Showing 72001 words to 75000 words out of 189325 words

Chapter 25 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

236

kuma alfanun faWin gaskiyar da za ta jaza masa rabuwar da bai shirya ba da Humaira. Yana tsoron ya kasance idan ya zayyana komai yadda yake tafiya a yanzu, ran Alhajinsa ya Saci ya nemi ya fita a hanyar Humaira, wannan ne dalilin da ya sanya shi yiwa zancen kwaskwarima.

"Ka yi hakuri Alhaji, ba wai babu wacce na tsayar ba ne. Akwai, sai dai yarinyar nan da watanni bakwai zuwa takwas za ta kammala makarantar da take zuwa, ta kuma ro?e ni na ba ta dama har su kammala. Wannan shi ne dalilin da ya hana ni gabatar da ita a wajenku. Ina neman ?arin lokaci zuwa sannan, idan Allah ya yarda ba zan ba ku kunya ba."

Alhaji ya Wan yi jim, ba haka ya so ji ba, ya so ace kawai Fadeel din ya ba da damar a nemi auren a haWa da na Wan uwansa (Ibb) amma hakan ma ya ji daWi tunda dai akwai wacce yake so. Don haka sai ya Wan saki fuska.

"Shikenan, su iyayenta sun sani cewa kana neman auren Wiyarsu?"

Ya ji gabansa ya faWi, anan kam ba ya jin zai iya Soyewa don haka ya girgiza kai ya furta kalmar a'a.

Murmushin manya Alhaji ya yi.

"Fadeel kenan, to kai ban da ma abinka, yanzu idan aka tashi mahaifin yarinyar ya aurar da ita ga wani sai ka ce ya yi maka rashin adalci ko?Idan ba kai ba, ina aka taSa wannan wautar? Kana son yarinya amma ka kasa gabatar da kanka wajen iyayenta? A zatonka sun san da zamanka ne kawai saboda kana zuwa hira wurin Wiyarsu? Me zai hana mu ka bamu damar tura wa gidannasu a san da zancenka?"

Ya Wan sosa ?eya kaWan, inama hakan abu ne mai sauki, inama kuma idan an aikata ba zai ga bore daga Humaira ba wadda yana da tabbacin a yanda take gudunsa za ta iya cewa ta fasa auren ma baki Waya, ai ba don haka ba da gudu zai yi na'am da shawarar Alhaji. Sai dai kuma ya sani, ba abu ne mai sau?i ba.

"Ayi hakuri zuwa lokacin da na faWa. Ni kuma zan yi kokarin samun mahaifinta mu gaisa."

Alhaji ya ji abin wani iri, kamar ya yi magana sai dai ya fasa. Can kuma sai ya Sige da nasiha akan kar ya biyewa soyayyar shirme da ake yi yanzu tsakanin matasa na wannan zamani. Abin har ya so ba Fadeel dariya don shi kam ya lura kamar ma Alhajin tunaninsa wani wuri daban ya tafi. Da wannan suka rufe babin zancen suka hau tattaunawa akan Hannatu dake shirin zuwa Kano don ganin mahaifinnasu da ta kwashi lokaci ba su sanya juna a ido ba.

***
Anti Amarya ta shiga har Wakin Murja dake kwance tana juyi, tsayawa ta yi gaban gadon tana ?aremata kallo rai a kuntace sai kuma ta ja mugun tsaki ta soma magana tana ji tamkar ta sha?o ta.

"Aikin wofi kike yi fa Murja, na faWamaki ke za ki wahala a banza muddin ki ka ce ba za ki kokarta ki Soye kishinki a kan Humaira ba a gaban Fadeel. Ke ba ma kishin ba, hatta da son da ace za ki yi hakurin dannewa babu abin da ba za ki iya cimmawa ba. Ke an faWamaki koda ace asirin za ki yi masa zai ci shi idan ba ki kasance gwanar kissa ba? Ai komai Wan dabara ne. Yanzu kiga, daga ganin hoto gaba Waya kin susuce har abinci sai kin yi dagaske kike iya ci? Yanzu idan kuma ace zancen auren kika ji ya za ki yi da ranki?"

Murja ta mi?e zaune, gaba Waya idanunta sun kumbura. Ta dafe kirjinta.

"Wallahi Anti ji nake yi kamar kirjina zai fashe, Anti ban san haka kishi yake da tsananin zafi ba sai akan Fadeel. Na rantse a yadda nake jin zuciyata zan iya sa wu?a na tsire Humaira da ranta muddin aka wayi gari ta kasance matar Fadeel balle kuma har abada hakan ba za ta afku ba idan har ina numfashi a doron ?asa."

Kausar dake bakin ?ofa wacce ta yi niyyar shigowa don duba lafiyar Murjar da ta ji Anti Amarya na cewa ba ta da lafiya, kawai sai ta ja baya ta juya jin maganganun da suke fitowa daga bakin Murja, iyakar abinda ta ji kenan, koda ace ma Anti Amarya ta yi magana kafin nan toh ita kam Allah bai nufe ta da ji ba. Ita gaba Waya gidan ma ya ishe ta, Fu'ad wanda ya je Abuja da niyyar kwanaki uku, sai gashinan har ya cinye satin ya ?ara shiga wani satin. Burinta kawai ta bar gidan ta koma nasu, ita sam ba ta gane rayuwar da ake gudanarwa a gidan ba, Anti Amarya dai lamarinta kamar gaske kuma wasu lokutan takan ji kamar kawai wasan kwaikwayo ne. Ga Murja a gefe wacce kallo dubu idan za su yi wa juna a rana babu abin da take samu a wajenta sai harara. Su Khadija ne abokan hirarta sai kuwa wayarta, sannan Fadeel wanda ba kasafai yake shigowa falon ba. Hakan yasa duk ta ke jin ta a takure.

A daki kuwa, motsin mutum ne ya sa Anti Amarya saurin fitowa, bayan Kausar ta hango lokacin da take barin wurin, ta dawo ciki ta rufe ?ofar. A fusace ta kalli Murja.

"Kin gani ko? Zai wahala idan Kausar ba ta ji abin da muke tattaunawa a kai ba. DaWina da ke ba kya iya Soye abin da ke ranki ko na sakanni. Kin san ba mu kaWai ke zaune a gidan ba amma ki yi ta faman suSul da baka. Mtsw, don Allah ji yadda kika maida kanki, babu wanka balle kwalliya, akan Wa namiji kamar wacce ba ta yi karatu ba kina son ki zautar da kanki. Ke idan da ace ni ce ke, ai wannan ne lokacin da zan soma shigewa Humaira da hujja. Ki raSe su, ki zama tamkar yar uwarsu, ki yawaita kai musu ziyara daga haka sai ki dinga gano sirrinta. Ke daga haka ma idan ma wani aikin ne sai kiga mun ci nasarar yi mata a sau?a?e mun farra?a tsakaninsu. ?angaren Fadeel ki kwantar da kai ki ba shi ha?uri ki nuna masa cewa ke fa kin ha?ura da shi tunda ba ya kaunarki. Ki yi iyakar ?o?arinki wajen ganin kin danne abin da ke zuciyarki a kansa, ki rage shige masa. Ladabi, rage kulashi da ma ba shi girma matsayin yayanki shi zai sa ki shawo kansa ya sakar maki fuska kamar yadda ku ke rayuwa a baya. Ki nuna masa kin fi shi so da kaunar Humaira, ki koWa ta a gabansa da ma duk sauran kissa da kisisina na mata, wannan kaWai idan ki ka aikata babu mai zarginki koda nan gaba wani mugun abin da za a yi ya kawo ?arshen soyayyar Fadeel din da Humairar. Komai fa Wan siyasa ne."

Murja wacce a farko taje jingine da gado tana dafe da ciki tsabar horon yunwar da take yi wa kanta, ba ta san ya aka yi ba ta mi?e zaune sosai tana ?ara baza kunne ga Antin dake magana ?asa-?asa kamar me raWa duk domin tsaro da kuma gudun kar wani ya ji su. Anti Amarya na kawo wa ?arshe ta rungume ta su na dariya, har ta Wan ji ?wari a jikinta, sai kuma ta Wan yi sanyi.

"Amma Anti anya zan iya danne son Fadeel?"

Harararta Antin ta yi.

"Da ya kike rayuwa babu soyayyar tasa? Hakanan za ki danne muddin kina son ki cimma manufarki. Ku yaran yanzu babu kissa ba dabara, sai soyayyar kawai. Toh abinci ma ki dafa shi zallarsa babu wasu sinadaran da zai ?amsasa shi ya ?ara mishi WanWano ai lami za a ci. Balle kuma soyayya, ai idan kana da kyau ka ?ara da wanka. Ba kashe Humaira ba, ko tsire ta za ki yi da wu?a a gabansa, wataran ba zai ko kalla ba balle ya ji abin a ransa. Ki soma wannan ni kuma na san inda zan je a yi maki aikin da zuciyar Fadeel din zai huce ya soma sanyi a lamarinki. A hankali za ki mallake shi."

Dariya Murja ta yi cike da jin dadi da annashuwa. Ta lumshe idanu tana jin wani sanyi a ruhinta, amma fa al?awari ta Waukarwa kanta sai ta WanWanawa Humaira azabar da sai ta gwammace kiWi da karatu. Ba don tsoron kar ta kashe ta da hannunta itama a kashe ta ba, ai da tun a ranar da ta san Fadeel ita yake so sai ta je har gidansu ta sha?e wuyanta har lahira.
Da wannan ?arfafa gwuiwa na makirci na Anti Amarya ta samu nutsuwa har ta mi?e ta shige wanka ita kuwa Anti Amarya ta fice a Wakin. Koda suka haWu da Kausar a falon, babu abin da Kausar Win ta nuna koda wasa kuwa wannan ya cirewa Anti Amarya zargin ta ji tattaunawarsu.

***
MU?ADDARI...

Ummita da Humaira tsaf cikin shiri, gidan Tasleem suka yi shirin zuwa ba ta jin dadi. Bisa umarnin Mami, Humaira ta yi mata romon Wanyen kifi mai Wan yaji saboda ta ji daWin bakinta, ta shirya shi a kwando, suka Wibarwa Raihana kayanta kala biyu kamar yadda ta bu?ata, tun soma ciwon Tasleem ta je gidan ta Wan kwana biyu.
A hanya su na tafe Ummita na amsa wayar Sahabi tana faman doka murmushi, abin da ba ta saba ba kenan, wato waya a hanya. Asalima ta tsani su fito hanya Raihana ta Wau waya tana dannawa ko kuma amsawa, hakan ya ba Humaira mamaki. Ummita na ajiye wayar ta dube ta.

"Yau ke ce da kanki kike waya a titi? Lallai an gaida Sahabi, daga ranar da ya aiko aka sa ranar aure, shikenan sai soyayyarsa ta ?ara girma a zuciyarki har ta sanya kina karya sharuWWan da kika Worawa kanki."

Ummita ta yi murmushi karo na barkatai.

"Ke ni kaina yau jin soyayyarsa nake yi har cikin ?o?on raina. Kin san Allah, a yadda nake jin Sahabi a yau Humaira, da ace a karshen watannan ma a yi bikinmu da.."

Sauran maganar ta ma?ale a fatar bakinta sakamakon wata mota da ta gifta su a guje, idanu waje ta bi motar da idanu. Humaira dake kallon hanya jin Ummitar ta yi shiru ya sanya ta dubanta don ta gani ko lafiya. Ganin hankalinta na wani wurin ya sa ta ce.

"Lafiya?"

Cikin alamar ruWewa kadan ta ce.

"Wallahi wata na gani kamar Anti Jannat a cikin mota ta wuce."

"Anti Jannat kuma? Ina ce sai jibi Mami ta ce za su taso?"

Ummita dai da har lokacin matar na mata gizo ta amsa.

"Eh, hakane, amma nidai sai naga kamar ita na gani a motar."

Cikin rashin ba zancen muhimmanci Humaira ta taSe baki gami da Waga kafaWa kaWan.

"Wata?ila kama ce kawai ba wani abu ba."

"Hakane."

Ummita ta amsa, daga nan suka bar zancen.

Kafin su kai ga tarar abin hawa sai suka ji wani Wan sahu na magana.

"Siii, ina ku ka yi?"

Suka dube shi, ya sha jallabiyarsa ga wani a gefensa matashi cikin ?ananun kaya. Ummita ta zubamusu idanu ba tare da ta ce komai ba, sai Humaira ce ta amsa da cewa Kuntau.

"Ku taho mu tafi."

Har Humaira ta soma tafiya, Ummita ba ta tako ba don haka ta juyo ta dubeta.

"Ki taho muje mana."

Jiki a sanyaye kamar ta cewa Humaira su sauya wani Wan sahun sai ta ji harshen nata ya mata nauyi ga kuma Humaira wacce har ta sanya kai a ciki wannan ya sa itama ta shiga. Sun soma tafiya hankalin Humaira a kwance idan ka cire Ummita da ta yi wani irin la'asar, sun yi gaba kaWan wani namijin ya tsayar da su ya shiga yana rangaWa sallama. Sallamar da ya yi ne ya sa Ummita Wan samun nutsuwa, ko ba komai ai ba za ka yi tunanin cuta daga wanda ya nemar maku amincin Allah ba ku ka amsa. Gudu sosai Wan sahun yake, Humaira na ta Wan yiwa Ummita hira jifa-jifa, ita kuwa ta kasa nutsuwa sam, hankalinta rabi na ga kallon hanya da kuma gilashin Wan sahun wanda ke kallonsu jifa-jifa suna hada idanu da shi. Ba ta san ya aka yi ba, ita dai ta kamar na kusa da ita ya fiddo wani hankicif, kafin ta yi aune ya hura mata a fuska, Humaira ma ta juyowa kafin ta kai ga wani yun?urin ya sha?a mata, ji kake yaraff, sun lafke bacci mai tsawo ya Wauke su.
***
Ummita ce ta soma farkawa, a hankali ta shiga murza idanunta da suke yi mata dishi-dishi kafin ta buWe su tarr cikin Wan tsurkukin Wakin da babu komai ciki. Daga wata ruSaSSiyar fanka wacce kallo Waya za ka tabbatar da ba ta aiki, sai ko shimfiWaWWiyar katifa wadda da ita da babu duk Waya tsabar yamutsewar da ta yi ta rabe biyu. Duk dai a ?okarinta na son tunano abin daya faru ta ci gaba da bin bangon Wakin da kallo wanda duk ya yi jirwayen ruwa ga yaana da gizo-gizo da suka cika lungu da kusurwarsa. Sai ko wata ?ofa wacce daga ?asanta gaba Waya ta rarake har kama iya hango ruwan jirwayen banWakin da ya kwanta har ya rine. Ban da tashin zarni da wari babu abin da ke fitowa daga cikinsa. Ta kuma mi?e tsaye a razane, ta tuna komai, su na hanyar zuwa gidan Tasleem ne su kai wa Raihana kayanta sai ko sa?on Tasleem din na girkin da aka yi mata. Toh nan ina ne? Ya aka yi suka ?are anan? Fuskokin matasan nan uku ciki har Wan sahun suka zo mata tarr tarr, da sauri ta nufi windon dake Wakin, a buWe yake sai dai an zagayeshinda wasu irin ?arafana masu nauyi, ciyayi ne cike a wurin har ba ka iya hango bangon dake waje.? Ta juya ga Humaira da har lokacin hodar ba ta sake ta ba ta shiga jijjiga ta tana kukan tashin hankali, ga jikinta da ke rawa ta ko'ina.
A Sangaren Humaira kuwa, ji ta yi kamar a can wani nisan wuri Ummita ke kiranta, a hankali ta buWe idanunta tana kallonta dishi-dishi. Sannu-sannu kuma har ta dawo hayyacinta ta fahimci dagaske ne dai Ummitar ke kwala mata kira. Ta mi?e zaune tana ambaton innalillahi. Irin yanayin da Ummita ta shiga, shi ta tsinci kanta a ciki. Da rawar murya ta ce.
? "Na...nn..nan ina ne?"
Ummita dake hawayen itama girgiza mata kai ta yi hankali a tashe.

"Ban sani ba Humaira, ban san ina muke ba. Mun faWa hannun mugaye azzalumai, jikina tunda muka fito yake ba ni cewa babu alheri a tafiyarnan amma ?addara ta riga fata. Na so na ce maki kar mu shiga dan sahun nan ban yarda da su ba amma.."

Sauran kalaman Ummita suka ma?ale a fatar bakinta sakamakon bankaWo ?ofar da aka yi da ?arfi aka sanyo kai cikin Wakin. Mutum biyu ne cikin samarin, da matu?in napep Win da kuma wanda ya zauna kusa da Ummita a hanyarsu. Hannun Waya ri?e da leda. Yayinda mai napep din ke shan taba hankalinsa kwance yana fesar da haya?i suna murmushi, matu?in Wan sahun ya ce.
? ? "Kun sha bacci, sannunku da tashi."

"Ku dubi Allah da annabinsa s.a.w ku yi hakuri ku kyalemu mu tafi. Iyayenmu ba su da kudin da za su bayar domin fansarmu. Ku yi hakuri mun tuba, wallahi komai da ke cikin jakkunanmu ku Wauka halak malak mun bar maku."

Ummita ke wannan zancen cikin rawar baki da murya. Ga kukanta da ta kasa tsaidawa, itama Humaira kukan take yi ta ma kasa cewa komai. Matashin da ya soma magana tun farko, ya kai duba ga na tsayen wanda ya fi shi sirantaka da tsawo, tun murmushin farko da ya yi bai ?ara koda buWe ha?ora ba, shi kuwa na dur?ushen ya bi Ummita da kallo sannan ya yi ?ar dariya. Madadin ya yi magana sai ya zu?i sigari ya busamata a fuskar, ta kauda kai tana tari, Humaira ma ta toshe hancinta. Hannu ya mi?awa na tsayen, ledar ya mi?o mishi ya karSa ya buWe ta. Shinkafa da wake ne sai manja da yaji, ya tura musu ledar ya ?ara fesar da haya?in sigari kana ya ce.
??
?? "Ga food ku eat. Kin gane bana son musu, if you follow za rules here, you will ji dadi sosai. If you break oza, za ku yi dana sanin haihuwar da uwarku ta yi."

Anan ne Humaira ta samu ?arfin gwuiwar taso mishi cikin Waga murya ta ce.

"Sai dai taka uwar ta yi nadamar haihuwarka idan tana raye! Ba dai namu iyayen ba!"

Tana fadin haka a zafafe ya Waga hannu ya sauke yatsunsa saman fuskarta ji kake tas! Ya fizgota ya take ?afarta kafin ya Wosana mata karan sigari inda haya?i ke fita a saman fatar wuyanta, ta saki ?ara iyakar ?arfinta na azaba, Ummita ta shiga ?okarin kwace ta tana haWa shi da Allah da Annabi kan ya yi ha?uri. Don kansa ya sake ta, wurin kuwa nan da nan ya yi jazur ya ja ruwa.

"Ke har kin isa na zageki ki rama don ubanki?! Banza ?ar iska kawai! Kika ?ara? yimin irin wannan kuskuren da shishshigin sai kin raina wayonki."

Ya ?ara ?udundumo ashar ya watsa mata, har ya sa kai zai fice ya dawo da baya ya sanya ?afa ya murje abincin ledarnan har ya baje a ?azantaccen tayils din wurin. Ya dubi wanda suke tare ya soma magana da muryar ?an daba.

? "Kai Bad boy, koda wasa kar a ba su abinci da ruwa har sai don kaina na baku iznin haka. ?an wahala kawai."

Daga haka ya sa kai ya fice, wanda aka kira da Bad boy ya watsamusu mugun kallo sannan ya bi bayansa gami da maida ?ofar ya rufe gam da mu?ulli. Su na tafiya Ummita cikin kuka ta Wago Humaira tana duba wajen da aka sanya mata wutar sigari. Humaira hawaye kawai ta ke yi idanunta a runtse ga raWadin da ya addabe ta.

"Kiyi hakuri Humaira, don Allah ki kai zuciyarki nesa har mu samu kuSuta daga hannun waWannan azzaluman."

"Toh." Shi ne amsar da Humaira ta iya bayarwa kawai, daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login