Showing 117001 words to 120000 words out of 189325 words

Chapter 40 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

208

suka bu?ata su na Wokin su gani.

Ana kammala jeran komai wadanda ba su samu wuri ba aka sanya su a store, bayan fitar masu kawo kaya Humaira ta dubi Raihana.

"Nifa gaskiya binsu zan yi a sauke ni a gida ba zan zauna har ta zo ba."

Ganin haka wuf Raihana ta dauki mayafinta.

"Balle kuma ni, ta ina zan zauna a yi borin nan a gabana? Wallahi ba da ni ba. Mu ba su mu?ulli idan ya so su yi mata waya ta faWi inda za su kai mata ko kuma ai za ta koma tsohon gidan ta yiwa Uwargidanta sallama, kinga sai ta karSa a can."

Murmushi Humaira ta yi, har ta tausayawa Futuha ganin yanda ta ke rawar ?afar shiga gidan da a yanzu ko na Tasleem ya fi shi tsari da wadatuwa. Tana ji koda suka kama hanyar tafiya gida bayan sun bada mu?ulli sai da ta ?ara kiran Raihana ta gama masifar dalilin da yasa ba su jirata a gidan ba salon ace ta shiga babu Wan rakiya kafin ta hau tambayar yanda girman parking space din gidan yake wai ko zai iya cin mota biyu. Raihana ta amsa da ita dai idan ta dawo ta shiga ta ganewa idanunta daga hakanta kashe wayar baki daya. Duk yanda Humaira ta kai ga son ri?e dariyarta sai da ta kufce mata, Raihana ta taya ta.

"Allah kuwa ta ban tausayi kuma ta ban dariya idan na tuna yanda take ta wani jijji da kai da Wora bidiyo wai a taya ta murnar tariya a sabon gidanta."

Humaira cikin faWaWWan murmushi ta amsa.

"Kin ga illar son a sanin da ta ke yi a idanun duniya kenan, yanzu da ace asirinta a rufe yake ba ta sanar da kowa ba shikenan babu mai ji balle gani. Ba ki ji ta ce washegari za ta yi walimar tariya ba har fa abinci kina dai ji a gabanmu ta ba da odarsa tana cewa akwai sabuwar mai abincin da ake yayinta a bukukuwa."

Takaici sosai ya kama Raihana.

"Ai shikenan, sai ta shirya naWe tabarmar kunya da hauka."

Haka suka yi ta hirarsu har suka Sullo gidan Tasleem inda anan za su wuce tare da Jannat wacce ta maida gidan wajen yininta. Wannan karon ba ta zo da yaranta ba saboda makaranta ta bar su can hannun kanwar babansu dake aure a Misra. Gargadin Abba ne bai aminta su kara shiga Wan sahu ba idan har ba wasu kwakkwaran dalilai ba ne da ya yi zafin da sai an nema an shiga. Wannan ya sa suka yanke hakuri da zaman jiran Jannat ta gama ta wuce da su a motarta gudun kar su je Abban ya yi musu faWa. Su kansu tsoron shigar suke yi yanzu musamman Humaira.

Sun zo dab da gidan Tasleem har su na hangowa ne wayar Humaira ta dauki ?ara.

"Idan ita ce please ki ce mata muna abin hawa mun ma yi nisa."

Humaira dai murmushi take don ita abin ma dariya yake? ba ta, gyaWawa Raihana kai kawai ta yi kafin ta fiddo wayar a jaka ta duba. Fadeel ne. Madadin Sacin rai ko ba?in ciki da haushi, sai ta ji ranta ya yi wani irin sanyin da ba ta yi zatonsa ba. Raihana da ta le?a ta ga waye ta kuma ga yanayin dake kwance a fuskar Humaira sai ta ji tamkar da daka tsalle tsabar farin ciki, amma sai ta ?arawa murnar armashi da ambaton sunan Allah gami da yin hamdala.

"To sai ya katse? Ki Wauka mana please."

Ta kuwa amsa sannan ta kara a kunnenta da sallama. Fadeel daga Sarinsa ya amsa. Ji ta yi muryarsa na sanyamata wata irin nutsuwa da sanyin ruhi, ta kasa hasko meke shirin faruwa da ita har sai da maganarsa ta katse tunaninta.

"Boddona, nayi kewarki sosai. Kin ji bawan Allahn nan shiru a waya kwanaki biyu amma ba ki nemi ki san ko lafiya ba ko?"

Sunan Boddona ya sanya ta dan lumshe idanu ta buWe su da wani Wan guntun murmushi a saman leSSanta, Raihana dai kallon ikon Allah kawai take yi tana washe bakin jin dadi na wannan sauyi da aka soma samu daga Humaira.

"Ka yi hakuri, nima ban samu nutsuwar zama ba ne balle har na kira na ji ko lafiya. Fatan komai lafiya? Ya mutanen gidan ya wajen Maman Husna?"

Sai da Fadeel ya yi wani irin dauke wutan da har ta yi tsammanin yankewa wayar ta yi, Raihana ma mutuwar tsaye ta yi domin cak ta tsaya daga tafiyar da suke yi baki a buWe sai kuma ta sa hannu ta rufe. Ganin haka Humaira ta fidda wayar a kunnenta ta kalla, sannan ta Wan juya kadan tana kallon Raihana. Wayar ta maida kunnenta tana murmushin yanayin mamakin fuskar Raihana ta kara magana.

"Ba ka ji ba?"

Wata doguwar ajiyar zuciya ta ji ya sauke da ?ararta sai da ta ji a kunnenta.

"I am with you Boddo, na ji komai. Dukkansu lafiya kalau, nagode sosai da wannan."

Ta yi Wan murmushi ba ta ce uffan ba har suka tsaya cak a ?ofar gidan Tasleem, Raihana sai ba ta kwankwasa ba tana jiran su kammala wayar bayan ta yi mata raWa akan ta taimaka ta sa a loudspeaker don ta ji. Ba musu Humaira ta yi hakan.

"Kin yimin iznin shigowa yau? Kiyi hakuri, ina kewarki a idanuna. Na jure Boddo, amma hakurina na neman gazawa da aski ya zo gaban goshi. Please kin min izni na shigo yau mu gaisa koda na mintuna biyar ne?"

Ta ji wani tausayinsa da ba ta taSa tsintar kanta a ciki ba ya kama ta. Meyasa wai ta ke ba shi wahala har haka? Me ya taSa yi mata don ya ba?anta ranta? Ta ba kanta da kuma zuciyarta da amsar a'a, wato babu shi. Ta Waga kai ta dubi Raihana, da hannu yake ro?onta akan ta ba shi damar. Lumshe idanu ta yi sannan ta amsa.

"Ba damuwa. Ka shigo ka Webi lokacin da ya yi maka sannan ka tafi."

Nan ma Fadeel sai da ya Wauke wuta har ya ba su dariya suka gimtse.

"Kamar a mafarki. Alhamdulillah. Ki yi hakuri da shirun da nake yi Boddo, in sha Allah ana yin Magrib za ki gan ni. Nagode."

"Nima na gode. Allah ya kawo ka lafiya. Sai anjima."

"Ba ki ji ba."

"Me?"

"Ba zan gaji da ce maki ina sonki ba."

Yana fadin haka ya katse kiran. Kalaman sun shige ta kwarai, ta ji ta tamkar an yaye mata kaso tamanin na damuwarta. Ba ta sani ba ko tana son Fadeel ba, amma tana matu?ar tausayinsa idan ma tana tunano wulakancin da ta yi mishi a rayuwa da ma wadanda ba su ji ba su gani ba sai ta ji tamkar ta tsire kanta don Sacin rai. A kwanakin nan dai ta sani tana nadamar abubuwa da dama data aikata a baya, babban tunanin dake cin zuciyarta bai wuce na dalilin aikatawar ba amma ta kasa tuna koda guda Waya.

Dariya da rungumar da Raihana ta kai mata ne ya farkar da ita daga zurfin tunanin da ta faWa.

"Son so yar uwata. Allah ya nunamana aurenku da Yaya Fadeel. Ya sauki yar uwarmu lafiya ya ba ta dukkan farin ciki itama."

Ta kasa amsawa sai dan murmushi kawai, tuna Ummita duk sai jikinta ya yi sanyi a kasan ranta ta ce amin din.

"Malama mu shiga ciki kar mu zama abin kallo."

Tana fadin haka ta ture ta ta yi gaba tana kwankwasa ?ofar itama ta bi bayanta tana dariya. Koda suka shiga da nishaWinsu, tana ji Jannat na hirar Satancin sunan da aka yi musu amma ta yi banza da ita musamman ganin har da rainin hankali a zancen don tana yi tana dariya har da cewa wai wa ya sani ma ko dagaske ne tunda abu a duhu babu wanda ya san gaskiya sai su biyun da abin ya faru da wadanda aka kira da suna kidnappers din. Duk yanda ta shiga da walwala sai da Jannat ta rushe wannan farin cikin, shiyasa ta dinga kaucewa haduwarsu tun da aka ce ta zo amma yau gashinan zamansu inuwa guda ya janyo tana gasa mata zantuka marasa kan gado. Haka ta kai zuciyarta nesa ta danne. Tana ji su na hirar gidan Futuha inda Raihana ke ta labarta musu yanayin gidan, Tasleem me za ta yi ban da dariya? Ta dinga kyakyacewa son ranta har sai da Jannat ta yi mata magana. Raihana kuwa duk yanda ta kai da yiwa Futuha dariyar gidan sai da ta ji haushin farin cikin da Tasleem ta hau yi har da ambaton Allah ya ?ara. Jannat ba ita ta tashi tafiya ba sai dab da magriba, Humaira da Raihana har suka gaji ga tunanin Fadeel da zai zo bayan Magriba. Tu?in ma yinsa ta dinga yi da gadara da yanga kamar ba ta so sai ka ce ta san da zuwan Fadeel din amma ko kusa ba su sanar mata ba. Don kanta kuma daga baya ta ware hannun sitiyari ta shiga gudu har suka isa gidan. A gurguje Raihana ta sanya Humaira shiryawa. Ummita na daga kwance tana kallonsu sai murmushi kaWan a fatar bakinta. Inda ta ga da bu?atar gyara za ta yi magana. Duk da halin da take ciki ta yi farin ciki kwarai da wannan sauyi na Humaira akan al'amarin Fadeel.
Humaira ta kammala shiri cikin wani rantsetsan yadinta mai adon maroon da yellow ta yi kyau sosai musamman da ta yafa mayafi yellow sai tashin ?amshi take yi. Raihana ta so ta yi mata kwalliya amma ta nuna ba ta ra'ayi, ita duk kaffa kaffar da take yi kada ta motsawa Ummita wani lamarin akan Sahabi, ba ta san cewa Ummita kwarai take jin dadin yanda ta sauya ba.

"Masha Allah kin yi kyau sosai."

Fadin Ummita tana dubanta. Ta maida mata martanin murmushin amma ba ta ce uffan ba can kuma ta dubi Raihana.

"Kinga ban sanar da Mami ba, na rasa ta yanda zan faWamata."

Cikin basarwa Raihana ta ce.

"Kar ki wani damu, tana wajen Abba, ke idan ma ta tambaya zan fadamata."

"Toh." Shi ne kawai amsar Humaira ta ba.

***
Wannan karon madadin ta gan shi tsaye a farfajiyar gidan, sai ta same shi a Wakin saukar ba?i na Abba. Ashe Mubarak ne ya kai shi can, shi suka yi karo ya sanar mata inda yake. A kunyace ta sunkuyar da kai ta nufi Wakin kai tsaye.
Da sallamarta ta sanya kai ciki bayan ya amsa. Suka Wan dubi juna ta kauda kanta, ya sha adonsa cikin yadinsa mai tsada fari ?al ga kuma hula ya Wora wanda ya yi matu?ar hawa da kayansa. Kallonta kawai yake yi ba ?aramin kyau ta yi mishi ba. Ta ?araso ta nemi wuri ta zauna can nesa da shi kaWan tana gaishe shi. Ya amsa mata zuciyarsa tamkar ?an?ara. Sai kuma ya rasa ta inda zai fara, sai ya ji kamar an Waure mishi bakin saboda tsabar shau?i, ita kuwa ta baza kunnuwanta don son ta ji me zai ce. Can ta tsinkayi muryarsa a tausashe.

"Kin yi kyau."

Ta kasa cewa komai sai murmushin da ta Wan yi. Jin lamarin ta ke banbarakwai, wai ita ce ke yin zance. Abin dai kamar a mafarki.

"Boddo." Ya kira sunan da take matukar jin dadinsa amma koda wasa ba ta taSa gwada mishi ba. Sai da ya ?ara maimaicin kira kafin ta amsa a hankali. Fadeel ya yi hamdala a ransa, tabbas babu wani abu mai girman da ya fi ?arfin addu'a. Komai idan ka sanya Allah ciki kuma ka dage da addu'a to fa zai zo ya zama tarihi. Hakan kuma yake fata, wannan ?iyayyar ta Humaira gareshi ta koma tamkar ba ta taSa yinta ba.

"Nasan za ki ce Fadeel ya fiye naci da takura. Kiyi hakuri, haka Allah ya yi ni, ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
yadda ban iya ?in abu ba haka nake idan na so ba, ba na mishi son da nake jin zan iya ha?ura da shi yau, gobe ko jibi. Kina daga cikin abu mafi girma da tsada da na taSa samu a rayuwa, a zatonki zan bari ki suSucemin?"

Ta kasa tankawa, jikinta ya yi la'asar, sai ta ji ya yi matu?ar ba ta tausayi kwarai har ta Wago idanu kaWan ta dube shi, kwayoyin idanunsu suka sar?e, ya harWe tafukan hannuwansa guri guda ya tallafa haSansa gami da Wan karkata kai kawai yana dubanta. Ta janye ?wayoyin idanunta gami da sadda kai tana wasa da zoben azurfar yatsarta. So ta ke ta ce ka yi hakuri Fadeel, na sani ban kyautata maka ba ka yafemin. Amma ta ji ta kasa, da wane idanun ma za ta dube shi har ta iya bayan shafi-shafin rashin mutuncin da ta sauke a kansa.

"Aa Boddona, in sha Allahu sai mun kasance a inuwar aure. Sai kin zama mallakina nan ma ba da jimawa ba."

Ya ?arashe zancen da murya ?asa-?asa. Abin mamaki idanunsa a saman fuskarta, ko kallonsa ba ta yi ba balle ya tsammaci kallon hararar da ya riga ya yi sabo a shi. Wannan sauyin da take yi sai ya ji zuciyarsa n kasa Wauka, ba kuma wai rashin aminci da shi ba. Ko kusa, sai dai kawai ya kasa sakin jiki yana ganin kamar na Wan lokaci ne. Duk da haka yana kokarin tunasar da kansa cewa addu'a ce ta kai su ga wannan munzalin ba kuma ya tunanin akwai abin da zai sauke su a kanta. Ya mi?e ya Wan matso kujerar da take kai ya zauna, tana can ?arshe kujerar kasancewar mai zaman mutum uku ce, shi kuwa yana gefe ya ba da tazara tsakaninsu. Magana mai muhimmancin da ya kasa sanar da ita ne ya ke ganin ya dace ta sani yanzu. Kirjinsa na bugu saboda fargabar kada ta tada bori kan tsarin bai mata ba. Amma da ya ambaci sunan Allah sai ya samu ?warin gwuiwa don haka ya karya bille ya soma magana.

"Humaira, iyayenmu sun yi magana sun kuma tsayar da ranar aurenmu."

Ta ji tsi?ar jikinta ya tashi, ita da aure? Babu wani yanayi da ta ji da ya wuce na sanyin jiki kamar wacce aka yi wa duka. Har wani zufa ne ya yankomata, sai ta shiga maimaita sunan Allah a ?asan ranta.
Shirunta ya haifarwa da Fadeel wata irin fargaba har sai da ya ji inama bai ce uffan a kai ba. Har ya fidda ran za ta tanka sai ta ?aryata tunaninsa ta hanyar magana tana dubansa fuskarta na nuni da damuwa.

"Amma ta ya ya zan yi aure na bar Ummita cikin wannan halin?"

Ya sauke ajiyar zuciya jin abin da ta ce, cikin ?arfafa gwuiwa ya ce.

"Kar ki damu Boddo, idan har wata Wayan da su Abba suka sanya ya cika, matu?ar aka Waura babu wanda zai takuraki da zancen tariya har sai lokacin da kika aminta don kanki. Hakan ya yi maki?"

Ga mamakinsa sai ta gyaWa kai da Wan murmushi kaWan a fatar bakinta. Ai sai ya ji inama yana da damar haWa jikinsa da nata. Hakan ma da ta aminta da aurennasa ya yi mishi sosai, muddin dai ta zama mallakinsa to sauran duka mai sauki ne. Hakan ya ayyana a ransa. Bai ja ta da hira ba gudun kada kuma a zancen ta yi wani tunanin ta sauya ra'ayi don haka ya zaSi su yi sallama a wannan gaSar, yana da tambayoyin da zai so ace ya yi mata na dalilin ?in shigar ta makaranta ta zaSi girki da ma dai son jin duk wani abu da ya shafe ta amma ba ya son kwaSarsa ta yi ruwa sai ya haWiye kwaWayinsa ta hanyar yi mata sallama ya mi?e, itama ta mi?e suka fito tare ta ja ?ofar ta rufe. Hannuwansa cikin aljihu ya ke dubanta kamar ya haWiye.

"Sai mun yi waya. A gaidamin yan uwana."

Ta gyada kai. Har ta soma tafiya sai ta juyo, yana tsaye cak kawai yana kallonta da shanyayyun idanunsa so na fisgarsa. Ta Wan kauda kai daga dubansa ta ce.

"A gaidamin su Baba, idan kun yi waya da Maman Husna ace ina gaida ta."

"Ko na turo maki lambarta? Sa?onnin sun min yawa kada na manta."

Ta Wan murmusa.

"Shikenan sai ka turo."

Ta juya za ta tafi ya dakatar da ita.

"Boddo."

Tsayawa ta yi ta juyo, murmushinsa ya yi har gefen kumatunsa na lotsawa.

"Ina ji da ke."

Ta yi saurin juyawa ta nufi ciki, sai da ya ga shigewarta kafin ya fice zuwa inda ya adana motarsa yana shafar sumar kansa duniyar na mishi dadi.

***
Mami kuwa ta cika ta yi fam, abu biyu ne suka haWe mata, ga hotunan gidan da Futuha ta aikomata da kuma wayar da suka yi tana rusa uban ihun kuka tana cewa gida za ta taho yanzun a daren, ga kuma labarin auren Humaira da Fadeel da take ji a wurin Abba sai aka yi katari a ranar kuma Humaira ta fita hira wajensa. Wannan ranar ta fi kowacce ba?in ciki a wajenta. Suna falo zaune har Anna da ta fito saboda tashin hankalin akurkin gidan da ta ga Futuha ta koma da kuma batun yajin da ta dako har ana batun tana hanyar dawowa gida, sai yare suke bugawa a falon Jannat tana yi itama Annar na yi, Raihana da su Mubarak dai sai tausarsu suke yi inda Mubarak ya dage akan lallai idan Futuha ta tako yau sai ta juya ta koma gidanta acewarsa ba za ta tayarwa Abba hankali ba ga shi yana fama da hawan jini. Anna kuwa ta dage lallai sai Futuha ta dawo gidan tunda ba haka aka yi da Yakubun ba, a wannan yanayin Humaira ta shigo falon fuskarta dauke da murmushi sai baza uban ?amshi take yi mai sanyi. Ganin yanayin mutan gida sai da ta ji dam saboda ta yi zaton ko wani abun ne ya kuma faruwa. Idanunsu a kanta, ga Anna da Jannat harara ne, Mami kuwa ba za ka tantance ba sai dai fa fuskar a haWe take tamau. Humaira ta dake ta ?arasa ta gaida Anna. Ba ta ko kalle ta ba balle ta amsa, ganin haka ta mike za ta nufi Waki Mami ta yi mata tsawar da kowa a falon sai da ya dube ta.

"Ke! Da iznin uban wa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login