Showing 165001 words to 168000 words out of 189325 words

Chapter 56 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

199

hana ta zuwa inda uwarta take fisabilillah idan dai ba ni Win ka yi shirin kora ba?"

Abba sosai ya yi mamakin son zuciya irin na wannan matar, wato don ba nata aka yiwa ba? Kai shi yanzu dukkanin dangin Maryama ma tsoronsu yake domin su na shayar da shi mamaki. Yanzun ne ya ?ara fahimtar cewa ashe dai ba tsanarsu wasu a danginsa suka yi ba, ashe Hajiya Maijidda ba a banza ta tsani ganin Maryama ba. Ita din ta jima da sanin ainahin fuskar Maryama.

"Isuhu ka yi shiru ina magana?"

Anna ta bu?ata a Wan zafafe, abin da bai taSa gani kenan a tare da ita ba. Koda dai ya sani cewa duk tafiyarsu guda.

"Kiyi hakuri Hajiya, ni dai Isuhu idan har wannan gida ikona ne, toh Jannat ba za ta ?ara shigarsa ba. Ban raba maku zumunci da ita ba tunda taku ce, amma idan dai a wannan gidan ne toh sai dai ku yi hakuri. Duk sadda kike da bu?atar zuwa wajenta in sha Allahu mota da direba ba zai gagareni samar maki ba."

Anna ta saki baki galala, yau Isuhu da kansa ke yi mata musu? Wato dai ba a shaidar Wan kuturu sai ya girma da yatsa.

"Ai shikenan, tunda dai hakanan ka ce nima yanzu dole zan ha?ura da zaman gidanka. Allah ya bamu alherinsa."

Abba ko a jikinsa ya mi?e.

"A gafarceni Hajiya, amma ni dai na gama yanke magana. Ban ce ki bar gidana ba saboda ba ki yimin komai ba.."

"Aa, wannan dai kora da hali ne. Ba Auta kaWai ka kora ba, nima dama watakila kana da niyyar kora ta tunda iyakar saninka ai ba zan rayu a gidan nan babu Auta ba. Nima dai watakila kana ?ullace da ni, babu yanda ka iya ne shiyasa."

Abba ya Wan yi murmushi mai ciwo jin abin da ke fita daga bakin ?AN ADAM mai mance halacci, mai son kai da son zuciya. A yau dai Anna ita ke korar kanta daga gidansa saboda son rai irin nata.

"Ni dai Allah ya sani, ban kore ki daga gidannan ba saboda na dauke ki tamkar uwa a gareni. Ina mai baki hakuri bisa abin da na yi idan bai maki dadi ba. Ki yi hakuri hakan ba zai sauya komai ba."

Daga haka ya sa kai ya fice, yana jin Anna na salati da kiran wai dama can ya gaji da ciyar da ita amma bai ko juyo ba sai murmushin ba?in ciki da tausayin kansa da ya ke ji na zaSen tumun daren da ya yi tun a farko. Kewar iyayensa ya ji na mamayarsa, ashe dai iyaye ba za a rabu da kewarsu ba musamman ma irin nasa nagari masu halayyar dattako. Ya yi musu addu'ar samun rahmar Ubangiji kana ya shiga mota. Madadin zuwa kasuwa sai kawai ya fice zuwa gidan ?anwarsa Baba Amina.

***
Ya iske ta zaune, Raihana ba ta nan ta fice jarrabawa, hakanan sauran ?anmatan yarannata su biyu su ma sun fice. Ita daya ya iske. Tana ganin da yanayin da ya shigo nan da nan hankalinta ya tashi, ta kira sunan Allah a zuci da kuma fili.

Bayan ya zauna ta gaidashi. Kawai daga tambayarsa ko lafiya, ya soma zubar da hawaye. Baba Amina mace mai saurin kuka don har Abba na cewa su Humaira ita suka biyo, nan da nan ta soma kukan itama.

"Yaya lafiya? Ko mene ya yi zafi maganinsa Allah."

Ya jinjina kai. Ya ba ta labarin dukkan abin da ya sani a yanzu game da Mami har da yanda suka yi da Anna. Ya kara da fadin.

"Amina na yi zaSen tumun dare."

Baba Amina zuwa lokacin kuka take yi sosai. Tausayin Abba da kuma tashin hankalin da ta ji na wai Mami na neman rayuwarsa ya sanya ta wannan kukan. Abban da ya zo don ya samu a rarrashe shi, sai shi ne ya koma rarrashin. Ta mike ta hado masa kayan shayi da abinci, ta yi mamakin yanda ya zage ya ci kuwa, tausayinsa kwarai ta ji, har ta kasa hakuri ?arshe ta dube shi.

"Toh yanzu Yaya hakanan za ka yi zaman rayuwa da ita? Nikam hankalina sam bai kwanta ba, shikenan ka haramtawa kanka cimar gidanka saboda Maryam?"

Ya dan yi murmushin ya?e bayan ya kora ruwan shayi mai dumi a cikinsa.

"Amina kenan, wallahi ganinta ma bana son yi. "

Takaici ya kama Baba Amina.

"Toh Yaya ka yi aure mana."

Ya Wan yi jim sannan ya jinjina kai.

"Tsoron matan nake Amina, ba zan iya auren kowa ba a yanzu."

"Ba duka aka taru aka zama Waya ba Yaya, ni wallahi dama na jima ina yi maka sha'awar auren wata baiwar Allah, da ace za ka bani dama ni zan san yanda zan shawo maka kanta ta amince."

Ya yi murmushi.

"Wato dama kin dade kina so na yi auren kenan."

Ta yi murmushin itama.

"Eh toh, gaskiya kusan hakan ne. Tun da na soma gane wace ce ainahin Maryam na ji haka kawai ina son zamanka tare da wata bayan ita."

Abba ya girgiza kai.

"Mutum abin tsoro ne Amina. Kedai kawai Allah yasa mu dace."

Ta amsa da amin tana mai kara tausayawa rayuwar Yayannata. Haka ya yi mata sallama ya tafi bai ko damu da sanin ko sunan wacce ta zaSar masa ba. Kusan ma bai dauki lamarin da muhimmanci ba. Ita kuwa ta dauke shi da matukar girma, ta kuma dauki Wamarar dagewa da addu'a har kafin ta tunkari Wan uwan mahaifinsu Baffa Tukur da zancen, tana son ta ga tabbatuwar lamarin ko don samar da farin ciki ga yayanta da kuma ganin yanda Maryam za ta ?ara bayyana munanan Wabi'unta kowa ya ankara da shi. Ai tunda har Raihana da kanta ta bude baki ta ce dama Abbanta ya kara aure, ta san cewa lamarin babba ne.

***
Tafiya ta yi tafiya har aka kwashi watanni biyu, Humaira cikin ikon Allah ta samu juna biyu, wani irin tarairaya na musamman ta ke samu daga Fadeel, a wannan watanni Abba ya hana ta taka koda harabar gidansa da sunan ziyara, acewarsa ta yi hakuri da zuwa gidan zuwa wani lokaci. Ita kuwa zuwa lokacin ?arshen damuwa ta shige shi domin so take yi ta ga Abbannata saboda ta sani tabbas yana cikin damuwa. Ta ji komai daga bakin Raihana.

Ganin wannan ne yasa Abba amincewa da zuwanta, ranar ko da ya kasance na zuwannata bai fita kasuwa ba, zamansa ya yi a gida. Yana zaune a falonsa Tasleem ta shigo gaishe shi, ya mance rabon ma da ya ganta don har mantawa yake yi ta a gidan, ya bita da kallo sosai ta sha zumSulelan hijabi tana ta kare cikinta wanda bai kai ga fitowa ba amma hakanan take tsarguwar kada Abban ya ankare da shi. Shi kuwa ramar da ta yi yake bi da ido. Ya amsa gaisuwarta a da?ile ya kauda kai.

"Abba don Allah ina son Wan wani abu zan siya kayan sanyawa na ciki."

Ya Wan yi jim, tabbas yanzun ya sani tana da hakki a kansa, idan bai mata ba yana tsoron Sacin zamanin nan. Ya dan kara dubanta, sai ta ba shi tausayi. Yarinya ?arama ta haWu da zawarci saboda kishin banza da ta Worawa zuciyarta har ya kai ta ga marin uwar mijinta.
Hannu ya sa a aljihu ya fiddo kudi ya ?irga dubu goma ya mi?a mata. Ta yi mamaki sosai don ba ta ma zaci za ta samu kamar hakan ba. Ta yi godiya, har za ta tashi sai ya kira ta, dawowa ta yi ta zauna jiki a mace. Zuwa yanzu ta gaji da zuwa wajen Babandi sai dai ta rasa dalili idan har ya dauki waya ya kirata toh ko me take yi ba ta kammalawa tana rawar jiki za ta je wajensa. Nasiha mai ratsa jiki Abba ya yi mata game da rayuwa da kuma faWa akan rashin alfanun zaman mace babu aure. Ya nuna mata hakan ba zai ?are ta da komai ba, yanzu idan babu shi a duniyar wa za ta tambaya? Abba dai sosai ya yi mata faWa akan ta tsoraci Allah a lamuranta, kada ta bari son duniya da abin da ke ciki ya rufe idanunta. Tasleem jikinta ya ?ara mutuwa, ita fa dama yanzu ta gane dama kyau ba ya kawowa mace miji mai arziki balle kuma surar jiki. Kawai ta gane kaddarar mutum ce komai dake faruwa, yanzu ta bar yiwa kanta hangen miji irin na Humaira don ta san ba za ta samu ba, ita babban abin da ke ramar da ita bai wuce cikin Babandi dake jikinta ba wanda ta ?i ta zubar saboda tsananin tsoron abin da zai biyo baya tsakaninsu idan ta zubar.

"?ar uwarki tana nan shigowa yau za ta kawomana ziyara. Ki sa Ladidi ta samar mata wani abin."

"Abba wa?"

Ya dube ta.

"Humaira."

Ta ji kwalla sun cicciko mata, ta sani Humaira ta zama hajiya, ko ba ta ganta ba ta san za a ganta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba kamar ita ba da ta rasa hakan. Gatanan ba wan ba ?anin, ?arfi da yaji ta zama kwartuwar Boka. Kullum cikin aikata zina take yi babu ji babu gani.

"Toh." Abin da ta firta kenan ta mike ta tafi.
***
Tun fakawarsu a harabar gidan take ta zumuWin fita, ya yi sauri ya danna lock. Ta juyo tana marairaice fuska.

"Kai don Allah Habeebee."

Ta faWi a shagwaSe. Ya yi murmushi gami da lakuce mata karan hanci.

"Ba wani Habeebee, mun zo tare amma sai rawar ?afa kike ki yi gaba ki kyale ni?"

Ta Wan turo baki kaWan, ya kai yatsunsa zai buge ta yi saurin ri?e yatsun ta sumbace su kasancewar gilasan motar masu duhu ne sosai (Tinted).

"Kai Boddo, kar ki sa fa a fasa shigar nan mu juya gida."

Ya faWi da murya mai cike da bege. Ta yi saurin sakin hannun.

"Toh yi hakuri na bari."

Ya Wan lumshe idanunsa kafin ya buWe su yana murmushi daga nan ya buWe motar suka fito tare.

Tana le?ensu ta window, tun da ta ji tsayuwar mota ta yi azamar zuwa jikin tagar Wakinnasu ta tsaya. Koda suka fito ma a kan idanunta ne. Kallon tsaf ta yi musu da ya ?ara haifarmata da tausayin kanta da ba?in cikin yanda rayuwarta ta ?are.

Sun yi kyau abinsu, Humaira ta ?ara haske da jiki, ta ci ado cikin wani tsadadden leshi ruwan toka mai adon ba?i ko daga idanu an san zai yi laushi, ba?in mayafi da jaka da takalminta kuwa, ai sun ?ara fiddota a matar manya ballantana idan aka je ga sar?ar da ta sanya silver colour da abin hannu. Ga wani arnen agogo shima. Hakanan shi ma Fadeel ya yi kyau cikin farar shaddarsa.

Tasleem dake tsaye jikin window sai ta ga tafiyar da suke yi ma da murmushi da ?ar hirar da ta ga suna yi tamkar da gayya suke yi don su ?ara turamata haushi. Sai ta yi saurin sakin labule ta nemi wuri ta zauna, kuka sosai ta shiga yi, ita kam babu wa balle ?anin. Ta samu labarin Hamza ma yana shirin tafiya ?asar waje don wani course da aka tura shi na aikinsa. Ita kam ba ta da rabo sai na wahala. Ta shafi cikin Babandi dake jikinta, sai kawai ta sa hannu a kai.

"Na shiga uku na kashe kaina ni Tasleem!"

Ta faWi da murya a Wage, kusan ma babu wanda ya ji, Mami na Wakinta yayinda su Walid suke can suna murnar ganin Humaira sun kaWa sashin Abba.

Wannan ne ya sa ta yi kiWanta da rawarta. ?arshe ta mi?e ta zura hijabi ta Wauki fos Winta, gwara ta je wajen Jannat don ta nemawa kanta mafita. Ciki dai ba zai zube ba, Babandi ya rantse idan ta zubar to fa sai ya Wauki mummunan mataki a kanta. Wannan ne abin da take shakka. Saboda ba ta son ya kirata a waya ne yasa ta kashe wayar gaba Waya ba ta ko marmarin buWewa gudun kada ya nemi ta zo.

***
Mami kuwa ko kadan ba ta da labarin zuwan Humaira, tana dakinta saboda abin duniya da ya yi mata zafi. Sauyin da Abba ya yi mata, ga waya da ta yi da Anna inda ta fesa zagi na uwa da uba ga Abba a wayar sakamakon ta bar gidan Jannat tana hanya za ta koma Agadez. Ba birninta ba, ?auye bisa rakiyar Jannat. Ita dai Mami ba ya iya cewa komai ba.

***
Humaira da Fadeel zaune a gaban Abba, hira suke yi har da Fadeel wanda yake yiwa kallon Wa a yanzu sama da suruki. Su Walid da Muhsin ko na gefen Fadeel su na cin cakulet din da ya ba su.

"Toh Mamana ba za ki kawo wa mijin naki ruwa ba?"

Sai kuma kunya ya kama ta, ta mi?e tana murmushi.

"Ki shiga can an yi maku girki sai ki taho da shi."

Ta amsa da toh sannan ta fice su Walid suka bi bayanta, Fadeel ya bi ta da kallo tamkar ya maida ta ciki, Allah ya sani, bai san adadin son da yake yiwa baiwar Allahn nan ba. Hakanan Allah ya sanya masa, ba ya fatan ya so wata bayan ta. Ya fi kaunar ?are rayuwarsa tare da ita.

"?ana Fadeel."

Maganar Abba ya katse tunaninsa. Shi yana can kallon Wiyarsa shi kuwa idanunsa na kansa yana murmushi da kokarin auna irin kaunar da ya gani a idanunsa da yake nunawa ?iyartasa. Ya yi saurin amsawa gami da Wan shafa ?eyarsa don ya Wan ji nauyin Abba, ban da iyayen nasa maza babu wani ko wata da ya ke jin nauyin nuna soyayyar Humaira a gabansa, hatta Anti Amarya ba nauyinta yake ba don sun je gidan sau daya da daddare bayan aure. Alhaji ya musu nasiha.

"Ka ce kana da magana kuma na ji ka shiru."

Sai yanzu ya tuna ma ya kira Abban a waya tun kafin zuwansu akan zasu yi wata maganar. Ya jinjina kai.

"Eh Abba, na Wan sha'afa ne. Dama akan zancen abokina ne, Ridwan game da Ummita.."

Abba ya tari numfashinsa yana murmushi.

"Nasan da maganar, yaron da kansa ya zo ya same ni ya nemi iznin zuwa wurinta a can Bichi don su ?ara daidaita kansu. Ban kuma amince masa ba sai da na nemi yardarta ta waya, ta kuma amince. Bayan wannan ne ban dai san ko akwai wani abu ba."

Fadeel ya sha mamaki, shi fa sati guda kenan da Ridwan ya nemi alfarmar ya je masa wurin Abba, shi ko ya na mance? domin idan ya gama wasu uzurorinsa babu abin da ke yawo a kwakwalwarsa face Humaira da tunaninta. Cike da kunya da Wan murmushi ya ce.

"Oh, Abba ai sati guda ma kenan da muka yi maganar da shi, ni ne dai ban samu zuwa ba sai yau.

Dariya Abban ya Wan yi.

"Toh ai shi tuni ma inaga dai ya je."

"Allah ya tabbatar mana da alheri."

Abba ya amsa da amin. Suka cigaba da hirarrakin duniya.

***
Ita ko Humaira shigar ta babban falon tana jin hirar da su Waleed ke mata wai Anti Tasleem tana nan, Anna kuma ta bar gidan sun yi faWa da Abba. Ita dai ba ta ce komai ba amma ta cika da mamaki, sam ba ta da labarin tafiyar Anna, wato dai saboda Jannat itama ta bar gidan? TaSe baki Humaira kawai ta yi. Ita kam tana tausayawa Abbanta, da ganin yanda ya rame ma za ka fahimci cewa akwai wata damuwar dake cin ransa wanda ta sani ba zai wuce sharrin Mami da a yanzun suka san da shi ba. Ganin sun kasa barin hirar gulmammakin da suke tsinta ya sanya ta tsawatar musu.

"Toh ya ishe ni hakanan, Mami tana gidan?"

Suka amsa da eh, ko don Abba ita kam za ta shiga su gaisa, ko ba komai ta haifi Raihana, ta haifi mutum irin Yaya Mubarak mai kirki, sannan su Yassar wadanda yanzu tsakaninsu babu laifi an samu sauyi.

Da sallama a bakinta ta sa kai a Wakin. Ta shiga, Mami ta Wago daga kallon wayar da take yi ta dube ta don ba ta gama tantance cewa ita din ce ba ko aa. Babu shiri fuskarnan ta koma tamkar an aiko mata da sa?on mutuwa. Kallonta take yi tana ?ara nazartar tsadadden leshin dake jikinta da ma mayafin, mayafi ne na masu kuWi. Fatarta kuwa tamkar ka taSa jini ya fito ga wani cikowa da ta ?ara yi. Wallahi da ace za ta iya yanzun za ta tsire Humaira da wu?a ko ta huta da wannan azabar ba?in cikin da ta ke ji game da ci gaban da ta samu. A Sangaren Humaira ko tana nufarta tana ?ara hankalta da yanda ta rame sosai.

"Mami ina wuni."

Ta gaishe ta a mutunce, madadin ta amsa sai ta kawar da kai ta mi?e tsaye ta juya mata baya. Hawaye ne suka zubo mata, hawayen ba?in ciki wannan daukakar da ba ta fito daga jikin tsatsonta ba, sai ma ya kasance yaranta sun ?are a wahale.

"Me ya kawo ki Wakina? Ki tashi ki ficemin bana bu?atarki balle gaisuwarki!"

Humaira ta shanye zafin maganar da ta jefa mata, wato dai ita Mami ba za ta taSa saukowa ba.

"Kiyi hakuri." A zafafe ta juyo

"Hakurin uwarki zan yi?!"

Ta yi mamakin ganin hawaye jage-jage kwance samam fuskar Mamin. Ta kuma cika da al'ajabin wannan zagi da ta bi marigayiyar uwarta da shi.

"Mami me ya yi zafi?"

Wani banzan kallo ta yi mata, itama Humaira ranta ya gama Saci sai tafarfasa yake yi.

"Har abada ke dai Humaira na tsane ki, ban taSa kaunarki ba ballantana kuma ita uwarki Fatima, ki gaggauta cirewa a ranki wai Maryam za ta taSa yi maki kallon wata aba da za ta kalla da mutunci a rayuwa. Ke dai annoba ce domin tun shigowarki cikin rayuwata nake fama da abubuwa iri-iri a rayuwa! Ki ficemin a Waki."

Murmushin ba?in ciki ta yi ta mi?e tsaye, ji ta yi babu wani sauran gurbi na daraja da ta ba wa Mami a zuciyarta. Dama ta jima tana hasashen wannan rashin kauna, a yau kuma ta tabbatar mata da hakan da bakinta.

"Ko ba ki furta ba zan fice Mami, na jima dama da fahimtar ba kya kaunata, fuska biyu kike nuna min. Sai dai ki sani Mami, ni dai Humaira Wiya ce ga Abba, ta jini da tsoka. Babu mai sauyawa tuwo suna,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login