Showing 138001 words to 141000 words out of 189325 words

Chapter 47 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

220

tana kuka da ihun a yafe mata don gaba daya kuma da ta ga al'amarin dagasken gaske ne sai ta shiga tashin hankali. Abba kuwa ana ficewa da ita ya fice zuwa dakinsa, tun a falon ya sanya mukulli ya kulle don ba ya bu?atar ji ko ganin Mami a wannan yanayin. Yana bu?atar samun hutun da zai yi tunanin da ya dace.

***
Duk wannan budurin da ya faru su Futuha ba su da masaniya a kai sai washegari labarin ya riskesu daga Dawud da ya yi waya ya zayyane musu komai da komai. Zo ka ga kuka da sheshsheka wurinsu musamman Tasleem da ta ji tamkar an tafiyar mata da wani sashe na jikinta don za ta rantse sha?uwa da kaunar dake tsakaninta da Jannat ta shallake nata da na Mami. Ita mai shirin fita zuwa makaranta inda suke shirye-shiryen zana jarrabawar ?arshe sai ta fasa suka Wunguma har Futuha zuwa gidan. Ba su iske Mami ba don tun ranar da aka tafi da Jannat suke asibiti sakamakon faduwar da Anna ta yi, ita ta kwana a wurinta bisa iznin Abba don shi dama ba shi da bu?atarta yanzun. Ta riga da ta gama sirewa a ransa. Raihana suka soma cin karo da ita kwance a falon da casbaha a hannunta tana ja.

"Ke ina suka kai Anti Jannat?"

Tambayar da Tasleem ta soma jifanta da shi cikin zubar hawaye ko zama ba ta yi ba. Guntun tsaki Raihana ta ja a ?asan ranta a fili kuwa dakyar ta ce.

"Nima ban sani ba."

"Uhum, nikam tun farko dama sai da na nuna rashin goyon bayana ga wannan.."

Idon da Futuha ta yiwa Tasleem ne ya sanya ta yin shiru, dagaske dai suSutar baki ta so yi, sai ta ji tsoron kada Raihanar ta fahimci komai. Ita kuwa Raihana koda ta fahimtar ma ba ta nunamusu komai ba, ta fi damuwa akan al'amarin kashe ran da uwarta ta so a yi. Har yanzu ta kasa kwantar da hankalinta, abin ya jefa ta cikin matsanancin damuwa da tunane-tunane.

"Kin je asibitin wajen Anna ne?"

Cewar Futuha, girgiza mata kai kawai ta yi. Futuha ta ja tsaki.

"Duk dai abinki duk wani guje-gujenki ba ki da sama da Annar da kuma mu, aikin banza kawai. Wato wai ke an taSa ?an uwanki shi ne kika dauki gaba da uwar uwarki. Dakyau."

"Rabu da ita dai Futuha, duk dai lalacewar naka naka ne. Tashi mu wuce asibitin don ni ko wajen Abban ba zan shiga ba. Ai yana ji yana gani aka titsa ?eyar Antin amma ya ?i hanawa saboda ya nuna son kai da fifiko tsakanin wasu can da mu."

Tasleem ya fadi tana huci gami da gyara goyon da ke kokarin kunce mata.

Sai a lokacin Raihana ta mike zaune a zafafe ta shiga ba su amsa.

"Su din dai jininmu ne koda kun ?i ko kun so. Kuma wallahi da ace ni ce ku zan ji da rayuwata ne ba na tsaya kallo da kushe ta wasu ba. Ke kuma da kike kiransu da wai ?an uwana, to ki goge kalmar wai din, yes jinina ne su kuma wallahi sun fiyemin ku nesa ba kusa ba. Kin tsaya ganin kuskure a rayukan wasu, kina nan mijinki har lefe ya kai na ?ar Snow zai aure ta. Mtsw! Nonsense!"

Tana kaiwa nan ta juya a fusace ta bar su a tsaye kamar an wawushe musu ?a?an hanji. Ba zagin da ta yi musu ne ya taSa su ba don dama batun raini to fa Raihana ta yi musu shi, ko kadan ba ta wani ba su girma tun a baya, yanzun ma da ya ragu sun sani ko sun ?i gaskiyar hakan ne albarkacin zama da su Ummita ne. Batun kai lefen ?ar Snow da Yakubu ya yi shi ne ya fi komai sanya su cikin razana. Lefe gagarumin da suka gani yana yawo yau kusan sati kenan aka ce na ?ar Snow ne, shi dai?

"Tasleem wai kodai ni ce ban ji daidai ba?"

Futuha ta fadi da wani irin ruWani, ita kuwa Tasleem ta Wan ji sanyi a ranta, kl babu komai idan har hakan ya tabbata ga Futuha zai kasance ba wai ita Waya ba ce ke sha?ar bakin cikin Wa namiji ba.

"Kai ta ya za ki biyewa wannan mahaukaciyar? Kema kin sani dai don ta sha?a maki ba?in ciki ne ta tayar da hankalinki."

Sai Futuha ta hau girgiza kai cikin mugun tashin hankali, Tasleem ganin haka ta ja hannunta suka fice tana fadin.

"Dallah Malama kar abin da ta fada ki bari ya yi wani tasiri a zuciyarki. Yakubun da ke Dubai yau kusan sati uku kike wani tunani na daban? Toh ina ce Wazun ma ya kiraki kun sha hira?"

Jin haka sai Futuha ta dan samu nutsuwa, sai kuma ta yi kwafa.

"Shegiyar yarinya kai, wallahi ta jefa ni cikin ruWani na Wan lokaci. Zan yi maganinta ne bari mu dawo."

"Atoh, ko kefa. Ni so nake Anti Jannat ta fito, don ba ma za'a kwaso kayana ba sai ta fito idan ya so na siyar mu haWa kuWin ta kai wa Teacher dinta ya karkatomin hankalin Fadeel."

Ta fadi Teacher gudun kar wani ya ji. Futuha dai jinta kawai take amma har a ?asan ranta ta san da wuya aikin ya ci. Yaudarar kai dai Tasleem ta ke yi, amma da aiki na cin Fadeel da Ibb da tuni wani labarin ake ba wannan ba.

***
Mami zaune a gefen gado bayan ta gama ba Anna abinci dakyar ta yi loma biyar ba ta ?ara marmarin ci ba. Sai kuka take yi tana tsinewa Abba kai ka ce shi ne ya sanya a kama Jannat. A wannan yanayin su Tasleem suka shigo dakin, haWa su tayi gaba daya ta rungume tana kuka wai an tafi da shalelenta. Mami kuwa sai ta mike ta bar musu gadon ta koma saman kujerar dakin cike da dumbin tunani. Toh wai waye ya sanya aka cigaba da bin ?wakkwafi har aka binciko gaskiyar al'amarin? Ta san dai Abba tuntuni ya bar maganar. Sai ta Wan ja tsaki, ita ba ma wannan ba, ta kasa gane wanda ya sanar da ?an sanda har aka kai wa su Abba Wauki, ga kuma wani sauyin da take fuskanta daga Abban, wannan kuma ta fi danganta shi da Jannat wacce asirinta ya tonu. Watakila fushin da ya yi da jin zancen ne ya shafe ta.

"Saki kuwa ni Hansatu?! Shi Hamzan ne ya sake ki?!"

Furucin da Anna ta yi ne cikin dafe kirji ya sanya Mami maido hankalinta ga hirarsu. Ta mike tsaye cikin mugun firgita tana duban Tasleem wacce ko a jikinta, haka ma mikewar Mamin ba ta wani razanata ba, Wan shakkar Mamin da take ji a baya yanzu duka ya kau adalilin jin wacece ainahin Mamin da ta yi daga bakin Futuha sai ta gane cewa ashe ita da ma su Jannat ba su yi komai ba kuma ba za su taSa shuka irin abin da ta shuka ba a rayuwa.

"Wa aka saki?"

Mamin ta ?ara tambaya don gani ta yi tamkar ba ta ji daidai ba. Tiryan-tiryan Tasleem ta ba su labarin abin da ya faru ta ?ara da fadin.

"Nifa Mami wannan abun ya yimin daidai kuma ya zo kan gaSar da nake da bu?ata. Ya je ya auri uwar Ramlatun ma ina ruwana. Ni yanzu Fadeel nake so na aura."

"Za kuwa ki mutu ba aure! Ke shashashar ina ce?! Waye ya faWamami akwai ranar da tsinannen yaron can zai aureki?! Wallahi na rantse maki har abada ba za ki taSa aurensa ba! Tun muna shaidar juna ki tashi ki koma Wakinki ko kuma yanzu na saSa maki!"

Ta turo baki.

"Nidai Mami bana son aurensa. Dama wallahi da nasan matsiyaci ne babu abin da zai kai ni ga aurensa. Ai kowa yana auren ne don ya samu gida hutun da zai ci karensa babu babbaka, idan ma mutum bai samu ba sai ya Sullo hanyoyin da ya san hakansa zai cimma ruwa. Toh ni dai ba zan iya aikata abubuwan da kika aikata ba amma zan iya ya?i da namiji har ya sauwa?emin na fito na samu cikar burina."

Maganganunta sun sa Mami ta yi Wif na wucin gadi, ta kuma kalli Anna wacce ke kallonta itama cikin rashin fahimtar komai sannan ta maida duba ga Futuha da alamar tambaya. Futuha kuwa ta kauda kanta tana Wan taka yatsun ?afar Tasleem, tana bin ta da kallon ya za ta yi mata haka? Ita kuwa Tasleem kafaWunta kawai ta Waga kaWan gami da kauda idanunta don ta rantse ta shirya ya?i da duk wanda ya ce sai ta koma gidan Hamza. Yanzu dai Mami ce za ta yi mata ya?in da za ta wanku a idanun Abba ko kuma ta yi barazanar tonamata asiri a wajensa. Wannan shi ne ?udurinta.
"Ke! Ni sa'arki ce? Ni kike yiwa wannan maganganun?"

Mamin ta fadi cikin zafi da kuma son sanin ainahin manufar Tasleem din.

"Nasan komai Mami, na san wace ce ke da abubuwan da kika aikata. Wallahi samun da za ki yi na rufamaki sirrikanki nayi shiru da bakina guda daya ne, ki wanke ni a wurin Abba ya amince na zauna a gidan ba tare da kwaSa ko wata tuhuma ba. Wannan kaWai za ki yimin ni kuma na maki al?awarin zan Soye komai."

Gumi ne ya tsirfowa Mami a goshi, kirjinta har wani tagwayen lugude ya shiga yi. Wane irin suSul da baka ta yi har ta zayyanewa Futuha komai da komai ba tare da tunanin hakan kan iya haifar mata matsaloli a gaba ba? Yanzu gashinan wa gari ya waya? Kai! Wai Tasleem dai Wiyar cikinta ke yi mata barazana ko kuma ta tona mata asiri? Ta kara Waga idanu ta kalli Tasleem din wacce Anna ta damu da tambayar mene ne shi din da Mamin ta aikata amma ba ta ce uffan ba itama idanunta a kan Mamin tarr babu shakkar komai. Wannan ya ?ara firgitar da Mamin, sai kawai ta sanya kai ta bar Wakin ta fice ba ya ko tsaya amsa kiran da Anna ke kwala mata ba.

"Kai bana son iskanci kun ji ko? Ku faWamin abin da Maryam ta aikata na san matakin dauka kafin itama wannan mugun uban naku ya sa a ficemin da ita."

"Haba Anna, duk fa lalacewar uba uba ne."

Futuha ce ta fadi don har ga Allah ta ji sosuwar rai bisa kiran Ubansu mugu da aka yi. Tsaki Tasleem ta ja.

"Sai ki yi ai, uban da bai damu da namu farin cikin ba za ki shigarwa don an fadi aibu a kansa? Anna bari kiji abubuwan ban mamakin da Wiyarki ta aikata."

Tana fadin haka ta kwashe dukkan wasu labaran da Futuha ta ba ta ta fesarwa Tasleem, inda ta yi kuskue Futuha ta gyara, idan ma mantuwa ce ta yi sai ta tuna mata. Anna wani irin murmushi take yi sosai. Sai da suka kai aya sannan ta girgiza kai.

"Ban yi mamaki ba. Maryama dai da na baku labari akan zafin kishi za ta iya aikata komai, ban yi mamaki ba. Sai dai na cika da al'ajabin yanda har ni ta Soyewa wadannan labaran. Kai an gaida Maryama. Muna mata kallon biri tana mana kallon ayaba."

"Uhum, ai ni kaina Anna na sha mamaki. Farko na yi zaton duk don soyayyarmu ce ta sanya amma kuma zuwa yanzu na fahimci son zuciyar Mami ne. Kanta kaWai ta sani ba ta damu da mu ba."

Tasleem ta furta a zafafe. Futuha ta girgiza kai ta bude baki za ta yi magana Anna ta tari numfashinta.

"Shashasha kawai, ke ba ki san Maryama ba. Son kanta ai ku din ne kan nata. Ni na sani tabbas dagaske domin ku samu jin dadi da walwalar ta aikata hakan, amma shi ne don ranki a Sace yake kike neman kwaye mata zani a kasuwa ko?"

Tasleem dai turo baki tayi kawai tana kokarin fiddo nono ta ba bebinta. Sai kuma aka koma jimamin Anti Jannat, Futuha ta kira Yakubu ta sanar masa komai saboda sanin da ta yi yana da manyan mutane watakila su shiga rigar alfarma a saki Jannat.

***
NIJAR.
Humaira cikin ?an uwanta da abokan arziki a garin na Maine. Gaba daya a kwanaki uku da ta yi ba ta da wata damuwa sai farin ciki da annashuwa. Kawunta sosai yake hidimar kawo mata dukkan wani abu da take so. Matarsa Tanti Hafsatu da suke kira da Hajjo kuwa ita da wasu cikin yan uwan Mamanta tun zuwanta aka soma yi mata gyare-gyaren aure. Ci wancan sha wannan, wasu kuwa tana ji sai dai su ce ba yanzu ba sai a ranar da za a kai ta. Wannan gatan da take samu ya sanya har hawaye takan yi, ta sani ba don Mami ta dauki fushi da ita kan lamarin Fadeel ba, babu abu daya da ba za ta samu daga gareta ba. Amma fushin ya kore komai. Sun gaisa da Abba a wayar Kawu amma koda wasa bai yi mata wani bayanin game da abubuwan da ke faruwa ba. Hakanan Fadeel da su Ummita, su din ma babu wanda ya ce komai. Shi Fadeel batu ne na Jannat, koda wasa bai bari ta ji ba don ba ya son abin da zai Waga hankalinta.

A rana ta hudu Kawu ya kawo mata magungunan tsarin jiki sai rubutuka da ya yi mata. Tun soma shan da ta yi ta soma jin sauyi daga gangar jikinta. Ya ba ta addu'o'i masu ?arfi ya ce ta dinga yi kullum safe da yamma sai kuma tashin dare da ya lura tana yi har ya zame mata jiki, nan ma ya bata wasu addu'o'in. Ya kuma ce ta dinga karanta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin ?afa arba'in duk sadda ta shiga wata damuwa.
A kwanakin da ta yi ta ga soyayya da kauna matuka, har ta cika sati cif bata da wata damuwa ko na Wigo. Ana gobe za ta wuce su na zaune su na shan hira da Kawu yana mata nasiha akan zaman aure da kuma irin kyawawan halayyar mahaifiyarta sak ta dube shi cikin nutsuwa.

"Kawu, don Allah mene ne ma?asudin rabuwar Mamana da Abba?"

Ya Wan yi shiru, toh meye amfanin Soyon tunda har Fatima a yau babu ita? Shi kansa akwai al'amarin da ya Waure masa kai a labarin wanda har yanzu bai fahimta ba sai dai ya yi karfin halin ba Humaira dukkan labari. Daga na irin soyayya da kaunar da Abba suka yi da Fatima, da ma kuma yanda a karshe ta zo ta tsane shi mugun tsana wanda sun sha tambayarta ta ce musu ita dai ba ta sani ba kawai ta tsane shi. Ya ?ara da fadin.

"Wannan tsanar har Fatima ta mutu ba mu gano silarta ba, idan ya taso mata sai ta dinga ri?e kanta tana ji yana mata ciwo tamkar ya fashe, wani lokacin kuma ta yi kuka mai yawa daga bisani bacci ya Wauke ta. Mun bar shi akan iskokai ne. Sadda za ta rasu kuwa, lafiya lau ta haifeki sai bayan ma har ?anwar Dada, Inna ta mata wanka ta shirya ta tsaf kawai aka shiga aka ga fuskarta da dukkan jikinta ya yi ba?i?irin kamar wacce aka ?ona. Aka tattaSa aka ji babu rai, gaba daya lokaci guda ta komaWe ta koma tamkar babu jini a jikinta."

Humaira da tun soma labarin take kuka sosai ga wani irin fargaba da ya shigeta da kuma tausayin Mahaifiyarta ta ce.

"Kawu kenan nima idan na haihu zan mutu ne irin yanda Mammana ta rasu?"

"Haba Humaira, wa ya ce maki haihuwa mutuwa ce?"

Ta girgiza kai.

"Kawu nima na yi fama da makamancin wannan halayyar na Mamma akan Fadeel. Ni tsana ce na yiwa kowane Wa namiji da zai ce yana sona."

Ya yi shiru yana kallonta da mamaki, ta cigaba da koramasa bayanin duk yanayin da ta tsinci kanta a ciki da ma haya?e-haya?en da Mami ke yi mata don taimakonta. Sai wani tunani ya zo masa, tabbas Fatima ta ce itama a lokacin Mami ta taimaka mata da haya?i wanda nan da nan ta ke jin kanta na juyawa bacci mai nauyi ya dauketa kuma idan ta farka muddin ba Abban ta gani ba to fa tsanar ba ta ?ara dawowa. Ya tuna har haya?in ta ba su akan su cigaba da yi mata.

"Ya aka yi kika daina jin tsanar?"

Ya yi mata tambayar cikin sauri. Nan ta kwararo masa bayani, ita dai tun maida hankali sosai da ta yi ga ibada shikenan kuma sai komai ya sauya. Ta ba shi labarin abin da ke damunta wato tsanar Fadeel din da Mami ta yi. Hatta da farkon zuwan Fadeel din gidan wanda Tasleem ta yi zaton wajenta ya zo ta shirya sai da ta ba shi labari. Kawu ya yi shiru yana sauraronta cikin wata irin fargaba da tunani. Kada dai a baya sun tafka kuskuren yarda da Maryam? Ya tuna tabbas Fatima mai yawan ibada da nafilfilu tun sadda ta dawo gida Nijar suka lura gaba daya ta bar yin ibadunta yanda ya kamata. Hatta da sallah sai Dada ta yi magana take tashi ta yi. Idan ma ta idar babu wata doguwar addu'a take mi?ewa.

Ya ambaci kalmar Innalillahi zuwa karshenta a zuciya, bai mance ba akwai sadda wani Malami tun lokacin Fatiman ya ce asiri ne aka yi mata kuma da sanya hannun abokiyar zamanta amma sai suka yi biris suka ji haushi suka ?aryata shi, a tunaninsu ta ya ya za'ayi matar da take zaune da su da zuciya daya ta aikata wani mummunan abu ga Fatiman?

Jikinsa sai ya yi mugun la'asar.

"Kawu akwai wani abu ne naji ka yi shiru?"

Sai ya yi mata murmushin ya?e.

"Babu komai Humaira, maza je ki kwanta dare ya yi kinga gobe sammako za ku yi."

Ya fadi hakan ne saboda tare za ta wuce da su Hajjo sai budurwar Wiyarsa sa'ar Humairar, wato Safina. Sauran masu zuwa Wiyoyin Inna ?anwar Dada sai ana bai fi sauran kwana biyu biki ba za su taho da Kawun.

Mi?ewa ta yi ba don ta gamsu da yanayin fuskar Kawun ba ta yi mishi sai da safe ta bar wurin. Hajjo dake gefe tana damawa Kawun fura tana jinsu ta mike bayan ta gama damawa Kawun fura ta ajiye masa da ludayi, cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login