Showing 168001 words to 171000 words out of 189325 words

Chapter 57 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

241

ai DUKAN RUWA ba zai hana gwarje amo ba, kin so ganin rayuwata ta lalace, kin so ki gan ni a lalace sai dai kuma ba alfahari ba, Alhamdulillah Wiyar Fatima ta samu abin da ba ki taSa zato ba. Rayuwarta ta inganta, ta kuma samu miji Waya tamkar da dubu. Bana alfaharin kasancewar na samu abinda wasu ba su samu ba, amma ina alfahari da mijin da Allah ya mallaka min. Da ke da babu a rayuwata ba zai amfane ni da komai ba, a baya ina maki kallon uwa kuma mai sharen hawaye a yanzu kuwa ina maki kallon MATAR UBA marar kirki mai son zuciyarta, ki sa a ranki in sha Allahu yanzu ki ka soma ganin cigabana a rayuwa ba dai ci baya ba. Na bar ki lafiya."

Tana kai wa nan ta juya ta fice jikinta har rawa yake yi saboda tsabar Sacin rai da tsananin fushi, idanunta sun kaWa jazur amma hawayen ya ?i zuwa sai sauke numfashi take yi akai-akai, gaba daya ta mance ma da wani batu na Ladidi da ruwan da za ta kai, sai kawai ta koma falon Abban cikin wannan yanayi.

Mami kuwa baki sake take kallon hanyar da Humaira ta bi, wani irin shock ne ya shige ta ba kaWan ba, Humaira dai yarinyar da ta ke rainawa ita ce ta budi baki ta yi mata Wiban albarka da maganganu masu zafi da soya zuciya? Ita fa Humaira da a baya ta ke mata biyayya tamkar ta kwanta ta taka gadon bayanta ta wuce?

Sai ta dube dirshan tana auna maganganun da ta yarfa mata, wani irin ashariya ta ?udunduma ta watsar a iska don babu kowa a Wakin. Mi?ewa ta yi a karshe ta yafici gyalenta da kudin da za ta shiga abin hawa. An kai gaSar da za ta kai kanta gaban Babandi, ta ji ta yarda za ta haWa shi da dukkan abin da ya cancanta ta ro?e shi akan ya yafemata ya fice a rayuwar Tasleem Wiyarta sannan ya nema mata mafita akan wannan masifar da ke damunta. Daga wannan sai wannan?

***
Humaira ko su Abba da Fadeel na cigaba da taSa hirarsu, kawai sai ganinta suka yi. Fadeel da ke kallon ?ofa shi ne ya soma ganinta, daga yanayinta ya san babu lafiya, tsaye ya mi?e har ya mance da Abba cikin sauri ya nufi matarsa. Abba ma tuni ya mi?e ganin halin da Humairar ke ciki.

"Boddo, lafiya?" Ya tambaya a rude yana ri?o kafaWunta.

Babu baki sai kawai ta shiga girgiza kai, sai a sannan hawayen suka zubo amma fa ba ta ce komai ba. Abba ma ya ?araso.

"Mamana ya aka yi na ganki haka? Meyafaru?"

Kalmar mamana da Abban ya furta ya sanya ta jin wani sabon rauni ya taho mata, gaba daya gaSoSin jikinta suka mutu tuna cin mutuncin da Mami ta yiwa Mahaifiyarta a yanzu. Sai kawai ta shiga kuka sosai har kafaWunta na girgiza.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Na tabbata aikin Maryam ne, ina zuwa." Daga haka Abba ya yi gaba, da wani irin zafin nama Fadeel ya haWa ta da jikinta ya rungume tsam, nan da nan nashi idanun suka kaWa, a duniya ya tsani abin da zai taSa Humaira tun a baya ballantana yanzun da ya ?ara sanin wace ce ita.

"Please ya isa, ya isa kiyi hakuri Boddo, so kike ki kashe ni? ?irjina zafi yake yi idan kina kuka."

Jin haka sai ta Wan soma rage ?arfin kukan, ya Wago ta ya shiga share mata fuskar yana lallaSa ta, ya sumbaci saman leSbanta, ya koma ga dukkan kuncinta biyu da saman idanu zuwa goshi. Gaba daya ya rikice neman abin da zai haifar mata da nutsuwa kawai yake, don haka sai ya ?ara sanya ta a jikinsa yana Wan shafa gadon bayanta. A hankali ta zame jikinta tana ?ara goge hawayen da suka zubomata gami da bin shi da murmushin ya?e don ta kwantar masa da hankali.

"Habeebee a falon Abba muke fa."

Ya Wan lumshe idanu ya buWe, har lokacin bai ga abin da zai sakar masa da zuciya ya yi murmushi ba, sosai Sacin ran Humaira ke sauya mishi yanayinsa, kusan zai iya cewa yana fin ta jin zafin duk wani abu da zai rusa farin cikinta.

"Gida zamu tafi, shiga ki yiwa Abba sallama."

Ta Wan yi narai-narai da fuska, abin mamaki, abin da bai taSa faruwa ba ta gani haWe rai sosai ya yi tamkar ba Fadeel ba.

"Kar ki yimin magiya Boddo, na riga na faWa, gida zamu tafi. Ki shiga ki bi umarnina kawai."

***
Shi kuwa Abba yana isa falon da shirin shiga wajen Mami sai ga ta nan buguzum-buguzum ta fito rike mayafi da ta kasa yafawa, ya yi daidai da fitowar Tasleem don ta je wurin Mamin. Ganin Abba da Mamin sun tsaya kallon-kallo sai ta yi turus. Abba ya dan dubi su Waleed gami da ba su umarnin su je wasansu, bayan sun fice ya maida duba ga Mamin.

"Maryam me kika yiwa Humaira?"

Ya fadi hakan saboda wasu lokutan yakan kira sunan Humairar musamman a irin lamari haka mai muhimmanci. Ta bishi da kallon tara saura domin a yanda zuciyarta ke tafarfasa ba shi ba, ko ma waye ya nemi faWa mata ba?a akan wata Humaira toh ba za ta bar shi ba.

"Ita Win banza! Kai yanzu Isuhu saboda ka kasance butulu har za ka iya duban fuskata ka ce wai me na yiwa Humaira! Toh uwarta Fatima na zaga ko za ka rama mata?!"

Ta na maganar kai ka ce duka za ta hau Abban da shi. Ya Wan runtse idanu sannan ya buWe.

"Kin zagi uwarta ba zan rama mata ba, amma zan dauki mataki a kanki. Nan dai gidana.."

"Kora ta za ka yi? Nace kora ta za ka yi butulu?!"

Ta tari numfashinsa tana hayagaga har da turo kirji da Wan ?ara tsawo don Abba ya fi ta tsawo sai ta Waga kai ta ke iya kallonsa.

"Ba zan kore ki ba, idan ma korar ce akwai lokacinsa. Sai dai ki sani ba zan lamunci ki dinga zagin Wiyata ba. Ki kiyayi harshenki a kanta Maryam don ba za ta ?are maki ta daWi ba. Zan iya ture wancan maganar da na faWamaki na aiwatar da abin da ba za ki taSa zato ba."

Mami ta daka wani tsalle ta yi wurgi da mayafi da dankwalinta ga wayarta na faWuwa ta buga tafi kamar wacce matsalar kwakwalwa ya sama.

"Ka sakenin mana Isuhu sai me? Nace ka sakenin! Butulu kawai wanda ke mance halacci! Ba don ni Maryam ba kana tunanin za ka samu wannan ni'imar da ka samu? Wallahi ba don ni ba da yanzu kana yawo da tsumma! Amma saboda kai ba ka san halacci ba har yau ni Maryam kake batun sakina akan wata shashashar banza ragowar maza Hu..."

Wani wawan mari ya sauke a saman ?ucninta, da wani irin gudu Tasleem ta taho ta ri?e kafar Abba tana kuka.

"Abba don girman Allah ka rufamana asiri, ba don halin Mami ba ka yi hakuri ka yafemata."

Mami kuwa tun daga marin ta yi Wif saboda b?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
a ta yi zatonsa ba, ita kokari ma take yi jinta da ya Wauke na wucin gadi ya dawo ga wani hazo-hazo da take gani. Abba ko maganar da ya yi niyyar yi har yana Waga yatsa, ya fasa sakamakon ri?o da magiyar da Tasleem ke ta yi babu ?a??autawa, sai kawai ya dan bugi Tasleem da ?afa don ta sake shi aikuwa da sauri ta saki ?afar saboda cikinta da ya Wan taSa ta kuma ji zafi, ta yi baya da sauri ta a rike cikin. Ya juya ya fice zuwa dakinsa. Mami kuwa sai ta hau bugun Tasleem.

"Don ubanki wa yace ki rike shi?! Yar iska kawai! Ki bar shi ya sake ni."

Tasleem na kuka kira take yi

"Mami cikina fa." Ladidi ce dake daga kicin tun dazu tana jin abin da ke faruwa ta shigo da sauri ta hau ro?on Mamin. Ta dai ji Mamin na batun wai Tasleem ba za ta haife mata Wan boka ba dole a san yanda za'a yi ta koma wa Hamza, sam idanunta ma ya rufe ba ta san me take firzarwa ba. Mamak da tsananin tsoro ya cika zuciyar Ladidi, wai kuwa Mami ?alau take? Tabbas a lura da ciki a jikin Tasleem amma maganar da Mamin ta yi wai ciki na Boka ne ya fi komai girgiza ta. Tsabar kaduwa sai ta tsaya cak rike da hannu a haSa tana kallonsu yayinda Mami ta kwashi tarkacenta ta fice sai dai wannan karon gidan Hajiya Lubna ta nufa. Tasleem ko Waki ta shige dakyar tana jan ?afar borin kunya don ta sani Mami ta gama kwaye mata zani a kasuwa, Ladidi ta san komai yanzu.

"Jar uban can!" Abin da Ladidi ta ce kenan kawai ta juya gwuiwa a sake don kwaso kulolin girkin da ta yi zuwa falo.

***
Daidai lokacin da Humaira ta juya da zummar zuwa kiran Abba don ta ce masa zasu tafi, sai ga Abban ya shigo. Ganin yanayinsa ta sani yana cikin damuwa. Shima bai ko zauna ba ya dubi Fadeel.

"?auki matarka ku tafi Fadeel."

Ya fahimci yanayin Abban kwarai, ya amsa da toh ya fice rike da jakar Humaira itama ta durkusa ta yiwa Abban sallama tana hawayen wannan kwantaccen damuwar da ta gani tattare da Abban. Mami ta zame musu bala'i.

"Abba ka yi hakuri."

Ya dan yi murmushin ya?e.

"Bakomai Mamana, jeki, Allah ya yi maku albarka."

Ta amsa da amin ta fice, wannan zuwa dai bai musu dadi ba sam.
Suna tafe tana satar kallonsa, hannunsa sar?e a nata amma ba ya ko kallon inda take sai ma fuskarsa da har lokacin babu Wigon walwala. Har suka je gida bai fasa yanda yake mata ba, ya fita a mota tana kallo ya zagaya ya buWe mata murfin ta fito sannan ya maida ya rufe motar.

?akinsa ya wuce kai tsaye tana kallonsa, tana kuma lura da shi. Sai ta kasa jure wannan fushin da ya shiga sanadin kukanta da Sacin ranta, ta ji kamar an ?ara ninka mata kaunar Fadeel, ita fa a yanzun ma gani take yi son da ya ke mata wasa ne, shafar mai ne akan wanda take masa. Ta kasa wucewa Wakinta kamar yanda ta yi niyya kawai sai ta bi bayanshi. Ta iske shi ya fidda riga daga shi sai farar singiletinsa, suffar kyakkyawar halittarsa ta fito ?al, wanda bayan ita ba ta fatan a samu wata da idanunta za su dinga tozali da shi. Ya ji shigowarta, ya daure iya daurewa bai Wago ya kalle ta ba amma fa kokawa yake yi da zuciyarsa, ta karaso ganin kansa a ?asa sai kokari cire agogo yake, ta sa hannu a saman haSanta ta Wago kansa idanunsu ya sar?e a na juna. Hawaye take fitarwa sosai tsabar ganin kamar a yau ta rushe dukkanin wasu al?awarurruka da ta Waukarwa kanta na ba za ta Sata ran mijinta abin kauna da sonta ba har abada, amma tun ma ba su je ko'ina ba ta hassasa mishi bacin rai.

"Habeebee ka yafemin don Allah." Shi kuwa ba ta san cewa kukan ne ba ya so ba. Ya yi saurin goge mata su zuciyarsa na Wan sassauta Sacin ran.

"No Boddo, please ya isa kar ki yimin illah, ni damuwarki ce na tsana, bana son abin da zai ?ara sanyamin ke kuka. Ba za ki gane zafin da zuciyata ke yi idan kin shiga damuwa ba. Wallahi nakan daina ganin girma da mutunci wanda ya haddasa damuwar dole gareki. Ke ce bana son na ga kin shiga damuwa, duba ki gani, mun fita da farin ciki mun dawo da abin Sacin rai. Wannan Mamin taki ni..."

Sai kuma ya haWiye abin da ya yi niyyar faWi, kawai sai ji ya yi ta kai bakinta saman nasa, nan da nan ya ji ya dauke wuta, ta sa hannuwa tana shafar wuyansa. Bai san lokacin da ya ri?o ta gaba Waya ba jikinsa har wani rawa yake. Yau dai Boddo da kanta ke sarrafa shi, wannan al'amari ne da ya jima yana son ganin ranar zuwansa. Ita da sau da yawa ke kasa yi mishi sumba sai ya yi kamar zai yi me don ro?o. Nan ma ana yi ake saurin juya baya a rufe idanu.

Abin da ya biyo kuwa ba zai rubutu ba, shikenan suka mance da dukkan wani Sacin rai da damuwa sai wacce ta zama dole.

***
A can Bichi kuwa Anti Maijidda ce ta yi shiru kawai ta zuba wa Baba Amina ido wacce tun safe ta yo sammako ta zo garin ita da Raihana da tuni ta kammala jarrabawa.

"Hakan mai yiwuwa ne kuwa Amina? Ke fa kin san komai tsakanina da Maryam. Kina ganin yaranta za su karSe ni?"

Baba Amina ta yi murmushi.

"Wannan fa duka mai sauki ne Maijidda, ai shi aure nufin Allah ne. A baya daga ni har shi Yayan ba mu taSa kawowa akwai ranar da zance makamancin haka zai gifta tsakaninku ba. Kar ki ga na riga shi zuwa ki zaci wani abu, kawai dai ya wakilta ni ne saboda ba ya son ya fara zuwa da kansa a samu rashin goyon baya. Nidai ki cire tunanin wata Maryam da yaranta a zuciyarki, Raihana ma ai Wiyarta ce amma ba ki ga yanda take murna da wannan haWin ba. Maijidda ki sa a ranki rayuwar Wan uwanki musulmi za ki taimakawa, ke din mace tagari ce da muka yi amanna da tarbiyyarki da kyawawan Wabi'unki, mun kuma sani za ki ri?e Yaya da amana. Ba sai mun tsaya Sata baki wurin labarin wacece Maryam ba, kusan ma kin fi mu saninta akan kowa. Amincewarki kawai muke da bu?ata a yanzu. Don Allah kar ki tuna kowa ki daure wannan zuciyarki ta ki, ki samarwa Yayana gurbi a cikinta."

Dariya Anti Maijidda ta yi.

"Amina kenan, shikenan, na ji saga gareki, sai ya zo din. Allah ya zaSa mana abin da ya fi alheri."

"Yeee Amin Anti Amaryarmu. Godiya godiya."

Suka juya gaba Waya, Raihana ce ta rungume Anti Maijidda ta baya tana murna da wannan sambatun. Itama Ummita ta fito tana dariya, ashe akan kunnuwansu aka yi komai.

"Ja'iran yara, dama laSe kuka yi mana? Oh ni Amina."

Anti Maijidda kuwa murmushi kawai take yi ba ta ce komai ba duk rashin shirunta a magana.

Raihana ta zagayo ta zauna tana dariya.

"Ni dai Baba ba laSe na yi maku ba. Ummita ce fa ta yi ba?o shi ne muka fito tarbarsa."

Jin haka suka kara duban Ummita, ta sunkuyar da kai tana murmushi a kunyace, ta shirya tsaf kuwa abinta cikin wata koriyar atamfa sai mayafi ta yi kyau shar da ita.

"Ridwan din har ya iso?"

FaWin Anti Maijidda, ta gyada kai tana murmushi.

"Ki je toh kar a bar shi da zaman jira."

Suka fice har Raihana tana cewa bari ta je sai ya ba ta tukwuicin kwalliyar da ta yi mata. Suka bisu da kallo su na murmushi.

"Af wai ina Ahmad tun zuwana ban gan shi ba?"

"Yana gidan Wanki (wato dan Anti Maijidda babba, Bashir) a can ya kwana."

"Ai naji Yaya na cewa a karshen satin nan shi Ridwan din zai turo ko? Shima dai Al'amin din mai neman auren diyarki (Raihana) a satin nan zai zo a yi magana. Ba dogon lokaci za'a sanya ba, wata daya kawai Yaya yace idan har ba su ne suka zo da wasu uzurirrikan ba."

Sosai Anti Maijidda ta ji dadi. Ta yi addu'a akan Allah ya amince. Su Baba Amina da Raihana ba su suka bar garin ba sai yamma cike da tsarabar da Anti Maijidda ta haWa musu.

Bayan tafiyarsu ta yi waya da yan uwanta akan bukatar da Baba Amina ta zo da ita, babu wanda ya kawo kushen abin sai ma fatan Allah ya tabbatar da alheri.

***
Mami zaune a falon aminiyarta tana kuka kishirSan. Hajiya Lubna ko sai afkin girgiza ?afafu take yi. Can dai ta ja tsaki.

"Maryam kukan nan fa ba zai mana wani magani ba. Ni yanzu kin kara dagula lissafina, da wannan auren na Daddyn Kabeer (mijinta) zan ji, ko kuwa da wannan rigimar da ta Sallo maki. Nifa a ganina kawai ki je ga Babandi ki ba shi hakuri, ita kuwa Tasleem ki mayar da ita can kauye wajen Anna ta haihu kafin wannan baragurbin labarin ya fashe a gari kowa ya ji warinsa."

"Nayi tunanin haka Lubna, sai dai kuma Anna ta rantse min muddin na turo mata tsatson Isuhu wajenta sai ta tsinemin. Kina gani yanzu fama suke yi na yanda auren Jannat zai koma, daga zuwa raka Annar da ta yi sai sa?on saki ta samu daga Baban ?an biyu. Dama danginsa a wuya suke da ita, yanzu batun da nake maki fa har sun aura masa wata yar uwarsa. Wannan tashin hankalin ma ni ya yimin yawa Lubna, ta ko'ina babu sauki, aikin Babandi ya kwaSe, kissar ma ta daina aiki. Ga Futuha cikin matsala, ga ?assim da shaye-shaye. Na shiga uku nikam." Sai ta kara fashewa da kuka, amincinsu babu yaudara, aminci ne irin wanda hali ne ya zo daya tun farko aka kulla, sai Lubna itama ta ji hawaye sun zubomata. Su dai masu wuni da yini cike da farin ciki, matsala ba wata aba ce a wurinsu ba nan da nan da sun dau waya sun kira Babandi ko sun kulla wani makircin shikenan suke magance ta, yau kuma su ne cikinta birjik amma babu wani sauki. Ita dai idan Honarabul ya auri Hajiya Fareeda Mai Daham ta ta ta ?are, mace mai tarin dukiya da usuli mai kyau. Yar gidan Malamai da maza da yawa suke kai mata hari, tana da bala'in nutsuwa da kamun kai uwa uba aji da girmama mutane. A yanda ita ko ba ta kallon dangin Honarabul da gashi ai ta san rayuwa dai ta jin dadi babu ita babu shi a gidannan.

"Ki bari Maryam, yanzu kin dai ji Babandi na kirashi a gabanki ba ya gari ya je ganin gida, idan ya dawo sai muje mu same shi."

"Yanzu a tunaninki ba ?arya yake yi ba?"

Hajiya Lubna ta girgiza kai.

"Kayya, bana tunanin haka ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login