Showing 60001 words to 63000 words out of 189325 words

Chapter 21 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

226

shiga ba ta amsa mata tambayarta ba sai da ta ?ara nanatawa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta Wan yi murmushi.
??
?? "Na lura sosai, amma ni abin da tunanina ya ban ko dai ta sauya ne tana gudun wani abu ya ?ara haWaku ki maimaita abin da kika yi. Kin san fa ba zai yiwu ace ta mance ba."

Dariya? ta yi.

"Ikon Allah, toh ni ai na mance. Kawai dai sauyin ne ya Wan bani mamaki. Babu kyara babu hantara, babu kirana da bare da ta saba yi ba komai. Sai na ke ganin kamar da walakin goro a miya."

"Ki yi mata kyakkyawan zato, Allah yasa sanadin abin da ya kasance ta yiwa kanta faWa. Ni kaina idan kin lura ai ta rage Woramin aiki tunda wannan zuwan ta sa an nemo mata yarinya mai kula da yara. Kawai dai mun saba da yaranta ba yanda za a yi ta iya raba wannan kaunar."

Humaira ta kalle ta, zuciyar Ummita mai kyau ne, da Allah ya tashi, sai ya yi haWa ta da mutumin kirki irinta wato Malam Sahabi. Mutum mai hakuri da kunya kamar wani mace. Amma abin mamaki duk kunyarsa idan suka ga sa?onnin soyayyar da yake turowa Ummita sai mamaki ya kusan kashe su ita da Raihana. Har rantsuwa suke kusan yi su ce ba shi ba ne waninsa ne.

Ummita ta harareta.

"Kallon fa?"

Murmushi Humaira ta yi mai kyau da ya fiddo wushiryarta.

"Kawai kina bani mamaki da kike kokarin kare wadannan mutanen da ba su taSa kaunarmu ba koyaushe."

"Uzurin kenan Humaira. Aure fa zasu yi su bar mu yanzu. Mu ma kuma..."

"Toh naji ya ishe ni hakanan Malama matar Sahabi."

Ummita ta sa dariyar jin abinda ya fito bakinta, ita din ma taya ta ta yi. Har suka isa ?ofar asibitin su na hira abinsu ana iska kaWan kaWan mai daWi.

??
?? Ibb ne tsaye tare da masoyiyarsa Dr Salma, yayinda Fadeel ke zaune cikin mota yana jira su yi sallama. Mahaifiyarta ce kwamce a asibitin inda anan take aiki, suka zo dubiya ta yo musu rakiya har gaban mota. Bayan sallama da Fadeel ya koma mota yayinda suke hirarsu da Ibb tamkar kada su rabu, shi kuwa Fadeel kansa ya kwantar jikin kujera yana Wan kallonsu yana murmushi. Shakka babu sun dace dari bisa dari. Dogaye ne su duka biyun don zasu kusan yin kai Waya, Dakta Salma ba?a ce, kwayoyin idanunta da ha?ora ne kawai idan ta bude masu haske a fuskarta. Tana da kyau, ba ta da jiki sosai amma ba za ka kirata da siririya ba. Tana da diri masha Allah, sanya take da doguwar riga sai coat na likitoci da ta sanya saman kayan, sai kuwa mayafi ?arami da ta yi rolling kanta da shi. Hannunta cikin aljihun rigar, gaba daya hankalinsu ba ya kan Fadeel da ya lula duniyar tunani da jin inama ace shi da Humaira ke wannan hirar ta nishaWi. Allah kaWai yasan yanda zai ji a lokacin. Ya soma gajiya, hakurinsa ya soma kai wa karshe amma yana dannewa gudun Sacin ranta. Ya horu da rashin ganinta ido da ido ba hoto ba, ya sha zuwa ya tsaya a nesa kaWan da gidansu ko zai ga wulkawarta sai dai ko mai kama da ita Allah bai taSa ba shi ikon gani ba. Tabbas Raihana na kokari gurin aikamasa hotunanta wasu lokutan ma ba ta san ana Waukarta ba. Hatta da karamin video sadda take aikin snacks sai da ta Wauka ta aikamasa. Yakan ji inama yana da iko da ita, inama matarsa ce yana kusa ya ri?o ?ugunta ya sanya ta a jikinsa ya bayyana mata irin yanda soyayyarta ke cin zuciyarsa sai dai kuma babu hali. Azabar da bidiyon ke sanya shi ciki ne ya sanya shi dakatar da Raihana daga turo bidiyo face hotuna.

? Ya ja dogon numfashi ya furzar gami da kallon gefe guda yana mai kauda kai daga kan lovebirds. Hango wata ya yi kamar Humaira, ya Wan yi tsai da idanu don so ya tantance abinda yake gani, sai kuma ya kauda kai. Ya fi tunanin gizo Humaira ta soma yi mishi, sai kuma ya kara kallo. Wannan karon ita ce tabbas, tana sanye da doguwar riga na material mai mayafi Jajaye. Yanayin kalar da garin ya yi, sai ya ba wa hasken fuskarta damar she?i musamman da ya kasance tana cikin annashuwa da kwanciyar hankali da alama babu wani abu dake damunta. Sai hira suke da abokiyar tafiyarta wadda ya gane ta, Ummita ce. Ya ganta a hoto don ba hoton Humaira kaWai ba, hatta da ?an gidan sai da Raihana ta turamishi hotunansu da kuma bayanin ala?arsu. Har ya kama murfin mota zai fito ya tuna al?awarin shekara da ya Waukar mata kawai ya fasa ya cigaba da kallonta. Dab da motar suka tsaya suna kalle-kalle kasancewar gilasanta tinted ya sa basu ganshi ba, shi kuwa Ibb shalelan Juliet, bai ma gansu ba ya lula wata duniyar sai buWe ha?ora yake yi kamar gonar auduga.

Humaira ta Wan yamutse fuska tana gyara gyalenta da iska ke kaWawa.

"Nikam asibitin nan juyar da kai gareshi, don Allah ?ara kiranta ki ce bamu gane wajen da ta ce ba kinga garin yana kara haWewa."

Itama Ummita duk ta damu ganin hadari ta fiddo waya ta dannawa Sadiya. Nan ta ce su tsaya inda suke ta gansu.

Suka ja kuwa suka tsaya, Humaira ta zubawa mutanen dake ta shawagi a wurin idanu tana godiya ga Allah a ranta idan ta ga an wuce da marasa lafiya dayake suna daidai Emergency. Ba su wani jima ba sai ga Sadiyar ta iso, bayan sun gaisa ta karSa ta yi musu godiya suka juya suka kama hanyar fita.

Fadeel kamar wanda aka tsikarawa allura haka ya zabura ya fito daga motar ya dubi Ibb.

"Malam ka zo mu tafi ba ka ganin yanda garin ke haWewa wai?"

Suka dubeshi, Dakta Salma ta yi murmushi.

"We are sorry Amininmu. Bari na kyale shi haka. Nagode sosai ku gaida gida."

Bai ko kalleta ba ya amsa da toh don shi gaba daya hankalinsa na ga su Humaira yana fatan Allah ya sa su amince su sauke su a gida. Ibb ganin an soma yayyafi ya yi mata sallama ya shiga motar ya tayar.

"Please and please ka yi sauri kada su hau abin hawa, so nake ko yaya ka yimin kokari ta amince mu kai su gida."

Ya tayar da motar ya soma tafiya sannan ya dubi Fadeel cikin rashin fahimta ya ce.

"Wa kenan kake magana a kai?"

Fadeel da idanunsa ke kan su Humaira wadanda suka kara Waga ?afa ganin ruwa ya soma sauka bai ce komai ba face nuni da ya yi mishi da hannu. Sam bai ga fuskokinsu ba sai baya, kafin ya yi magana Fadeel ya sake tarar numfashinsa.

"Humaira ce."

"Ohh." Abin da kawai Ibb ya ce kenan.

Yana zuwa daidai saitin inda suke ya tsaya har yana tare musu hanya, Humaira dake saitin wurin ta kalli motar ranta a Sace don a ganinta ko waye yana sane ya sha gabansu. Ta bude baki da zummar magana Ibb ya sauke gilashi suka kalli juna. A gaggauce ta gaishe shi, itama Ummita haka, ta gane shi saboda tana ganin hotunansa a wayar Raihana, shi ne dai wanda y taimaki Raihanar.

"Gida ku ka nufa ne? Ku shiga na sauke ku don yanzu idan ku ka shiga napep ji?ewa zaku yi."

Ruwan sosai ya ?ara ?arfi, Humaira ta buWe baki za ta ja musu Ummita ta dafe hannun da sauri ta amsa.

"Toh mungode." Ta kalli Humaira, a hankali kuma a gaggauce ta ce.

"Muje Humaira, yanzu ba lokacin jan musu ba ne, wallahi nidai ina mura kin sani, ruwannan ya dake ni kuma lafkewa zan yi da bikin nan."

Jin haka Humaira ta amince suka shiga, ita ta soma shigewa sai Ummita. Motar sanyi sakamakon Ac dake aiki. Sai a lokacin ta lura da wanda ke zaune a gefen Ibb din, ji ta yi kirjinta ya buga dam, ta rasa dalilin bugawar kamar yanda ta kasa dauke idanu a kansa. Shi Winma ita yake kallo babu ?ak?autawa har bai iya ya amsa gaisuwar Ummita ba. A bangaren Humaira ji ta yi idan ta cigaba da kallonsa ranta zai iya fita saboda wani irin zafi da take ji a kirjinta ga kanta dake faman sarawa don haka da sauri ta kauda kai ta matsa ta ma?ure a kujerar bayansa tana jingina da kofar motar. A hankali Ibb ya dan bubbuga kafaWar Fadeel, firgigit ya dawo hayyacinsa ya gyara zama, gilashinsa ya zaro a aljihu ya rufe kwayoyin idanun da so da tsananin kauna ga kewa suka haWu suka galabaitar. Dakyar Humaira ta iya gaida Ibb sannan ta gaida Fadeel din ba tare da ambaton suna ba. Shi ma amsawa ya yi can ?asa.

Ibb ke tambayar Ummita abin da ya kawo su asibiti.

"Kuna da marar lafiya ne?"

"Aa, aiko mu dai Anti Tasleem ta yi. Ita Win Waliba ce a nan. Nursing take karantawa ne."

Dan jinjina kai Ibb ya yi.

"Ok, na fahimta."

Jin motar ta Wauki shiru sai rediyo dake aiki sai ko ruwa da ke ji?a gilasan motar yana sauka a guje saboda karfin da ya yi. Ummita ta dubi Humaira.

"Wai, da tuni yanzu fa mun ji?e."

"Uhm." Shi ne amsar da ta ba ta. Fadeel kuwa lumshe idanun ya yi ya ji sautin Uhm din har tsakar kansa, gaba Waya sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi. Kamar kuma haWin baki sai ga gidan rediyon sun saki wa?ar Breaker mai taken Kalmar So. Humaira sam hankalinta ba ya jikinta, ji take kamar ta buWe motar ta dira a cikinta. Gaba daya koina a jikin rawa yake, Ac ke kaWawa a motar amma ita zufa take. Ta tuna da ambaton Allah ba shiri ta shiga ambata a ?asan ranta a hankali ta soma dawowa cikin nutsuwarta.

A bangaren Ummita da Ibb, hira suke Wam taSawa kaWan, shi kuwa Gogan da Humaira ba ka jin komai daga bakinsu, babu kamar Fadeel da yake jin wa?ar ta zo daidai da yanayin da yake ciki. So yake ya tambayi ya take? Ya lamuran rayuwa? Ba ta hakura ba har yanzu? Ba ta amince ya turo iyayensa ba? Sai yaushe? Amma ina! Babu ko kalma Waya da yake jin zai iya furtawa, ba ya fatan rabin shekarar da ya kusan cinyewa ya tashi a banza balle ya ga shekarar ida? da rai da lafiya, wannan ya sa yake takatsantsan ya kuma jure bai ?ara kallonta ba tunda ko ya kalli side mirror ba ya ganin komai face danshin ruwan dake kwarara sai ko hasken fitilun motocin dake saman titi.

Har suka iso gidan ba ka jin uffan daga Fadeel, shi kansa Ibb sanin halin mutumin ya sanya bai takale shi da hira ba ko sau Waya. Ya dai san yau Humaira ta fama mishi inda yake mai ?ai?aiyi.

"Ko mu karasa da ku har cikin farfajiyar?"

Wannan kalmar ya sa Fadeel cire gilashin idonsa, ya dubi gidan su Humaira, wato har an iso kenan.

"Aa, mungode sosai. Bari mu karasa ciki."

Cewar Ummita. Humaira kuwa har ta kama ?ofar ta bude, amma ina, iska mai karfi da ruwan da ya fesomata ya sa dole ta koma ta rufe. Fadeel ganin haka ya juya bayan, sai a sannan ya kara kallonta ido cikin ido, da sauri ya dauke idanunsa ya dan kai hannu baya ya dauko lemar dake ajiye a wurin. Fitowa ya yi ya buWe lemar, babba ce don ta fi ta Ummita girma, Ummita kam tuni ta fita itama ta bude nata lemar da ba zai ishe su ba su biyu koda a dazun ne. Kofar Humaira ya bude gami da mi?amata lemar. A sanyaye take dubansa.

"KarSa mana Humaira." Ibb ya furta, ta kalleshi.

"Mungode sosai, Allah ya kiyaye hanya." Daga nan ta fita, sai ya kasance su biyun a ?asan lemar. Kan Fadeel a ?asa ba ya son kallonta gudun Sarowa kansa aiki, ta sa hannu ta karSa sannan ta dan ja baya kaWan.

"Idan na shiga zan aiko a kawo."

Murmushi ya yi mai kyau har a sannan bai kalleta ba ya amsa da toh. Daga haka ya fice ya koma cikin motar ya rufe. Ita ma ta nufi kofar da gudu-gudu.

"Muje."

Ba musu Ibb ya yi reverse ya juya kan motar suka bar layin. ?ar dariya ya yi.

"Fadeel kana son Humaira."

Fadeel bai iya kallonsa ba ballantana ya samu amsa. Ya kara cewa.

"And you know what? Kun dace sosai."

Nan ma bai kalleshi ba sai dai ya yi murmushi. Ganin ba ya son magana ne ya sa Ibb rabuwa da shi.

***
A can kuwa Humaira na shiga ta bada lemar a mi?a musu, Wan aike ya dawo ya ce babu kowa a wajen, ta karSa a sanyaye ta shige Wakinsu da shi. Madadin ta karasa ciki sai ta ajiyeshi a Wan gefen don ya sha iska. Suka sauya kayan jikinsu saboda ji?ewar da suka Wan yi. Ummita ta Wauro alwala sannan itama ta Wauro, koda ta idar da sallah kwanciya ta yi saman dardumar don kanta har lokacin sarawa yake yi kamar jijiyoyin kan nata za su tsinke. Tuna Fadeel kaWai yana haifar mata da rawar jiki da ciwon kai, daga haka kuma sai ta ji kamar ana mata ihu a kunne. Kafin ka ce wannan sai ga Humaira ta soma kuka sosai. Ummita da ke kwashe ji?a??un kayansu ta juya da sauri ta juyo. Allah ya taimaka su kaWai ne a Wakin ta ro?i yanmatan akan su fita ta gyara don sun yi kaca-kaca da shi. Tuni ta fahimci matsalar jinnunta ne, ta sha mamaki ma da bai tashi a mota ta yiwa su Fadeel rashin mutunci ba.
Da sauri ta fice zuwa kicin, can baya ta zagaya inda ake dora babban tukunya a icce saboda yawan da aka yi. Garwashi ta zuba cikin kasko ta dauka da sauri gudu-gudu ta nufi dakinsu. Mami dake kokarin shiga kicin don ganin kwandunan kayan miyan da Abba ya ce an kawo na girki ta tsaya cak hankalinta ya yi kan Ummita wacce ke tafiya kamar wani abu ya faru. Da sauri ta bi bayanta.

Ita kuwa Ummita, tun cikin babbar sallah da ta je Bichi ta karSowa Humaira haya?i a wurin Wan uwan mahaifiyarta hakan yasa Humaira na fara kuka ta yi niyyar turara mata. Abin mamaki har ta isa yanayin kukan Humairar bai sauya ba. Ta ciro maganin ta barbaWa cikin kaskon ta ajiyeshi kusa da Humaira. Nan da nan kanta ya soma juyawa. Daidai lokacin Mami ta faWo Wakin. Abin da ta gani ne ya sanya ta kallon Ummita,

"Lafiya? Meke faruwa da Humairar? Wannan wane irin hayaki ne kuma?"

Ummita ta sha jinin jikinta don gaba daya ba ta sanar da Mami ta karSowa Humaira haya?i ba.

"Ba komai Mami, kukan nan ta soma wanda take yi idan aljanunta suka tashi shi ne.."

Mami ta daka mata tsawa.

"Shi ne me?! Shi ne kike yi mata haya?i ba tare da kin sanar da ni ba? Haba Ummita, yanzu idan Abbanta ya ji wa zai yiwa faWa? Maza Wauke haya?in nan."

Ummita ta dauka ta fitar zuwa bandaki ta kashe, ta sani ta yi kuskure amma kuma cikin ikon Allah Humaira ta yi shiru sai gumi take haWawa da alama kuma bacci ya Wauketa.

Ummita ta kai duba ga Mami, zuwa lokacin tana zaune gefen gado.

"Ki yi hakuri Mami."

Girgiza kai Mami ta yi.

"Ba laifi kika aikata ba Ummita, na sani kulawa ce da yar uwarki, amma ko mene ne ya dace na sani saboda nima ina nawa kokarin a kanta don har na yiwa Abbanku maganar wani mai bada magani zan kai ta wurinsa bayan biki ya ga mece ce matsalarta."

GyaWa kai Ummita ta yi tana murmushin farin ciki. Ba ta da fatan da ya wuce ta ga Humaira ta samu lafiya ta amince da auren mai kaunarta irin Fadeel.

"Toh Mami. Allah ya sa a dace."

Mamin da murmushi ta amsa da amin. Har ta mike ta kai ?ofa ta juyo.

"?aukomin maganin da kike turara mata, idan ya so sai na yi mishi bayani."

Ba musu Ummita ta Wauko ta ba ta, murmushi ta yi ta juya ta fita a dakin.
***
BIKI BUDURI.
Yau ranar ta kama ranar Kamun ?anmatan Mami, Futuha da Tasleem. Tun safe Humaira? ba ta zauna ba, tana tsaye akan aikin suyar snacks da aka haWa tun ana saura kwanaki biyu aka sanya a firij, sai da aka ci rabin aikin kafin ta bar wurin bisa umarnin Mami acewarta yanda ta kwashi gajiyarnan gwara ta je ta huta kafin lokacin da za a tafi event center da aka tanada don Kamun. Haka ta karasa Wakinnasu a mugun gajiye tana jan ?afafunta da suka yi tsami. Hayaniyar ?anmatan? dake Wakin ko kaWan bai mata ba, ji ta yi da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ace tana da hali da kaf sai ta sa an fice an bar ta ta huta. Hakanan dai ta karasa tana amsa sannun da wasu ciki ke mata tana murmushin ya?e. Ummita tun safe ta raka Anti Jannat ?unshi har lokacin ba su dawo ba. Ita dai daga wannan kwanciyar tana jira ta a fito daga bandaki ta shiga wanka, ba ta san ya aka yi bacci ya yi awon gaba da ita ba.
? Ba ita ta farka ba sai da aka kira sallar la'asar, nan Win ma Raihana ce ta tashe ta.

"Kai, har kin ban tsoro. Kin fa jima kina baccin nan tun Wazu nake safa da marwa ba ki tashi ba."

Humaira dake dubanta da manyan idanunta da suka kaWa suka yi ja ta ce.

"Har an tafi ne?"

Harararta ta yi.

"Jimin ke Winnan, an tafi ne za ki gan ni anan? An dai soma kwalliya da shirin tafiya. Ki tashi kiyi sallah ki wanka mu tafi lar mu makara."

"Ina kuma za mu je?" Humaira ta tambaya da mamaki. Sai kuma don kanta daga yanayin kallon da Raihanar ta jefamata ta tuna.

Ta gyaWa kai tana hamma da mi?a lokaci guda.

"Oh na tuna, kin ce wajen kwalliya za mu je ashe. Toh ita Ummitar ta dawo?"

Raihana da tuni ta mi?e ta hau fiddo karamin akwati da zummar daukar sar?a ta amsa da eh. Ji tayi kamar ta rufe Humairar da duka, dama dakyar ta amince za ta yi kwalliyar.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login