Showing 39001 words to 42000 words out of 189325 words

Chapter 14 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

234



"Matsalarsa, ni dai ai ban yaudareshi ba, tun farko kuma na faWamasa ya rabu da ni, ya ficemin a rayuwa amma ya ?i. Aikuwa babu abin da zan ce mishi, ya je can ya ?arata da Tasleem."

Ba su ce uffan ba sai kallon mamaki da suke mata, dagaske dai take ko a jikinta don ba su ga wani Wigon kishi a saman fuskarta ba.

A Sangaren Tasleem kuwa, tana ?arasawa falon ta ci karo da Mami a zaune tana amsa waya. Ganin ta da shirin fita ya sanya ta yi sallama da abokiyar wayar ta dube ta dakyau.

"Ke kuma sai ina haka?"

"Mami ba?o fa nayi, bari na shigo da shi falon saukar ba?i sai na zo."

Ba ta ma kara jin abin da zai fito a bakin Mamin ba ta yi wuf ta fice, Mami ta yi kasake tana duban hanya, fitowar Futuha ya sanya ta maida akalar tambayar a kanta.

"Wannan wane ba?on ta ?ara yi a yanzu ne? Duka-duka yaushe shi Hamzan ya zo da har zai ?ara zuwa?"

TaSe baki Futuha ta yi cike da jin kishin ?ar uwarta ta amsa.

"Uhum, wai fa abokin Ibb ne yake sonta shi ne take wannan rawar jikin."

Wani Wan murmushi Mami ta yi.

"Wato dai ruwan ido ne abin nata kenan? Ya za ta yi da shi wanda ta yiwa iznin zuwa su gaisa da Abbanta?"

"Mami, wannan fa ya fi Hamza kudi da haWuwa, na tabbata abin da ya ruWe ta kenan."

Mamin ba ta ce komai ba face Allah ya kyauta.

***
Yana zaune a cikin motar hankalinsa rankatakaf akan ?aton ?yauren gidan da Tasleem ta yi mishi kwatance, ji yake tamkar ya yi tsuntsuwa ya shiga ya yi ido huWu da abar ?aunarsa, ganin ya kwashi mintuna babu alamar Tasleem sai ya ji gaba Waya ya karaya. Kodai ba gidan ba ne? Waya ya fiddo da niyyar ?ara kiranta sai ya hange ta ta fito daga gidan. Da farko sam bai gane ta ganin tamkar wannan Win shirin fita unguwa ta yi, ga dukkan alamu ma ba gidan ba ne. Amma a hankali tana matsowa ya gane ita ce don haka ya sauke tinted glass din motar wanda ya katange ta daga ganinsa sai waige ta ke.

Tasleem kuwa yana saukewa ta ji numfashinta na barazanae Waukewa ba don tsoro ba sai domin tsananin burgeta da ya yi, ga kuma wani irin kyau da ya yi mata. Shadda ce a jikinsa coffee colour, ya Wora hula a kansa, wannan karon babu gilashi a idanunsa don haka kyawun fuskar ya ?ara bayyana muraran. Ta kasa furta koda harafi har sai da don kansa ya fito daga motar ya rufe. Murmushi mai tsada ya sakar mata.

"Ashe kin iya kwatance."

Ta yi farr da idanu haWi da sakarmasa nata kalar murmushin itama. Cike da yanga da kwarkwasa ta ce.

"Kai kuma kana da basira tunda har ka iya ganewa. Barka da zuwa, bismillah mu shiga daga ciki."

Ba musu ya karSi tayinta, bayan sun gaisa da maigadi dake zaune a benci, tana gaba yana biye da ita yana ?arewa gidan kallo. Hatta da gidan sai da ya ji kaunarsa a zuciya, ya kuma rantse albarkacin masoyiyar tasa ce.? Falon suka shiga ya zauna bayan ta mishi bismillah, sai ?amshi kuwa ke tashi a ciki don dama tunda ya yi mata kiran farko ta ba mai wankin Abba dari biyu akan ya taimaka ya kara share mata a sa turaren wuta.

"Ina zuwa." Ganin ta furta haka tana niyyar ficewa sai bai ce mata uffan ba, ba ya son ya yi garaje da tambayarta Humairar, tunda har ta ce tana zuwa to ya sani ba zai wuce ita za ta rako ba.

Ya lumshe idanunsa kafin ya buWe ya sauke saman hoton Abban dake ma?ale jikin bangon. Ko wani bai faWamasa ba, wannan mahaifin Humaira ne, kamannin ya Saci kwarai. Sai ya ji kaunar Abban ya lulluSeshi, ?auna dai kwatankwacin irin kaunarsa da Alhajinsa. Sallamar Tasleem din karo na biyu ya katse dukkan tunaninsa. Ganinta Wauke da tray na kayan sanyi nan da nan ya Wan Waure fuska, shi fa duk ba wannan ne a gabansa ba. Tana ajiyewa ya ga tana kokarin zama ya karya bille ya ce.

? "Where is she?"

Ta dube shi cikin rashin fahimta, ta yi ?arfin hali ta ce.

"Who?"

Ya dauke kai daga kallonta, ya soma hasaso wani abun, ya gane ita Win manufarta daban, tunaninta ya tafi wani wajen. Mafarkinta daban.

"Wacce na zo domin ta, Humaira."

Kirjin Tasleem ya hau bugu, har ji ta yi ganinta ya Wan dusashe. Miyan bakinta haka ta neme shi ta rasa, dakyar ta tattaro jarumta ta ce.

"Humaira kuma? Dama wajenta ka zo."

Sai a sannan ya dube ta tsakar ido.

"Yes, wurinta na zo. Ko sadda muka haWu dama haka nace wujenki zan zo?"

Tasleem da har ta soma hawaye ta kasa magana, eh bai furta cewa wajenta zai zo ba, amma wane rainin hankali ne ya sa bai nemi kwatance daga Humaira ba sai a wurinta? Ta kuwa daure fuska tamau, ta rantse daga ita har Humairar sai dai su yi biyu babu. Kowa ya rasa don hana ta ce.

"Toh Humaira ban santa ba, asalima a wurin biki muka haWu. Na yi zaton gidanmu kake nufin na kwatanta mana. Don haka babu Humaira a gidannan."

"Ko?" Ya furta idanunsa a saman hoton Abba, itama ta kalli hoton. Ranta ya Saci ainun, ta san kamannin Humaira muraran da ya gani a fuskar Abba ya sanya shi furta hakan. Ta mike tsaye ta? koma gefen Fadeel? ta zauna. Zuwa yanzu ransa ya kai ma?ura wajen Saci amma yana tausar zuciyarsa da tunanin bai dace ba, ta ci alfarmar abin sonsa. Ko babu komai tace masa? mahaifinsu guda. Ita kuwa da muryar kuka ta soma magana.

"Wallahi ina sonka. Tun ganin farko da nayi maka zuciyata ta kamu da begenka. Me za ka yi da Humaira? Da me ta fi ni? Na rantse babu abin da za ta nunamin."

Ya runtse idanu, ransa Saci yake ya na kokarin danneshi, amma jin ana kushe abar sonsa ya bude idanunsa da suka yi jawur tarr a cikin nata. Sai da ta ji rishin kukan ya tsaya na Wan lokaci tsabar fargabar kar ya sha?o ta.

"Ki san kalaman da za ki faWi a kanta. Idan kuma kina son kanki da mutunci, ki yakice ni a ranki. Ki sani kuma ki kara, Humaira ta fiyemin ire-irenki dubu. Kyau da sura ba su ne a gabana ba. Da ace su ne, na bar da yawansu a inda na fito, ba na sonki, ba kuma na son kowa sai ita Win. Idan za ki iya ki shiga ki yimin sallama da ita, idan ba ki iyawa ni zan sa a kira ta."

Da gudu Tasleem ta mike ta yi hanyar fita tana kuka sosai. Fadeel ya mike tsam ya fito farfajiyar gidan inda ya ci karo da Muhsin na wasa da keke. ?arasawa ya yi wurinsa ya Wan durkusa daidai tsawon yaron yana murmushi kamar ba yanzun aka Sata ransa ba.

"Boy, ya sunanka?"

"Muhsin."

Ya jinjina kai, da alama duka sunayen yan gidan su Humaira masu dadi ne, shi kam dadi yake mishi, ya ji ance Futuha, Tasleem yanzu kuma ga Muhsin.

Ganin yaron na shirin janye keken ya sanya shi saurin ri?e keken.

"?an shiga ciki ka ce Humaira ta zo, Fadeel ya iso."

Jin haka Muhsin ya amsa da toh, ya juya kan kekensa bayan Fadeel ya saki ya wuce ciki.

***
A can kuwa, Mami da Futuha na zaune sai gani suka yi? Tasleem ta fado falon a guje, tana? zuwa ta zube cinyar Mamin tana kuka.

"Ke lafiya? Meyafaru?" Cewar Mami cikin Waga murya gaba daya ta ruWe. Wannan ya yi sanadin fitowar su Humaira daga Waki sai a sannan Tasleem ta Wago ta dubi Mami.

"Wai ba ki yake so ba, wajen Humaira ya zo."

Jin haka Futuha ta ji zuciyarta dan yi sanyi, ko ba komai Tasleem ba za ta ?ara hura mata hancin ta yi wanda ya fi Ibb ba kuma ta gane ba Ibb ne masoyin Humairar ba. Amma a gefe kuma kishi da tsanar Humaira ne ya kara mamaye ta, mene ne da ita wanda har namiji irin Fadeel zai gani ya ma?ale mata, su da suke buzaye ma ta kasa shawo kan Ibb ya kaunace ta sai wata can bafulatanar ruga?

Mami kuwa gaba daya fuskarta ta sauya, kafin ta yi magana dai ga Muhsin a guje da kekensa ya shigo falon, yana cin karo da Humaira ya ce.

"Adda Humaira, ki je inji wani a waje."

"Ka je ka ce ba za ta fito ba! Kada ya kara gigin zuwa gidannan!"

Gaba daya suka dubi fuskar? kowannensu dauke da mamaki idan ka cire Humaira da kalaman ya yi mata dadi ainun, haba ta gaji da naci irin na Fadeel, shi bai san ba ta son komai da ya danganci saurayi ba. Meyasa ya ?i fahimta? Ai gwara Mamin ta kora mata shi. A bangaren Raihana da Ummita kuwa tunaninsu daban da nata. Akan me Mami za ta ce Fadeel ya tafi? Wato don ba ya sin Tasleem shikenan kowa ma ya rasa? Tasleem da Futuha kuwa dadi ne ya mamaye su, wato dai uwa uwa ce, ta damu da yaranta. A farko sun yi zaton kwata-kwata Mamin ba ta kaunarsu ta fi kaunar ?an ri?onta musamman ma Humaira. Amma a hukuncin da ta yi abin ya musu dadi, Tasleem ta ji gwara ma kowa ya rasa.

Muhsin kuwa tuni ya fice don cika umarnin Maminsa. Humaira dai ta juya zuwa daki don ci gaba da abin da ya rage na ninkin da take yi, ganin haka Ummita ta bi bayanta, Raihana kuwa da sauri ta bi bayan Muhsin. Futuha na kwala mata kira ta yi mata banza.

***
A can farfajiyar gidan kuwa, Muhsin ne ya karaso har kusa da Fadeel, yana shirin faWin sa?on Mami da sauri Raihana ta kwala mishi kira.

"Kai Muhsin." Suka juya har Fadeel suka dube ta, ta karaso da sauri ta ce.

"Jeka zan faWamasa." Ya kuwa tura kekensa ya ci gaba da zagaye a gidan yana wa?e-wa?ensa da ake musu a boko. Ta gaida shi ya amsa, zuwa yanzu ya karaya da ganin Humaira.

"Suna na Raihana ?anwa ce ga Humaira, don Allah ka yi hakuri ba za ka samu ganinta ba a yau sai dai ko watarana idan an Wan kwana biyu."

Murmushin da bai kai zuci ba ya yi, ta tabbata shi kadai ke kiWa da rawar sa, wacce ya ke ya?in don ita ba ta san yana yi ba, ko kuma ya ce ta sani amma ra'ayinsu ya sha bamban.

"Kar ki damu, ba komai. Idan kin shiga ki ce ina gaishe ta, na kuma cika al?awarin da na daukarwa kaina na zuwa gidansu. Amma hakan ba ya nufin ko a mafarki zan iya fita a rayuwarta. Ina sonta."

Daga nan ya juya ya fice. Raihana ta zuba masa idanu har ya fita daga gate din gidan, tausayi sosai ya ba ta, Humaira dai tana neman cutar da kanta. Samun masoyin gaske irin Fadeel abu ne mai matu?ar wahala. Ta ji haushin Humaira a zuciyarta kamar ta je ta rufe ta da duka. Gwuiwa a sake haka ta juya ta koma ciki.

***
Tun faruwar wannan lamarin Fadeel ya shiga damuwa ainun, yana da tabbacin shi yake so ba a sonsa, ya kuma shirya rungumar wannan jarrabawar ya ya?e shi. A gefe ga mahaifansu da suka soma matsawa akan su fito da matan aure shi da Ibb. Satinsa guda bai kira ta ba balle ya aika mata sa?o, jarrabawa ya yi domin ya ga ko zai iya yakice ta a rai bisa shawarar Ibb amma sai ya ji kamar yanzun ne ma ya soma kaunarta. Ba kuma ya jin zai iya ha?ura da ita. Ya mi?e daga saman gadon da yake kwance wanda tashinsa kenan daga bacci mai cike da mafarkan Humaira, kamar daga sama ya ji ana kwankwasa ?ofar falon, agogon dake ma?ale a bangon Wakin ya kalla, ?arfe goma har ta gota. Ya Wan ja ?aramin tsaki, ya tuna yau suka yi da Alhaji zai soma zuwa kamfaninsa ya kama aiki, jin ?arar kwankwasar yake har cikin kansa dake radadin ciwo, iya sati Waya zuciyarsa ta jigatu da rashin ji ko ganin Humaira, ta ina zai soma fidda ta daga rayuwarsa? Wannan abu ne da ba zai yiwu ba sam. A hankali ya mi?e daga shi sai vest da dogon wando ya fito falon.

"Waye?"

"Ni ce Yaya Fadeel, abin kari na kawomaka."

Guntun tsaki ya ja jin muryar Murja. ?ofar kawai ya bude ya juya ba tare da ya ko kalle ta ba ya ce.

"Ki ajiye ki fice. Na gode."

Ta ji ciwon hakan amma da ta tuno da batun Malam na cewa idan har ya ci abinda ta girka da la?anin da ya ba ta to fa ba makawa hankalinsa zai karkato gare ta. Ya yi mata gargadi akan lallai ta tabbata ya ci, idan kuwa bai ci ba to fa haka za ta kara narka uban kudade a yi mata wani sabon aikin. Don haka sai ta zauna a falon ta ?i bin umarninsa, shi kuwa wanka ya shiga bayan sun yi waya da Alhaji ya buWe mishi wuta akan rashin zuwansa ofis da wuri, hakuri ya dinga? a shi ya ce yana tafe. Suka yi sallama. Koda ya fito wankan a gaggauce ya shirya cikin kananun kaya, dark green din tshirt sai wandon jeans. Ya Waura agogo a tsintsiyar hannunsa, ya gyara sumar kansa. Fitowarsa falon ya ga mutum zaune, nan da nan ya tamke fuska, ita kuwa Murja da rawar jiki ta ce.

"Barka da safiya, bari na haWa maka shayin."

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce.

"No ki bar shi nayi latti, Alhaji na jirana. Ki je da su kawai."

Murja cikinta ya bada sautin kululu, ita dai ta shiga uku, wannan rashin sa'a har ina? Yanzu shikenan ta yi asarar dubu tamanin? Ita kuwa wa za ta je ya ba ta wasu kudaden a ?ara maimaicin aiki?

"Ba kya ji ne?"

Wannan karon ya yi maganar yana ji kamar ya Wauke ta da mari hagu da dama, abu Waya da ya sa yake raga mata bai wuce na tunanin shi Win ma fa haka yake fama da soyayyar wata ba ta sonsa.

Ganin yanayinsa sai ta maida kayan kwandon ta dauka ta fice har da kwallarta. Fadeel yana so ya kashe ta, yanzun ma ji take kamar ta faWa wannan faWaWWan kirjin nasa ya yi mata rumfa da hannuwansa, sai dai kash! Wutsiyar ra?umi ta yi nesa da ?asa. Amma kuma komai nisan jifa ?asa zai faWo kuma sannu sannu ba ta hana zuwa, ta na ji a jikinta watarana ha?anta zai cimma ruwa.

***
Abba ne zaune fuskarsa cike da walwala, babu jimawa iyayen Hamza suka tafi bayan sun nemawa Wansu auren Tasleem kuma ba musu ya amince ya ba su. Tasleem da kanta ta kira Hamza ta ce ya turo saboda bakin cikin abinda Fadeel ya yi mata, ga faWan da suka yi da Futuha me? yi mata dariyar ta rasa shi, ita kuma don ta nunawa Futuha tana da mai sonta dagaske ba irin ita me bin Ibb ba ya sonta ba yasa ta kiran Hamza ta ce matukar dagaske yake toh ya turo a nema mishi aurenta a kwana uku, idan kuwa ya wuce haka to kaunar da yake mata a baki ne. Dama kuma shi abin da yake jira kenan, don haka sai kawai ya ba da kai bori ya hau.

Mami ta shigo itama fuskarta dauke da walwala ta zauna gefen Abba. Kafin ma ta ce wani abu ya riga ta.

"Maryama yau ina cike da farin ciki, ba ni da burin da ya wuce naga na aurar da yarannan mata lafiya kowaccensu ta tare a Wakinta. Ina tsoron sharrin wannan zamani. Ita ma Futuha zan mata magana, ta fito da miji na haWa aurensu baki Waya zai fi min. Karatun can su je su ?arasa a Wakin mazajensu, naji da kannensu masu tasowa."

Mami ta jinjina kai,

"Hakane Abban yara, in sha Allahu itama zamu yi magana da ita naji ko tana da tsayayye. Na san dai wani yaro da ta kwallafa rai a kansa amma shi bai san tana yi ba."

Abba ya Wan yamutse fuska.

"Ai kinji irin shirmen yaran yanzu masu biyewa soyayya, ban da shiririta ke ba manema kika rasa ba, mutane nawa ne suka tare ni akan suna sonki amma ki nacewa wanda ba ya so? Allah ya kyauta, lallai ki ce mata nace ta nutsu ta fiddo miji a haWa aurensu da ?ar uwarta. Kina ji dai iyayen shi Hamza sun ce nan da wata shida suke so a yi komai a ?are."

"Shikenan, zan mata magana." Mami ta amsa a sanyaye, fatanta Allah yasa Futuha ta cire ran da ta kwallafa akan Ibb ta kama wani.

***
? Futuha na zaune tana danne-dannenta a waya kamar koyaushe, bidiyo mai zafi ta Wora tana bin wa?a, ta ci ado a bidiyon har ta gaji, ta yi Waurin ture ka ga tsiya da dankwalinta na leshi, karanta comments kawai take tana jin dadi tana zabga murmushi, wasu kuwa zagi ne da addu'ar nema ma ta shiriya. Irin wannan sai dai ta ja tsaki ta wuce. Ta ci gaba da kallon bidiyoyin jama'a nan ta ci karo da wani bidiyo da ya Waga hankalinta wacce wata Sa'a ?ar snow ta yi a kanta, zagi ne na cin mutunci da sharri, wai Baby Futuha ta tiktok karuwa ce kuma tana da hotunanta da shaidu akan hakan. Tashin hankalin har da hotonta daga ?asa gefen bidiyon. Ba ta san sadda ta kwalla ?ara ba a Wakin bar ya farkar da Humaira me baccin sha biyu. Su biyu ne dama kaWai a Wakin, ita Humaira ma ba ta san Futuhar ta shigo ba domin gaba daya sun fita makaranta, kenan ta dawo ita. Kuka sosai Futuha ke yi hannunta har yana kakkarwa. Humaira ta ji hankalinta ya tashi, duk kuwa da cewar ba sa shiri ta mi?e ta ?arasa gareta.

? "Anti Futuha lafiya?"

Ba ta ko kalleta ba ta wuce da sauri ta yi hanyar fita. Humaira dai na kallon ikon Allah. Toh me ya yi zafi haka? Ta watsar da batunta gami da buga hamma.
Futuha kai tsaye falo ta nufa, babu kowa, cikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login