya duramata ashariya ta ban mamaki. Illoli iri-iri sun gani a wajen yaron ga ba ya shakkar kowa a cikinsu. Ganin haka yasa Abba kai shi makarantar allo ta kwana da zummar ya je can a hora shi.

Bayan watanni uku da dawowarta labarin mutuwar Anna ya riske su, wannan ne ya yi silar zuwan yaranta kaf Nijar har mazan bisa umarnin Abba. Shi dai bai je ba amma ya kira Mami ta waya ya yi mata gaisuwa. A wayar ma sai kuka take da nemarwa mahaifiyarta gafararsa. Ya ce babu komai. Hakanan Humaira da ta yi kiranta ta dinga kuka tana neman yafiyarta.

***
Zuwan su Nijar ne yasa koda suka tashi dawowa sai da mazan suka hada karfi da karfe suka gyarawa Mamin muhalli gami da nema mata ?ar aikin da za ta dinga taya ta hidimar girki da ma abinda ba za ta iya ba. Jannat ma sai da su Mubarak suka yi mata gima sha tara ta arziki. A karshe Raihana ta fidda sakon da su Anti Maijidda da Humaira suka bayar a ba Mamin na kudade suka ba ta.? Mami ta daga kudaden tana kuka hawayenta na jika takardun. Lallai ka so naka duniya ta ?i shi, ka kuma ?i naka duniya ta so shi. Yau ta ci arzikin wadanda ta raina a duniyarta. Wannan kadai ya ishe ta ishara. Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.

Tammat Bi Hamdulillah!




















































? ??

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login