Showing 132001 words to 135000 words out of 189325 words

Chapter 45 - DUKAN RUWA COMPLETE NOVEL

23 Feb 2026

196

murmushi tana dan lumshe idanu domin dagaske ta soma jin bacci, sai hirar da shi ta Wan kawar mata da damuwar maganganun Mami akan matukar ta auri Fadeel toh ta tabbata ta yi asarar ingantacciyar rayuwar farin ciki. Ita kuwa yanda take jin kaunar Fadeel ta amince da duk kalubalen da za ta fuskanta a dalilinsa.

"Kin yi shiru."

Ya furta cikin son jin abin da zai fito daga bakinta.

"Ka yi hakuri, na faWamaka ba jimawa zan yi ba, sati kawai Abba ya Wibarmin."

Sauke ajiyar zuciya ya yi.

"Shikenan Boddo, amma lallai fa zan yi kewarki."

"Kwana nawa ne zan zama mallakinka?"

"Me kika ce?"

Sai da ya faWi hakan ne ta ankarar da suSul da bakan da ta yi. Kawai sai ta rufe ido da tafin hannunta na hagu tana dariya ?asa-?asa, ashe dai za ta iya mayar masa da martanin magana mai dadi? Shi kuwa a bangarensa fasalta irin farin cikin da kalamanta ya jefa shi ciki ba zai yiwu ba, koyaushe shi ne mai amayar da abin da ke ?asan ransa ita kuwa ko oho sai dai ta bi shi da Hum, um, eh ko aa. Sai hakurin da take yawan ba shi idan ya yi wata ?ar ?orafin ko ya ya. Haka suka raba dare su na hira a karshe ya dinga magana ya ji shiru sai hucin numfashinta da ke amsa kuwwa ta cikin wayar, anan ne kuma ya fahimci? bacci ya yi awon gaba da ita. Dole hakanan ya hakura shima ya katse kiran.

***
Bisa shawarar Mami, Tasleem ta ?i zuwa gidan saboda tsoron haWuwa da Abba sai kawai ta sauka a gida Futuha. Tun zuwanta babu abin da suke zantawa sai lefen Humaira da ya bi ya tsone musu idanu. Futuha ta yi kwafa.

? "Ki rabu da yar iska, yanzu za ta soma yiwa mutane fiffika tana ganin duka ta fi mu. Ni fa wallahi zan so ace yanda kika fito daga gidankin nan ke kika aure Fadeel din ko ba komai mu ga ta tsiya."

Fadin haka ran Tasleem ya Wan yi sanyi. Ta ji ashe Futuhar na kaunarta da alheri ba kamar ya da ta zata ba a baya.

"Hum, bari ke dai yar uwa. Nima dai zan so hakan ta kasance amma Abba kinsan shi zai toshe dukkan wata kafa da mutum zai yi wancakalarsa a rayuwa. Ni wallahi a baya Mami nake zargin ba ta sonmu amma yanda ta hakikance akan ba ta son auren Fadeel da Humaira yasa na ?aryata zargi. Abba shi ne mugun."

Futuha cikin yanayi na suSutar baki da kuma dadin zance ta taso.

"Ke! Inji wa? Wallahi toh kf duniyarnan ba mu da masoyiyar da ta wuce Maminmu. Kinsan irin sadaukarwar da ta yi duk don mu samu rayuwa ingantacciya?"

Ba ta jira jin ta bakin Tasleem ba ta shiga Saro zance babu ?a??autawa. Sai da ta ba Tasleem labari kaf na irin abubuwan da Mami ta yi a rayuwa sannan ta yi shiru. Dama zancen ya jima yana cinta a rai, ita ta tsani ka ba ta sirri don sai da ta yi dagaske ta ke iya ri?eshi. Tasleem ta ji zantukan tamkar a mafarki har dai sai da ta ?ara matsawa kusa da Futuha.

"Idan wasa kike yi kinsan Allah bana son irin wannan."

Tsaki Futuha ta ja kafin ta rantsewa Tasleem cewa dagaske ne kuma Mami da bakinta ta faWa mata. Wani ihun murna mai cike da al'ajabi Tasleem ta yi, tana mai ji a ranta cewa dole ta fesawa Anna da Jannat ko don su bar ganin laifin Mami sannan Anna ta ?ara samun tabbaci akan babu abin da ya sauya daga Maminta. Jin Futuha kawai take yi tana jaddada mata kada ta sanar da kowa komai ta rike sirrin Mami, ita dai ta bi ta da toh, tana kuma da ya?ini akan ai Jannat da Anna masoya ne ga Mamin, lamarin sosai zai yi musu dadi.

***
Washegari tun da asuba Humaira ta yi wankanta tsaf ta shirya cikin wata atamfar super da Mami ta Winka mata. Sai da ta kammala shiri tsaf su Ummita na zaune da Raihana cikin jimamin tafiyarta ta bar su, ta karasa ta dauki inda Ahmad ke shimfide ta ta sumbaci goshinsa sannan ta gyara masa lulluSi. Suka kara yin sallama da su Ummita, daga bisani suka yo mata rakiya. Mami na sashin Abba, Abban yana falon Mami yana jiran Humaira ta fito ya je ya sanya ta a mota. Sai da suka gaisa sannan ya ba ta umarnin su tafi.

"Abba zan yiwa Mami sallama."

Ya girgiza kai.

"Bacci take yi kwa yi a waya."

Ko kadan ba ta so haka ba, tana da tabbacin akwai abin da ke faruwa. Maganar Abba karo na biyu akam ta kama hanya su tafi ya sanya dole ta bi umarninsa ta yi gaba bayan sun kara yin sallama da su Ummita tamkar kada a rabu.

***
Mami dake kallonsu ta windon Abba ta saki labule cikin huci ta furzar. Wayarta ta fiddo ta dannawa Wizzy kira.

"Kana bu?atar Wanka, ni kuma ina bu?atar ka cikamin wannan aiki da na sanyaka ya kasance na ?arshe."

Ya yi wata muguwar dariya yana hangen motar Abba da aka buWewa ?yaure ta fito.

"Ai ki sha kuruminki Hajjaju, a yau babu su babu kwanan duniya."

Ta jinjina kai tana murmushin mugunta.

"Dakyau! Sai na samu kyakkyawan labari."

Daga haka ta katse kiran, Raihana dake yun?urin shigowa ta ja baya tana mai ri?e kirjinta da ya tsananta bugu, kalmar innalillahi shi ta shiga ambato domin kunnuwanta sun kasa gas?ata abin da ta ji na fita a bakin Mami. A cikin sakanni kadan ta dawo hayyacinta, da wani irin azama da gudu ta bar wurin zuwa dakinsu hannunta har kakkarwa yake yi wajen danna waya. Ummita na tambayarta ko lafiya sai dai ina! Babu baka sai kunni. Wayar Abba ta kira, ringing biyu ya Waga da sallama. Yana tafe tana tu?i lokacin har ya fita zuwa babban titi.

"Ab..ba..ba.."

"Lafiya Raihana? Meyafaru?"

"Abba za a kashemin ku, ka tsaya ka juyo gida."

Madadin ta ji razani a muryar Abban sai ta ji kamar ko a jikinsa.

"Kar ki damu Raihana, babu mai tsallakewa kaddararsa. Amma ki sani, ina da labarin da kika tsinta ko kuma kika ji a yanzu tun a daren jiya ya ris?i kunnuwana. Na sanar da D.P.O tun a daren jiya ya kuma bani shawarar da ta dace. Ina tare da rakiyarsu. Kin ji ko?"

Humaira dake gefe ta kasa gane zantukan da Abba ke yi, kirjinta sai duka yake. Abba kuwa bai jira cewar Raihana ba ya katse kiran. Tun daren jiya ya tsinci wayarbda Mami ke yi da wani inda take ba shi umarnin kashe shi da Humaira gaba daya. Har gari ya waye ya kasa tufka da warwara, ga mamaki mai tsanani da ya kewaye zuciyarsa. Ya ka sa gas?ata cewa Maryam ce da wannan yun?urin.

***
Can Sangaren Wizzy kuwa, yana tafe a bayan su Abba sannu da sannu don ya cimma su a inda ya gama dukkan wani tanadi da shiri, har a lokacin duhun asubahi bai gama washewa ba. Kallon da zai yi ta mirrow ya hangi motar dake biye da shi a baya, ganin da ya yi duk inda su Abba suka kurWa a mota shima ya kurWa ana biye da su ya sanya shi buga sitiyari, ya tabbata ko wace motar ce ba zai wuce na masu tsaro ba, zarginsa bai gama tabbata ba sai da ya ga yana shan wata wawuyar U turn an bude gilashi an bishi da harbi sai da aka fasa gilashin motarsa ta baya.

***
Mami ta fito afujajan daga bandaki daure da zani jiki duk kumfa da azama ta nufi wayarta dake faman ?ara, ganin Wizzy ya sanya ta murmusa don ta san ha?anta ya cimma ruwa. Sai dai me? Wani wawan ashariya ya jefa mata.

"Kin janyo an kusa kashe ni a madadin na kashe?! A gidan uban wa ?an sanda suka sami labarin nan?"

"Me kake nufi? Ban fahimta ba?" Ta jefa masa tambayar a rikice, ya yi mata bayani yanda za ta gane. Ya kara da fadin.
"Ke Madam, na baki nan da gobe ki gaggauta kawomin ajiyata idan kuwa ki ka yi wasa da hankalina zan zo har cikin gidan na ga uban da zai hana ni Waukarsa! Useless kawai!!"
Daga haka ya katse mata wayar, Mami kuwa ai sai ta ji kafafunta sun dauki rawa, toh waye ya san da zancen da har maganar ta isa kunnuwan ?an sanda? Ta ya ya hakan ta kasance? Duk iyaka tunani da zarginta ta kasa fahimta, a iyaka saninta sadda take waya a falon Abba yana dakinsa yana bacci, koda ta kammala ta shiga yanda ta bar shi hakan ta tarar da shi. Toh waye wannan da ya ji sirrinta? Sai ta zaSi shigewa banWakin don ta ?arasa wanke jiki a gaggauce ta je ta duba mutanen gidan ko za ta samu wata shaidar.

***
Fadeel ya ?urawa hoton da Ridwan ya aikomasa idanu, hoto ne na wacce ake zargi da yin Satanci ga Ummita da Humaira, kamar ya san fuskarnan sai dai ya kasa tuna inda ya santa. Sai ya zaSi buWe Wayan hoton na bayanin da Ridwan ya turo masa. Sunan ya sanya shi mi?ewa tsaye babu shiri. JANNAT MOHAMMAD AGADEZ.
Tabbas idan idanunsa ba su gane mishi ?arya ba, ita ce dai ?anwar Mami daya taSa gani a gidan su Humaira har ta ke jajanta masa lamarin Satan su Humaira. Kai ya sha ganinta ma ba sau daya ba ba biyu ba. Wannan shi ne ana zaton wuta a ma?era...
***
"Abba lafiya?" Tambayar da Humaira ta yi mishi hankali tashe jin ?arar bindiga ga kuma juyin da motar dake bayansu tayi babu shiri.
"Kwantar da hankalinki. Babu komai."

Yana fadin hakan ya gangara gefen titi ya tsaya, motar su D.P.O su dinma fakawar suka yi don sun tabbatar ba za su samu damar cafke mutumin ba.

"Ina zuwa." Abin da Abban ya ce kenan kafin ya bude motar ya fita. Humaira dai har wata zufa ke karyowa a goshinta, kirjinta kuwa bugu yake yi ba ?a??autawa, babu abin da ya faWo ranta sai waWancan mugayen masu garkuwar da suka kama su. Waigen Abba kawai take yi tsaye da wanda ta tabbatar Wan sanda ne don ta gan shi ba sau Waya ba kuma ba biyu ba a gidannasu duk da cewar bai sanya kakin aikinsu ba. Hakanan sauran mutane biyar da ke tare da shi babu kayan aiki a jikinsu.


D.P.O Alhussain ya dubi Abba dakyau.

"Kar ka damu Alhaji, in sha Allahu zai zo hannu. Mun kwafi lambar motar zamu tsaurara bincike ta yadda komai za ya bayyana a zahiri. Amma Alhaji a shawarce ina so ka Soye batun kawo maku harin nan da aka yi koda kuwa ga iyalinka ne sannan abin da ka fito da niyyar yi kada a fasa shi yin hakan zai bada wata ?ofar da za a ?ara yin wani shirin nan gaba. Zamu yi bincike sosai har mu gano waye."

Abba ya jinjina kai har a sannan cike yake da Wumbin mamakin Maryam wanda ko a mafarki ya ga za ya aikata makamancin hakan zai ?aryata a yayin da ya farka. Dakyar ya daurewa zuciyarsa suka yi sallama da D.P.O sannan ya koma ga motarsa ya shiga. Murmushin ?arfin hali ya sakarwa Humaira wacce wayarta ke ta ?arar shigowar kira daga Fadeel amma tsabar ruWani ya sanya ba ta ko fiddo ta a jaka ba ballantana ta kai ga Wagawa.

"Abba mu koma gida don Allah. Na fasa tafiyar."

Kallonta ya yi, sosai sai ta ba shi tausayi, ko ya za ta yi idan ta ji abin da ke faruwa ko kuma ya yi nufin afkuwa garesu kuma daga wacce suka yi amannar har abada ba za ta taSa cutar da su ba? Sai ya girgiza mata kai cikin murmushi na ?arfin hali ya amsa.

"Aa Mamana, babu inda za mu juya. Muje na sanyaki a mota, kada ki damu nasan direban kamar yanda na faWamaki Wa ne ga tsohon Maigadin Wan uwana. Yana da amana, na kuma sani sai dai abin da Allah ya riga da ?addarawa zai afku toh wannan babu wani mahalu?in da ya isa ya tsallake. Ki kwantar da hankalinki in sha Allahu lafiya kalau za ki je ki dawo kinji ko?"

Da kalaman Abba masu ?arfafa gwuiwa kuma lokaci guda masu karya zuciya ta Wan samu sassauci, ko ba komai ya tunasar da ita abin da ruWani ya so ya mantar, wato ambaton Allah. Abba kuwa tu?i kawai yake yi amma gaba Waya yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa mai Wumbin yawa. Humaira dai hankalinta ya rabu kaso barkatai, abin da ya faru yanzu da kuma yanayin Abba sai ko kirjinta dake faman bugu tun faruwar al'amarin.

Abba kuwa ya dam?a ta a hannu na amanan, Rabe. Mazaunin gaba ya zaSar mata ita Waya yadda ba za ta takura ba, duk kuma yadda ya so Raben ya karSi kudin motar ?i ya yi saboda karamci da kuma albarkacin Marigayin da ma shi kansa Abban wanda zai wahala su kai mishi wani kuka nasu ya ?i yi ba idan da halin yin.

Sosai Humaira ta yi kuka da suke sallama da Abban domin sai da ta ji tamkar kada su rabu. Sai dakyar Abba ya samu ta nutsu ya yi mata ?ar nasiha har da zolaya kafin ta saki ranta.

Bayan tafiyar Abban ta fiddo wayarta don ta kira su Raihana sai ta tarar da missedcalls har goma sha, wasu daga Raihanar wasu kuwa Fadeel ne. Kafin ta kai ga wani yunkurin sai ga Fadeel ya ?ara kira. Tana Wagawa da sallama ya rufe ta da faWa.
"Meyasa Boddo! Meyasa za ki tsoratar da ni wai?! Raihana ta kirani a ruWe ko na yi waya da ke nace aa, mun gwada kiran wayoyin Abba a kashe. Ina kike yanzu ganinan a hanya."

Ta tuna dagaske wayar Abban a kashe take tun amsa wayar Raihana da ya yi tana ganin sadda ya kashe ta gaba daya. Ko kusa faWan Fadeel din bai yi mata zafi ba, ta sani damuwa da lamarinta ne ya yi silar hakan.

"Ka yi hakuri, wayar tana cikin jaka, ina tasha har na shiga abin hawa."

"No ki jira, ni zan zo na kaiki."

Cikin sauri ta girgiza kai tamkar yana gabanta.

"Aa wallahi, ka yi hakuri dai tunda har Abba ya san direban kuma sun gama magana."

"Wace tashar ce?" Abin da ya nemi sani kenan kawai, ta faWamasa sunanta daga nan ya katse kiran sai lokacin ne kuma ta samu damar kiran Raihana. Jin muryar Raihanar a sha?e ya sanya ta tabbatar da ta san komai.

"Raiha, kiyi hakuri wayar tana jaka."

"Babu komai, Abba ina ta kiran wayarsa a kashe. Lafiya ku ke?"

Ta yi tambayar cikin kokarin kwantar da murya da Soye damuwa bisa shawarar Ummita.

"Ba mu jima da rabuwa ba, ya juyo ya taho gida."

"Toh, Allah ya tsare ya kiyaye hanya. Zamu yi kewarki ko ince har mun fara."

Ta dan yi murmushin ?arfin hali.

"Nima haka Raiha, a gaidamin Ummita da Ahmad. A sanya mu cikin addu'a."

Daga bisani suka yi sallama, tana nan zaune har ya yi saura bai fi mutum biyu motar ta cika ba sai idanunta ya sauka kan Fadeel dake tsaye ya yi shigar tshirt fara ?al da maroon wando na Adidas. Sumar kansa idan ka ?ura idanu za ka fahimci ko tsayawa taza bai yi ba. Sai rarraba idanu ya ke yi a tashar, sai ya ba ta tausayi da kuma murmushi lokaci guda. Ta dan yunkura da zummar buWe ?ofa ta fito idanunsa suka shiga cikin nata, da azama ya ?arasa ita kuwa tuni ta bude murfin ?ofar. Ya sa hannu ya ri?e murfin gami da dur?usawa su na fuskantar juna, ta kauda idanunta ta maida ga kallon gaban motar.

"Barka da asuba."

Abinda ya fito daga bakinta kenan. Madadin ya amsa sai ya yi shiru yana ?aremata kallo. Can dai ta juyo, daidai lokacin Rabe ya karaso.
"Ranki ya dade kin san shi ne?"
Fadeel ya kalle shi sai kuma ya mi?a hannu suka yi musabaha.
"Eh na san shi." Sai a lokacin ya dan murmusa.

"Waye shi?" Ya tambaya, Rabe dai na tsaye kallon ikon Allah, ya dai fahimci ko waye daga yanayin kallonsa da nata, ita din cike da jin nauyi da kunya, yayinda shi kuwa kallonta yake morewa, ga duk wanda ya kalle shi kuwa zai gane ba ?aramin nisa ya yi a kaunarta ba.

Ta Wan bishi da hararar wasa, Rabe kuwa ya yi ?ar dariya. Fadeel ya dube shi.

"Aurenmu nan da sati biyu in sha Allahu. Ina gayyatarka."

Nan da nan ya ?ara washe ha?oransa wadanda yawan yin asuwaki ya sanya ba su dafe ba.

"Sai Oga, ina taya murna. Allah ya nunamana lokacin."

Daga haka ya yi gaba ya bar su. Fadeel ya harareta kadan, ta yi mishi kyau, fatarta ta ?ara gogewa sakamakon mayukan gyara fata marasa haske da Baba Amina ta kawomata har ma da na wanka da take amfani da su.

"Kin yi kyau. Sai dai meke faruwa ne naji kamar Raihana na cewa an yi attacking Winku? Ban fahimci komai ba."

Sai a lokacin ta tuna tashin hankalin da suka tsallake cikin ikon Allah. Tunaninta kuma ya tafi ga son gano yanda aka yi Raihana da ke zaune a gida ta san da wannan magana, toh waye? Ko dai na gida ne?

?an ?as da ya yi da yatsunsa saitin fuskarta ya maido ta hayyacinta.

"Kin wani zubamin idanu ina tambayarki. Kwana nawa ne zan zama mallakinki?"

Ya karashe da wani kalar kallo da ma murmushi. Ita sam ba ta ma san cewa idanunta a kansa ta tsayar ba. Sai ta Wan yi wuri wuri da idanunta tana kallon mazauna bayan motar, macen ma hankalinta na ga wanda ta ke da tabbacin mijinta ne su na kwasar hirarsu.

"Ki bani labari idan wani abin ya faru da ku a hanya."

Nan da nan ta labarta masa komai da ta ji kuma ta gani, ya dan yi shiru yana nazarin zantukan, akwai dai alamar tambaya babba.

"Antinku Jannat na gida ko ta tafi?"

Tambayar da ya watsa mata kenan, shi gaba daya yanzun bai yarda da Jannat din ba, matar da son zuciyarta zai sa ta yi yunkurin munana sunan wadanda ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login