Showing 150001 words to 153000 words out of 189325 words

Chapter 51 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

227

ta sa kai ta bar falon tana jin Mami na bambamin faWan wai Abban ya nuna dagaske ba ita ta haifi Humaira ba kuma ba ta ita ta ce mata ta yi, ta yi din ba. Ita dai ta fice da sauri tana share fuskarta.

Abba ya dubi Mami dakyau, kamar zai ce wani abu sai kuma ganin Raihana a wurin. Juyawa ya yi zuwa bangarensa can din ma bin bayansa ta yi.

"Diyarka ta dawo gida saboda maci amanan mijinta zai auri abokiyar faWanta. Nima kuma ina goyon bayanta don ban ga wani dalilin da zai sa ya yi mata wannan tozarcin ba a idon duniya."

Cikin al'ajabin wannan sabon labari da ma rashin fahimtar inda aka dosa Abba ya kalleta kallon tsanaki.

"Wane tozarcin? Wa kuma kike magana a kai?"

Ta harareshi kamar idanunta za su zazzago.

"Matan da ka aurar har su nawa ne? Ina magana ne kan Wiyarka Futuha. Shi Yakubun ko sanar da ita batun ?ara auren bai yi ba saboda ya san auren cin amana ne. Kuma ni dai Maryam yanda ba zan dauka a yimin ba hakanan ba zan zuba idanu a halakar da kuruciyar yarana ba a hana su walwala da jin dadin zaman gidajen mazajensu. Tana nan gida na kuma hana mata komawa, ta yi zamanta har sai ya zo ya janye batun auren can da zai yi. Ya rasa wacce ma zai aura sai yar iskar Tiktok da ta yi mata ?azafin zina a baya?"

Tsananin Sacin rai da ba?in cikin da ma nadamar kyawawan shaidun halayyar da ya yiwa Mami a baya suka bi suka lulluSe shi, ga kuma zafin da maganganunta suka haifar a cikin ?irjinsa. Ya mi?e tsaye jijiyoyin kansa sun fito raWau tsabar Sacin rai. Wayarsa kawai ya fiddo ya danna lambobin Futuha, umarnin ta zo ya yi mata, ba jimawa ta shigo tana War????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? i-Wari ta zauna can gefe kusa da Mami. Shi kuwa Abba har lokacin yana daga tsaye yana safa da marwa, sai bayan zaman Futuhar ya soma magana murya a kausashe.

"Maryam! Idan har na isa da ke da kuma Wiyar da kike tutiya taki ce, ni Isuhu ba zan lamunci zamanta a gidana ba alhalin da igiyar aure a kanta. Ke kuma na rantse maki kika yi gangancin kwana a gidannan sai na nunamaki ni Isuhu na haifu kuma babu wata Wiya ko Wan da zan haifa a cikina ya yi tunanin zan biyewa son zuciyarsa na banza!"

Mami dama a ?ule take don babu abin da ke yawo a kwakwalwarta sai maganganun Babandi, wani mugun haushi Abban ke ba ta. Ta kuwa mi?e itama a zafafe ta ce.

"Ni kuma nace babu inda za ta je! Ba zan yarda da auren cin amana ba! Idan kai ba ka san darajar abin da ka haifa ba har ka nema mishi ?anci, ni nan Maryam ban haifar yarana ga wasu ?attin banza don su tozartamin su ba! Ai ba su tashi sun ga uwarsu da kishiya ba!"

"Ba zan yi mamakin kalamanki ba Maryam saboda a yanzu ne nake sanin ainahinki ba lulluSin da kika yimin ba a baya, yanzun kike nunamin ke wace ce. Toh ki sani, ni dai gida nawa ne, ban ginashi da kwandalar kowa a cikinku ke da yaranki ba. Wallahi a yau sai Futuha ta koma gidan mijinta ba za ta kwana a gidana ba, idan kuma kika taka umarnina sai dai ki sa ?afa ki bita duk inda za ta je amma na yi rantsuwa babu kaffara yarinyarnan ba za ta kwana a gidana ba. Ba kuma tsoronki nake ba da kike tutiya da fankamar wai ba su buWi idanu sun ganki da kishiya ba! Amma ki sa a ranki zan nunamaki ni din namiji ne ba MIJIN MACE DAYA ba."

Kirjin Mami ya buga dam! Maijidda ita ta faWo ranta.

"Me kake nufi?"

Ta tambaya a rude, madadin ya ba ta amsa sai ya sa kai ya shige dakinsa. Futuha kuwa kuka sosai take yi jin irin yanda iyayen ke musayar yawu. Ta mi?e tsaye ta kama hanya.

"Ke, na fa ce babu inda za ki je. Ki shiga cikin dakina kiyi kwanciyarki."

Za ta so hakan amma fa ba za ta iya ba don ta tsorata da yanayin Abban. Ta sani mutum ne dama tun can mai zafi idan an taSo shi sai dai kalar Sacin ran yau da ta gani ba irin wanda ta saba ganinsa ciki ba ne a ire-iren lokutan da aka taSo shi ba. Wannan ne dalilin da ya sa cikin sheshsheka ta ce.

"Aa Mami, zan koma amma na rantse idan Yakubu ya dawo sai ya bani takardata ba zan iya cigaba da rayuwa da shi ba."

"Don ubanki ni za ki watsawa ?asa a ido?"

Futuha ba ta amsa ba sai kawai ta yi gaba ta fice da gudu gudu. Mami kam zama ta yi ta fidda dankwalinta tana yiwa kanta firfita saboda ji take ma iskar dake wulwulawa a dakin kamar feshin iskar wuta ce ba ta yi mata yanda ya kamata. Yau dai Abba da kansa ya iya kallonta ya faWamata maganganun cin fuska son ranshi? Wato rigar mutuncin da ta ara ta yafa ya fiye mata alheri akan zahirin ita a idanunsa? Dama ba mallakarsa ce ta yi ba yake shakkarta kawai albarkacin wancan kyawawan halayyar da ta ke nunawa ta ci? Toh wai ita ba ta ma fahimta ba, aure yake nufin zai yi?

"Wallahi Isuhu ba ka isa ba! Ka yi kaWan!!"

Ta yi furucin cike da hargagi da Waga murya, babu wani da zai ba ta amsa don haka ta kwashi jiki ta yi bangaren uwarta, yau ce ranar farko tun bayan aurenta da ta ji tana bu?atar shawararta wajen waWannan ?ullace-?ullacen da take yi. Shakka babu idan gininta na tsawon shekaru ya rushe ko kuma ya karasa rushewa za ta kwashi kashinta a hannu.

***
Fadeel ya yiwa Humaira duba na tsanaki, tana cikin wata damuwar da duk iyaka kokarinta na yin murmushin ya?e sai da ya Wago ta.

"Ka yi shiru." Ta furta a sanyaye ganin sun kwashi mintoci cikinsu babu alamun wani zai ce uffan. Ita tunanin sabuwar Mami da manufofinta ke dukan zuciyarta shi kuwa damuwarta ce ta haifar da ta sa. Tun da ya ga yanayin da Mami ta tarbe shi ya san akwai wata a ?asa, ya kuma fi tunanin rashin nutsuwar Humaira saboda ganin Mamin cikin wani yanayi ne. Bai kawo komai bayan wannan ba.

"So nake ki gama tunaninki."

Ta girgiza kai.

"Ni ba tunani nake yi ba fa."

"Boddo please. Ko meke damunki kiyi hakuri ki cire shi a rai idan ba haka ba zan samu Abba da Alhajina yanzu kawai a daura auren na wuce da ke gidana."

Ya ba ta dariya dagaske, ta Wan bishi da hararar wasa. Shi ma murmushin ya yi mata gami da Wan Waga gira kaWan. A ?arshe suka sha hirarsu sosai da ta mantar da ita Mami da sabgarta. Sun Wan jima kafin su yi sallama ya fice.

***
Anna ta muskuta tana kara tamke fuska, ai ita yanzu kam a duniyarta babu abin da ta tsana sama da Abba da wadancan yarannasa biyu da suka yi sanadiyyar kama autarta. Ta sanya gonarta Waya babba ta can Agadez a kasuwa yanzu haka an samu mai siya duk da akwai faWuwa sosai a yanda aka taya amma ita dai burinta a samu abin cikawa a fiddo Jannat wacce mijinta ya yi ?ememe ya kuma rantse ba zai ba da ko biyar ba tunda ba shi ne ya sanya ta aikata ba. Dama yana cike da jin haushin yawon da ta ke yi bini-bini idan abu ya tashi sai ta matsa mishi za ta zo Nijeriya. Ga rashin Waukar yan uwansa da daraja, ganinsu take ?an ?auye futuk.

"Ke Maryam, idan za ki buWe zuciyarki ki fito ki nunawa wancan sokon mijinnaki Maryam ce da ba a nunamata Wan yatsa ba ta karya ba. Ai ni da ace tun farko ma nasan wautar da kika yi kenan na wannan makircij da bai kai ki ko'ina ba da ba zan bari ba. Ai gwara mutum ya sanka da halinka amma yanzu zai dinga yi maki wani kallo saboda ba haka kika nunamasa a farko ba. Yanzu dai ki jira ?ar uwarki mu samu ta biya wadancan karnukan kuWinsu sai a san me za a yi."

"Yanzu Anna sai Jannat ta fito za ki duba matsalata?"

Mamin ta furta cike da takaici.

"Ke ba kya tausayinta ashe? Ita tana can a gar?ame cikin yanayin a tausayawa ke kuwa ai naki mai sauki ne. Ki tashi tsaye ki ?watarwa yaranki ?ancinsu ta ?arfin tuwo idan ba haka ba dama na fadamaki tun ba yau ba, Isuhu zai iya tattara rabi da kwata na dukiyarsa da sunan na Ummita ne yake juyamata."

Annar ta yi mata wani tuni mai ?arfi da muhimmanci, tabbas akwai dukiyar Ummita a hannun Abba, duk kuwa da cewa shima Abban ya samu gadonsa a dukiyar ?anin nasa. Tana tsoron Ummitar ta tashi aure ya ce zai tattara komai ya dam?a mata abinta da mijinta, idan kuwa hakane ita ya dace ta samarwa Ummita miji ba kowa ba. Mijin da za ta iya juyashi son ranta ba wanda zai gagareta sarrafawa ba. Mijin da ba zai zama Wan da ta haifa da cikinta ba. Toh wa za ta samu haka?

"Ina magana kin yi shiru."

Kalaman Anna suka katse tunaninta. Mi?ewa tsaye tana wani murmushi mai tarin ma'anoni.

"Zan san abin yi."

Daga haka ta fice ba tare da ta ?ara ba Anna amsar tambayarta na me za ta yi ba.

***
A kwana a tashi cikin hukuncin Allah har ranar sanya Humaira a lalle ya gabato. Ana gobe za a soma shagalin bikin sai ga yan uwanta daga Nijar sun dira a gidan. Mami duk shige da ficen da Baba Amina ke yi da ma wasu a ?an uwan Abba da kuma Hajjo babu ko Waya da ta sanya hannunta ciki. Ita kuwa Humaira ta tattara batun Mami ta ajiye gefe bisa shawarar Hajjo da Baba Amina. Ta bi Mamin bi bana wasa ba amma Mamin ba ta ko sauraronta. Ga Tasleem a dakin da babu damar a yi wani abin sai ta tanka ta faWi ba?a, a ?arshe ma ta tattara ta koma Wakin Anna da kwana. Hankalin Tasleem ya yi masifar tashi ganin dagaske dai bikin Humaira da Fadeel za'a yi, wannan na nufin za ta tashi a tutar babu kenan? Ta iske Mami hankali a mugun tashe tana kuka kamar ranta zai fita ita fa lallai Mamin ta san abin yi don zuciyarta ba za ta iya zama ta yi ha?urin ganin hakan ya kasance ba. Mami ta dafe kanta dake tsananin sarawa, kwana biyunnan ba ta iya bacci saboda damuwa.

"Don Allah Tasleem ki rabu da ni da wannan koke-koken naki. Na samu tabbaci daga Babandi aurennan fa sai an yi babu makawa. Wannan borin naki zai tashi a banza."

Tasleem ta dora hannu a kai wani sabon kukan na kwace mata har da majina. Ashe haka ba?in ciki yake? Haka radadin kishi yake? Toh ita yau duk biyun take WanWana, ganin Humaira kamar wata sarauniya ya sanya ta ji inama ta kashe kanta ta huta saboda ba?in ciki da azabar kishi. Har ji ta yi wasu ?an uwan Abba na ce mata ranki ya daWe don hauka, acewarta.

Mami da ta ?uramata idanu gaba daya sai ta ba ta tausayi, Fatima ta haifa mata ba?in ciki ta kuma bar duniyar ta bar ta da shi, gashinan tana ?unsa. Can ta nisa ta ce.

"Toh ko za ki je wajen Babandi, dama ya ce ko bayan auren na fadi abin da nake son a yi musu amma saboda takaicin abin da naji gami da Abbanki da Maijidda sai idanuna ya rufe na ci mishi mutunci. Ki je ki ce nace ya yi hakuri ya dubi lamarinki ya samar maki da mafitar da ta dace. Zan biyashi ko nawa ne."

"Mami ki kirashi a waya toh."

Harararta ta yi ta ja tsaki.

"Kiran me zan mishi bayan na ce maki ga yanda muka yi da shi? Ke dai zan ba ki lambar da kwatance ki je."

Ta amsa da toh, a take kuwa Mami ta dauki waya ta turanmata lambar ta whatsapp dinta ita kuwa ta yi mata sallama ta fice bayan ta bi umarninta na shiga banWaki ta wanke fuskarta.

A wajen Anna ta bar Wiyarta ta fice bayan ta sa facemask ta rufe hanci da bakinta yanda babu wani da zai gane ta a hanya.

***
Babandi ya kalle ta tsaf, ya buga wani murmushi mai tarin ma'ana bayan gama sauraronta da kuma jin daga inda ta zo wajensa.
'Kin tafka kuskure babba Hajiya Maryam. Kin kashe Wiyarki da hannunki.' Ya yi furucin a ?asan ransa.Ya nisa kafin ya ce.

"Ha?i?anin gaskiya ba don ina ganin mutuncin Hajiya Lubna da ta zama silar haWuwata da Mahaifiyarki ba, da babu abin da zai sa na ?ara karSar wani aikin da ya shafe ta da ma wani nata. Amma tunda har ta fahimci ni Babandi ba za ta iya gudanar da rayuwa yanda take so ba tare da taimakona ba (Waiyazubillah) toh shikenan zan taimaka maki albarkacin hakan."

Tasleem ta saki wata doguwar ajiyar zuciya tana Wan murmushin da ya ?ara kwaWaitawa Babandi ita. Ya lashi leSSansa gami da mayar mata da martanin murmushi kafin ya hau buge-bugen ?asarsa sannan ya Wago ya dubeta

"Gaskiya Malama Tasleem yau dai kin zo a sa'a domin kuwa koda na ?ara bincikawa na tabbatar za a iya fasa auren Humaira da Fadeel, akwai kuma gagarumin sa'a da ke nuni da cewar za ki zama mallakinsa nan gaba. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, aikin da za ki yi hakan ya faru ba mai sauki ba ne.""

Da sauri ta tari numfashinsa.

"Na rantse kowane iri ne aikin zan iya yinsa muddin zan auri Fadeel."

Ya jinjina kai yana shafa gemunsa.

"Sai mu'amala ta shiga tsakaninmu har na tsawon wata Waya kafin aurenki da Fadeel. Ita ko Humaira a yau zan fara aiki a kanta zuwa ranar da ki ka ce za'a Waura auren ina mai tabbatar maki ba zai yiwu ba. Idan dai kika ba da haWin kai yanda ya dace kuma kika yi gum da bakinki ma'ana kika Soye cikinki hatta ga wacce ta turoki nan, toh shakka babu za'a dace. Za ki yi mamakin irin mahaukacin son da Fadeel zai soma yi maki har sai kin ce ya yi yawa."

Tasleem ta Wan yi dum, ga ?oshi ga kwanan yunwa. Tsaf ta karanci me yake nufi da mu'amala amma sai ta ji kamar dai hausarta akwai gyara a jikk wannan ya sanya ta ?ara neman ya yi mata ?arin bayani. Nan fa Babandi ya buWe mata komai ta tabbatar dai saduwar ita yake magana a kai ba komai ba. Ta ?are mishi kallo, jibgegen ?ato mai mummunan fuska daidai gwargwado. Sai dai ga dukkan alamu yana amfani da manyan turaruka masu ?arfi marasa dadin kamshi. Ba dai za ka ce yana tashin hamami ba.

'Kar ki sake ki cuci kanki, mene ne a ciki don kawai dai saduwa? Fadeel fa ne za ki aura ya zama a ?ar?ashin ikonki.'

Wani sashi na zuciyarta ke mata tuni, nan da nan ta ji ta yi na'am musamman da ta ?ara hasko kanta cikin wannan katafaren gidan da ta samu labarin ya dan?ara na Humaira. Ga kuma kayan alfarma na lefe wanda zai dawo mallakinta. Duniya ta yiwa idanunta rumfa ruf, ba ta hangen komai sai Waukaka da shaharar da ke gabato ta. Wannan ya sa ta dubansa a tsanake.
?
"Na amince amma da sharaWin sai na yi tsarin iyali gudun daukar ciki."

Ya yi wani murmushi na mugunta, a ransa faWi yake.?

'Ashe ba ma fansar nayi niyyar Wauka akan Hajiya Maryam ba. Ai sai kin haifa mata ?aramar bokanya ko kuma boka.'

A fili kuwa sai cewa ya yi.

"Ke da kike gaban Babandi, ai ba ki da matsala akan tsarin iyali. Akwai layar da zan ba ki, muddin kika sanya a bakinki yayin komai, ina mai tabbatar maki babu ke babu samun ciki. Ba ma a kaina kawai ba, ko tsakaninki da sabon Angonki Fadeel idan har ba ki shirya ki haihu da shi da wuri ba wannan la?anin zai maki aiki da ma wasu na sirri. Mallakarsa kuwa kin yi kan gama."

Wani dadi ya ratsa zuciyar Tasleem, ta kara samun ?warin gwuiwar da ta ji ko rai aka ce ta kashe akan ta samu cikar burinta za ta iya saboda kwaWayin duniyar da kuma daukakr da ta ke hasasowa kanta muddin ya kasance Fadeel ya zama mijinta.

"Shikenan, Malam nidai na shirya komai ma a yi tunda za'a dace. Sannan nidai koda ace Humaira an raba ta da Fadeel, bana son ta auri mijin da ya fi shi ko nan gaba. Na fi kaunar ta auri ?as?antaccen da za ta dinga zuwa wurina da ?o?on bararta na neman taimako."

Babandi ya jinjina kai, ai barewa ba za ta yi gudu ba Wanta ya yi rarrafe. Ya san ba a ?as ta tsinci wannan muguntar ba.

"Burinki zai cika. Ina zuwa."

Ya mi?e ya shiga Wakinsa kafin ya fito ya mi?a mata laya da umarnin ta tura bakinta. Ta bi umarninsa sannan ta mike suka nufi dakin kirjinta na harbawa amma hakanan ta daure, ba ita ta bar gidansa ba sai kusan goma da mintoci na dare. Babandi ya bi ta da kallo bayan ta fice ya kyakyace da dariyar nishadi, wa ya ?i banza a rayuwa? Ai wannan lamarin karSaSSe ne ba kuma ya jin zai bar rayuwarta ta sarara. Hakika Tasleem ta faWi hannunsa. Daga nan ya mike ya gyara jiki ya bada umarnin kada hadiminsa ya bar wani ko wata su shigo ganinsa a sanar da kowa ba ya nan. Aiki sosai ya zauna yi na mallake Tasleem da kuma sa mata tsoronsa ta yanda ba za ta taSa iya tsallake umarninsa ba saboda ba kadan ba ya ji ya kamu da matsanancin bu?atarta kuma yana son hakan ya Wore ko don ya gwadawa Maryam ita ba komai ba ce.

***
Hankali tashe Mami ta ja Tasleem zuwa dakinta ta rufe. Dubanta take yi a tsanake. Jikinta banda ?amshin turarukan da Babandi ke amfani da su babu abin da ke tashi. Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login