Showing 3001 words to 6000 words out of 189325 words

Chapter 2 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

192

a wajenta ba. Koda dai, ba ma ita kaWai ba, ta lura da irin kallon da Mami ta watsamata. Ko ya zamantakewarta a wannan sabuwar duniyar za ya kasance?

"Hey, tunanin me kike? Amm..nidai bari kawai na kiraki da Humaira, kinga babu damar ce maki Aisha kai tsaye saboda sunan Umman Abbanmu kika ci ko? Hakan ya yi?"

Humaira ta gyaWa kai karo na biyu tana mai sakin fuska, ta lura Ummita akwai kirki.? Bandaki ta nuna mata, ita kuwa ta yi? godiya, har za ta shige ta dakatar da ita.

"Yauwa Humaira ga wannan zanin ki yi amfani da shi ki goge jiki."

Ta sa hannu ta karSa, zani ne a wanke a goge. Ummita har ta kama hanyar fita sai kuma ta dawo ta shiga bandakin gami da ba ta umarnin ta bi bayanta. Su na shiga ta kunna mata famfo gami da faWin amfanin kowannensu. Ta fiddo mata sabon sabulun wanka daga cikin wata ?ar kwaba dake a gefe jikin bangon, sai kuma ta tambayeta ko ta taho da soso, Humaira ta amsa da eh. Hatta da ?ofar banWakin sai da Ummita ta nuna mata yadda za ta ?ulle kuma ta buWe, daga haka suka fito, nan ma sai da ta ajiye mata dardumar sallah saitin gabas sannan ta fice ita kuma ta ciro? sosonta a akwti ta koma banWakin ta rufe.

Wanka ta yi gaba Waya ta Wauro alwalar Magriba, koda ta fito wannan budurwar ta Wazu tana zaune gefen gadonta tana waya, suna haWa ido ta bita da harara ba shiri Humaira ta kauda kai. Idanunta ya kai ga akwatin kayanta, ?arasawa ta yi ta buWe sai dai gaba Waya ba'a nutse take ba sakamakon idanun wannan budurwar a kanta suke duk kuwa da wayar da take amsawa. Turanci zallah take zubawa har wani shagwaSa take yi tana dukan gadon, kalmar I Lobiyun da ta ce yasa Humaira ta fahimci koma dai wane ne toh masoyinta ne. Ba ta ko ?ara kallonta ba gudun ganin abin da zai sosa zuciya, ta fiddo doguwar rigarta ta yadi ta warware ta zura. A gurguje ta ciro hijabinta, ta linke kayan da na cire na ajiye daga saman akwatin. Ba ta jima da tada salla ba sauran ?anmatan nan biyu suka shigo suka cika Wakin da hayaniya, rabin hirar tasu da harshen turanci suke yi. Koda ta idar ba ta iya nutsuwar jan addu'a mai tsawo ba, ta yi istigfari da hailala da salati ta shafa. Zama ta cigaba da yi anan ba tare da ta mi?e ba gudun ma kar ta yi wani abin ya jazamata ba?ar magana. Hankalinta yana ga Abbanta wanda take da tambayoyi birjik da za ta yi mishi a kwakwalwarta. Eh yana sonta yana ?aunarta, amma meyasa bai ?ara waiwayarta ba, meyasa ba ta taSa ganinsa ba? Meyasa kuma koda a waya bai kira domin su gaisa ba? Dukkan wannan rashin kulawar nasa da ba ta samu ba, ace yana kaunarta ya kuma damu da itq? Ita kam tana son sanin amsar da zai fito daga bakinsa.

"Ke Indo."

Ta Waga kai ta dube su kawa, suka kwashe da dariya.

"Kai Raihana ba ki da kirki wallahi, au ba ma za ki kirata Humairar ba sai Indo ko?"

Wacce aka kira da Raihana ta yamutse fuska.

"Aa, ina ce sunan Umma gareta, tunda kaka ce ai ko Indon ma da na ce ta gode min. Ku ni ba wannan ba, wallahi mu tashi mu yi magana fa tun kan a ?a?aba mana ita a Wakinnan. Ni wallahi? tsoro ma take ban. Mu faWawa Granny ta yiwa Abba magana don Mami ba za ta goyi bayanmu ba."

Humaira ta kalle ta dakyau, doguwa ce kamar dai Abba, don ta fi Maminsu tsawo, Mamin ba ta da tsawo sai jiki kuma? gajeriya ce. Fara ce tas itama kalar buzayen, gashinta da ya sha kalba ya sauka har gadon bayanta, riga doguwa ce ?ar kanti ta sa mai kama jiki.

"Kallon me kike yimin kamar wata mayya? Kar ki ji ance wai wani ke ?ar Abbanmu ce ki yi ?o?arin haWa kanmu da ke, wallahi kar ki kuskura don bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne, atoh. Gwara ma Abban ya zo a yi meeting Win a bambance tsakanin aya da tsakuwa."

Duka wannan bayanin daga bakin Raihana su ke fitowa, Humaira ta sauke idanunta a hankali zuciyarta na zafi, dagasken dai ba ta samu karSuwar kenan ba, zuciyarta na da ?arfin jure abu idan har wanda ya fi ta a shekaru ne ya aikata gareta, amma ba ta jin za ta iya Waukar wannan rainin wayon.

"Futuha mene ne haka wai? Meyasa kullum burinku ku tozarta mutum?"

Maganar Ummita ya sanya Humaira Wago kai, ashe wai akwatinta wacce aka kira Futuha ta nufa ta buWe. Ita dai wacce ke faman? waya tun Wazun.

Ai kuwa kamar an mintsile ta haka ta mi?e tsaye a zafafe, ta ?arasa daidai sadda Futuha ta Waga akwatin da niyyar doka shi da ?as, da wani irin zafin nama ta ture ta, daga ita har akwatin suka faWi, akwatin ya faWa saman? gado, ita kuwa ta yi rashe-rashe a ?asan gadon bayan ?ugunta ya bugi katakon. Ai kuwa? ta kurma ihu, Raihana da Waya budurwar da? Ummita ta ambata da Tasleem suka yo kai Humaira gadan-gadan, Ummita ta tare su. Ita kuwa Humaira? ko a jikinta ta nufi akwatin ta shiga harhaWa kayan da suka zube tana maidawa lokaci Waya hawayen da ta fi zaton na Sacin rai ne, su na kwaranya. Ya yi daidai da faWowar Maminsu Wakin wanda hakan? bai wuce sanadiyyar ihun Futuha da ya mamaye ilahirin Wakin ba. Jin muryarta da ta yi sai da gabanta ya faWi, ta rasa dalilin da yasa take jin haka a kanta. Ta shiga ambaton sunan Allah a ?asan ranta.

? "Lafiya? Me nake gani haka kamar waWanda aka ?wato daga bakin kura? Ke Ummita sake ta, kyale su na ga gudun ruwansu. Au, don ku nuna mata rashin tarbiyyarku ba komai ba ne ba ko? Har kun soma yada halin?"

Tana maganar ne fuskarta a murtuke tana bin su da kallo Waya bayan Waya, ita dai Humaira sam ba ta tofa ba sai ci gaba da tsince kayanta da tayi tana harhaWawa tana mayarwa ciki. Ba ta san ma'anar juya harshe zuwa wani can daban da ba ta sani ba, ta dai ji Mamin a cikin yare ta yi musu magana wanda ba ta fahimci koda harafi guda a ciki ba, sai gani kawai ta yi duka sun fice daga Wakin idan ka cire Ummita da ta durkusa tana taya ta haWi da ?ara ba ta ha?uri. Tana niyyar amsawa Ummita ta ji? an shafa kanta, ta runtse idanu ba tare da ta? Wago kai ba don tasan Mami ce.

"Ki yi hakuri kin ji Humaira, su Tasleem su na da irin wannan halayyar na son yiwa ba?o sha?iyanci. Kinga yau ki ka zo kuma kafin su karSe ki za'a Wan kwana biyu, a hankali idan sun gane ke Win Waya ce a cikinsu komai zai wuce kin ji ko? Ki Wauke ni madadin Uwa, don mahaifiyarki mun yi zaman mutunci da nutunta juna da ita. Kema kuma nasan muddin dai kyawawan Wabi'unta kika kwaso, ba za mu samu kowace iriyar matsala ba. Ina fatan haka?"

Jin bayanan Mamin sai ta tsinci zuciyarta da yin sanyi, ta ji lokaci guda kaso saba'in na fargabarta akan Mami ya ragu, wannan furuci nata na madadin Uwa, ba ta jin za ta iya kwatanta daWin da ya sanya ta. Kai ta gyaWa alamar toh,? Mamin ta maida dubanta ga Ummita.

"Sai ku hanzarta ku fito ta ci abinci daga nan zuwa bayan sallar isha'i, Abbanku na neman mu duka."

"Toh Mami." FaWin Ummita cike da girmamawa. Daga haka ta fice ta bar mu. Ummita ta kalli Humaira da murmushi saman fuskarta.

"Sai fa kin yi hakuri sosai Humaira, da gaskiyar Mami, dama ya lafiyar giwa balle an jefe ta da kashi. Su Tasleem ba su da kirki, har gwara su Yassar a kansu, don su ba su kunyar ido, za su yi maka abin da suka so. Ki yi hakuri don Allah. Nima haka nake fama da su, don ma dai babu yadda suka iya da ni ne, Mamin na taka musu burki sosai a kaina."

Jin haka ta ji ta sosamata inda yake mata ?ai?aiyi. Aikuwa ta kasa shiru sai da ta furzar.

"Yauwa nikam Ummita, amma ba Mami ce ta haifeki ba ko?"

Ummita ta yi dariya.

"Kin gan ni ?ar ba?a ko?"

Sai kuma ta gyaWa kai ta Wan sauya fuska alamar damuwa.

"Ba Mami ce ta haife ni ba kuma ba Abba ne mahaifina ba. Mahaifina ?anin Abba ne, mahaifiyata kuwa ?ar asalin garin Bichi ce, gaba Waya sun rasu ne a sanadiyyar gobara. Ni kaWai ce rai da aka fitar a gidanmu ko kwarzane tun ina da shekaru biyar a duniya, amma daga su har ?annena jarirai ?an biyu duka sun rasu. Tun daga wannan lokacin ne, na soma rayuwa a hannun Kakarmu sai daga baya ne Abba ya maido ni gidansa ya dam?a amanata ga Mami. Matar da ta ri?e ni har zuwa yau ba tare da ta nuna bambanci tsakanina da nata yaran ba, kusan ince a zamanin dai samun irin Mami abu ne mai wahala. Ga kirki da son mutane, ke ba don dai kar nayi hauka ba zan iya ce maki Mami ta fi nunamin ?auna da so fiye da nata yaran domin hatta da ragamar kula da Wakinta da na Anna ni ta dam?awa. Ke daidai da shawara wani lokacin da ni take yi. Sai ta ture shawarar nata yaran ta Wauki nawa."

Jinjina kai Humaira ta yi, eh lallai kam Mami ta yi abin a yaba mata, a zamanin nan kafin a samu mai fifita Wan wani akan nashi abu ne mai matu?ar wahala.

"Wace ce Anna?"

Humaira ta watsa mata tambayar.? Ta mi?e ta shiga rufe akwatin a lokaci guda tana ba ta amsa.
??
? "Anna kakar su Tasleem, wacce ta haifi Mami. Ai anan gidan take rayuwa, a baya ma har da ?anwar Mami da ba ta yi aure ba muka zauna. Amma yanzu Allah ya taimaka tayi aure tana zaune a can Misra da mijinta, ke kam ai Allah ya taimake ki ba za ki rayu inuwa Waya da ita ba. Don ta fi su Tasleem zafi da tsangwama, ke ta dai tsani duk wanda ba jininsu ba. Hatta da dangin Abba ba ta kaunar gani a gidannan, sai kuma Allah ya sa su Win ma ba su fiye zuwa ba."

Humaira ta buWe baki za ta yi magana kenan sai ga wani ?aramin yaro cikin yara ?ananu uku da ta gani Wazun ya shigo a guje. Masha Allah yaron kyakkyawa duk kuwa da cewar bai Wau hasken Mamin sosai ba, ya fi yin kalar Abba, amma kuma hakan ma sai ya ?ara mishi wani kyan na daban.

"Adda Ummi ku zo inji Mami."
Ya kai ?arshe yana nuna su duka biyum da yatsa, alamun dai mu biyun ake nema. Sai ma ya ba Humaira dariya. Suka mi?e a tare zuwa falon. Ko Waya ba abokan faWan nata a ciki, bada Wayansu ba sa nan sai Mami da yaran, sai kuwa Waya a cikin matasan nan na Wazu kwance saman doguwar kujera ya toshe kunnuwa da earpiece.

Suka ?arasa ga Mamin, ta zauna a gefe a ?asa. Duk yadda Mamin ta so ta hau kujerar ta ?i, haka dole ta rabu da ita. Ummita ta kawomata abincin amma gaba Waya ta kasa sakewa balle ta ci, ?arshe dole dai Wakin suka yi da abincin bisa umarnin Mami. Nan din ma dai kaWan ta ci ta ce ta ?oshi. Hankalinta kuma ya koma ga Kawu da Abba, ba ta gaji da ganin Abba ba, ba ta kuma gaji da jin muryarsa ba. So take ta samu damar da za su yi doguwar hira da shi, tasan dai ba yau ba domin dare ya yi.

Suna nan da Ummita tana ?ara ba ta labari akan zuri'arsu har lokacin sallar isha'i ya yi, koda suka idar kai tsaye falon Abba suka nufa sakamakon kiran da ya yi musu. Nan suka tarar shima Kawu har ya ci abinci ya yi wanka, hirarsu kawai suke yi da Abba wanda shima ya sha doguwar jallabiya ruwan madara. Har Humaira ta zauna kallonta yake da murmushi saman fuskarsa kafin ya maida duba ga Kawu ya girgiza kai.

"Allahu Mai Halitta." Kawun shima murmusawar ya yi, ita kam sai ta yi kasa da kai. Zamansu ba jimawa sai ga Mami ta shigo ta lulluSe jikinta da ?aton mayafi. Sai da ta zauna ne ta dubi Kawu.

"Umar, kwana da? yawa. Idan babu Fatima? a gidan shikenan kuma sai zumunci ya yanke? Dama kun raba ni da Wiyata, toh dama ?arshen alewa ?asa, ka ga yau dai ungulu ta komo gidanta na tsamiya."

Kawu ya yi ?ar dariya.

"Hajiya Maryam kenan, idan dai kin yarda kin amince da komai lokaci ne, ba za ki ga laifinmu ba. Sai dai kamar yadda kika ce, na yi kuskure kuma na ji kunya da ban tashi zuwa ba sai bayan babu Adda Fatima, Allah ya gafartamusu. Ina kuma neman afuwa."

Gaba daya suka amsa da amin.? Abba ya yi gyaran murya ya dubi Mami.

"Ina yaran nan suka shiga ne wai?"

"Su na can wurin Anna, na rasa me suke yi alhalin na sanar da su. Bar..."

Ba ta ?arasa ba sai ga su sun faWo Wakin kamar daga sama, babu Waya cikinsu da ya yi tunanin yin sallama. Yaron Wazu ne da ya je kiranmu ya shigo a guje ya rungume kafaWun Abba, wani da ya fi shi tasawa yana biye da shi a gujen. Sai kuwa su Tasleem da samarin nan uku.

"Kai Muhsin, me ya yi maka ne?"

Wanda aka kira Muhsin ya turo baki ya nunawa Abba bindigar ruwa da aka raba gida biyu.

"Ba shi ne ya karyamin bindiga ba. Allah kuwa sai ya biya ni."

Abba ya ja hannun karamin mai suna Waleed ya maido shi gabansa.

"Haba Autan Mami, ya haka? Ba shi hakuri toh."

Da dariya irin na yarinta ya furta kalmar sorry. Abba ya maida idanunsa ga su Tasleem waWanda suka yi Ware-Ware saman kujera ba su ko gaisar da Kawu ba. Fuska ya Wan Waure.

"Ba ku iya gaisuwa ba ne?"

Jin furucin Abban ya sa suja gaida Kawu ciki-ciki, ba tare da jin komai ba? ya amsa har da nema musu albarkar Allah. Babu wanda ya amsa da amin a cikinsu. Mami ta kalle su ta yi musu alamar su sauko ?asa su zauna, ba a son ransu ba dole suka zaune a ?asan kafet kamar dai yadda Humaira da Ummita suka yi. Sai dai Abba ya buWe taron nasu da addu'a sannan ya gabatar da Humaira a wajensa. Ya kuma gargaWe su da kar su kuskura ya ji wani zance na daban koda nuna bambanci ne. A karshe ya sa kowannensu ya gabatarwa da Humaira sunansa. Su tara ne cif, Mubarak ne babban Wan Abban, shi kuwa yana ?asar Ghana yana karatu, sai Dawud, Yassar, ?asim, Futuha, Tasleem, Raihana, Muhsin da autansu Usman da ya ci sunan baban Mami suke kiransa Waleed.

"Humaira toh, yanzu dai ba wanda ba ki sani a ?an uwanki ba ko? Sai babban yayanku shi kam sai ranar da ya samu hutu idan ya dawo sai ku gaisa. Ko kuma ma ina iya haWa ku a waya wataran."

Jin abinda ya fadi ya sa ta murmushi, ta gyaWa kai tare da furta toh. Daga haka Abba ya sallame su baki Waya suka tashi.

A wannan daren dai ba ta samu damar hira da Abbanta ba, ta koma Wakin da ba ta kauna dalilin yadda suka kaya da masu Wakin. Mami ta sa aka yi mata shimfiWar katifa a ?asa kafin nata gadon da sif ya iso, acewarta. Hakanan ta kwanta, mutanen ba su ?ara tanka mata ba musamman ma Futuha da ta sha ?asa har lokacin ?ugunta na ciwo. Sun dai sha jinin jikinsu, sun kuma fahimci Humairar ba kanwar lasa ce ba itama.

***
Washegari tun da asuba ta ga ?anmatan ba su koma bacci ba, ita daman baccin safe ba ya daga cikin Wabi'unta, a can ?auyensu daga sun tashi to sannan za'a hau Wora ruwan wanka da kuma abin kari, wannan dalilin yasa ta kwanta kawai tana kalle-kalle da sa?e-sa?en zuci. Tana kallo suka yi wanka har Ummita, kowannensu ya hau shiri. Ummita da Raihana cikin shigar uniform na makaranta, ita kuwa Tasleem shigar fararen kaya ta yi na ma'aikatan asibiti riga da wando da Wan ?aramin hijab. Sun mata kyau kwarai, gogar kuwa, wato Futuha, kayan gida ne jikinta, riga doguwa ta atamfa da ya Wame ta Wam ya fiddo da surarta.

"Wai ke Futuha ni ban gane ba, ina mamakin yadda kike rawar ?afa da jiki duk sadda aka ce kuna da English, ko uban me yasa oho." FaWin Tasleem kenan sa'ilin da take Wora agogo a tsintsiyar hannunta. Kafin Futuha ta yi magana, Raihana dake fesa turare a jikin uniform dinta wanda iri Waya ne da na Ummita, kalar fari da ruwan makuna dinkin riga da wando sai Wan hijab da ya rufe kirji kaWan, dariya ta yi ta amsa wa Tasleem.

"Wai ke ba ki da labarin IBB Gusau? Tab, ai kusan kaf matan department dinsu sonsa suke ban ciremaki matan aure ba, toh itama har da ita a ciki, ba ki ganin kwalliyar ta daban ce."

Futuha ta jefowa Raihana murfin man shafawa, Raihana ta kauce tana dariya.

"Af, akwai ?arya cikin maganata ne? Ke fa naji kuna hirar da wannan ?awartaki me wuya kamar mari?in lema, ni me ma sunanta? Yauwa Khalisat, kina wani koWa shi kina cewa nan duniya shi kike so."

A fusace Futuha ta nufo ta, Raihana ta sunkuci jakar makarantarta da waya a gefen gado ta fice daga dakin da sauri tana dariya. Itama Tasleem dariyar ta yi.

Ummita kam dama ta fice daga dakin tun da ta zura uniform, dakin su Muhsin ta wuce don yi musu shirin makaranta.

Humaira lumshe idanunta ta yi tana ji suna faman hira tsakanin Tasleem da Futuha inda Futuha ke kara jaddada dagasken

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login