Showing 111001 words to 114000 words out of 189325 words

Chapter 38 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

248

Antinta ke magana a kai ba, sai ta yi tunanin ko don cikin dake jikinta ne kuma ga shi nan an soma sani a gari. Abba kuwa, ya yi shiru yana nazarin maganganunta, da alama sun yi tasiri a zuciyarsa. Ganin haka da sauri Mami ta dube shi.

"Yau kenan kana ?o?ari ka nuna ba ni na haifi Ummita ba? Kokari ka ke yi ka sallamawa Maijidda Ummita ta wuce da ita ko? Kana son nunamin ba ni na haifeta ba, ashe Raihana idan ace ita hakan ya faru a kanta ba zamu yi hakurin duk abin da zai je ya zo ba mu bar ta karkashin kulawarmu ba? Lallai ka sani Yusuf, a yau idan ka amince da dauke Ummita daga hannuna toh ka sani cewa ta tafi kenan har abada ba za ta dawo wurina ba. Na kuma gode da nunamin iyakata da ku ka yi."

Tana kai wanan ta juya ta soma tafiya cikin zubar hawaye, wannan ya tashi hankalin Abba da ma su Ummitan.? Abban na kiran sunanta ta yi banza da shi, ita dai Anti Maijidda na tsaye ri?e da hannuwa a kirji tana kallon irin salon makirci na Mami mai ban mamaki. Ummita cikin sauri ta mi?e ta ri?o hannun Mami tana kuka? kamar ranta zai fita lokaci guda tana girgiza kai amma kalma Waya ta kasa fita daga bakinta. Mami ta dube ta cikin hawayen sai kuma ta shafi gefen fuskarta ta yi murmushin yaudara. Cikin karyar da murya ta ce.

"Kar ki damu Ummita. Da nan din da can duk Waya ne."

Sai a sannan Ummitan ta magantu.

"Aa Mami, kiyi hakuri. Wallahi babu inda zan je, ke din tamkar uwa kike a gareni. Idan har a duniya za iya barin mahaifiyata toh kuwa zan iya rabuwa da ke. Kin rungumeni a sadda na buWi idanuna babu iyaye, kin maida ni tamkar Wiyar cikinki, kin kaunace ni ta kowace fuska. Ni kuwa me zai sa na zama mai butulci a gareki? Kiyi hakuri da kalaman Anti Maijidda, ta yi su ne saboda tsantsar tausayi da kuma ganin kamar zan fi samun kwanciyar hankali a can, amma na tabbata ita kanta ta sani kina nunamin kaunar da ba don kar nayi wauta ba, zan ce ta fi na Raihana da su Anti Tasleem."

Anti Maijidda ta kasa cewa komai tayi gum sai kallo, Abba kuwa sai kalaman Ummita suka kashe mishi jiki, shakka babu gaskiya ta fadi kuma ba zai so a yiwa Mami butulcin nan ba. Ya dai so a farko ya amince da batun Anti Maijidda idan har sauya wurin zai dawo da walwala da farin cikin Ummita. Humaira sosai ta ji dadin kalaman da Ummita ta yi ga Mami, ta tabbata hakan ne kawai zai sanyaya zuciyar Mamin, sai kawai ta ji Anti Maijidda ta sire a ranta. Ita a duniya yanzu ba ta da ma?iyi irin mutumin da zai kushe Mami da ?o?arinta a kansu, abin da dai ta fahimta shi ne, ba a iyawa DAN ADAM, wannan sai mahaliccinsa. Ba ta san mene ne ribarta na aibata Mami ba.

Murmushi Mami ta yi tana dubanta kafin ta dubi Anti Maijidda da ta yi mutuwar tsaye. Sai a lokacin Anti Maijidda zuciya ta tunzurota ta soma magana tana duban Ummita.

"Yau kin watsamin ?asa a ido ko Ummita? Ni kika nuna bani da wani matsayi ko ?arfin iko a wajenki? Wa.."

"Anti please. Ki duba yanayin da take ciki mana ki rabu da zancen nan haka. Ina haWa ki da Allah ki bar komai har ta rabu da abin da ke jikinta lafiya idan har dagaske farin cikin kike nema mata."

Mubarak ke wannan tun soma zancen ya shigo yana kuma sauraronsu. Ransa ya Saci ba kaWan ba da yanda Anti Maijidda ke kushe masa uwa kuma mahaifiya amma ya fi jin zafin yadda take neman haifarwa da Ummita wai sabon Sacin ran na daban. Jinjina kai Anti Maijidda ta yi, ta hadiye Sacin ran nata kamar yanda ya nema. Dagaske ta fi kaunar samun lafiyar Ummita a yanzun da kuma kwanciyar hankalinta wannan yasa ta taka zuwa ga Ummita ta janyota ta rungume. Yadda Ummitan ke kuka hakanan itama take yi.

"Kiyi hakuri ya isa hakanan, shikenan magana ta wuce. Kiyi zamanki anan zamu dinga waya kin ji?"

Ummita ta gyada mata kai, daga haka kuma aka kashe zancen. Abba da Mubarak suka fita don haWuwa da D.P.O don tsaurara bincike akan wanda ya yi wannan aika-aikar da ma neman alfarma gurin D.P.O akan ya fito gidajen yaWa labarai ya faWi abin da ya sani kan satar su Ummitan zuwa yanda aka kaya sadda aka je kwato su.

Mami kuwa ta ?ara jifan Anti Maijidda da murmushin cin nasara sannan ta juya ta bar falon zuciyarta fari ?al yayinda ta bar Anti Maijidda da Wumbin takaici da cizon yatsa. Ta sani addu'a babu abin da ba ya magani, za kuma ta dage da kai kukanta ga Allah, watarana halin Mami zai bayyana ?arara a idon duniya.

***
Anti Amarya ta dubi Alhaji bayan gama nuna masa jita-jitar da ake yaWawa akan su Humaira ta ce.

"Yanzu Alhaji wannan magana ko ?arya ne a yanda sunan gidannan ya Saci fisabilillahi sai ka aminta da auren Fadeel da Humaira?"

Nan da nan Alhaji ya Waure fuska ya ajiye wayar.

"Me kike son ki cemin? Sai na tauyewa Wana farin cikinsa akan ?aryar da ma?aryata suke yamuWiWi da shi?"

Ta tari numfashinsa.

"Saboda farin cikin Wanka mu kuma za ka zubar da namu ?imar gidan a idon duniya? Ka san wannan Sacin sunan kuwa ba iyaka Nijeriya ya zagaye ba? Allah kaWai ya san inda lamarin ya tsaya. Alhaji ya kamata ka buWe idanunka sarai ka dubi lamarin da idanun basira, ni ban taSa ?in Humaira ba saboda ban ga abin ?i tattare da ita ba kamar yanda babu wani aibu da ta taSa yi gareni ba. Amma ana magana ne na haWa zuri'a, idan ya kasance sai bayan mai afkuwa ya afku maganar duniya ta tabbata gaskiya sai ka sa hannu a kumatu ka ce za ka yi tagumi da nadama?"

Shiru Alhaji ya yi, maganganun Anti Amarya suka shiga tasiri a zuciyarsa. Dagaske yanzu idan har zancen duniya ya tabbata shikenan ya haWa iri da Sata gari?

Anti Amarya ganin ya yi shiru sai ta yi Wan murmushin mugunta, ko babu komai dai alamu sun nuna kwalliya za ta biya kuWin sabulu, al?awari ne ta Waukarwa kanta yanda Fadeel bai auri Murja ba ya yi sanadin barinta gidan, toh shima har abada sai ta raba shi da Humaira. Sai ta ga iya gudun ruwansa.

"Shikenan Antin yara, zan dai duba zancen. Mu yi addu'a mu kuma jira mu ga ta inda gaskiya za ta yi halinta."

Ta sauke ajiyar zuciya ganin ta yi nasara.

"Hakane, Allah ya bayyana gaskiyar."

Ya amsa da amin.

?angaren Fadeel kuwa har tsawon kwanaki uku da al'amarin ya fasu yake cikin wani irin tashin hankali da ba?in ciki. Soyayyar da yake yiwa Humaira ta yi ?arfin da ko daidai da ?iftawar idanu ba ya zarginta da fasi?anci balle kuma ya aminta da jita-jitar da ake yaWawa. Wannan ya sanya a Sangarensa shima ya sanya aka soma bincike akan al'amarin don a gano bakin zarensa. Ga bikin babban amininsa nan da kwanaki uku amma hakanan damuwar yanayinnan ya gusar da murnar bikin a zuciyarsa. Ta yaya mutanen da aka ceto su cikin wani hali na maye da kuma muguwar rama da ba?i ace yawon duniya suka shiga? Har abada ba zai yarda da wannan ba. Da taimakon wani abokinsu na makaranta wanda yake babban ma'aikacin sirri na SS, bincikensu ya dinga zurfi. Ibb dai ya zuba idanu kawai yana ?ara mamakin wannan irin zazzafar kaunar ta Fadeel akan Humaira. Har shakka yake yi kada bayan aure ya zame mata mijin tace saboda shi kam abin ma ya shallake tunaninsa.

***
Tasleem tsaye tana safa da marwa a ?uryar Wakinta daga ita sai vest wacce ta Wage mata saboda girman da cikinta ya yi sai ko ?aramin short, waya ne a kunnenta, burinta kawai Antinta ta Waga domin ta ?agu ta ji labari. Har sai da ta kusan katsewa sannan Jannat ta Waga muryarta a sake. Ko gaisawa ba su yi ba ta gangara inda yake ci mata tuwo a ?warya.

"Anti, ina ta neman wayarki a kashe na ?agu naji daga bakinki. Kin ji labarin da ke yawo a media akan su Humaira ko? Anti hala aikinki ne?"

Wata dariya Jannat ta yi daga Sangarenta tun ma kafin ta ce komai Tasleem ta samu amsar tambayarta, sai kuma ta magantu.

"Ni ce nan my daughter, ai ban fanshi marin da munafukar ?anwarki ta yimin ba. Idan sunansu ya Saci a idanun duniya wa kike tunanin zai aminta da auren Waya a cikinsu? Ko a zatonki wancan sakaran Fadeel Win zai ?ara kallonta? Tasleem ki kwantar da hankalinki, yanzu na san na gama Waukar fansa akan Humaira don uwarta. Ita kuwa Ummita kinga cikin dake jikinta ya taimaka wurin da jama'a za su yi saurin aminta. Ke tun sadda al'amarin ya faru nake bibiyar kalaman jama'a ina dariya. Huumm muje zuwa."

Tasleem ta yi murmushi sosai.

"Na ji dadin rabuwar Fadeel da Humaira, na sani ko ya nace akan sonta zai wahala iyayen da suka san mutuncin kansu su yarda Wansu ya aure ta. Amma Anti naji fa wai Abba zai sa ayi binciken wanda ya fara yaWawa don a gano gaskiyar magana. Bakya tunanin idan aka kama shi asiri ba zai tonu ba?"

Tsaki Jannat ta ja.

"Nawa aka yi irin haka Tasleem, kin taSa ganin waWanda aka yi nasarar cafkewa?"

"A'a."

"Toh ki sa ranki a inuwa tawan, babu abin da za su iya. Yanzu ai na kira Abbannaku na jajanta masa har da kukan shegantaka, shi kuwa sai faman godiya da ban hakuri yake."

Suka yi dariya Tasleem har tana ri?e cikinta da ya Wan motsa saboda dariya.

"Ina yinki sosai Antina."

"Nima haka yar uwa. Maminki ce dai ta matsamin da tambayoyi tun ranar farko shiyasa nake ta kashe waya, wai ita ga mai wayo, bugar cikina take yi don ta gane ko ni ce na sanya a yi amma na nunamata ban san komai ba sai ma da ta faWamin. Kema ina jan kunnenki koda wasa kar ki kuskura kiyi maganar da kowa."

Tasleem ta amsa cikin jin dadi da walwala.

"Kar ki samu damuwa Anti. Ba ki da matsala da ni."

Daga haka suka yi sallama zu?atansu cike fal da annashuwar ?untatawa bayin Allah.
***
A kwana? a tashi babu wuya cikin ?udurar Allah, har dai jita-jit????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ar da ake ga su Humaira ya kai watanni biyu, a wannan lokacin ?ura ta lafa sosai sakamakon shaidu daga D.P.O har ma da shi kansa Abba da ma waWanda Abban ya yiwa tayin gidansa don ceto yaran nasa, likitocin da suka taimaki rayuwarsu da ikon Allah,? da dai sauransu sun bayyanawa manyan gidajen jaridu abin da suka sani akan zancen har ma da irin gudunmuwar da suka bayar a lokacin. Wannan ya sanya jama'a suka gas?ata hakanan waWanda suka aminta sai suka rinjayi masu kushe da ?aryata zancen. Da wannan aka rufe babin Ummita da Humaira aka shiga kuma wani labarin daban ya zama abin tattaunawa a sosha midiya. Amma a Sangaren Fadeel, magana ba ta mutu ba don yana nan a kan bakansa na sanya wa a binciko mai wannan aikin? duniya ta san shi kuma ya WanWani yadda ake ji idan aka Sata wa mutum suna.

A ?arshe ma da ya ga ba a samu haWin kai daga jama'a ba, sai ya sanya kuWi har dubu dari biyar ta hanyar tsohon abokin karatunsa ma'aikaci a SS,? ga duk wanda ya kawo labari ko kuma ya ke da sanayya da wanda ya aikata laifin. Nan fa jama'a kowa ya yi ca, burinsu kawai su samu wadannan kuWaWe, a yanda rayuwar ta yi zafi sun san ba ?aramin taimako zai musu ba.

Lokacin da Mami ta ci karo da wannan sanarwar a wani group dinsu na hamsha?an mata wanda Hajiya Lubna ta buWe, sosai ta ji hankalinta ya tashi. Ta ji ta ?ara tsanar Fadeel musamman da ya kasance zuwa lokacin Jannat ta gaji da ?aryata cewa ita ta aikata a wajenta ta fito fili ta faWamata cewar ita ce kuma fansa ta Wauka. Ta sani, muddin ya kasance Fadeel sun ci galabar gano mai laifi to fa sunan Jannat zai Saci kamar yadda ?imarta zai zube a wurin Abba.

Wannan ne yasa ta fita a whatsapp ta kira Jannat, ringing bai fi sau uku ba ta Waga. Mami ba ta jira komai ba ta hau magana.

"Kin karanta labarin dake yawo?"

Cikin rashin ba abin muhimmanci ta amsawa yar uwar.

"Yes, na gani na karanta. Sai me?"

Mami ta danne jin zafin ire-iren magana gatsal da Jannat ke yawan yi mata a lokuta mabambanta ta ce.

"Sai ki girbi abin da kika shuka tun da ke ba kya shawara da? uban kowa idan kika tashi Sarna. Shi dai Fadeel da kike yiwa kallon tara saura gashinan yana shirin ba ki mamaki. Ko kina zaton ?arfin kusancinmu ya kai ya hana shi daukar fansa a kanki?"

Tsaki Jannat ta ja.

"Ni babu wanda ya isa ya kama ni balle kuma ya ce zai yimin hukunci.? ki ga kwantar fa hankalinki kawai, ni abin ya shafa kuma nawa hankalin a kwance yake don haka ba abin da zai faru."

?wafa Mami ta yi.

"Shikenan, kiyi kuka da kanki duk abin da ya je ya zo."

Daga haka ta katse wayar tana sauke numfashi cike da Sacin rai. Ta rasa yaushe Jannat za ta yi hankali. Ita komai ba ta iya bin sa da sauki ba sai ta yi garaje? Ai sai ta je ta ji da kunyatar da za ta yi a idon duniya da ma su Abba.

***
Yakubu ya dubi Futuha da murmushin yaudara bayan ta nutsu tana sauraron abin da zai ce ya soma magana.

"Na lura sam zamanki da Uwargida tun farko ba ra'ayinki ba ne, nawa ra'ayin ne. Hakan yasa na siya maki gida daban a can kusa da yar uwarki Tasleem. Kinga ke kadai abinki babu takura. Hakan ina fatan ya yi maki?"

Wani dadi ya kashe Futuha har ta kasa Soyewa ya bayyana saman fuskarta, dagaske aikin da ta sa aka yi ta hanyar abokiyar karatunsu Anti ba karamin ci yake yi ba tunda har gashinan ya soma tunanin kawo mata sauyi cikin rayuwa ta hanyar keSance ta da abokiyar zamanta da nuna bambanci. Ta yi farr da idanu bayan ta rungumeshi ta sakar masa sumba a lebba.

"Hakan ya yimin sosai fiye ma da zatonka. Yaushe zan koma?"

Wani dadi da sanyi suka lulluSe zuciyar Yakubu ganin ya shawo kanta cikin mugun sauki. Ya san da ace ta san dalilinsa na tashin wannan zancen sauya muhallin da ba ta fara aminta da hakan ba.

"Nan da sati Waya an kammala komai sai tariya. Yanzu ana aikin ?arasa haWa kayan wutar solar ne."

Dadi ya ?ara ?ume ta. Ta ji sosai kaunar Yakubu na ?ara mamayarta. ?acin ranta na hotunan auren Ibb da matarsa Dakta Salma da aka turo group din makarantarsu ya wanku a zuciyarta. Batun karatu dama tun tafiyarta Dubai da dawowarta ta watsar, Yakubu ya nuna ba ya so zai wadatar da ita da komai da take so, hakan ya sa ko a kanta ba ta damu ba balle kuma Abba da dama shima ya fi kaunarsu da zaman auren sai dai ya so ace ta kammala. Mami kuwa itama ganin Wiyarta na samun dukkan abin da ya dace na jin dadin duniya sai ta share zancen karatun.

"Allah ya kaimu lokacin."

Ya amsa da amin, daga haka ta mi?e ta na fadin bari ta kawo mishi abu mai sanyi, shi kuwa ransa ?al ganin nan da sati biyu ?ar Snow za ta zama mallakinsa matsayin matar aure.

***
_Sosai Ummita ke ihun daya cika kunnuwanta tana ambaton sunan Allah iyakar ?arfinta, wannan ya sanya ta nufarta a guje ba ta damu da jinin da ke yawo a tsakar Wakin ba tamkar ruwan famfo ta dam?o kafaWunta tana jijjigawa tana fadin._

_"A'a Ummita kar ki mutu ki bar ni, zasu kashe mu idan suka riske mu a nan. Kinga ki tashi mu gudu!"_

_Rigarta Ummita ta dam?a da ?arfi tana hawaye take fadin._

_"Innalillahi..Kai...Kai..Humaira anya zan rayu? Humaira ko na mutu kar ki bari a jefarmin da gudan jinina. Kar ki bari su yi nasarar rabaki da Wana._ _Ki kira shi da suna Ahmad sannan ki kularmin da shi tamkar ina raye._ _Wayyo Humaira ga Wizzy nan!"_

_Wai sai ta juya ta dubi Wizzy, ri?e yake da ?aton adda a hannu yana kiran sai fa ya raba Ummita da jaririn. Kawai sai kuma ta ga jariri a hannunta, Wizzy zai karSe ta shige gabansa kawai sai ta ga? Mami ta zo ta tureta ta fisge jaririn a hannun Ummita ta dam?awa Wizzy._

"Humaira! Humaira!!"

Sunanta da Raihana ke faman kira tana jijjigata iyakar ?arfinta ne ya sanya ba shiri ta mi?e daga nannauyen baccin da ya kwashe ta a saman darduma. Gaba Waya ta haWa zufa sharkaf duk kuwa da iskar fankar dake kaWawa a Wakin. Ta dam?e hannun Raihana manyan idanunta suka ?ara girma har hakan ya yi mugun kaWa ?an hanjin Raihana, tsoronta kada dai aljanun Humairar ne suka tashi, cikin rawar murya ta ce.

"Lafiyarki kuwa?"

"Ina Ummita?"

Ta nuna mata ?ofar banWaki.

"Wanka ta shiga."

Sai a lokacin ta sauke doguwar ajiyar zuciya cike da tunanin irin wannan mafarkin, me kuma ya haWa Wizzy da Mami? Ta yi Wan nisa a tunani muryar Raihana ta ?ara katse ta.

"Mami ta ce ki shirya ku yi abin kari sannan ki Worawa Sis Tasleem farfesu ta haifi Wiyarta mace suna asibiti. Yanzu zamu wuce da Mamin, idan an kammala tace ki ba Yaya ?assim ya kawo."

Humaira ta gyaWa kai.

"Toh, Allah ya raya. Ki gaidamin ita."

Raihana ta amsa ta fita a Wakin, daidai lokacin Ummita ta fito daga banWakin. Baiwar Allah duk ta rame sai ciki da ya ?ara fitowa, bai fi sauran sati biyu ta shiga watan haihuwarta. Hancinta duk ya buWe. Ta dubi Humaira tana Wigar da ruwan wanka.

"Anti Tasleem ta haihu? Naji kamar haka Raihana ta ce."

GyaWa kai Humaira ta yi jikinta a sanyaye cikin tunanin mafarkinta, Ummitar cikin mafarkinta tana so da kaunar abin da za ta haifa har tana ba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login