Showing 144001 words to 147000 words out of 189325 words

Chapter 49 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

219

wallahi ban ga amfanin kukanki ba. Mu godewa Allah ma tunda ya yi mana maganin komai."

Cewar Humaira dake kokarin kauda nata hawayen, Raihana ko tana zaune shiru ba ta ce musu uffan kwakwalwarta cike da tunani iri iri. Tasleem ba ta dakin suna can bangaren Anna ana maida zance.

"Don Allah ki bar tunanin komai ki godewa Allah. Ai babu babban makami a yanzu irin addu'a kuma Alhamdulillah gashinan ta yi maganin komai."

Da wannan Ummita????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  ta hakura da kukan ta share hawayenta, ita babban tashin hankalinta bai wuce kuma abin da zai ?ara faruwa a gaba ba. Ko ba a fada ba ta san azzalumin mahaifinsa ne ke biWarsa. Ita kuma idan duniyarnan za ta haWe babu mai raba ta da Ahmad.

"Wayarki tana ta ?ara tun Wazu, Yaya Mubarak ne ke kira amma kin ?i ki Waga." Fadin Humaira tana mai mi?a mata wayar, ta sa hannu ta karSa ba ita kuwa ta faWa bandakin don gyara nata jikin.

***
Bayan dawowar Abba daga mi?a Nusy hannun hukuma inda akai akai ta faWi wanda ya sanya ta ta ?i, yana zaune yana amsa wayar Alhaji mahaifin Fadeel dake jajanta al'amarin Jannat da kuma kwantarwa da Abban hankali ganin dole ya shiga damuwa tunda kanwar matarsa ce, kasantuwar hakan kuma ya jawo kananun magana iri-iri a kafafun yada labarai kowa na cewa watakila ma ita ta sa aka sace su. Abba ya yaba sosai da samun surukin da ya rikiWe ya zame masa abokin kuka a rayuwa ya dinga godiya. A haka Mami ta shigo falon ta iske shi. Ganinta bai sa Abba fasa wayar ba, tana ji yana bada labarin abin da ya faru bayan dawowarsu daga kotu amma sam ba ta fahimci da wanda suke wayar ba sai daga baya. Ta matsu sosai ta ji ya kai gaSar da take so wato sanin hannun da Nusy take, ba ?aramin girgiza ta yi da jin wai tana hannun Ridwan ba. Wata irin zufa ta karyo mata. Ridwan dai da Jannat ta zama karkashinsa a can ofishin SS, kai kai kai, ita kuwa ta san zai wahala Hajiya Lubna ta iya wani abin a kai amma dai za su gwada sa'arsu. Har Abba ya kammala wayar ba ta sani ba sai da ta ji ya yi magana.

"Hajiya Maryam lafiya?"

Ta Wan yi firgigit gami da dan muskutawa da tattaro dukkan damuwar duniyarnan ta Wora saman fuskarta. Dama ya lafiyar kura?

"Ina fa lafiya Abban yara, kana tunanin zan zauna cikin nutsuwar ruhi bayan abubuwan da suke biyowa baya? Wallahi idan aka ce wani nawa zai cutar da jininka zan ?aryata hakan. Wai Jannat dai da kanta ta aikata wannan mummunan abu ga yarannan? Haba Abban yara, ni gaba daya kunyarka nake ji. Don Allah ka yafemin kar ka hukuntani da laifinta. Tabbas ta aikata wauta."

Sai ga Mami ta soma kuka da hawaye, Abba ya Wan yi shiru kawai yana kallonta. Ba don da kunnuwansa da kuma idanunsa ya ji ya gani tana bada umarnin a aiwatar da kisa a kansa da gudan jininsa ba, zai iya dafa Alkur'ani dukkan abin da take faWi kuma take nunawa a zahirance da zuciyarta Waya ta ke yinsa. Sai dai ina, Maryam ta gama sirewa a ransa, kullum kuma kodayaushe cikin addu'a yake akan Allah ya kara buWa idanunsa ya nunamasa gaskiyar matar da yake rayuwa da ita kuma ya rayu da ita tsawon shekarunnan cikin rufewar idanu da rashin sanin ha?i?aninta.

Mami ta Wan yi turus jin babu wani sauyi ko kuma yanayin da zai nuna maganganunta ya shige shi a saman fuskarsa, ta dube shi da dan mamaki kirjinta na Wan dukan tara-tara, kada dai zarginta yake yi?

"Abban yara kodai kana tunanin da sanya hannuna cikin abin da Jannat ta aikata?"

Ya numfasa gami da girgiza kai da ri?o yatsun hannunta.

"Ko kusa Maryama, ni ba na zarginki da komai. Idan na zargeki na ce na zargi wa? Matar da muka rayuwa tsawon shekaru sama da ashirin cikin so da kauna ta gaskiya? Ko kuwa wacce ta ri?emin amanar gida da na yara har ma da wadanda ba ita ta haifa ba cikin kauna da aminci? Har abada ke ba abar zargina ba ce."

Mami ta Wan yi ya?e, a karan kanta sai ta ji tsarguwa, ba ta gamsu da zantukan Abban ba. Shi kuwa idanunsa ?urr cikin nata, danne zuciyarsa yake yi sosai don ya fi kaunar tafiyarsu a hakan har zuwa sadda zai kama ta dumu-dumu.

"Kawai dai lamuran ke dauremin kai, waye ya aiko a sace Ahmad? Idan kuma ba aike bane, ita din wace ce da ta zo tafiya da shi? Akwai dai lauje cikin naWi wanda na tabbata Ridwan zai tsaya tsayin daka wajen ganin ya warware wannan ?ulli."

Kirjinta ya ba da dam! Bayan sunan Fadeel, a yanzu Ridwan shi ne suna na biyu da kaf duniya ta ji ta tsana. Wato shi ga Wan iska, ya shigo rayuwarta don ya wargaza ta, toh kuwa bai isa ba. A fili kuwa jinjina kai ta yi cikin nuna damuwa ?arara da mamaki.

"Tabbas nima abin ya Wauremin kai Abban yara, koma wace ce wannan yarinyar da ta kira kanta da Nusy, akwai wani sirri tattare da zuwanta da bincike kadai zai tona shi. Ka kwantar da hankalinka gaskiya za ta bayyana."

Murmushi ya yi sosai.

"Nima gaskiyar na fi son ta bayyana. Zan so abin da yake Soye ya fito fili. Na dai yanke shawara da zarar an kammala bikin ?ar uwarta zan maida ta hannun Hajiya Maijidda na Wan wani lokaci mu gani. Ba don saboda bikin ba ma tun yanzun za ta wuce, toh amma ba na son na yanke mata wannan farin ciki."

Mami ta daure fuska tamau.

"Wace irin magana ce wannan kake yi? Wato ka raina dukkan kulawar da Ummita ke samu a wurina?"

Shima nan da nan ya Waure nasa fuskar.

"Nayi zaton ke ce farkon wacce za ta yi amanna da wannan shawarar Maryama, idan har dagaske kwanciya da nutsuwar hankalin Ummita ki ke buri, toh fa babu abin da ya fi wannan? samar mata nutsuwa."

Sai ta gane tana shirin kwafsawa da sauri kuma ta gyara zancen ta hanyar raunana murya da fuska.

"Na sani Abban yara, amma kewarta na fi tunani da zan yi. Shikenan dai Allah ya kawo karshen komai."

Abba ya amsa da amin, ba shi da tabbacin ko dagasken take yi akan lamarin Ummita, ya dai bi ta da hakan ne kawai.

Sai da Abban ya fice zuwa masallaci don gabatar da sallar la'asar sannan ta samu damar kiran Hajiya Lubna ta sanar da ita. Hajiya Lubna ta tambayi cikakke sunan Ridwan din, nan ta sanar da ita, sai kawai ta ja tsaki.

"Aikin banza kai, ai wannan Wan Hajiya Fa'iza ne, matar Late General Mukhtar AbdurRashid. Sai dai yaron a yanda na san shi yana da wani irin kafiya akan ra'ayi da taurin kai. Za dai mu gwada sa'ar mu. Kar ki samu damuwa. Idan ma ya ?i bada haWin kai ai sai mu biyo mishi ta sama."

A farko zantukan Hajiya Lubna sun Wan sa jikinta mutuwa, amma jin ?arashen sai ta samu kwarin gwuiwa. Suka rabu akan duk yadda ake ciki za su yi waya.

Daga nan Babandi ta dannawa kira ta labarta masa komai, ya ce kada ta samu damuwa zai yiwa abin tufka. Sunan Ridwan kawai ya tambaya cikakke daga nan ya ce zai mata aiki a kansa.

Haka ta sallame wayar zuciyarta fari ?al.

***
Matashin ma'aikacin dogo mai ?ira, ba?i ne, irin ba?in da hutu ya ratsa. Yana da cikar sumar kai, ya na sanye cikin ?ananan kaya ya tsaya gaban tebur gami da ?urawa Nusy idanu babu wasa ko kaWan a cikinsu. Ita kuwa tana binsa da kallo tamkar ta lashe shi, a baya tana yiwa Wizzy kallon wani haWaWWe kuma jarumi musamman a fagen bariki, amma a yanzun da Ridwan Mukhtar AbdulRashid ke tsaye a gabanta sai ta nemi sauran ruwa a jikinta ta rasa. Sai dai ta sani wannan ba sa'anta ba ne, ko za ta mutu ba zai auri ?AR BARIKI irinta ba da ba ta san adadin wadanda suka ci moriyarta ba.

"Idan za ki yiwa kanki adalci, ki faWi gaskiya ki huta kuma hukuna ta huta. Ke din wace ce kuma mene ne dalilinki na shiga gidan Alhaji Yusuf da niyyar satar Wan mutum?"

Ta ji idanunta sun cicciko da ?walla amma ta yi shiru babu amsa. Idan ta fadi ba amanar Wizzy kadai ta ci ba, har da na kanta don ta tabbatar za ta yi biyu babu, wato dai babu auren Wizzy balle kuma samun wani ?anci na rayuwa.

Ridwan ya Wan kwankwasa tebur, ta Wago idanunta ta kara dubansa. Fuskarsa kaWai ta isa sanya matarsa samun nutsuwa da bacci mai dadi. Ko wace ce ta same shi ta huta.

"Ba ki shirya magana ba kenan? Ki sani Nusaiba akwai hanyoyi da dama da zamu sanya ki magantuwa, idan kin zaSi ta hanyar tsananin hakan ce za ta faru. Idan kuwa kin shirya sanar da mu ba tare da Sata lokaci ba, wannan ma kin kyautawa kanki."

Wani tunani ya faWomata sai ta yi saurin magana ba tare da hango matsalar abin da take shirin faWi zai jawo ba.

"Nidai ba satar Wanta na je da niyyar yi ba. Babansa ne ya ke da bu?atar ganinsa ya nemi alfarma na kawomasa shi ?ofar gidan koda kuwa na mintoci ne sai na maida musu shi."

Ya ji zuciyarsa ta yi wani irin tu?u?i. Babansa? Shi dai da ya ke da alhakin keta alfarmar macen da a yau yake jin babu ya ita a zuciyarsa? Shi din dai da ya yi garkuwa da ita? Nan da nan jijiyoyin kansa suka fito raWau, idanunsa suka kaWa. Ya murza yatsun hannunsa suka yi ?ara ?as ?as.

"A ina zamu same shi domin mu tabbatar da abin da kike magana a kai?"

Sai kuma ta hangi wautarta, nan da nan ta soma zufa. Ya dakamata tsawar da sai da ta mi?e tsaye tsabar firgici.

"Ki sanar da ni!"

Wayarsa dake gefe ce ta katse shi, ganin mahaifiyarsa ce ya sanya shi saurin Wauka ba tare da ya Waga ba ya fita a dakin da sauri, a duniyar Ridwan ba shi da abin girmamawa sama da ita. Mutum ne mai matukar gudun zuciyarta. Ya samu kyakkyawar shaida ta girmama uwa a wurin mutane. An kuma ci sa'ar da ya kasance ba ta fiye yi mishi katsalandan kan aikinsa ba.

A wannan karon da Hajiya Lubna ta shaida mata alfarmar da take nema na sakin Nusy bayan ta ro?i alfarmar ta sirranta sunanta. Sai ta yi kiran Wan nata don jin ta?amaiman wace ce Nusy din.

Ridwan jin tambayarta ya yi mamaki, koda wasa bai sanar da ita komai game da Nusy ba amma lamari an Jannat da ma su Ummita babu wanda ba ta sani ba. Kasancewar ba su yi zaman hira ba ne ya sa koda wasa zancen Nusy bai haWa su ba. Bai nata tambaya kan tambaya ba, sai ya zaSi labarta mata dukkan komai. Hajiya Fa'iza ta amsa masa bayan gana sauraro.

"Ka cigaba da bincikenka, ina fatan Allah ya baka nasarar magance komai. Allah ya yi maka albarka. Ya nunamin cikar burina kafin mutuwata. "

Ya yi murmushin jin dadin wannan addu'a, ya sani ba ta da buri sai na son ganin aurensa, shi kuma ya sani kukanta ya zo karshe da yardar Allah don ya riga da ya gama samun wacce yake jin zai iya ?are rayuwarsa da ita.

***
Labarin Jannat ya karaWe ko'ina, mijinta ya samu zuwa ya kuma kawo sar?o?inta da aka nemi ya kawo, an siyar an haWa da motarta amma duk da haka su na bu?atar cikon wurin miliyan hudu da rabi. Anna ta tattara nata ajiyar da bai cike miliyan ba ta bayar, Mami kuwa dakyar ta sanya dubu dari takwas inda ta rantsewa Anna su kadai gareta, duk da haka dai da sauran rina a kaba. Futuha ta bada dubu dari uku, Tasleem ko ba ajiye ba balle ta bayar, sar?arta Waya ta gwal da ta mallaka ta yi shiru don ta san ba lallai ta samu ta mayar ba. Akan haka har Futuha sai da ta yada mata magana, wai duk tsananin kusancinta da Jannat ta kasa bada ko biyar da za'a haWa a biya don a samu ta fito. Ita dai ba ta biyemata ba ta banzatar. Anna da kanta ta taka har zuwa gaban Abba da ya yi burus da batun Jannat sai shirin bikin Humaira da yake gudanarwa, ro?onsa ta shiga yi da kuka sosai akan ya taimaka ya sa hannu ko iyaka hakan a bayar don Jannat ta fito. Abba ya bata hakuri ya nunamata babu abin da zai iya yi a kai tunda dai magana ba a hannunsa take ba. A hannun hukuma da kuma yaran da aka Satawa yake. Wannan al'amari ya yi mugun dasa haushin Abban a zuciyar Anna. Ta kuma daWa ro?onsa toh ya taimaka ya cika koda bashi ne idan ya so bayan fitowar Jannat din sai ta biya shi.

"Kiyi hakuri Hajiya, a yanzu dai ba zan ce akwai su ba, na tattara abinda ke hannuna na bada odar kaya na shaguna na, abin da ya rage kuma shi nake amfani da shi wajen fita kunyar jikarki da bikinta ke tafe."

Ina wuta Anna a jefa Abba don kiran Humaira da sunan surukarta da ya yi. Kamar ta dura masa ashariya haka ta ji sai dai ta daure ta haWiye Sacin ranta. Shi kuwa Abba mi?ewa ya yi yana gyara zaman babbar rigarsa don ya kammala shirin fita kasuwa a ladabce cikin danne Sacin rai ya ce.

"Ni na fita Hajiya, lokaci na tafiya. A yi hakuri za a samu mafita in sha Allahu."

Yana kaiwa nan ya sa kai ya bar falon sai ?amshin turarukansa da suka bi bayanshi suka shige kofofin hancinta.

"Kai wannan Isuhu an yi Wan duniyan ?arshe, yanzu a dubi tsabar idanuna ya shirgan uban ?arya duk don kar ya taimaki auta? Oh ni, yau naga abin da ya fi karfina. Aikuwa duk muguntarka sai yarinyarnan na fito tunda kai azzalumin mutum ne, sai ba?in mugunta kamar wani arne a cikinsa."

Ita kaWai dai ta dinga bambamin nan har ta kai aya babu wani a falon da zai taya ta daga karshe ta yi kwafa ta mi?e ta bar falon.

***
A yau Raihana ta ?udurta sai ta bincika wayar Maminta, duk irin kwaSar da zuciyarta ke yi mata ta kasa hakura. So take ta ga da wanda Mamin ke waya har ta kai ga ba shi umarnin kashe Abbansu. Idan har ta yi nasarar samun lambar mai shi, toh kuwa ta yanke Abban za ta kai wa don ya bayar a kamo mutumin. Wannan ya sa a yammacin yau ranar Talata tana dawowa daga jarrabawar da suka soma na WAEC ta dinga fakar idanun su Tasleem da Yassar dake zaune a falo ana hira ta mike ta bi bayan Mamin zuwa dakinta da ta shiga. Ta kudurce idan har suka yi kiciSus za ta wayance da tambayarta maganin ciwon kai wanda gajiya da kuma damuwa suka haifarmata, idan ko ba su hadu ba to wayarta za ta durfafa. Cikin iko na Ubangiji kuwa ko kyallin Mamin babu sai motsin ruwa da ta ji a banWakin. Hamdala ta yi jiki da hannu na rawa ta dauki wayarta dake saman gado ta bude don ta san lock din. Kai tsaye ta shiga Call log ta hau dubawa har ta kai kan na kwanan watan da Humaira ta tafi, tana yi tana kallon ?ofar bandakin, har idanunta ya kai ga lambar da aka yi saving da WZY wanda lokacin kiran hya kasance da asubahi. BuWewa ta yi ta karanta lambar har sau uku nan da nan ta ji ya zauna a kanta don babu laifi tana da hadda, da sauri ta fita ta kashe wayar ta bar dakin tana maimaita lambar a ?asan ranta, Allah ya taimake ta su Tasleem ba su ankara da ita ba, kai tsaye dakinsu ta shiga su Humaira na mata magana ba ta amsa ba don kar ta mance lamba sai da zare wayarta daga chaji ta shigar da lambar ta yi saving sannan ta dago ta dubi Humaira.

"Yi hakuri kina magana hankalin yana nan, kaina ke ciwo kinga har yanzu bai bar sarawa ba."

Humaira wacce Hajjo ba ta jima da yi mata gyaran jiki ba fatarta sai kyalli take yi don tun a Nijar aka soma ta ce.

"Wayyo sannu, bari na samo maki magani wurin Mami."

Daga nan Humaira ta mike ta fice, dama tana son ganin Mamin su gaisa sosai, tun zuwanta har yanzun ba su wani gaisa ba. Sun dai gaisa da Hajjo itama sama-sama, ko me Mamin za ta yi a ganinta uwa ce a gareta. Tunda dai aure za ta yi gwara a rabu lafiya.
A falon ?amshinta ne ya bayar da zuwanta, Tasleem ta kuramata idanu kamar ta sha?o wuyanta ta mutu, cikin dogon hijabi take amma sai wani kamshi da kyalli jikinta ke yi. Ta gaishe da su Yassar waWanda a yanzu babu komai tsakaninsu face mutunci. Kai ka ce ba su taSa tsangwamarta a rayuwarsu ba.

"Ina kike tunanin za ki je?"

Ta ji muryar Tasleem a kanta, ta juya ta dubeta. Wani irin duba na ke a wa? Tasleem ta bude baki don mamakin hararar da Humaira ke yi mata, kafin ta samu abin faWi sai kawai gani ta yi yarinyar ta sa kai a Wakin.

"Amma wannan yarinyar ta mugun rainamin wayo. Don uwarta har ina ma ta magana ta harare ni ta yi gaba?"

"Ke dai za ki ji tsoron Allah ki bar takura rayuwar ?ar mutane. Haba Tasleem, kina girma kina cin ?asa. Nifa dama can kawai taya Sera Sari ne amma idan za a titse ni ba zan nuna laifi guda da yarinyarnan ta aikata gareni ba."

Cewar Yassar kenan. Tasleem ta kara kufula.

"Ai ba za ka gani ba saboda kai babu abin da ka sani."

"Sanar da mu."

FaWin Dawud. Ita kuwa sai ta basar, ai da kunya ta ce musu wai kwacen saurayi Humairar ta yi mata, ita a karan kanta ta san zance ne kawai ba hakan yake ba. Su ma kuma sun san komai. Sai ta zaSi waskewa ta hanyar nunamusu irin fifikon da Abbansu ke nunamata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login