Showing 57001 words to 60000 words out of 189325 words

Chapter 20 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

242

a yanzun suke Wan gaisawa sama-sama.

"Na ji Abba, ina neman gafararka, zan samu Mami na ba ta hakuri. Na kuna yi alkawarin ba zan kara ba"

Murmushi Abban ya yi.

"Masha Allahu, ko ke fa. Maza tashi ki je wajen Mamin taki."

Itama Wan murmushin ta yi kafin ta mi?e ta bar falon. Kai tsaye Wakin Mami ta nufa, sallama ta yi aka amsa sannan ta faWa. Mami dake zaune gefen gado ta yi shiru ta Wago ta dube ta sai kuma ta sunkuyar da kai. Gaban Humaira ya faWi, tabbas Mami kuka ta yi, idanunta sun tasa sun kumbura. Sai ta ji nata hawaye sun dawo sabbi, ta durkusa gami da Wan dafa gefen gadon. Dakyar ta iya tattaro jarumta ta ce.

"Ma..Mami nayi kuskure, nayi babban laifi. Ki yafemin, ki yi hakuri. Maganganun ne suka yimin nauyi, zuciya ta kwasheni na aikata haka."

Sai ta kasa kara wani abin a kai, ta yi shiru. Mami ta kalleta ta Wan yi wani murmushi mai kama da ya?e.

"Tabbas kin aikata babban laifi Humaira, kar ki damu, abinda ya faru ya riga da ya afku. Ni na sani, matsalar ni za ta shafa yanzu. Uwa ce ya zama wajibi ga duk mai neman dacewa da rahmar Allah ya bi ta sau da ?afa, ba zan iya sauya tsanarki a zuciyarta ba kamar yanda ba zan iya jure ?iyayyar da ake nunawa jinin Fatima ba don a duniya da ace za'a samu abokiyar zama ta gari irin mahaifiyarki, shakka babu da an zauna lafiya. ?ar uwata kuwa, ni da ita mu biyu kaWai Allah ya mallakawa Anna, zan iya cewa ?auna da soyayyar da Anna ke yiwa Jannat ya ninka nawa son a wurinta. Da ace tana da damar zama tare da ita, da tuni yanzu ba ta tare da ni sai ita. Hakuri nake yi ina takatsantsan da abin da zai haWani faWa da Jannat sabida na sani Sacin ran Anna kawai zan fuskanta. A wasu lokutan har nakan yi tunanin Anna ba ta sona kwata-kwata, sai dai son da naga tana yiwa jikokinta ya shafe zargina. A hankali kuma na ke gudun zuciyarta, amma faruwar wannan lamarin, Anna ta yimin maganganu masu zafi wanda ba sani bakinta halaka ce gareni. Har cewa ta yi ba zan gama da duniya lafiya ba. Wannan shi ne dalilin kukana. Na san kema mutum ce mai zuciya a kirji, yau da gobe ana maka abu wataran dama dole a kai ka ma?ura. Ina da ya?inin hakan ce ta kasance yau, amma ina mai baki hakuri a madadinsu."

Humaira wacce ta gama narkewa sosai a tausayin Mami, ta yi saurin girgiza kai ta ri?o hannuwanta, cikin muryar kuka ta ce.

"Mami ki daina faWin haka. In sha Allahu bakin Anna ba zai kama ki ba saboda mu ma shaida ne akan iyakar biyayyar da kike mata, ni nayi laifi Mami, ni ce mai bada hakuri ba ke ba. Na kuma yi maki alkawarin jure dukkan wani abu daga Anna da Anti Jannat albarkacinki. In sha Allahu hakan ba za ta sake afkuwa ba. Ki yafemin, ina jin kunyarki."

Murmushi Mamin ta yi.

"Kar ki damu, ya wuce. Share hawayenki, kukan ya isa. Allah ya sa mu dace."

Humaira ta share fuska bisa umarnin Mamin tana mai amsawa da amin. Itama Mamin ta sauya darasin da yin batun odar da aka ba Humairar. Ita sai a sannan ma ta tuna da wata oda, nan fa ta kara yiwa Mami bayanin matar da ta kirata.

"Toh kinga kuwa zama bai ganki ba, anjima ki zo muyi lissafin komai, idan ya so sai mu ga nawa ya kama sai a sanar da ita ko?"

Zuciyar Humaira tas ta gyaWa kai tana murmushi. Daga nan ta mi?e ta fita, Mami ta bita da kallo har ta fice.

? Raihana ta fahimci Humaira sai dai ta Wan nuna rashin jin dadin marin Anti Jannat a fili, ta dai Wan basar da Humaira na lokaci sai kuma aka shirya suka Winke. Su Futuha kuwa ta rasa? me ya hana su yi mata maganar sai dai kallon banza kawai da suke watsa mata a duk sadda aka yi katari suka haWa ido. Ummita dama ba ta da matsala, wata iriyar yarinya ce mai sanyi da hakuri, ta nunawa Humaira kawai bata kyauta ba da har ta bari zuciya ta kwashe ta suka kasa cin albarkacin Mami. Koda ta fadi haka da toh kawai ta bita, ita kanta ta sani Ummita ta juri abubuwa da yawa wanda ko rabinsa ba za ta jure ba. Ta taso tun bata san mene ne ma'anar hankali ba, ta rayu cikin duka da zagin Jannat, ga Anna a gefe wacce a baya Ummitan ke bala'in tsoro kamar mutuwa. A wurin Mamin kaWai take samun sa'ida, su Yassar ba su wani damu da zamanta ba tunda tun kafin ta gama mallakar hankalin kanta take basu girma. Komai suka ce ta yi ba ta ?i, koda kuwa ya fi ?arfinta haka za ka jagula. Ummita ta ci wahala ta kuma yi hakuri ta jajirce, wannan ne ya sa har gobe ?an uwan Mamanta na Bichi ba su taSa kaunar zamanta a gidan ba.

***
? Mami da Humaira sun lissafa komai yadda ya kamata, hatta da ribar sai da suka fitar sannan ta tura acc number din Mamin ga Hajiya Rukayya tunda ita Win ba ta da account kamar yanda Mamin ta ce. Aikuwa ko mintuna biyar ba'a yi ba sai ga shi ta aiko kudin. Wannan abu ya yi musu dadi, washegari kuwa da wuri ta fice siyayya ita Waya, sauran sun tafi makaranta.
? Koda ta dawo da kaya ni?i-ni?i ga uban rana a garin haka Wan sahu ya dinga tayata sauke ledoji. Ta kinkima zuwa ciki. A falo ta yi karo da Jannat za ta fita tare da yaranta, dama ta ga an wanke motarta tas yana she?i, tun faruwar lamarin sai a ranar suka haWu, ta gaida ta amma ko kallon arziki ba ta samu ba sai giftawa da ta yi ta fice yaranta na biye da ita. Humaira ta yi mamaki don ta yi tsammanin da duka za ta rufe ta ma duk ranar da suka yi karo. Ba ta wani tsawaita tunanin ba ta maida hankali ga kayanta. Mami ta fito ta dinga yabon siyayyar. Bayan ta watsa ruwa ta sauya kaya zuwa tshirt da zani sannan ta fito zaman aiki. Sai wani nishaWi take yi, ita da Ladidi ne suka soma, bayan dawowar su Ummita, ita ma ta shiga su ke yi tare.
? Aikin da aka ba Humaira kwanaki biyar sau gashinan a kwanaki uku an kammala komai an haWa. Hajiya Rukayya ta sha mamaki da ta tsinci wayar Humaira cewa an gama don babu laifi da Wan yawa snacks din. Ta yi godiya ta kuma nemi kwatancen gidan acewarta za ta turo direbanta a karSa, nan Ummita ta karSi waya ta kwatanta mata. Awanni bai fi uku ba sai ga direban ya karSa ya tafi. Humaira ta dawo ciki bakinta ya ?i rufuwa tsabar murna. Futuha ganin yanda take washe ha?ora yasa ta jan tsaki.

? "Sana'a ba ilimi shirme kenan, mu dai mun yi gaba mun bar mutum, hakanan zamu kammala karatu mu zama manyan ma'aikata muna daga sama? kujera muna juya kowa. Ai Tasleem nan gaba wasu na da kallo."

Tasleem ta tuntsire da dariya. Humaira kuwa hijabinta take ninkewa da ta sanya ta fita waje ba tare da ta ce musu uffan ba, a yanda take jin zuciyarta cike da walwala ba ta jin cewa za ta biye musu su Sata mata rai a banza. Raihana ce ta yi caraf ta sanya musu baki kuwa.

"Tab, ai? wallahi yanzu a zamanin nan dai babu abin alfahari kamar sana'a, ita fa mace mai sana'a ta huce takaici. Ba ruwanta da jiran sai an bata ko kuma an yi mata, kawai gani za'a yi a jikinta tana fitowa Was abinta. Muna nan daku in sha Allahu Humaira sai ta zama abin kwatance, wacce ko mai Masters ba zai nunamata arziki ba. A wannan lokacin kuWi kawai, ilimi ba a taSa yin latti da nemansa, ballantana ma me zai damu mutumin da yake neman ilimin Muhammadiyya. Ai shi ne ma?urar ilimi, sauran duka bogi ne."

Jin haka ai sai Futuha ta harzu?o ta kai wa Raihana bugu, Raihana? ta kauce.

"Shegiya kai! Na sa da ke? Ko kin ji na ambaci sunan wata? Da ke nake magana ko Tasleem, iskanci kawai. Ina magana kina sanyamin baki duka zan maki a gidannan. Kin wani raina mu sai kace sa'o'inki. Kema watarana idan ba mu yi dagaske ba sha?e mu za ki yi tunda ai zama da maWaukin kanwa shi ke kawo farin kai."

Ta karashe tana? watsawa Humaira wani banzan kallo ita kuwa ta kauda kai tana murmushi. Aikin banza, idan rashin kunya ne na nawa kuma suna gwada yiwa har Mamin balle a junansu, babu kamar Futuha da yanzun kanta ke bala'in rawa ana lallaSa ta, hatta da Mami kamar ma tsoron sanya Futuhar aiki take yi a yanda ta lura, ba ta sani ba ko don Alhajinta mai hidima ne ko kuwa dai kawai saboda ta kusa aure ne. Tasleem dama ba koyaushe take wuni a gidan ba, saboda zuwa asibiti.

Ba ta kara bi ta kace-nace da suke yi da Raihana ba ta Wauki takarda da bironta ta koma wurin Ummita wacce itama a yanzu ke kokarin koyamata wasu kalaman na boko irin na yau da kullum da take ji ana Wan faWi. Sosai kanta yana Wauka.

***
Ya lumshe idanu yana taunar samosa,? har ya kammala bai iya ya buWe ba, sai can ya buWe gami da kai hannu zai ?ara, caraf Ibb ya ri?e tsintsiyar hannun yana dariya.

"Wai kai na tambayeka, ni da na zo wurinka, ni ka kawowa na ci ko kuwa dai kanka? Tun dazu ka kawomin abu amma ka zage sai ci kake, oh don ban ce a bani nawa kason ba tunda dai a gabana aka ?ulla kasuwancin?"

Fadeel ya harareshi.

"Ban da wanda Anti ta cemin ka ci a can? Wannan kuma ni da kai na kawo wa, idan za ka ci ka ci, ka biyemin kaf zan tashi da shi."

Ibb ya saki hannunsa yana murmushin wannan irin kauna. Shi kuwa bai ko kalleshi ba ya cigaba da kai girkin Humaira bakinsa. Can a gajiye ya dubi Ibb.

"Yarinyarnan tana son kashe ni da raina."

Ya kalle shi da kyau kawai ya ji ya ba shi tausayi. A sanyaye yace.

"Meyasa za ka yarda da hukuncinta? Fadeel ka wartsake daga baccin da kake, sorry to say, amma yarinyarnan ba ta sonka. Idan kuma ba za ka hakura ka cire ta a zuciya ba, toh ka yarda mu samu su Alhaji a je nema maka aurenta."

Fadeel ya girgiza kai yana jin ciwo a kirjinsa idan ya tuna wai Humaira ba ta sonsa.

"No, ba zan taSa yi mata dole ba, amma zan Waukar maka al?awari Waya."

"Mene ne shi?" Ibb ya faWi cike da za?uwa.

"Muddin lokacin da ta ban sun cika, zan sanar da Alhaji a neman aurenta. Idan kuma ba ta amince da ni ba, zan ha?ura da ita saboda ta samu nutsuwar zuci."

Ibb ya sauke ajiyar zuciya, shi fa sam ba haka ya so ji ba. So ya yi aminin ya furta kalmar rabuwa wanda ya sani sai dai ya yaudari kansa, ba mai yiwuwa ba ne. Yana kuma ji a ransa, muddin Fadeel ya yi dakon shekara, toh shakka babu ba abinda zai sa ya iya hakuri da rashin Humaira. Amma sai ya bar komai a ransa.

"Shikenan, Allah ya yi maka zaSi nagari."

"Ameen." Ya amsa shi ma.

"Ba za ka ci ba ne?" Cewar Fadeel wanda zuwa lokacin cikinsa ya ?oshi amma bakinsa na son WanWanon don haka ya ha?ura ya Wau gorar ruwa. Harararsa Ibb ya yi.

"Oh, bayan ka cinye kenan ko?"

Murmushi Fadeel ya yi ya cigaba da kora ruwa a cikinsa ba tare da ya tanka ba.

***
BAYAN WATANNI BIYAR
Gidan Alhaji Yusuf wanda aka fi sani da Maiagogo sun wayi gari ranar alhamis da shirye-shiryen bikin yaransa biyu, Futuhatul-Khair Yusuf da kuma Tasleem Yusuf wanda kwanaki uku kawai ya rage a fara. An samu sauye-sauye da dama, na farin cikin ya fi kowanne yawa ga Humaira da duk ma wanda ke tare da ita. A wannan watannin ta samu alheri mai yawa daga sana'arta. Babbar customer dinta ita ce Hajiya Rukayya wacce ta hanyarta kaWai ma ta samu oda na biki da party har ya zamana tana gwada na abinci bayan snacks sai dai gaba Waya sau biyu ta gwada abincin taro ba laifi kuma masu shi sun yaba hakanan Hajiya Rukayya ta ji dadi da ba ta ba su kunya ba. Duk abin nan ba su taSa ganin juna da ita ba sai dai waya. Mami ta sa an buga leda da stickers mai tambarin DEELSHA'S DELICACIES. Suna na musamman da Raihana da Ummita suka ba Humaira a sadda Mamin ta ce ta yi tunanin sunan da za'a sanya a ledar. Sunan ya yiwa Humaira daWi ko kadan kuma ba ta tambayesu ma'anarsa ba. Mamin ma ta ji dadin sunan, ganin kalmar turancin ya sa ta tambayar wacce ta sa, nan Humaira ta sanar da ita su Ummita ne. Daga haka ba ta kara cewa komai a kai ba.

? A yau da ya rage kwanaki uku bikin yan matan Mamin, gidan nasu ya soma karSar ba?i ?an uwan Mami daga Agadez sai ko ?awayen Futuha waWanda suka zo daga nesa kasancewarta mai jama'a fiye da Tasleem. Yan uwan Abba kuwa ba wanda ya zo gidan da zummar kwana. Mubarak shima ya zo gari, sai kuwa Anti Jannat. Ya kasance a wannan lokacin gidan ba ya rabo da jama'a, Mami ta sa Ladidi kawo mataimaka a aiki har su uku saboda yanayin cikar gidan da zummar bayan biki za ta sallame su.
? Anko har kala biyar aka fitar, na ?awaye daban wanda zasu sanya ranar kamu da na daurin aure da yini sai ko na ranar dinnerparty. Na manya su ma kala biyu, na fita kamu sai na ranar daurin aure.

Humaira, Raihana da Ummita daban aka fitar musu da na sisters wanda zasu saka na yini sai kuma na dinnerparty da Mami ta yiwa su Futuha jan ido ta karSar musu katinsu ta ri?e a wajenta don a farko sun nuna su ko kusa ba su kaunar su halarci dinner din.

?? Amare sun sha gyara ba na wasa ba daga mai gyaran jiki na musamman da Mami ta samar musu suke sintirin zuwa. Hajiya Lubna ita da kanta ta Wauki nauyin gyara su, gyara irin na mata. Ta kashe kuWaWe masu kauri kuwa wanda hakan ya burge aminiyarta kwarai ta yaba.? Ba ma ita Waya ba, ?awayen Mami da dama manyan mata masu kudi sun ba da gudunmuwa mai yawa na kudi, kanta ya fasu sosai ta kuna ga fa'idar mu'amala da masu hannu da shuni.
Su Raihana sun karSi dinkunansu a hannu, sun yo ?unshi da kitso abinsu sun fito fes.
?? A na washegari kamu ne su na zaune suna hira a daki tare da wasu yan uwan su Raihana sa'anninsu da suka zo daga Nijar, Tasleem ta shigo. Fatarta har wani Waukar ido yake, ba ta da ?iba irin na Futuha ita nata jikin daidai misali ne, duban Humaira ta yi fuska ba fara'a.

"Ke Humaira, ke da Ummita ku zo na aike ku."

Humaira ta ji ciwon ke din da tayi kiranta da shi, ita kuwa Ummita ko a jikinta ta mi?e tana murmushi. Hakanan halittarta yake, tana da yawan murmushi, abinda zai sanya hawayenta zuba kuwa, toh fa ba ?aramin abu ba ne kamar dai akan Humaira ko kuwa wani abun daban. Kamar ba za ta mi?e ba sai kuma ta yi tunanin ba komai ta yi tunda dai aure ma za su yi su bar gidan sai ziyara don haka ta taushi zuciyarta ta mi?e itama. Sa?o ta ba su a leda na ankon Dinner su je su kai can asibitin Malam wajen ?awayenta kuma abokan karatunta da suka samu dakyar don har ta ?are. Ta mi?awa Ummita dubu su yi kuWin mota sai kuma lambar wayar Waya daga ciki, Sadiya, sun gane ta, takan rako Tasleem din gida wasu lokutan don ta dauki wani abun ko kuma ta zo takanas ziyara.
?? Bayan sun fito waje Humaira ta dubi sararin samaniya yanda garin ya haWu da hadari ana cida, lokacin uku da mintoci, ta ja guntun tsakin takaici.
?
"Kinsan Allah, sa'ar da ta ci kawai na ganin wannan shi ne aike kusan na karshe da za ta yi mana kafin ta bar gidannan shiyasa kawai zan je, amma ban da haka wannan ke Win da ta ce wallahi da babu inda zan je matukar ba Mami ce ta sa baki ba."

Ummita dake kokarin cusa ?aramar lema a jaka ta Wago tana murmushi.

"Humaira ko rigima, rabu da ita lokaci ne ai wataran sai labari fa. Yanzu kalli, ina Anti Jannat? Ba ta yi aure ba sai dai ta zo kawai ziyara ta tafi? Toh su din ma hakan ce za ta kasance, mu ma watarana sai ki ga mun yi namu auren mun tafi mun bar gidan. Sai a dade ma kafin a ganmu."

Tsaki Humaira ta ?ara ja.

"Ke dai Ummita kina son aure na lura, magana kaWan za a yi da ke sai kin yi zancensa."

Da mamaki Ummitan ta kalleta kafin ta amsa.

"Aure ai abin so ne saboda sunnar ma'aiki (s.a.w) ne. Ke din ma ba sunnar kika tsana ba, mazan ne. Ban kuma san laifi kwakkwara da suka yi gareki ba."

TaSe baki Humaira ta yi daidai lokacin da suka fito babban titi.

"Mu bar wannan magana, nikam ba kya ganin lamarin Anti Jannat da Waure kai?"

Ummita ta yi shiru cikin nazari, tabbas da daure kai, tun bayan sadda ta zo hutun sallah lamarin nan ya afkuwa tsakaninta da ita, ba ta kara dawowa gidan ba sai yanzu. Wannan dawowar kuwa, daidai da kallon Humaira ba ta yi balle har ta jefe ta da kallon banza. Ta lura ko tana wuri Humaira ta shiga, mikewa take ta bar wurin. Haka dai tana ta kaucewa abinda zai haWa su a inuwa guda.Har Humaira ta tarar musu abin hawa suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login