Showing 1 words to 3000 words out of 189325 words

Chapter 1 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

232

??ࡱ?>?? '????????????? ?
?
? ?
?
??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?FWordDocument????1?%0Table????????X&Data
???????????????????? P??KSKS?1?%?????????rr? ? ? ? ? ? ??[< ? ?2&2&2&2&2&2&2&2&4&$?"?I%*r? ? 2&2&? ? ? ? 2&s%?? s%2&? 2&s%? 2&2&? ?  ?^`????^Normal d??,CJmH sH nHtH_HOJPJQJ^JaJTA`????TDefault Paragraph FontOJPJQJ^Jfi`????f Table Normal :V ?4?
l4?a? OJPJQJ^J(k`????(No List ??f!J:[>t,?.???f???X??z?**??OB_ni>~?? ??????F???
*B'?=?Bismillahir Rahmaanir Raheem.
Dukan Ruwa paid book ne. Akan ? 400, ka/ki duba girman Allah kar a fitarmin da wannan Doc din. Nagode.
? Acc no: 0452523875 Ibrahim Rufaida Umar. Gtbank. ?


? ? ? ?? *DUKAN RUWA...*

FARKO.

Ta yi zugum kanta jingine jikin kujera tana kallon halittun manyan? duwatsun da suke ratsawa a wannan dajin, tafiya suke yi tamkar ba za su kai ba. Wani lokacin idan sun gifta bukkokin jama'ar wani yankin, takan yi murmushi cike da al'ajabin ta yadda mutum ?AN ADAM ke iya rayuwa a wannan wuri. Tun tana kallon har dai ta zame ta gyara zama gami da lumshe idanu, bacci ke ?o?arin Waukarta tana yakicewa. Babu abin da ta tsana sama da bacci a hanya, hanyar ma da ko a mafarki ba ta taSa ganin za ta bi ba,? zuwa Nijeriya daga Nijar.
Ajiyar zuciya ta saki tamkar wacce ta ci gudu, lokaci guda nannauyen tunanin da take ?o?arin kaucewa na ?ara yi mata saukar aradu a kwakwalwa. Idanunta ta sauke akan matar dake kusa da ita, baccinta take hai?an har carbin da ke ri?e a hannunta tana ja, ya faWi. Sai dai duk da baccin da ta lula, hakan bai sa ta saki yaronta ba, yana rungume a kirjinta Wam! Kai ka ce wani ne zai ?wace mata shi. Juya kai tayi ta koma kallon hanya da murmushi Wauke saman fuskarta. Soyayya da sha?uwar dake tsakanin Wa da uwa na daban ne, a kowane yanayi, a kowace rana burin kowace uwa ganin gudan jininta cikin walwala da annashuwa, ba ta fatan wani mugun abu ya same shi. Shakka babu duk wanda ya rayu da uwa ya more.
? Sai kuma kewa ya lulluSe ta dalilin Dada da ta tuno, watanni biyar kenan da rasuwarta amma jin sa take a rai tamkar jiya-jiya. Kullum mutuwar kakarta kamar sabo ne fil a wurinta, mace mai hakuri da dattako, ta yi namijin kokari wurin ba ta kulawa daidai gwargwado da kuma tarbiyyar islama. Ba ta sha?u da kowa ba sama da ita sai ko Kawunta Wan uwan Mamanta, Kawu Umaru. Shi ma ba ta jin za ta manta da irin namijin ?o?arin da ya yi a kanta, koda dai dama barewa ba ta yi gudu ba Wanta ya yi rarrafe, wannan kyawawan Wabi'un Dada ne suka kwaso. A wannan irin namijin ?o?arin ne a yau Kawunta ya tashi hai?an suka bi wannan doguwar hanyar kawai don ya sada ta da mahaifinta, mutumin da tun da ta buWi ido ba ta taSa ganinsa ba. Hatta a waya ba su taSa koda gaisawa ba.? Duka wannan bai sa ta ri?e mahaifinta a zuciya ba domin kuwa ya samu kyakkyawar shaida a gurin Dada da Kawu. Ko sau Waya ba su taSa kawomata kushensa ba, asalima sun ce yana sonta sosai, kuma acewarsu ya sha zuwa ganinta tana ?arama, su Win ne suka ?i amincewa ya tafi da ita bisa dalilan da su kaWai suka bar wa kansu sani. A yau kuma da aka wayi gari babu Dada, Kawunta ya Wauki Wamarar cika wasiyyar da Dada ta bari na cewar ya sada ta da Mahaifinta idan har rai ya yi halinsa.

? ?an girgizar da motar ta yi sakamakon taka wani Wan tudu ne ya sa ts ji saukar ruwa a saman leSSanta, sai lokacin ta gane kuka take. Kukan kewa da damuwa ne, Dada ta tafi, tafiya ta har abada, ta tafi wajen da ba za ta sake ganinta ba sai ko idan nata ajalin ya iso, ta je ta tarar da ita.
? _"Kar ki taSa bakin ciki da zuwa wurin Mahaifinki Shatu, mutum ne nagari mai sanyin hali, za ki yi farin ciki da ganinsa. Yana sonki sosai Shatu."_

Kalaman Dada suka faWomata a rai, ta sauke ajiyar zuciya na samun nutsuwa, lokaci guda ta ciza leSSanta na ?asa tana ?ara murmusawa karo na barkatai. Ya mahaifinta yake? Da wane ido za ta Waga ta kalle shi ya kalle ta? Dagaske tana kama da shi ko kuwa dai Kawu ya faWi ne don ta ji dadi? To an ce yana da wasu yaran, su ma tana kama da su ko aa?

Duka waWannan tambayoyi ne da ta hargitsa lissafin kwakwalwarta da su alhalin babu mai ba ta amsa. Haka dai ta yi ta sa?e-sa?enta har suka fita gaba Waya daga Nijar suka nufi bodar Nijeriya.
Nan Win ma bayan kammala cike-cike da duba kayyakinsu, suka gangara cikin Nijeriya, ta baza ido tana kallon yanda cikin iko da hukuncin Allah, shuke-shukensu ya sha bamban da na ?asar da ta fito.

***

"KATSINA" Ta karanta sunan a hankali, sannan ta dinga bin garin da kallo tana ?arewa bambance-bambancen garin da nasu. Tunaninta ya katse sa'ilin da direba ya? tsaya a gefen hanya domin ba su damar gabatar da sallar la'asar. Mazan duk suka riga su sauka, su ma suka sauko. Kawu ya dube ta.

"Ki bi su ku yi sallah kar ki je ko'ina kin ji ko?"
Ta gyada kai ta amsa da toh, tana rungume da ?ar ?aramar jakarta ta hannu haka ta dinga bin matan su uku har zuwa wani Wan wuri da aka katange, suka samu gefe guda da ba mutane, masu jin fitsari suka yi sannan suka Waura alwala. Bayan sun idar suka dawo motar, nan kuma kowa ya hau zuge jaka ya na siyan abin motsa baki. Tana nan zaune cikin motar Kawu ya kawo mata ruwa da lemu sai nama a leda, kaWan ta ci bayan ta yiwa ?an motar bismillah, sauran ta naWe ya ajiye a gefe, lemun dai ta sha sosai.

Daga nan suka ?ara mi?a hanya har dai cikin hukuncin Allah suka ?araso cikin garin KANO.

Ta nanata sunan a kan harshenta jin wata Mata ta ambata, ta maimaita har sau uku, lallai idan ba ta mance ba shi ne sunan da Dada ke yawan ambata idan ta tambaye ta sunan garin Mahaifinta.? Nan da nan zuciyarta ta yi fari ?al, ta kasa rufe bakinta, wannan karon murmushi take tun daga ?asan zuciyarta har saman leSSanta don har siririn wushiryarta na bayyana. Sai da suka ?arasa tasha suka sauka, daga nan ne kuma Kawunta ya Wauki akwatin kayanta suka fito bakin titi. Suna hawa taji ya ce unguwar Gadon ?aya, daga nan direban ya hau tafiya ita kuwa tana ta kallon hanya har suka sauka. Sun yi ?ar tafiya a ?afa sannan ta ga ya tsaya daidai bakin wani Wan shago ya yiwa mai shagon sallama. Koda suka gaisa ya ce.

"Don Allah gidan Alhaji Isuhu Maiagogo nake tambaya."

Mai shagon ya gyada kai ya Wan fito sarari ya hau yi musu kwatance da hannu. Ya yi godiya suka nufi inda ya ce.

Koda suka karasa wajen wani ?aton gini ta ga ya tsaya cak a gaban ginin, ta bi ginin da kallo ta ji gabanta ya yanke ya faWi lokaci guda, ba kuma don tasan dalili ba. Ta kasa kwakkwaran motsi har Kawunta ya taka zuwa ga kofar gidan yana tambayar wani dattijo ko nan ne gidan, amma ita kam ba ta dauke kai daga kallon ginin ba, gwuiwoyinta suka yi wani irin saki, ganin yanayin da ta shiga har zufa na tsastsafomata a goshi yasa ta dinga maimaita kalmar innalillahi.

"Shatu ke!"

Kiran da Kawu ya kwalamata ne ya maido ta hayyacinta, a hankali ta soma takawa har ta ?arasa gefensa, ba ta kuma san dalili ba ya ji ta sa hannu ta ri?o nashi yatsun gam!
Hakan da tayi ya sanya shi dubanta, itama shi din take kallo, ya yi dariya.

"Tsoro gidan ya ba ki ne? To ki shirya ya?ar tsoron nan don nan ne gidan zamanki daga yau in sha Allahu."

Dattijon ya taya shi darawa kaWan duk da bai fahimci komai ba. Amma ta lura da yadda yake ta kallonta har ya kasa hakuri ya tanka.

"Amma dai wannan ?ar uwar Alhaji ce ko?" Kawuna ya yi dariya ya amsa da eh kawai. Ita dai ba ta ce musu uffan ba sai sadda kai ?asa da ta yi, ta na ji Dattijon nan na kara zuzuta kamanninta da Alhajin wanda shi ya sanya shi tankawa.? Suna nan dai? tsaye sai ga wani Wan matashin yaro ya fito, ashe wai Dattijon ne ya aika shi gidan don a shaida wa Maigidan zuwansu.

"Ya ce maza ku shigo ciki. Muje na raka ku."

Daga haka? suka shiga ciki. Madadin faWuwar gabanta ya ragu, sai ma ?ara hauhawa da ya yi, ta ci gaba da maimaita innalillahi har ?arshe, sai ta ji gaba daya ta bar rawar ?afar son haWuwa da Babanta Isuhu.

?? Koda suka ?arasa cikin ?aton falo, wani irin sanyi da ?amshi mai dadi ne ya daki hancinta. Ta gefen ido take bin wurin da kallo tana so tayi ido huWu da Babanta, sai dai kuma duk irin girma da daular da ke shimfiWe a falon wanda ya ?ara ?awatashi, babu rai ko Waya mai numfashi face su ukun da suka shiga.
Wuri ya nuna masu saman kujera suka zauna, ita kuwa ?asa ta zauna gefen Kawu don ba'a ba ta tarbiyyar zama saman kujera alhalin manya na zaune ba. Matashin ya kara juyowa fuskarsa a sake.
? "Ku jira YallaSai nasan ba zai jima ba zai fito." Kawu ya amsa daga nan ya fice ya bar su a nan. Sun samu mintoci goma da sakanni, don gaba daya hankalinta yana kan ?aton agogon da ta zauna saitinsa, kafin ta ?arasa ?irgenta suka tsinkayi sallama. Lokaci guda suka kai duba ga gefen da muryar ta Sullo, baki da ido ta saki tana kallon mutumin yayinda shi kuma idanunsa ke kan Kawu, kallon mamaki da tsantsar farin ciki yake binsa da shi.

A gefenta kuwa halittar fuskarsa take ?arewa kallo. Eh, tabbas suna kama, fuskarsa doguwa kuma siririya irin nata, yana da dogon hanci masha Allah, sai kuwa bakinsa daidai. Idanunsa manya kamar naya hatta da cikar halittar girarsa da gashin kai, duk kuwa da cewa shi nasa gashin ya yi fari fat na manyanta amma kamanninsu da shi sun fito fes har tsawon. Ba ta ?ara gani ba sai da ya saki dariyar farin ciki, anan kuma baki hangame ta ce. "Kai!" Ta furta a fili ba tare da ta shirya ba. Gaba daya suka juyo su na dubanta. Ta kama bakinta da sauri gami da ?ara sunkuyar da kai, mutumin ya matso ya dur?usa a gabanta, zuciyarsa ta yi wani irin nauyi, abubuwa da dama suka shuWe a tsawon shekarun baya suka dawo mishi sabo fil. Ita kuwa kunya ce ta kama ta, bata ma gaida shi ba, ta gaishe shi a hankali don a zaton ta ma bai ji ba, amma ga mamakinta ya amsa.

"Barka da zuwa Mamana. Ki saki jikinki nan gidanku ne, gidan Abbanki, ba ki da inda ya fi nan kinji ko?"

Da ya fadi haka wai sai ta kalli Kawu, hakan da tayi ya ba su dariya. Kawu ya gyaWamata kai.

"Idan eh kike so nace ko aa, toh eh Shatu, gidan mahaifinki kenan. Abin tun?ahonki."

Ta yi murmushi tana kara duban wanda ya kira kansa da Abbanta, sai nan da nan kwalla ta cikamata idanu. Wannan fargabar ta kau, so da kaunar suka dawo daga hutun da suka je, ta rungume hannunsa ta saki kuka sosai. Abubuwa da dama take tunawa, tabbas ta yi kewarsa a rayuwa. Koda ace ba ta rasa ci, sha da sutura ba daidai da kwana Waya a rayuwa, to ta rasa wannan kusancin na Wa da mahaifi, shi din na dabanne. Ko ma dai tace ta rasa soyayyar iyaye gaba Waya.

"Kiyi hakuri Mamana, ba zan ?ara yin nesa da ke ba, wancan ma ?addara ne, amma wannan karon in sha Allahu ni da kaina zan mi?a ki Wakin mijinki. Allah ya ji ?an Mahaifiyarki da Hajiya Dada."

Suka amsa da amin. Nan kuma ya shiga jan ta da hira kadan har ta sake, waya ya zaro a aljihu ya danna kira, sunan wata ya ambata, Ummita, ya ce ta zo yanzu. Daga haka ya? juya ga Kawu suka yi ta hira yana ba shi labarin rashin lafiyar Dada har zuwa rasuwarta. Suna nan zaune ita kam ta kasa Wquke ido akan Abban, suka tsinkayi sallamar wata ?ar budurwa da ba ta wuce sa'arta ba. Ba?a ce, irin ba?in da hutu ya ratsa, riga da wando ne a jikinta sai dai ba su Wame ta ba, ta saka hijabi iyaka kafaWarta. Ta gaida Kawu sannan ta maida hankali ga Abba.

"Yauwa Ummita, kama hannun ?ar uwarki ku je a ba ta abinci ta ci ta yi wanka. Ki kuma faWawa Maminki ina da ba?o a shirya masa abinci kafin mu yi sallah. A kawo ruwan sha."
Ummita ta amsa da toh tana kallonta fuskarta a sake ta ce.??

?? "Lah Abba wallahi kuna kama sosai."

Duk sai ta ba su dariya, Abba ya dubi Aisha Humaira kafin ya maida duba gareta.

? "Itama ?ata ce, ita ce mai sunan Umma."

"Abba ita ce wacce ka ce tana Nijar ko?" Wannan karon da wani irin zumuWi ta yi tambayar. Ya amsa mata da eh. Ta kuwa karaso da sauri ba tare da nuna kyankyamin komai ba ta rungumeta tana fadin. "Welcome Sister." Ba ta gane me ta ce ba amma itama ta rungumeta tana mai jin kaunarta har can ?asan ruhinta.
? Ummita kenan, tana daga cikin mutane masu girma da matsayi sosai a rayuwar Humaira, har abada Humaira ba za ta cire ta a tarihin rayuwarta ba, ta karSe ta a yadda take, ?ar kauyen Maine. ?amshi take a yayinda ita kuwa ba ta ma sani ba, ?arnin kifin da ta ci a mota take yi ko kuma naman da ta ci ne. Kai ko ma mene ne, ta sani Ummita ba ta irin wannan ?arnin, ?amshi ne a jikinta, amma ba ta duba komai ba ta rungumeta. Ta tabbata tana daga cikin masoyanta na ha?i?a. Ta kama hannunta Wayan hannun kuma ta Wauki akwatin kayanta wanda duk ya ci gidansu, akwati ne irin na da da aka yi yayinsa, Dada ta ce nata akwatin tun na auren Mamanta ne.
? Suka nufi wata ?ar siririyar hanya suka fito wurin wani ?aramin hanya nan ma gefensa duk shuke shuke. Wurin ya burge Aisha Humaira sosai, a daidai ?ofar shiga wajen ma, shukoki ne sun kewaye jikin ?ofar da bango sun ba da zane mai kyau. Ummita ta ci gaba da tafiya har suka nufi wani Sangaren, baranda ne sai kuwa wata ?ofa, suka shiga Ummita ta shiga kwala ihun kira.
"Mami! Mami!! Fito ki gani!"

Ihun da take tana kira ya sa sauran mutanen dakin suka fito. Maza da mata wadanda sun Wan girme ta sai ko yara.

"Wai Ummita me ke damunki haka? Tun Wazu bakinki ya ?i..."

Aisha Humaira ta lura haWa idanun da suka yi ne ya sa sauran kalaman bakin matar suka ma?ale. Kallonta take kamar a razane, ita kuwa kallonta take tana so ta ga ta inda suka yi kama da Ummita don ko kaWan ba su yi kama ba. Ummita ba?a ce, wannan kuwa ta tsaye a gabanta da alama ma buzuwa ce. Gashinta a tufke a baya, ta kai duba ga wasu a cikin yaran, su ma farare ne ?al, kyawawa da su.

"Wace ce wannan?"
?aya daga cikin ?anmatan ta tambaya tana bin Aisha Humaira da kallon tara saura. Ummita ta yi dariya ta jawota ta rungumo kafaWarta.

"Mami, mai sunan Umma ce ta zo daga Nijar, Aisha Humaira. Abba ya ce shikenan ta dawo nan da zama cikinmu."

Wacce aka kira da Mami, ta tamke fuska babu ko Wigon annuri, suka kalli juna a kar na biyu. Kallon da ya da ya sa Aisha Humaira ta ji hantar cikinta ta kaWa, dariyar matasan ne ya sa ta maida idanu kansu.
??
"Wai! Ni da yagwalgwal, amma wannan ma a Nijar Win a can ?auyen kike ko?"

?aya a cikin matasan ya furta yana dubanta, idanunta nan da nan suka cicciko da kwalla.

"Kai Yassar, bana son haka. Sannu da zuwa Humaira, maza Ummita kai ta Wakinku ta yi wanka lokacin sallah ya gabato."

Da sauri na kalli matarnan, na sha mamaki ganin kamar ba ita ba, ta saki fuska sosai tana murmushi har ha?orin makkanta ana gani. Har Ummita ta faWi sa?on Abba, Humaira ba ta iya tankawa ba hakanan ba ta iya Wauke idanu daga kanta ba, itama jefi-jefi tana magana da Ummita tana kallonta ta kuma rasa dalili. Har Humaira ta bi bayan Ummita zuwa Waki ba ta daina waigenta ba, kuma itama Mami ta ?i matsawa balle ta dauke ido a kanta.? Ita kam Humaira jikinta ya ba ta kamar akwai wani abu.
A hankali ta bi kowace kusurwa a Wakin da ido, gado ne kananu har hudu kowanne a nashi wurin, a gefen kowane gado akwai sif na kaya kamar dai Wakunan makarantun kwana, babban daki ne mai yalwa wanda har akwai gurbin da ire-iren gadon uku za su samu matsuguni. Daga can gefe jikin taga kuwa, ?aton madubi ne a saman dirowar gaban cike da kayayyakin kyalkyali na adon fuska da mayuka. Dakin tsaf-tsaf babu ?azanta, Wakin ?anmata kenan. Ummita ta Waga akwatin tana shirin ajiyewa saman Waya daga cikin gadajen nan, baki bude tana kallon Humaira da niyyar magana, aka daka mata wani uban tsawa daga baya.
Muka juyo, wannan dai budurwar ce ta Wazu mai ?ibar ciki. Ta zo da sauri ta janye akwatin ta yi wurgi da shi gefe. Idanu cike da masifa ta soma magana.

? "Wallahi kar ki kara? gangancin ajiyemin jakar wannan korar yunwar a gadona, don gulma da kinibibi idan abin naki dagaske ne meyasa ba za ki ajiye a naki gadon ba. Aikin banza kawai, uwar shishshigi. Haka za ki ?are."

Tana kai wa nan ta? fice daga Wakin tana mita,? Ummita ta kalli Humaira gami da jifanta da murmushin ya?e.

"Ki yi ha?uri."

Ta gyaWa mata kai tana maida mata martanin murmushin sai dai can ?asan ranta, tana maimaita kalmar da ta ambata "Korar Yunwa". Ta fahimci manufarta tsaf, ta kuma gane ko wace ce ba ta samu karSuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login