Showing 75001 words to 78000 words out of 189325 words

Chapter 26 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

210

haka ba ta ?ara ko harafi ba saboda azaba. Ummita ta yi mata tofi a wurin sannan suka yi zaman shiru sai ambaton Allah da suke faman yi.

***
? Mami suna tare a kicin ita da Ladidi, abinci suke ta hadar-hadar shiryawa na dare tana ta mitar zaman da su Humaira suka je suka yi a gidan Tasleem alhalin ta ce musu kar su jima.

"Gashinan yanzu har an fara kiraye-kirayen sallar Magriba, itama gwanar duk da na gargadeta kar ta bari su yi zaman hira da mutuniyar tasu (Raihana) amma ta yi kunnen uwar shegu."

Ladidi ta yi ?ar dariya tana goge kwanukan da ta wanke don yin kwasar tuwo.

"Ai fa kam, ?anmatannan naki uku idan suka haWu a wuri sai ha?uri. Ji suke yi kamar ba su taSa zaman hira ba a duniya sai a lokacin."

Mami ta buWe baki za ta yi magana sai ga Walid ya shigo da gudu ri?e da wayarta, a bayansa kuwa Muhsin ne.

"Mami Mami! Anti Tasleem tana kira."

Wayar a lokacin har ta katse, Muhsin yana kawo ?arar Walid wai game yake ta yi har ana kira yana katsewa. Mami ta Wan yi musu tsawa akan suf fice a kicin Win su ba ta wuri. Ta na kokarin dannawa Tasleem din kira sai ga kiran Raihana ya shigo, ta Waga ta kara a kunne.

"Raihana, yanzu nake shirin kiranku, maza maza ki cewa yarannan su dawo. Ku idan ku ka samu hira ba ku san dare ba ya yi ku ha?ura ko?"

"Mami su wa kike magana? Ai kiran ma da Sis ta yi maki kenan ta ce kodai ta cire rai ne ta sanya Yaya Hamza ya yi mata odar wani abun? Nidai tun Wazun ma na kikkira wayoyin su Ummita a kashe."

Mami ta fiddo idanu gami da dafe kirjinta, cikin rawar murya ta ce.

"Me kike shirin cewa? Kina nufin wai su Humaira ba su zo gidan ba? Kinsan tun ?arfe nawa suka bar nan?"

Raihana itama muryarta cikin tsananin ruWewa da tashin hankali ta amsa.

"Wallahi Mami ba su zo ba."

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Na shiga uku ni Maryam."

Hakan da ta faWi ya sa Ladidi maido hankalinta gareta, itama gaba Waya jikinta ya Wauki rawa. Mami ta kasa cewa Raihana komai sai kawai ta katse kiran cikin tsananin tashin hankali ta fito falon inda ?asim ke kwance saman kujera yana latsa waya.

? "?asim! Tashi ka bi sahun su Humaira! Na shiga uku, tun da rana suka fita a gidannan har yanzu ba su dawo ba."

Gaba Waya a ruWe take maganar, ta kasa nutsuwa balle ta yi mishi bayani yadda zai fahimta. Ba ta jira cewarsa ba ta yi gaba ta nufi Sangaren Abba amma ina, ta iske ya fice zuwa masallaci. T???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a dawo falon inda ta tarar ?asim tsaye Ladidi na mishi bayanin abin da ya faru. Shi ma nan take ya ji hankalinsa ya tashi.

? "Amma Mami kodai sun biya gidan ?awayensu ne?"

Mami wadda gaba Waya cikinta ya Wuri ruwa ga tsananin tashin hankalin da ya bayyana saman fuskarta ta amsa mishi.

"Kayya ?asim, ba dai su ba. Ba su da wannan rawar kan, da ace dai Raihana ka ce shi ne zan yarda. Ni dai jikina yana ba ni akwai matsala."

?asim ya yi shiru, sai ya shiga kiran layukansu amma gaba Waya a kashe.

"In sha Allahu lafiya kalau suke. Ku kyautata zato."

Fadin Ladidi jiki a sanyaye. Itama ta rasa nutsuwar zuciya, a wannan lokaci da satar mutum sukutum ba shi da wuya, lallai dole ko rabin awa suka yi hankali ya tashi, balle kuma kusan awanni uku zuwa huWu? Abin dai akwai Waga hankali.

"Bari nayi sallah."

Mami ta furta gami da mi?ewa ta yi Waki. Ladidi ma ficewa ta yi kicin don kwashe tuwon da har ya soma kamu yayinda ?asim shi ma ya fice a sanyaye zuwa masallaci.

***
Tasleem kuwa, Raihanana ajiye waya suka dube ta ita da Fauziyya da ta maida gidan na Tasleem gidan zuwanta hira da kuma kallo.
?
? "Meyafaru da su Humairar ne?"

Cikin halin tsananin firgici ta faWamata abin da Mamin ta ce. Tasleem ta yamutse fuska kaWan tana ci gaba da taunar tsamiyar da ke bakinta.

? "Ke yanzu kin yarda Satan suka yi kenan? Kika sani ko Ummitan ta yiwa rakiya Wakin Sahabi?"

Maganar ta dake Raihana, wannan wane irin ba?in ?azafi ne marar daWin ji? Ba ta taSa tsammanin jin makamancinsa daga bakin Tasleem ba musamman ma a gaban ?anwar mijinta. Fauziyya kuwa ta ce.
?
"Kai Anti Tasleem, wannan Humairar da na gani dai kamar ba za ta aikata irin haka ba. Ummitar ma ba ta yi kama da ?an iska ba."

Sai a sannan ita ta tuna ashe ba su kaWai ba ne. Don haka ta yi saurin gyara zancenta gami da nuna tarin alhini a saman fuska.

"Hakane, amma kinsan zamanin nan, samarin yanzu ?an iska don su hurewa mutum kunne ba komai ba ne. Allah dai ya tsare, ya sa su koma gidan."

Raihana wacce ta lula tunanin inda ya kamata ta kira don jin ko su Humairar sun je ta dawo hayyacinta, firgigit ta mi?e tana fadin.

"Nidai wallahi ba zan iya zama ba ana neman ?an uwana, gida zan koma."

A fusace Tasleem ta ce.

"An fadamaki nima ban damu ba ne? Ai daren bai yi ba, kika sani ko napep din da suka shiga ne ya samu matsala? Toh wallahi babu inda za ki je ki jira har sai mun ji ya ake ciki."

Raihana kamar ta yi magana sai kuma ta fasa, a fusace ta shige ciki tana jin kuka na taso mata, ta ina za ta iya nutsuwa alhalin ba a ga ?an uwanta ba? Fauziyya ganin haka ta mi?e ta bi bayanta, ita kuwa Tasleem da sauri ta bi hanyar da suka yi da idanu sannan a gaggauce ta fiddo wayarta ta rubuta text ta tura kamar haka.

? ? *_Aikin har ya kammala ne da wuri haka?_*

Tana aikawa aka maido mata amsa.

*_Tukunna dai, wani abun ya faru?"_*

Ta yi shiru ta kasa maida amsar wannan tambaya, jikinta ya Wan yi sanyi. Ita kanta ba ta da tabbacin abin da ke shirin faruwa.

***
? Mami tana jin shigowar Abban falo ta mi?e da sauri har ya dube ta da Wan mamaki.

"Lafiya Maryama, ya na ganki a rikice?"

Kawai sai ta fashe da kuka. Ya shiga tashin hankalin ganin haka, wannan ya sa shi saurin ri?o hannuwanta.

"Ki samu nutsuwa ki faWamin, meke faruwa?"

Muryarta dakyar take fita ta amsa.

"Kasan na aiki yarannan gidan Tasleem amma babu su babu dalilinsu. Ba su je gidan Tasleem din ba, kuma wayoyinsu gaba Waya a rufe. Hankalina ya tashi."

Tabbas ya san da maganar amma kasancewar ya shiga tsananin ruWani ya ce.

"Su wa kenan? Ni ban fahimci komai ba. Wa kika aika?"

"Humaira da Ummita da na ce maka za su je gidan Tasleem kai mata sa?o."

Abba jin haka nan da nan ya soma haWa zufa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Kun tabbata ba sa? gidan ita yarinyar?"

Mami ta amsa ta hanyar gyaWa kai da motsa lebba don sautin muryar ma ta kasa fita. Jin haka Abba ya zari mukullin mota daga shi sai jallabiya sai ko wayoyinsa ya fita yana fadin.

"Ina zuwa." Har ya kai ?ofa sai kuma ya juyo ya dubi Mami.

"Maryama, ki kira dukkan inda kike tunanin za su iya zuwa ki ji ko can suka tafi, ni bari na je ofishin ?an sanda na sanar."

Ta kasa magana sai gyaWa kan da ta yi.? Daga haka Abban ya fice. Kai tsaye babban station Win mandawari ya je ya yi report ya ba da hotunan su Ummita, ba shi da su sai da ya sanya Raihana ta turo masa. Anan ne itama hankalinta ya kara mugun tashi ta tabbatar dagasken dai an sace su.

***
Raihana ta birkicewa su Tasleem ita lallai a daren take son komawa gida, kuka take yi ba ta jin koda rarrashi, wannan ya sanya ba shiri suka mi?e har Tasleem din suka nufi can gidan a motar Hamza.
? Su na isa Raihana ta faWa cinyar Mami ta ?ara ?arfin kukanta. Wannan ya ?ara karyar da zuciyar Mamin, ta dafa Raihanar tana Wan hawaye. Tasleem ta ?araso ta zauna fuskarta Wauke da damuwar kukan da Mami ke yi ta ce.

"Kiyi hakuri Mami, in sha Allahu za a gansu. Bana tunanin an sace su, idan da hali ku kira Sahabi ku ji ko..."

"Malama ya isheki hakanan! Haba! Da wanne kike so a ji? Da Satan su ko kuwa da ba?in ?azafin da kika ?okarin yi musu na zuwa wajen saurayi? ?azu dama na maki shiru ne darajar Fauziyya, yanzu kuwa daidai nake da ba ki amsa. Ki faWi muji, tarbiyyar wa kike shakku a cikin su biyun? Ke da kanki a bayan idanunsu kin sha yabon nutsuwarsu, ki dai ji da abin da ke jikinki ba ki zauna zaman Waukar ha??in mutanen da ba su Waukeki yadda ke kika Wauke su ba!"

Tasleem wacce ta cika ta gama batsewa da wannan kalar maganganun da ta ke musu kallon rashin kunyar Raihana gareta tuni ta harzu?o za ta soma caccakawa Raihanar zagi sai Mami ta dakamata tsawa.

"Ya ishe ni! Ya isa! Ku marasa tunanin ina ne? Da wanne zan ji ne? Ashe ba kwa hangomin abin da nake hangarwa kaina?! Ba ku hangen ire-iren maganganun da zan sha wajen jama'a sanadiyyar Satan? yaran amana da nake ri?o? Da ace cikinku ne wa zai ce sakacina ne?!"

Mami na kaiwa nan ta ji kukanta ya ?aru har da sheshshe?a, ?arshe kawai sai ma ta mi?e ta fice zuwa sashin Anna don tana da tabbacin ba ta sani ba.

***
Duhun da Wakin ya yi ne ya sanya suka matsu a gefe guda suka cure jikinsu ga uban sauro da ke yawo a kunnuwa yana kuma cizon fatar jikinsu.

"Humaira, ya zamu yi? Babu ruwan alwala a banWakin nan da na duba, bamu yi sallolinmu ba. Ma?ogwarona ya bushe ?ishin ruwa nake ji."

Ummita ta yi furucin cikin sha?a??iyar muryarta da ya dashe sanadin kukan da suka sha, itama Humairar wacce ?ishin ruwa da kuma yunwa suka galabaitar gefe guda ga wani fitsari da ya cikamata mara ta ce.

"Ban sani ba Ummita, ban sani ba. Fitsari nake ji amma tunanin wannan banWakin da muhallin ya sa na kasa yi. Sun bar mu a duhu kamar waWanda ke cikin ma?abarta, ko a ma?abartar muna saka rai da rahmar Ubangijinmu. Mu cigaba da addu'a, ba zamu rasa mafita daga gareShi ba."

"Toh." Shi ne kawai abin da Ummitan ta iya furtawa, ta koma ta nannaWe a jikin bango ta runtse idanunta tsabar tsoron wurin, cikinta ya Wuri ruwa sosai, ta cigaba da jan dukkan wasu addu'o'in da suka zo bakinta.

Suna a haka suka soma jin muryoyin garada daga waje suna dariya har da kyakyatawa abin babu dadin sauraro. Kafin su tantance komai suka ji alamar buWe ?ofar, gaba daya suka ?ara ru?un?ume juna don fargaba. Aka haske musu fuskokinsu da torchlight mai shegen haske, wannan ta sa suka yi amfani da hannuwansu wurin kare hasken sakamakon ?arfin da suka ji ya yiwa idanunsu da suka jima cikin duhu. Wannan karon matasan ne su ukunsu gaba Waya suka shigo.

"Don uwarku ku saki juna, ?an iskan banza kawai."

Sun ji ciwon zagin sai dai tsoro ya sa da azama suka matsa gefe, kowaccensu babu inda jikinta ba ya rawa. Shi ne dai ba?in azzalumin na Wazun.

"Wizzy, a ina aka kwana ne?"

Anan suka ji ashe sunansa Wizzy, ya watsawa mai maganar mugun kallo.

"Kai Babba, don't kawo yaawa mana. Ka yi everything a muhallinsa mana ok? Here is not good to ce wani abu. Sai mun go out."

Wanda aka kira da Babba ya amsa da.

"Na fahimta Oga."

Daga haka Wizzy ya yo gaba ya dan sa ?afa ya shuri Humaira.

"Ke gwanar na iya, koda wasa wallahi ki ka kara try din zagina sai na kasheki na yi killing banza! Kuma a nan za ku zauna har sai mun gama sanin makomarku! Badboy, a ba su abincin da ruwa, ka ajiye musu fitilar ba don halinsu ba shegu."

Yana kaiwa nan ya sa kai ya fice yana ba wa Babba umarnin ya biyo shi su yi magana. Shi kuwa Badboy ya ajiye musu leda da ruwan sha na purewater sin?i guda, sai kuwa fitilar daga nan ya fice ya gar?ame ?ofar. Da sauri Ummita ta jawo ruwan hakanan itama Humaira, suka sha suka yi kat, daga nan haka suka daure suka kama ruwa a banWakin ba don suna so ba, suka yi alwala, Wankwalayensu suka mayar darduma, suka yi sallah.

Humaira ta yi shiru ta zuba uban tagumi tana Sarin hawaye, Ummita ta jawo ledar, shinkafa da miya ne garau garau.

"Ke kika ce kina jin yunwa Wazu, ki daure ki ci."

Ta Wan dubi abincin sannan ta dubi Ummita ta girgiza kai.

"Ba zan iya ci ba Ummita, innalillahi wa inna ilaihir raaji'un, haka za mu yi ta zama tare da waWannan azzaluman? Yanzu nan wurin zamu kwana? Su Abba na can hankalinsu a tashe Ummita. Wayyo Mami."

Kawai sai ta sa kuka hakan ya sa Ummita itama da take danne nata sai kawai ta sake shi. Wannan karon ma babu mai rarrashinsu, su suka gaji suka yi shiru sai faman sheshshe?a.

***
*LITTAFIN NAN NA KU?I NE. SIYA AKAN NAIRA ? 400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645




Kamar wasa, ?aramar magana ta zama babba. Babu su Humaira ba labarinsu har aka yi kwanaki biyu, wannan ya ?ara tayarda hankalin iyalan gidan sosai. A ranar ne kuma Jannat ta diro gidan, labarin Satan yana ris?arta ta hau buga salati, cikin sanyin jiki ta ce.

"Koda ace ba na kaunarsu, bana murnar Satan su. Allah ya sa a gansu."

Mami ta amsa da amin, Raihana kuwa ba ta um bare um um a kwanakin nan sai kallon kowa da idanu. Tasleem itama dai tana gidan ba ta koma gidanta ba, Abba ne ma ke faWan zamanta acewarsa zaman ko rashinsa ba shi zai sa a gansu ba. Wannan yasa a ranar ya ba ta umarnin tattarawa ta tafi. Jannat ce ta ce za ta kai ta tunda Hamza ya tafi ofis. Anna kuwa nunawa tayi ko a jikinta, cewa ta yi ba ta yarda ma da batun Satan ba, ta fi tunanin dai wani yawon nasu suka je za su dawo. Babu wanda ya ce mata komai a wannan bahagon tunanin nata. Zancen dai zuwa lokacin ya yaWu har gidajen rediyo da social media inda Raihana ta Wora hotunansu a dukkan shafuka tana mai tagging shafin Humaira saboda abokan kasuwancinta su taya ta yaWawa.

***
*_Tafkeken fili ne babu gida gaba da baya, tafiya kawai yake yi yana jefa ?afafunsa yana faman kwala kiran sunan Humaira ga wani irin ba?in hadari da ya cakuWe a sararin samaniya sai wal?iya dake haskawa akai-akai har bai ankara ba ya cimma ?arshen hanyar yana shirin afkawa ?aton ramin dake a gabansa ya ji an ri?o hannunsa da ?arfi. Juyawa ya yi yana mai duban mai shi, wata mace ce dattijuwa fara tas, tana sanye da farin hijabi har da na hannu, komai na tufafinta fari ne ?al. Hawaye ne kwance saman fuskarta ta ce. "Ka taimaka ka ceci rayuwar Humaira, tana cikin hatsari. Ka kularmin da ita. Duk runtsi kar ka rabu da ita. Alheri ce a gareka." Zuciyarsa ya ji ta tsinke, ya dawo da baya murya a sama ya ce "Ina Humaira ta ke?" Kawai sai ta nuna masa ramin dake gabansa, Humaira ya hango saman wani ?aton dutse a kwance gaba Waya gaSSanta an sanya wasu sar?o?i an Waure ta tamau. Sannan ya maida duba ga Matar shima lokacin hawaye yake. "Ba ta sona, ba za ta amince na taimake ta ba." Matar karo na farko ta yi mishi murmushi "Kaf duniya babu matar da za ta so ka sama da Humaira. Tana sonka, ka bata lokaci ka zama mai hakuri." Tana kaiwa nan ta saki hannunsa ta soma tafiya da baya tana cewa "Ka ceci rayuwarta daga hannun azzalumai. Ina ro?onka a matsayina na mahaifiyarta._*

Yana kai wa nan ya soma jin kiraye-kirayen sallar asuba a kunnensa, firgigit ya farka ya mi?e zaune yana ambaton Allah. Na'urar sanyaya jikin dake aiki bai hana zufa wanke mishi fuska da jiki ba hakan ya sanya shi saurin yaye bargon yana ajiyar zuciya kamar wanda ya yi tseran gudu. Kansa ya ji yana sarawa, wannan wane irin mafarki ne kuma? Wace ce? Meke faruwa da Humairar? Kwana biyu kenan rabonsa da duk abinda ya shafi social media balle ya samu damar magana da Raihana ko tambayar lafiyar Humairar, hakan kuma ya faru ne sanadiyyar ayyukan ofis da suka yi mishi yawa saboda shirye-shiryen tarbar ba?in ?asar waje da suke yi a kamfaninnasu. Addu'a ya yi sannan ya mi?e jiki a saluSe gabansa har lokacin na bugu da ?arfi yana jin kamar ya kira wayar Humairar a sannan ya ji ko za ta amsa. Hakura ya yi ya shiga ya Wora alwala ya zura jallabiya ya fice zuwa masallaci. Koda ya dawo wayarsa kawai ya Wauka, ba ya jin zai iya ha?uri da kiran Humaira koda ace hakan na nufin rusa tsawon jiran da ya yi, ya gaji zai tunkareta kawai da batun aure. Zantukan matarnan da ya gani cikin mafarki da kuma yanayin da ya ga Humairar sun fi komai Waga mishi hankali duk da yana kyautata zaton alheri ne mafarkin.

Ya kira ya fi sau uku amma amsar Waya ce, a kashe. Don haka ya yanke shawarar kiran Raihana, shi dai babban burinsa jin muryar Humairar.

Ko ringing uku wayar ba ta yi ba ya ji Raihana ta Waga a gaggauce. Sallama ya yi mata ta amsa.

"Ina son jin muryar Humaira, ki haWa ni da ita please."

Kawai sai ya ji ta fashe masa da kuka wanda ba ?aramin rikita shi ya yi ba.

"Me ya faru?! An yi wani abun ne? Ki faWamin."

Gaba Waya ya ruWe, nan take sanar da shi ai kwanaki uku kenan babu Humaira da Ummita balle labarinsu ta kuma ?ara da cewa.

"Abin damuwar shi ne ba a san su waye ba, idan kidnappers ne, ai za su kira su ce a ba su kuWin fansa, waWannan kuwa babu kira ba.." Maganarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login