Showing 177001 words to 180000 words out of 189325 words

Chapter 60 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

245

ba. Futuha kuwa ta bi bayan Anti Maijidda da harara da tsaki.

Koda suka je, sosai Abban ya ja kunnuwansu akan kar wacce ta sake ta kawo raini ga Anti Maijidda, a yanzu uwa take a wurinsu. Ya kuma yi musu nasiha na rayuwa irin yanda ya saba lokaci lokaci. A karshe ya dubi Futuha ya tambayi mijinta, ta amsa da fadin yana lafiya amma ciki-ciki. Daga nan ya mike suka kama hanyar falonsa da Anti Maijidda dake salon tafiya, ko me ta faWawa Abban har wata ?ar dariya ya yi wacce t ?ara sha?awa Futuha. Sai kawai ta fashe da kukan taya uwarta kishi.

"Wallahi Tasleem duka maza halinsu Waya."

Ita dai Tasleem ba ta ce komai ba, hankalinta a tashe yake da wannan gamon da Anti Maijidda ta yi, ta ji gwara ta bi shawarar Antinta Jannat ta koma wajensu a can Agadez ta haihu tun kafin Anti Maijidda ta tona mata asiri. Ta yanke za ta sanar da Mami haka wannan dalilin yasa kamar an tsikareta ta mike ta shiga dakin Mami. Sai dai me, waya ta ga Mami ta saki a kasa tana kurma uban ihu, a guje Futuha ta shigo. Abba da Anti Majjidda wadanda su ma ihun ya shiga kunnuwansu suka dawo da sauri zuwa dakinnata.

Mami a gigice take magana idanunta rufe.

"Shikenan! Shikenan Babandi ya mutu! Ya ce zai kawomin sirrin da zan mallake Abbanku! Wayyo na shiga uku! Babandi ka dawo! Shikenan ka mutu ba ka bani asirin ba! Ka bar min Wiya da ciki! Wallahi ba za ta saSu ba sai an zubar da cikin nan!"

?akin ya yi tsit, Tasleem sai kokarin rufewa Mami baki take yi amma ina! Kusan zaucewa za'a ce Mamin ta yi, sosai take bori tana tone-tone! Futuha ta yi kan Mamin tana girgiza ta da karfi.

"Mami ya isa! Kiyi shiru haka don Allah!"

Abba kuwa baki ya saki yana ambaton sunan Allah, ya ji kamar jiri na kokarin kayar da shi Allah ya taimaka Anti Maijidda dake bayansa ta yi saurin ri?o shi.

A can falo kuwa Raihana da su Baba Amina dake doka sallama suka ji hayaniya a dakin Mamin da gudu Raihana ta soma yin gaba Ummita na biye da ita sai ko Baba Amina. Suka shiga daidai sadda Mami ta fincike daga rikon da Futuha ta yi mata tana nuna Maijidda.

"Wallahi Maijidda sai na kasheki yanda nayi sanadin mutuwar Sani da Jamila! Kema sai kin bar duniya! Kin yi kaWan rayuwata ta ?are sanadinki!"


Nan fa idanun kowa ya kuma sauka ga Mamin, Anti Maijidda ?arfin da yun?urin da take na ture Mamin sai ta ji gaba daya jikinta ya saki, Maryam ta yi sanadin mutuwar Jamila ?anwarta? Raihana kuwa ta toshe kunnuwanta ta runtse idanu lokaci guda tana mai dur?ushewa a ?asa, so take ya kasance mafarki ne ba gaskiya ba abinda kunnuwanta suka tsinkaya. Ummita kuwa ta ma rasa halin da take ciki balle kuma Abba da ya hau furta kalmar innalillahi har karshensa a fili da kuma ?arfi.
"Ke ce kika kashe Jamila?"

Anti Maijidda ta samu damar ya?ar harshenta da lebbanta dakyar ta jefawa Mamin wannan tambayar idanunta gaba daya sun kaWa, ba ma na azabar sha?ar da Mamin tayi mata kawai ba, aa har da ba?in ciki da mugun firgici na jin wannan sabon labarin. Mami ta ?yakyace da dariya hakan yasa jikinta Wan saki da har Baba Amina ta yi nasarar ture ta daga jikin Anti Maijidda.

"Eh ni ce nan na sanya kananzir na cinnawa gidan Sani wuta don na tsane su, na tsani duk wani wanda ya fi mijina dukiya. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu tunda yanzu da bazar Sani mijina Yusuf ke rawa! Sai dai shima fa Yusuf akwai shegen ma?o da rashin sakin kudi."

Ta Wan dakata tana ri?e ?ugu gaminda jujjuya kai, abubuwa dai na wacce kwakwalwarta ta samu taSuwa. Sai kuma ta ?ara tuntsirewa da dariya har da tafi da shewa sannan ta dora tana nuni da Ummita.

"Wannan yasa na yanke shawara na sanya a sace wadannan shegun yaran don na samu arzikin Yusuf gaba daya yarana su ci moriyarta. Haba! Ya hana su sukuni, yara sai da kudi ai, amma dan banzan rowarsa abinka da wanda ya tsinta a ?asa ya sanya yarana shiga damuwa."

Ta hau juya kai tana buga kan da hannayenta.

"Ni, ni, ni Maryam na tsani damuwar yarana! Sai dai su zauna a keSe a yi ta zagin Yusuf, ni kuma nasan saboda rashin sakar musu dukiya su yi facaka ne sai ka ce gadon ubansa!"

Ta zare ido tana kallon Abban gami da danna masa harara. Shi dai hawaye kawai yake fitarwa hannunsa Waya dafe da kirjinsa dake zafi. Ashe sauran mamaki da tsoratarwa na gaba sadda Mami ta dora daga inda ta tsaya bayan ta je gaban Ummita ta tsaya.

"Ina Waya ba?ar ashanar? Humaira! ?iyar ba?ar annobar Fatima?! Na rantse da Allah na so na kasheta kamar yanda nasa Babandi yiwa Fatima turen aljanu su aikata lahira! Kash! Babandi ka mutu ba a kan lokaci ba? (waiyazubillah), ka mutu ka bar Tasleem da cikinka, ga shi ban mallaki Yusuf ba, ban kashe Humaira ba! Ke kuma Maijidda sai na sanya kin tsani Yusuf fiye da tsanar da na jefa a zuciyar Fatima wanda har ta mutu ba ta son ganinsa. Fiye da tsanar da Humaira ta soma gwadawa wancan la'anannen shegen! Kai Babandi ba ka kyautamin ba!"

Sai ta kurma uban ihu. Baba Amina kuwa salati take yi ga kuka sosai, Futuha da Tasleem su dinma kukan suke yi, sun tabbatar shikenan Maminsu fa ta haukace kuma nata ya ?are don irin wannan taSargazar da ta yi ba zai hana su maka ta gaban kuliya ba. Sai abin da Al?ali ya yanke. Abba dake shirin zubewa suka yi saurin yin kansa har Raihana, aka fita gaba daya inda nan Mami ta yi yun?urin bin bayansu da hauka, wani hankaWa da Anti Maijidda ta yi mata ta kuma Wauke fuskarta da mari hagu da dama ya ba su Futuha mamaki. Futuha ta ji kamar ta sha?o Anti Maijidda, ita dai duk lalacewar uwarta tana son abarta, ita kuwa Tasleem ?arfin kukanta ne ya ?aru, ai koma mene Mamin ce ta ja wa kanta kuma ta jaza musu. Akan idanunsu Anti Maijidda ta rufe Wakin da mukulli ta kuma ri?e mukullin a hannu ta bi bayan su Baba Amina sashin Abba. Nan da nan Raihana ta fiddo waya ta kira lambar likitan Abban, amma bai shiga ba, sai ta kira? Fadeel wanda shi ne ya haWa su da shi don idan irin haka ta tashi ya zo har gida duba Abban.

Fadeel cikin sauri ya kira Likitan Abban, Dr Mansur, bai kuma sanar da Humaira ba amma ya ga dacewar zuwanta duba jikin Abban wannan dalilin ne ya sanya shi dakatar da fitar dda mota daga gate din gidansa da ya yi niyya don har sun yi sallama. Ita kuwa lokacin har ta dauki waya don dama jira take ya fita ta kira Raihana su dora daga inda suka tsaya jiya batun biki da fidda anko. Ganin an bude ?ofar ya sanya ta Wan tsorata ta juyo, ya dube ta da murmushin ya?e kuma a sanyaye.

"Lafiya? Mantuwa ka yi?"

Ta fadi tana binsa da kallon rashin gamsuwa da yanayinsa sai ya yi kokari sosai wurin saita kansa.

"Lafiya Boddo, ji nayi ban kyauta ba har Abba ya yi aure amma ba ki je ba. Oya shirya ki zo muje na kaiki."

Ta ji dadi sosai, sai da ta rungumeshi tana murna da godiya kafin ta sake shi ta yi saurin ficewa zuwa dakinta. Dama ta yi wanka abinta ta shirha cikin atamfa. Mayafi kawai ta dauko sai Woki take wannan yasa koda ta ga Raihana ba ta biyo bayan kiranta ba bai dame ta ba. Shi kuwa Fadeel taimaka mata ya yi da kashe fitilu da sauran kayan wuta na gidan bayan ta fita ya ?ulle suka fice.

***
Alhamdulillah tun ma kafin zuwan Dakta Mansur, Abba ya Wan samu ya dawo hayyacinsa kawai dai sai gumi da ya dinga haWawa akai-akai. Koda Daktan ya iso, ya dai duba shi ya kuma ba shi taimakon da ya dace sannan ya ro?i su kula da abin da zai sosa zuciyarsa daga nan ya tafi. Su na nan jugum-jugum, ba ka jin komai sai sautin kuka da jan majina, ba daga su Anti Maijiddan ba kuma ba ga su Ummita ba musamman ita da take jin wani irin yanayin da ba ta taSa riskar kanta cikinsa ba, inama sadda su Wizzy suka kama su sun kashe ta tun a lokacin ta huta, da ba ta ga wannan ranar ba, da kunnuwanta ba su jiyemata cewa wai Mamin da ta ri?a matsayin uwa ta rayu ?ar?ashin ikonta tsawon shekaru ashirin da Woriya ita ce ta yi sanadin yanke mata farin cikin rayuwa gaban uwa da uba ba.

"Raihana mi?on wayata."

Maganar Abba ta katse tunaninsu. Ba musu ta mi?e jikinta har wani rawa yake yi tsabar tashin hankali da kuma kukan da ta ci, ga muryar Mami dake ihu da kururuwar sai ta kashe su duka ya cika kunnuwansu. Ta dauko saman kujera kusa carbi da kuma hankicif dinsa na shirin fita kasuwa ta mi?a masa. Kai tsaye lambar Ridwan ya kira. Bayan sun gaisa ya ce ya zo gidansa yanzu yana son ganinsa. Koda ya ajiye wayar sai kawai Futuha ta rarrafo gaban Abba cikin kuka ta ce.

"Abba don Allah ka yi hakuri kar ka sa a kama Mami. Ku yafemata wallahi sharrin shaiWan ne."

Abba kallonta kawai ya yi sai ya girgiza kai yana murmushin ya?e. Wato dai Futuha ba za ta taSa yin hankali ba.

"Abba kar ka saurareta, Mami ta cancanci a yi mata kowane kalar hukunci. Abin da ta aikata ba ya bu?atar a yafemata. Da ace ana sauya uwa wallahi yau ni Raihana sai na sauya."

Sai ta ?ara fashewa da kuka mai tsuma zuciya, tausayinta sosai suka ji, Anti Maijidda ta rungumo ta jikinta tana rarrashi nata hawayen na zuba. Shi dai Abba har sannan bai ce uffan ba.

Sallamar Humaira ne ya sanya suka dubi hanyar falon. Dama ita kam kai tsaye Sangaren Abbanta take soma shiga kafin ko'ina tun bayan aurenta. Ganin yanayinsu ya sanya annurin da ta shigo da shi ya Wauke Wif. Ta ji kirjinta na bugu, sai ta shigo falon da sanyayyar gwuiwa, ga dai Abbanta zaune ballantana ta ce ko ciwonsa ne ya tashi. Ta dur?usa a gabansu ta kasa cewa uffan sai dai ta bi wannan da kallo sannan ta koma kan wancan. Sautin muryar Mami da ya karaWe gidan ya shiga kunnuwanta, ihu take tana a bude mata ?ofa sai ta raba kowa da numfashinsa. Anan ta gano inda matsalar take, wato kishin auren da Abban ya yi ne ya ke cin Mami har ta tada hankalin mutan gidan. Amma kuma kai, kamar dai wani abun ne babba ya faru. Yanda ta ga Ummita da Raihana su na kuma sai itama ta ji nata zuciyar ta karye, ba ta son ganin babba yana kuka kawai sai ta shiga nata hawayen.

"Don Allah meyafaru? Meke faruwa da Mami take ihu babu wanda ya je taimakonta?"

Ummita ta girgiza kai.

"Wa zai je? Babu wanda zai je. Humaira Mami ta cuci rayukanmu, ta kashemana iyayenmu saboda son zuciyarta. Mami ce silar mutuwar iyayena a gobara, ta kuma yi silar mutuwar mahaifiyarki."

Sai Humaira ta Wauke wuta, har wani jiri ta ji na son kama ta.

"Wannan wace iriyar banzar magana ce kike yi?"

"Ba maganar banza ba ce Humaira. Dagaske Mami ta aikata."

Fadin Raihana tana sheshssheka. Ita Humaira kasa magana ma ta yi don ?asan mararta har wani irin Waurewa ta yi ta ri?e shi tamau tana salati da girgiza kai, hawayen kawai kwaranya suke yayinda kwakwalwar ke tuna tarin alkhairan da Mami ta nuna mata a farkon zuwanta. Ashe duk na banza ne ita ta kashe uwarta?

Zuwan Ridwan ne ya katse wannan zaman jimami, suka shigo tare da Fadeel wanda ya ke tsaye jikin motarsa yana neman layin Humaira.

Su kansu sun sha jinin jikinsu na yadda suka tarar da mutan gidan, zuwa lokacin Mami ta bar maganganun sun dai ji ta shiru. Fadeel gaba daya hankalinsa na ga matarsa da ke cikin wani hali na tashin hankali, ga dai Abba da alamun sauki a tattare da shi. Sai da aka gaisa sannan Abba ya korawa Ridwan bayanin dukkan laifukan da Mami ta fadi da bakinta ta aikata su. Sun girgiza matu?a. Babu Sata lokaci Ridwan ya yi waya don a zo a tafi da ita bisa umarnin Abba, koda dama ko Abban bai ce a kama ta ba, ya halatta a hukunta a shari'ance. Futuha da Tasleem sai faman kuka za'a tafi da Maminsu. Futuha har da mi?ewa ta yi falon Mami ta kira Mubarak hankali tashe ta sanar da shi dukkan abin da ke faruwa, dama yana shirin tahowa Kanon. Ba ta tsaya anan ba sai da ta kira su Yassar ta ce su dawo gida don Abba ya sa a kama Maminsu a tafi da ita.

Jim kaWan kuwa sai ga jami'an tsaro mata da maza, koda aka buWe tana zaune tana ta surutai ita kaWai sai kuma can ta kwashe da dariya. A kan idanunsu aka sanya mata ankwa ta a fisge-fisge ita dai a bar ta ta kashe Maijidda da Abba da su Humaira haka aka titsa ?eyarta aka tafi. Humaira kuwa wani sabon ciwo da ya murWo mata sai ga ta a dur?ushe a kasa. Da azama Fadeel da ma jama'ar wurin suka yi kanta, kan kace me kuma sai ga jini ya Salle mata. Aka kwashe ta zuwa asibiti, sai dai ina, tuni sun yi asarar cikin da ke jikinta Wan watanni biyu wanda ko Fadeel ba ta kai ga sanarwa ba a cewarta za ta ba shi mamaki ne. Wannan zubewar cikin ya ?ara jefa Fadeel cikin tsananin damuwa, da ace yasan ma tana da cikin ai ba zai ko bari ta zo gidan ba duba jikin Abba ballantana wani abun ya taso. Sai kuma can ya ja istigfari tunawar fa ya yi ba fa ikonsa bane.

Kan ka ce me, labarin kama Hajiya Maryam ya karaWe unguwa da ma wasu mutanen. Alhajin Fadeel da su Ibb da Daddynsa har gida suka zo jajantawa Abba. Hakanan ?an uwan Abba haka aka dinga zuwa masu kuka nayi masu zagin Mami su na yi. Sai ya kasance kamar yanzu ne aka yi rasuwar Jamila da Sani da kuma Fatima.

Kawu takanas Humaira ta kira ta labartamasa komai, haka ya biyo hanya shi da Hajjo zuwa Nijeriya don ya tabbatarwa kansa.

A dai sati da fitar wannan zance, babu inda bai shiga ba. Yanar gizo, kafafen talabijin da gidajen rediyo duka.

Mubarak koda ya zo sai ya tarar da tashin hankali biyu, ga na batun auren Ummita da Ridwan ga kuma na Mami. Yana kuma ji a jikinsa koda babu Ridwan, abinda mahaifiyarsa ta aikata ga Ummita ba ya jin za ta aminta ta auri jininta. Kai shi kam kunya ma yake ji na wannan abin da ya faru.

***
Yankewa Mamin hukunci ya ?i yiwuwa dalilin taSin kwakwalwar da likita ya tabbatar bayan bincike cewa tana da shi, hakanan akantura ta zuwa gidan mahaukata da zummar sai ta warke sannan za'a yanke mata hukunci.

Gidan gaba daya babu dadi, Abba koyaushe cikin hawaye da kuma dana sanin auren Mami. Sai ko Ummita da ta ?i kwantar da nata hankalin kullum cikin kuka. Kasa zaman gidan ma ta yi ita da Raihana suka tattara suka ?ara komawa wajen Baba Amina. Humaira kuwa daga asibiti ma bayan an sallame ta Fadeel gidansa ya yi da ita inda Hajjo ta ke kula da ita da yi mata duk abin da ya dace don jikinta ya dawo daidai gami da kwantarmata da hankali.


Abba sam ya ?i a Waga bikin su Ummita, hakanan aka Waura auren don ma na Raihana ne aka kusan fasawa dalilin ?ananun magana daga dangin Al'ameen inda kai ya rarrabu, mahaifiyarsa da wasu a yayyunsa nata na cewa ba zai auri jinin azzaluma Mami ba, wasu kuwa musamman mahaifinsa sun ce babu gudu ba fashi tunda dai Wiya ce wacce ta samu kyawawan shaidu daga jama'a to shi kam ba zai fasa ba kuma Wansa ya ji ya gani yana so. Haka aka Waura auren ba da son ran mahaifiyarsa ba.

Sati guda kawai suka ?ara a gida sannan suka tare. Baba Amina ta yi iyakar kokarinta wajen gyara su da ma yi musu dukkan abin da ya dace. Ta kuma samu yaran sun Wan dawo nutsuwarsu, hakanan Humaira ma an samu kanta ta fawwalawa Ubangiji komai. Balle kuma da Anti Maijidda ta zama mai Webe masa kewa ko kadan ba ta bari ta bar shi zaune jugum a halin tunani. Tasleem dai Abba ko kallonta ba ya yi, gaba daya ta koma wata abar tausayi, ga Hamza ya zo har gida ya karSi Wiyarsa Aneesa, Abba ko kadan bai hana shi ba sai ma goyamishi baya da ya yi. Wannan ya ?ara sanyawa ta yiwa kanta karatun ta nutsu.

***
BAYAN SHEKARU BAKWAI...

Katafaren falon gidan Alhaji Yusuf Maiagogo cike yake da yara dake faman hayaniya wanda ya cika kunnuwansa har ba ya jin abin da ake faWi a tashar CRTV da ya ?urawa idanu. Shigowar matarsa Hajiya Maijidda ne ya sanya shi saurin yin hamdala a fili bayan ya amsa sallamarta.

"Madallah da ?ar aljanna, kin shigo a daidai, tattara jikokin nan naki su ficemin na ji halin da duniya take ciki."

Ta yi murmushi ta dube su. Ahmed wanda shi ne shugaban sanya su tsalle da ihun Wa ga Ummita, sai ?an biyun Humaira, Fareeda da Fadeela, sai ko Afnan da Yazid ?a?an Raihana da kuma Yusra Wiyar Ummita, su shida amma kamar goma sha shida ne ajiye a falon.

"Ahmed, maza ja tawagarka ku je can ?asa falona ga Innarku Amina ta zo."

Jin haka yaran suka Wunguma da ihunsu da komai wanda ya fi na baya zuwa babban falon Hajiya Maijidda dake ?asa. Idan ka ga gidan na Abba a yanzu ba za ka ce shi ne aka taSa rayuwa a cikinsa can baya ba, babu wani abu da ba'a sauya tsarinsa a ciki ba. Ta karasa ta zauna, daidai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login